MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   48 / 67

141K to 144K   out of 198.3K words

da babu makawa sai ya faru. Ku sani Allah shi ya shirya ma Bulama Babba rayuwa. Har ya shinfiɗa aurenshi da Zubaina da zuriyar da suka tara tare. Yaronnan yarone mai cikar kamala da hankali. Gashi da son ƴan uwa da dangi baki ɗaya. Cikinmu babu wanda baiyi alfahari da Bulama Babba ba. Wannan yana daga cikin ƙaddararshi. In ba'a rarrasheshi ba, bai kamata a ga laifinshi ba ni a tunanina. Ba Bakura kayi haƙuri ku bi su da adda'a, zancen tuna baya ma bai taso ba" Jikin kowa ya mace mus, da dukkan halama zantukan Ya Bagulaji ya shigesu, nan suka shiga ƙaremun kallo cike da tausayi. Ina hango sona da ƙaunata a idanun Ba Bakura, ya jima bai mun irin wannan kallon ba. Ni kuwa jikina rawa yake yi na zazzaɓi sosai. Ana cikin haka aka fara kiraye_kirayen sallah. Tare mu ka yi sallah dasu a masallaci. Muna dawowa muka samu an bada izinin masu dubiya su shiga. Kai tsaye ɗakin muka wuce tare da su Ba Bakura. A cikin ɗakin muka tarar da su Ya Innana suna tsaye. Yahanasu tana kwance idanunta biyu, sai kallon kowa da kowa take yi. Ba um ba um um. Ba Bakura ya isa kusa da'ita ya dafa kanta a hankali yana ƙare mata kallo. Murmushi tayi mishi bayan ta kalleshi. Shima sai ya sakar mata murmushi, ga hawaye na bin kuncinshi.
"Ku bani ruwa a kofi inyi mata tofi." Ya faɗa yana duban su Aissa. Ya Innana ce ta matso da kofi a hannunta ta bashi. Jigum tayi tana kallon Yahanasu, sai hawaye take sharewa kawai bata iya magana sam. Tofi Ba Bakura yayi mata a cikin ruwa ya ɗagata zaune ya bata ta sha. Wanda yai ragowa ya shafa mata a fuskarta da hannayenta, har cikin gashinta. Kallon kowa yayi ɗai _ɗai yace.
"Salati goma ga Annabi. Ku ɗaga hannayenku muyi ma marasa lafiyar dake ɗakinnan adda'a Allah ya yaye musu lalurar dake tattare dasu." Dukkanmu kowa ya ɗaga hannayensa muka soma amsa addu'ar da Ba Bakura yake ragargazowa. Dukka ƴan ɗakin suma suka ɗaga hannu sukai ta amsawa da ameen Ameen. Yafi minti sama da talatin yana adda'a kafin daga bisani ya sauke hannunshi bayan mun ƙare da salatin Annabi kamar yadda muka soma dashi.
"To mu kam zamu koma gida. Amman ya yanayin kulawar da ake basu yayi dai_dai ko kuma zamu tafi da'ita can Damaturun ne ayi mata magani acan?" Ahmad ya amsa da cewa.
"Ba Bakura ga abinci can Hajara ta kawo yanzu naku ne. Dangane da batun kulawa kuma, agaskiya likitocin suna iyakar bakin ƙoƙarin su wajen kulawa da marasa lafiyansu. Kuma ana samun ci gaba sosai. Kasan sha'anin ƙwaƙwalwa sai a hankali. Amman ni ina ganin a barta a nan ɗin in sha Allah, addu'arku muke nema." Ba Bakura yace.
"To shikenan Allah yayi muku albarka ya haska gabanku da bayanku baki ɗaya. Ya raya muku zuriyarku. Ku kula da zumunci da haɗa yaranku auren zumunci. Ko bayan ƙasa ta rufe mun idanu Bulama ka riƙe Yahanasu da daraja. Ka kula da ƴan uwanka ka kula dasu Bulama. Modu Hajja sai mu kama hanya ko? Mama Gana da Bagulaji zasu ci gaba da kulawa da Yahanasu, ku kuma duk zamu koma tare zaman bai da amfani azo a tare a asibiti. Kuɗi ya zaro rafa biyu ya miƙa ma Mama Gana. Nima ya miƙo mun rafa ɗaya, ya ba Ahmad rafa ɗaya.
