Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
sororo a tsaye yana bin kowa da kallo, an rasa wanda zai ba Ba Bakura haƙuri. Hajja gana kuwa sai sharar hawaye take yi. Ba Modu yace.
"Ahmad ku fice umarni ake baku fa. Ita kanta Yahanasun ta fice tabi mijinta su koma. Ta'aziyya ku ka zo mana mun gode, kun san bama yin ma zaman makoki a gidannan" Mama Gana tayi maza ta kama hannuna ta shigar dani ɗakinmu, tana hararar Ba Modu.
"Zauna anan, babu inda zaki daga zuwanki har sai anyi bakwai. Wannan irin muguwar rama kamar wacce ta haɗiyi allura fa?" Hawaye na shiga shatatarwa, ita kanta Mama Gana hawayen take fitarwa na tausayina. Haka Ahmad yaja hannun Bulama Babba suka fita jiki ba laka, kowa ya watse a tsakar gidan. Duk yanda Ya Innana ta kai da kawaici sai data tambayeni meke damuna, bayan na dawo daga cikin gidan, na bi kowa nayi mishi ta'aziyya.
Ba komai, na dai ɗan yi ciwo ne kwanaki"
"Hmmm Yahanasu baza dai ki faɗa ba. Kinga yanda kika zuge kuwa, Fanda fa ta fiki kumari sosai yanzu. Ki sanar dani matsalarki, ko dai ciki ne da ke?" Murmushi nayi, ga hawaye na zubowa a idanuna. Nace.
Rashin kwanciyar hankali ne kawai, bani da ko da matsayin ƴar uwa a idanun Bulama Babba. Ni na ɗauka ko da aure nayi a wani gidan, na shiga damuwa, Bulama Babba me iya tsaya munne ba sai kun shiga ba. Amman kash sai gashi shine ya sani a garari" kukane ya ci ƙarfina, sai rairawa nake yi. Ya Innana kuma ta tusani a gaba sai Ajjiyar zuchiya take saukewa, da dukkan halamu yanayin da nake ciki yana gasa ranta.
"Tun farko kuskurene yasa aka haɗa wannan auren. Gashi zumuncin da ba'aso ya taɓun ya taɓu, tunda dole Hajja Gana ranta ya sosu dake, sabida duk sanadin aurenki ne wannan abun suka faru har BaKura yace bashi ba Bulama Babba, Ita uwace, ko da ta ɓoye haushinki a zuchiyarta bazai taɓa goguwa ba. Tana ji tana gani an korar mata yaro. Kuma sabida shi duk tabi ta rame, kullum a cikin tunaninshi take. Ni dai abinda zance dake shine ki dage da adda'a baccin dare ba naki bane. In kika riƙe Allah da karatun Alqur'ani mai girma, da izinin Allah matsalar gidanki sannu a hankali zata kau. Muna cikin tattaunawa Ba Modu ya shigo ya zauna a bakin kujera. Ƙur ya zuba mun idanunshi.
"Uwata kiyi haƙuri da ƙaddara, kiyi biyayya, zaki samu riba. Abinda nake so dake shine, ki shirya ki bi mijinki, nasan bazai wuce gidansu Ahmad ba. Wakil yana jiranki a waje." Da sauri na ɗago kaina na dubi Ya Innana, halamar ina neman agajinta a taimaka a barni in samu salama, carab kuwa tace
"Amman Modu ba zaka bar yarinyar nan mu kwana ba, in yaso gobe a kaita can gidan su kama hanya su koma ba?" Murmushi yayi.
"Ai tunda har Bulama bashi da waje a gidannan to ya zame mata dole itama ta bi mijinta, hakan shine kara. Innana kiyi haƙuri, itama uwata tayi haƙuri, irin haƙurin da Hajja gana tayi. Ku baku ji furucinta ba? Nifa duk abunda zai kawo kwaɓewar zumunci ba sonshi nake yi ba." Ina kuka na miƙe tare da zaran akwatina. Hannu yasa a aljihu ya ciro kuɗi ya damƙa mun ba tare daya ƙirga ba. Ya Innana tace.
"Ina zuwa ki jirani kaɗan" fita tayi a ɗakin harta dawo ina share hawayena, ga wata iriyar yunwa dake sakutar cikina. Wata leda ta miƙa mun, na karɓa. Har bakin mota Ba Modu ya rakani, sai da ya ga tashin motarmu sannan ya koma.