"Duk abinda ake buƙata ayi a cikin waɗannan kuɗaɗen. Bulama zan sa ƴan uwanka su turo da nasu taimakon ta asusun bankinka, maza da matansu. Ku da kuke nan zan soma daku, gwargwadon abunda Allah ya hore muku ku taimakawa ɗan uwanku. Na janye daga maganata ta baya. Ku haɗe kanku, kuci gaba da shawartar ɗan uwanku a kan duk lamarinku dan ni tawa ta ƙare bana jin zanga wannan abun kuma in ci gaba da nunfashi, Yahanasu ta karyar mun da zuchiyata. Modu kaima ka saka idanu sosai akan sha'anin zumunci ko bayan babu ni. Muje su matan suci abincin sai mu kama hanya."
Mrs Bukhari ce
[13/08, 3:52 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
40


















Ba Bakura sai da ya zagaye duk marasa lafiyan dake cikin ɗakin ya gaishesu tare da basu dubu goma_ goma. Sannan muka fito baki ɗaya, Mama Gana kuma ta zauna tare da Yahanasu tana bata abinci a baki, lokacin shan maganinta na rana yayi. Kayan sawarta da Hajara ta kawo mata na shigar musu dashi.
Ga kayan sawarta, zan siyo hita ko kettle sai a jona mata ruwan wanka tayi, ko zata ji daɗin jikin nata." Karɓan kayan Mama Gana tayi, taci gaba da ba Yahanasu abinci. Ni kuma na koma wajan su Ba Bakura. Yusuf yana kan cinyarshi yana mishi wasa. Kallona Ba Modu yayi yace.
"Zamu tafi da Yusuf a rage ma Ahmad da Hajara ɗawainiya. Sai nake ganin tunda mijin Fandau ya fita ƙasar waje yin cous ina ganin itama a barta ta zauna tare da su Bagulaji tunda bata da goyo. Zan faɗa ma mijin nata. Ko girki da shirya yara ta taya Hajara. Sai su dinga yin aikin gidan tare. Su kuma su Mama Gana su dinga kulawa da Yahanasun. Ko me kace Bakura?"
"Hakan ma yayi, tunda ba yanzu mijin nata zai dawo ba, sai nan da watanni shida. Yaran kuma dama a ɓangaren kakanninsu suke zama. Amman kirashi yanzu muji daga gareshi tukunna." Ba Modu baiyi wata_wata ba ya doka ma mijin Fandau waya. Bayan ya ɗaga suka gaisa ya tambayi mai jiki. Sai ya shigo mishi batun zaman Fandau dan ta taya su Balaguji jinyar Yahansu. Nan take ya amince ma Ba Modu da buƙatarshi. Godiya yayi mishi su ka yi sallama, Ba Modu ya ajjiye wayar.
"To ya amince Bakura. Sai mu barta ɗin ta dinga yi musu girki tana taimakon Hajara."
"To shikenan Allah yayi albarka duka. Mu zamu tafi sai in an kwana biyu zamu sake zagayowa in sha Allah. Allah ya bata lafiya." Dukka muka ɗinguma wajan motocinsu domun musu rakiya. Ba Bakura sai nasiha yake yi mana mai kama da wasiyya. Yana hawaye motarsu ta soma tafiya, sai albarka yake shi mana yana share hawaye. Ni kaina a take naji hawaye na zuba a kan kumatuna. Gani nake kamar bazan kuma sa Ba Bakura a idanuna ba. Ahmad yaja hannuna muka koma ciki su Fanda suna biye damu a baya. Cikin ɗan lokaci na dinga samun Alert daga ƙannena, ko wanne yayi iyakacin ƙoƙarinshi. Kai kawai na shiga girgizawa ina ambaton Allah. Haƙiƙa ƴan uwana suna ƙaunata ƙauna mara algus. Allah ya isa tsakanina da Zubaina data shigo rayuwata ta tarwatsamun. Ktile muka siyo da bokitin wanka. Nan da nan Mama Gana ta jona ruwan zafi, ta taimakawa Yahanasu ta tsabtace jikinta tas. Suna fitowa Mama Gana ta taimaka mata ta sake kayanta. Wanda ta cire ta saka a bokitin ta fito ma da Fanda ta wanke. Haka dai muka kuma wuni a asibitin cir sai magriba mu kai ma Mama Gana da Ya Bagulaji sallama muka tafi da Fanda. Ko da Fanda ta shiga ɗakin ƴar uwar tata sai ta saki kuka. Haƙuri na dinga bata kawai dan bani da wani ta cewa. A waje na kwanta, Fanda kuma suka kwana a ciki ita da yaran. Da sassafe ta tashi da aikace_ aikacen ɗakin Yahanasu itace harda kwalima. Fita nayi na barta na fita inyo cefanen abincin da za'a dafa ma ƴan asibiti. Ahmad kuma sassafe ya fita aiki yau.




Fanda:
Tana bakin ƙofar Yahanasu tana shafa ma Maryam mai, Matan gidan suka iso inda take aka gaggaisa tare da tambayar mai jikin. Maman Hassan tace.
"In zaku tafi asibiti muna son zamu biku muje mu duba Umman Maryam. Uwatale ƙawarta ma tace in zamu je muyi mata magana zata bimu. Fandau tace.
"Sai dai ko zuwa azahar ku tawo tare da Anti Hajara, sabida ƙarfe biyu ake iya shiga dubiyar. Ni kuma yanzu zan kammala in koma asibitin. Maman Iklima tace.
"Iko sai Allah. Muryarku ɗaya da umman Maryan. Ke ƙanwarta ce?"
"E uwa ɗaya uba ɗaya ma." Nan suka shiga ɗan mata tambayoyi a fakaice. Ganin ta haɗe raine yasa suka watse a ƙofar ɗakin. Shirya su Bawa tayi tsab suka saka kayan makaranta, suna zaune a tsakar gidan. Bulama Babba ya shigo kici_kici da kayan cefanen abinci.


Bulama Babba:
"Fanda ga kayayyakin abinci nan na siyo. Sai ki yi abunda kika ga ya dace. Ban samu nama ba yayi safiya, amman na siyo ɗanyan kifi kiyi amfani dashi. Bari in yo wanka kafin ki gama." Ɗaki na shiga na ɗebi ruwan sanyi cikin bokiti naje na watsa ruwa na fito. Ina ɗaki ina sa kaya naji Fanda na kiran sunana wai ana nemana. Kayan na ƙarasa sakawa na fito tsakar gidan. Wata mata na gani a tsaye. Gaisawa mu ka yi take shaidamun ita abokiyar aikin Yahanasu ce.
"Allah ya bata lafiya. Dama akwai maganar data kawo ni dangane da gidan da Yahanasu take ginawa ne dama. Ganin wannan lalurar ta sameta shine nace bari in zo in sameka, tunda kaine mijinta sai in danƙa maka takaddun gidan a hannunka, da takaddun suna hannunta ma, daga baya kuma ta kawo mun tace in adana mata." Da mamaki na dubi matarnan. Ganin Hajara ta dena aikin da take yi tana kallonmu yasa nace.
Fanda ki shigo da'ita ciki muyi maganar a zaune zaifi" Komawa ciki nayi, su kuma suka shigo tare. Nan wannan baiwar Allah ta zayyanamun komai dangane da siyan fili da Yahanasu tayi, da gama ginin da tayi, buga rabta da ƙofifi ne kawai ya rage mata. Takaddun ta miƙo mun. Nasa hannu na karɓa jikina a mace, ina jinjina girman tunanin Yahanasu.
Allah sarki baiwar Allah, ashe gida take gina mana a ɓoye ba tare da ni na sani ba. Allah yai miki albarka ya baki lafiya ki dawo muci gaba da rayuwarmu mai daɗi." Ajjiyar zuchiya na sauke nace da wannan matar.
"Nagode sosai baiwar Allah. Ko zan iya sanin a inda ginin yake dan Allah. Sannan meye sunanki?"