"Yahanasu kinga abunda aurenku ya ja a family ko? Yayyun Hajja Gana sai surutai suke yi, akan wai bai dace ba abinda akaima Bulama Babba ba. Naga yayyenta maza ma sun fita, kamar Bulama Babban suka bi. Zumunci na shirin samun tangarɗa, ni dama baku zo ba. Danna tabbatar wannan ramar taki sai ta kwantar da Ya Innana jinya. Kullum a cikin maganarki take." Cewar Wakil
Ai Wakil nayi ɗan daka ce ban zo ba. Ka duba a barni in keɓe da mahaifiyata da ƴan uwana in ɗan ji sanyi amman abu yaci tura. Naso har gidan su Yabulu da Fanna duk in leƙa in gano"
"Ai Fanna tana nan a cikin gidan, hankalinki ba'a kwance yake ba shi yasa baki ganta ba, tana bayanki. Tazo gidan ai tun sanda jikin Ba Baana yayi tsamari, dama tana fama da laulayi, uwar mijinta ce ma ta kawota, satin ta biyu." Murmushin farin ciki nayi, tare da sake jin tausayin kaina. Gidansu Ahmad bayan layinmu ne, muna shan kwanar layin, muka hango Ba Bature wan Hajja Gana tsaye a ƙofar gidansu Ahmad suna tattaunawa da Bulama.
"Fita kije Yahanasu ni bazan ƙarasaba naga sun ɗauki abun da zafi. Ni wallahi Bulama Babba tausayi yake bani, ko sunanshi Ba Bakura ya kafa dokar kar ya kuskura yaji an ambata. Ni dai jikina yayi murus, kafin in fito sai ga Hajja gana ta wuce ita da ƙanwarta Hewa. A sanyaye na bi bayansu, Wakil kuma yana cikin mota bai tafi ba. A sanyaye na isa wajan, ina gaishesu. Hajja gana ce kaɗai ta amsa mun gaisuwata, tare da riƙemun hannuna.
"Me kuma kika zo kiyi anan? Nan ɗinma kin biyoni ne dan ki sake rabani dasu? Gidan da nayi rayuwa a ciki, nayi guje gujena tun kafin a haifi kowa, yau shine akaimun korar kare, duk akanki kuma.
"Kai ɗannan kar ka ɗaurama ƴata laifi, wanne irin cin kashi da cin mutuncine mu baka yi mana ba. Duk wannan jarabawar data sameka ai bazai wuce akan fishin da mahaifinka yake yi a kan ka bane. In banda uwa bata iya haifar yaro ta tsame hannunta a kanshi, wallahi da ko kallonka ba zan kuma yi ba. Mara mutumci wanda baisan ciwon kanshi ba. Ba Bature yace.
"Ya isa Hajja Gana duk tashin tashina bai taso ba. Ni dai zan haɗashi da Alhaji sambo, ma'aikacin gidan yarin dake Kano. Ya nema mishi aikin gandiroba in bai raina ba, ya samu ya riƙe iyalinshi, kafin Allah ya ɓullo mishi da wani aikin, aikin ne a ƙasarnan yayi wuya. Tunda Alh Sambo ne, babu wani atisaye da zaka yi, ɗaukar ka kawai zaiyi, shima Ahmad ɗin in yana so ku je ku yi tare. Ni iyakar taimakona kenan, mahaifinka kuma kayi ƙoƙari ya yafe maka, in dai kana son rayuwarka tayi albarka. Mahaifiyarka ko itama ta huta, kai baka ga yanda ta rame ba? Ke kuma Yahanasu kiyi haƙuri Bulama wanki ne, kici gaba da yi mishi biyayya. Modu ne ya koroki ko?" Kai na gyaɗa mishi.
"Na san Modu da kara da kawaici daga shi har Innana. Ahmad in zai je wajan Alh Sambon, sai ku tafi tare kaima ka kai mishi takaddun naka. Gobe ku kama hanya kawai ku koma, amman ku dinga ƙoƙarin kiran gida da dangi" Nan sukai ta mana nasiha, daga ƙarshe mu kai sallama muka shiga cikin gidan su Ahmad. Ranar daga ni har Bulama Babba babu wanda yayi cikakken bacci, sallah ya dinga yi, yana rera karatun Qur'ani. Nima alwala na ɗauro bayan na yi gamje gamjen magunguna. Washe gari haka dole muka sake nuƙo hanya. Bayan mun koma da sati guda Ahmad da Bulama suka soma zuwa aiki a babban gidan yarin kurmawa dake bayan gidan sarki, a matsayin ƙananun ma'aikata masu matsayin ( correctional assistant CA 1 na Ahmad kenan) na Bulama Babba kuma ( Correctional assistant CA2) Kofur itama ta kama aiki ka'in da na'in. Ni ma nan na bazama neman aiki, cikin yardar Ubangiji na samu, a gidan talabijin na tauraron ɗan Adam, akan lamba ta 127 gidan Tv mai suna Nagarta. Inda na riƙe ɓangaren mu tattauna, shirin dake zaƙulo matan dake cikin gida, dan jin tarihin rayuwarsu da irin gwagwarmayar su. Tuƙuru na mai da hankali akan aikina. Aikin gida kuwa babu wanda aka ɗauke mun, nike yin komai na gidan, hatta shirya su Maryam su tafi makaranta ni ke yi, sabida Zubaina tana fama da lalurar ciki. Hajara ma ta samu aikin shara a cikin makarantar su Maryam (AL FURƘAN) dake saman ƴan lemo, ita ke tafiya da yaran, tare suke dawowa kuma. Matsalolin gidan Bulama Babba babu sauƙi sai ƙaruwa, sabida ita kanta Zubaina a halin yanzu kullum a cikin rashin jituwa da Bulama Babba take. Sabida yanda rayuwa ta juya mishi, albashin nashi ba wani yawa, ita kuma bata taimakawa da komai a cikin gidan, da an taɓata tace gini take yi. Ni kuma albashina kusan duka a hidimar gidan data yara yake ƙarewa. Shaye _shayen muyagun ƙwayoyi kuwa, sun zamemun tamkar sallah biyar a rayuwa, dan bana ɗaga ƙafa ko sau ɗaya. A halin yanzu sai na yi haɗe haɗe sosai kaina ke iya ɗaukar caji, amman bana wasa da ibada, ban gajiya wajan kai kukana ga Ubangiji ba. Wata ranar alhamis da misalin ƙarfe huɗu. Ina zaune a dokin ƙofata ina yanka alayyawo. Muna ɗan taɓa hirarmu da Hajara, wacce take tsintar shinkafa. Itama girkin take yi, a gawayi yanzu muke girki, shima duk wata ni ke siya, na ɗauke ma Bulama Babba wannan nauyin. Banda kifi da nama da nake siya in saka a miya. A hakan na sai ma kaina gado, da wadrope. Duk da wannan siyan kaya da nayi ya haddasa gagarumin tashin hankali a tsakanin Bulama Babba da Zubaina. Dan a gaba ta tusashi kamar ɗanta ta dinga zazzaga mishi kwandon jaraba. Shi kuma sai faman rantse rantse yake yi mata kan shi ba shi ya siya mun ba. Bata barshi ba, har sai da yace mata kafin ta haihu zai siya mata sannan ta barshi ya sha ruwa. Bulama dai ya rage hantarata, tunda mu kan ɗan taɓa hira, misali ya tambayeni, Zubaina ta dawo, ko kuma ya tambayeni ya yaran? Shikenan abunda ke shiga tsakanina dashi, mu'amular aure kuwa, sai dai in jiyo yana yi da Zubaina, ni na zama fanko. Babu abunda ya kai haka ciwo, waɗanda suka ɗan ɗana irin wannan yanayin ne ka ɗai zasu fahimci halin da nake ciki, kullum ɗaukar kaina nake tamkar ba mace ba, tamkar mai wata nakasa a jiki. Har nakan tambayi kaina, ko dai haka mumana suke gudanar da rayuwarsu a gidan mijine? Ni dai nasan ba mai kyau bace, kuma bana kai kaina inda Allah bai kaini ba.