"Zaka sani sosai ma. Ko yanzu ai sai in rakaka muje. Sunana kuma Binta." Godiya mu kaima Binta mai yawa. Nasa Fanda ta karɓi number ɗan uwanta da tace shi ke kula da ginin. Nace zuwa yamma zamu je muga wajan. Sallama tayi mana ta tafi. Fanda kuma ta gama girkinta ta zuba na ƴan asibiti ta zuba mun nawa, ta zuba na yara . Ni abincinma ba shiga yake yi ba. Bakina ba daɗi sam,ko bacci bana samu, babu kwanciyar hankali da nutsuwa a tare danu sam. Haƙiƙa Yahanasu ta zama wani ɓangare na rayuwata, ina mata son da bashi da iyaka. jiya cike da mafarkan Ba Bakura na kwana. Wayata ce ta shiga kuka ina ɗagawa naga number Ba Modu ne. Da sallama na soma. Sai naji muryar Ba Modu cikin tashin hankali. Ras gabana ya faɗi, jikina ya riga daya bani mai afkuwa ta afku akan Ba Bakura. Ai kuwa hakanne, abunda Ba Modu ya kira ya sanarmun kenan.
"Allah yayi ma Bakura cikawa yanzu Bulama. Sai kayi hanzarin tawowa. Su kuma iyayenka zasu zauna su kula da Yahanasu, amman anan muna buƙatarka." Salati na soma yi, hawaye na wanke mun fuskata, jikina take ya shiga rawa. Fanda ta shigo a dibibice, ganin halin da nake ciki ne ya tilasta mata fasa ihu. Tana faɗin.
"Shikenan Ba Bakura sa'i yayi. Dama ni nasan wasiyya kake bamu. Jikina ya bani mutuwa zakayi shikenan." Lokaci guda Fanda ta tara mana mutane, matan gidan duk suka tawo suna tambayar abunda ke faruwa. Ahmad na kira na sanar dashi halin da ake ciki, yace mun gashinan dawowa zamu tafi tare. Cikin minti goma sha biyar Ahmad ya dawo. Sallamar Hajara yayi da kuɗin cefane. Muka kama hanyar asibiti. Har muka isa asibitin Fanda kuka take aikin yi. Su Bagulaji ma a irin halin da muka tarar dasu kenan an rasa me ba wani haƙuri. Ni kuwa kukan nake son inyi, amman ya ma ƙi zuwa. Bakin gadon Yahanasu na tsaya na shafi fuskarta, sai lokacin hawaye ya zubo mun. Sumbatar bakinta nayi na fita a ɗakin, sai baccinta take yi.
"Mama Gana mu kam zamu kama hanya. Jirgi ma nake son mu hau zuwa Yobe sabida mu samu jana'izar. Ku dena kuka ku yi mishi adda'a." Sallama mu ka yi musu a gaggauce muka isa filin jirgi na malam Aminu Kano Airport.








Ghana:
Zubaina.
Cikin raɗaɗi da azabar da ban taɓa jin kwatankwacinta ba na kwana. Tsabar ciwo har zabure_zabure na dinga yi. Rashida ce ta kwana dani. Da safe Nabila ta shigo hannunta riƙe da kofin kokko ta dure a ƙasa, ta nemi waje ta zauna.
"Sannu Zubaina ya kufan jikin naki. Naga hannun kumburin yayi yawa." Rashida tace.
"Ai tana jin jiki, wallahi bamu ko rintsaba haka na kwana a zaune. Itama ta kwana wash_wash. Amman mahaifiyarta tana Lagos ma yanzu haka zata hau jirgin Ghana, bata daɗe da kiran waya ba. Tama kasa ɗaga wayar sai dani tayi magana. Na kira wayar Baba kiran duniya yaƙi ɗagawa, daman in sanar mishi halin da take ciki ne." Nabila tace.
"Rashida ho kamar baki san halin uban naki ba. Inya tafi fataucinshi ai baya ɗaga wayar kowa. Allah dai yasa mahaifiyar tata ta iso da wuri a samu a kaita asibiti ko ta rabu da azaba. Hanun sai sake kumburi yake yi. Ni dai ina jinsu sama_sama azaba ta isheni. Fuskata tayi wani irin mugun kumburi sabida tsabar kukan dana kwana cur inayi. Kokkon da Nabila ta kawo mun ma kasa sha nayi, in tashi zaune ma abu ya gagara. Sai wajajen jefin azahar Mama tayi kiran waya, ta ari wayar wata mata da suka sauka a jirgi. Kwatancen layin da muke Rashida taima matar. Basu fi awa ɗaya da rabi ba sai ga Mama na jiyo muryarta a tsakar gida tana gaisawa da yaran gidan, da su Hajiya kubra da basu jima da fita a ɗakin nawa ba.