Bulama Babba ne ya shigo da kayanshi na gandiroba, hannunshi biyu kici kici da cefane, anyi musu biya kenan, dan sanda zai fita nera ɗari uku ya bayar kuɗin abincin safe. Nan Zubaina yana fita ta aiki Zulai ta siyo musu kayan tea, da Indommie da ƙwai ta dafa, suka ci da yaranta. Da naje wajan aiki shine na ari dubu ɗaya a wajan abokiyar zamana a wajan aiki, shine nayo cefanen miyar kabewa, zan dafa buski. Da sauri na miƙe na karɓeshi, ina mishi sannu da zuwa. Abun mamakin shine yanda naga yana ta Murmushi, har yana tambayata ya gida ya aiki. A sanyaye nace.
Lafiya lau, bari in kai maka ruwan wanka" Ina adana kayan a kitchen na zari bokiti na cika dam da ruwa, na miƙa mishi ban ɗaki, na dawo naci gaba da aikina, shi kuma yana tsaye yana gaisawa da Hajara. Misalin ƙarfe shida da kusan rabi na kammala komai, na share tsakar gidannan na wanke shi tas, sai na shiga bayan gida na watsa ruwa, ina zaune a kujerar tsugunno ina alwala, Bulama Babba ya fito da shirinshi na zuwa masallaci.
Adawo lafiya" Nace mishi, da fara'a ya amsa mun da.
"Allah yasa" Yana fita Zubaina ta shigo tana faman tura ciki gaba. Harara ta zabga mun, da ƙyar na cije ban rama ba, Amman turar da take yi mun ta kusan kaini bango. Jira kawai nake yi ta haihu, a soma rabon girki, dan yadda take jin zaman aure take yi, nima zaman auren nake yi. Yanda take jin aiki take yi nima aikin nake yi, haƙurina ya kai iyaka" Haka al'amura su ka ci gaba da shurawa, Bulama Babba dai ana samun canji, dam jiya abun mamaki ya kira number Ba Bakura bai ɗaga ba, ya kira ta Ba Modu shima bai ɗaga ba. Sai naga duk ya damu, harma yana tambayata yaushe rabon da inyi waya dasu? Sai nake sanar mishi, kullum sai munyi waya, in basu kira ba ni zan kira.
A kwana a tashi harna shekara guda a gidan Bulama Babba, na dawo siririya sosai, sabida damuwa, da rashin samun nutsuwar aure. Ga sha'awar son kasancewa da mijina daya soma addabata, ga yawan shan kayan maye daya ƙaru mun, in ban sha ba, har ji nake kamar haukacewa zanyi. Wata ranar lahadi da daddare Zubaina ta suntulo ɗanta namiji mai kama da ubanshi. Murna a wajan Bulama Babba ba'a cewa komai. Da murna yazo ya same ni yake ce mun, in kira su Ba Modu in sanar mishi anyi haihuwa. Bayan kwana biyu da haihuwar Zubaina aiki ya kuma kacamemun, dan ma Hajara ta ɗauke mun hura wutar jego na asuba, ita ke hurawa, ni kuma in hura na yamma, ga aiki, ga hidimar yara. Ranar data ƙwan uku da haihuwa Bulama Babba ya shigo da wata atampa a leda chiganvi ya miƙo mun tare da nera dubu biyar.