"Bismilla ga ɗakin nata nan tana ciki" Cewar Hajiya Kubra kenan. Godiya Mama tayi mata ta shigo ɗakina, salati ta shiga rabkawa tana tafa hannayenta, cikin ta'ajibi take kallon ɗakin da nake kwance a ciki tace.
"Me zan gani ɗuwawu ya mutu ya bar zani. Zubaina inane nan kuma?" Cikin rishin kuka nace.
Mama ki yi haquri ki kaini asibiti mutuwa zanyi. Ku bar zancen komai Mama " Sai lokacin idon Mama ya sauka a kan hannuna cikin kururuwar kuka ta soma sakin salati a jejjere. Yaran gidanne suka nemo mana mori har cikin gidan ta shigo. Mama da Rashida ne suka rirriƙeni na shiga mori ɗin. Tare da Rashida da Mama muka je wani prive asibiti mafi kusa damu. Daga nan suka turamu general asibiti, domun suke da ƙwararrun likitocin ƙashi. Da isarmu aka shigar dani wani ɗaki, likitoci biyu ne suka rufu a kaina, Mama tana gefena tana sharar hawaye. Ɗayan likitan ya dinga faɗan danme zasu yi mun dorin gargajiya, saida hannu ya suntuma zasu kawo ni. Ɗayan yace.
"Allah yasa hannun bai ruɓe ba, dan yanda ya aune haka, in infection ya shiga cikin ciwon dole mu yanke mata hannun. Dajin haka daga ni har Mama muka tsure. Tashin hankalin dana shiga yafi gaban misalin da za'a rubuta. Allura sukaimun, ban sake sanin inda kaina yake. Sai wajajen bayan isha na farka a wahalce. Hannuna na kalla a tsorace, ajjiyar zuchiya na sauke dan ganin hannun yana jikina ba'a yanke mini ba. Yana sagale a wuyana an ɗaure da farin zaren asibiti. Fuskata a ciccike dan kumburi. Da Mama muka haɗa idanu ta zabga uban tagumi ta shiga wani irin zurfin tunani.
Mama. Na ambaci sunanta da sanyin murya. Ta juyo muka haɗa idanu, ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Kin farka Zubaina, sannu da jiki kinji ƴannan."
"Kinci abinci Mama, yunwa nake ji ni."
"Naci abincin dana saima cikina. Allah ya auna mun arziki tun a Airport nayi canjin kuɗi daga nera zuwa cedi. Zubaina naga rayuwa ni kaɗaice zaune a ɗakinnan ina kula dake. Na kashe kuɗi fin dubu ɗari a kuɗinmu na Najeriya. Na ƙosa ki farka ki bani labarin duhun dana ganki a ciki. Kaina ya ɗaure ainun. Yanzu muka gama waya da Rakiya ta wayarki nasa kati na nemeta. Bari ina zuwa in siyo miki abinci a bakin asibitinnan." Bayan Mama nabi da idanu, ina hawaye. Lokaci yayi da zan bar Ghana ko ana ha maza ha mata. Tunda dai har na riga na fito daga gidan Alh Liti. Da wannan tunani likita ya shigo ya ganni idona biyu. Dubani yayi tare da duba yanayin hannun nawa, yai mun tambayoyin abunda yake yi mun ciwo a halin yanzu.
Hannun yana mun ciwo sosai, sai kuma zazzaɓi dake damuna shikenan. Likita yace.
"Dole hannun yayi miki ciwo sabida yayi tsami sosai. Da ace kun kai gobe baku zo asibiti ba da sai dai kina ji kina gani zamu yanke hannun. Dan nama da ƙashin wajan har sun soma laushi. Hakan yasa ko da hannun ya warke bazai yiwu kiyi aikin ƙarfi dashi ba. Allah ya ƙara sauki. Nurse zata kawo miki magani, in kika ci abinci sai ki sha kafin ayi miki allura. Ina Mama?"
Ta fita yanzu zata dawo" Kai ya gyaɗa yayi ficewarshi. Yana fita Mama ta shigo hannunta riƙe da ledar abinci da pure water ɗaya a saman robar abincin. Fried rice ce koriya fatau, sai kaza a saman da coslow a gefe. Hannu baka hannu ƙwarya nake cin abincin, Mama ta zuba mun idanu nan da nan na cinye abincin nasha ruwa. Nurse ce ta shigo taimun allura ta bani magunguna na haɗiya.
"Ke Zubaina bani

48 / 67