"Ki yi haquri kayan fitar sunane, da kuɗin ɗinki, sai ki yi maleji" Albarka na saka musu. Washe gari na ɗauki atampar, da lace ɗina na cikin kayan akwati na kai ɗinki, nice harda siyan ɗan kunne da sarƙa ɓarawon zinare da ake yayi. Ana gobe suna da yamma sai ga Bulama Babba da Ahmad da kayan gado da wadrope, harda dressing mirror masu tsada. Su da kansu suka jera komai. Inata jiran
Kuɗin abincin suna, amman ko da Bulama Babba ya shigo na tambayeshi sai yake ce mun. Ai ƴan uwanta yanzu suka iso, ya ba ƙanwar mamanta kuɗin cefanen sunce zasu yi komai, Asiya kuma ta ɗauki nauyin drinks. Murmushi kawai nayi, bance komai ba, naci gaba da harkokina. Washe gari yaro yaci suna Yusuf. Bayan na gama share gidan na wanke tsab, sai na fita kasuwar ƴan lemo nayo cefanen jallof da kosulo. A gidan Maman Adam na shiga, muna hira na gama girkina tsab, itama ta tayani, sabida na ɗan gayyaci abokan aikina, kuma nasan tunda suka ce zasu yi girkinsu, ko ɗanɗane ba zasu bani ba. Dan tunda suka shigo gidan da daddren suka soma zubar da habaici. Hajara uwar gulma cikinsu ta ƙule sai shewa take yi. Ina shigowa naci karo da me jego da ƙawayenta, suna ta hotuna a waya, tayi kyau, sun fito shar dasu. Nima wanka na shiga, na saka atampar da Bulama Babba yai mana. Na sakko da akwati na ciro atamfa, na haɗa da rigar yaro dana siyo dubu tara, nayi sallama na miƙa musu. Sai wani kallon banza suke yi mun. Ni kuwa yi nayi kamar bansan me suke yi ba. Da yamma ƙawayena suka iso, da ƴan maƙota haka da ake gaggaisawa, na sake shiga na saka leshi na . Nan mu kai ta hirarmu, nima naji sanyi a zuchiyata. Da yamma lis suka soma watsewa, duk wanda zai wuce sai ya ɗan dungule hannunshi ya miƙo mun kuɗi. Ni kuwa inata amsa. Ai kuwa na samu kuɗi sosai, harda su omo da sabulai. Da yake nima mai ƙoƙarin bayarwace in naje suna ko biki. Na adana kuɗaɗena, suma omon na adana abuna, dan ba bata zanyi ba. Jira nake baƙi su watse inyi fito na fito daga ita har Bulaman dama duk wanda zai goyi bayansu. Na gaji ni ba jaka bace, naga halama saina tashi tsaye zan kwaci ƴancin kaina. In ba haka ba, a tsaye zuchiyata zata buga ta fashe.
Zubaina:
Tunda su Bulama suka dawo daga gida,muka shiga tababa, sabida ya riga ya saba ciyar dani abinci mai kyau, amman yanzu mune shinkafa da mai da yaji, mune tuwo, mune ɗan wake, mun saje mun zama kanawan sak, in ina son abinci mai daɗi sai dai in ratsa gidan Asiya in ciyo. Ko in zata zo gidana ta tawo mun da kayayyakin daɗi. Ni kuma bazan iya saka ƙwandalata a hidimar gidan Bulama ba. Kaina nake ginawa, dan harna kusan kashe ginina tuni, da ragowar kuɗin mota naci ginin, duk wata kuma albashina nake turama Mama duka, rabi su samun a gini, rabi ta riƙe a hannunta. Duk da nasan mijin Asiya bai ragesu da komai ba, amman nima ina neman albarka. Kullum saina kira Mama mun shafe mintuna muna tattauna matsalolin su Sagiru da Musa, a kullum abun nasu sake ta'azzara yake kuma yi, kullum a cikin jaye_jayen magana suke. Mama kuma ta fito tai ta faɗa da jama'a, dama haka Mama take, a kullum ita dai nata ne mai gaskiya. . Asiya kuwa da yake mijinta ya tsaya mata, a cikin wata shida ta gama gininta, harta zuba ƴan haya. Nafisa kuwa, tayi watsi da karatu, ta biye ma ƙawaye sun shiga gari neman dukiya, Mama kuma ta goya mata baya ɗari bisa ɗari. Ko da su Asiya suka zo suna, da zungureren cikinta, a hakan tayo tuƙi tazo. Dan bata fiye zuwa ba, sai dai ni daga wajan aiki in wuce can gidanta, in huce takaici abuna. Mabaruka da Hadiza, da Zainab ƙawayena sunyi mun kara. Naji kunya ainun da suka ganni a cikin wannan yanayin. Duk da Bulama ya gwangwajeni da kayan katako, amman zuchiyata ba tai fari ba sam amman da yake duk abokan cin mushe ne ban ji na damu sosai ba. A haka akai suna, washe gari kowa ya watse ya koma, bayan sun soye mun ragon suna. A ɗaki na ƙunshe abuna, Hajara kawai na ƙunsama. Amman waccan yarinyar ban ko bi ta kanta ba. Bayan sati biyu da haihuwata ranar da zan koma bakin aikina kenan sakamakon wani aiki na gaggawa da ake son a ɗauramu a kai, ina