MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   36 / 67

105K to 108K   out of 198.3K words

labarin da Hajara ta bani bayan ta kawo mun abinci da ruwan Tea, tayi mun ya jikin.
"Ki ci abinci gashi nan Yahanasu, ruwan wankan ki yana bayan gida in kika gama cin abincin sai ki watsa da zafin shi." Murya a dakushe nace.
Nagode sosai Hajara, sannunku da ɗawainiya, ina yaran fa?" Ɗan Murmushi tayi tace.
"Haba ai mun zama ƴan uwan juna Yahanasu, yara gasu can a tabarma sunyi baccinsu. Sai kika ji labarin an sallami su Abban Anisa daga wajan aiki ko? Hummm abun yayi mun ciwo. Kinsan ɗaukarsu akayi ba tare da sun shiga shashin horaswaba, to an sake musu shugaba, shine fa akayi bincike aka sallami mutane sama da ashirin, suma abun ya faɗo ta kansu." Da sauri na dubi Bulamana wanda shima idanu ya zuba mun. Hawaye tuni suka wanke mun fuskata, cikin rawar murya nace.
Da gaske ne abinda Hajara ta faɗa an sallameku a aiki?" Kai ya gyaɗa mun baice komai ba. Ahmad ya ƙaraso inda muke yace.
"Sai da na kwaɓe wannan bakin naki mai shegen surutu akan kar ki faɗa ma Yahanasu halin da ake ciki, ki barta ta ji da jikinta. Amman taurin kai yasa sai da kika sake sanya zuchiyarta a damuwa ko? Dame kike son taji to?" Kuka nake yi mai ɗan sauti kaɗan, Bulamana ya kasa rarrashina ya kasa magana. Hajara kuma Ahmad ya tusata a gaba suka koma ƙofar ɗakinsu, sai balbaleta yake da ruwan faɗa.
"Ki share hawayenki, Allah yasan da mu, shi zai kawo mana ɗauki. Daure ki sha ko da tean ne sai ki yi wanka zaki fi jin daɗin cin abincin naki. A wannan daren da ƙyar bacci ya ɗebe ni a bisa tursasawa da rarrashin Bulamana. Shi kuwa a kan dadduma ya kusan kwana, sai jefin assalatu bacci ya ɗebeshi a tsakar ɗakinmu, dan wajajen sha biyun dare da garin ya ɗan yi dama dama sai muka shiga ciki. Washe gari haka muka wayi gari cikin rashin walwala da kuzari. Bayan mun gama karyawa nasha magunguna, da misalin ƙarfe bakwai da rabi Bulamana ya kama hannun yaran yace.
"Zan kaisu makaranta, daga nan zamu fantsama gari neman aiki, ko na ƙarfi ko na abinda muka karanta. Kinsan yadda ƙasar ta dawo, aiki yayi wuya kafin a ba mutum ofa sai fa ya sauke kuɗaɗe masu yawan gaske. Digree ta zama abun banza a ƙasarnan. Amman Allah zai rufa mana asiri, zan dage ko ni ɗinne in jona mastas, in yaso inna gama kya jona naki. In sha Allah zamu samu sauƙi. Akwai abinda kike buƙata in siyo miki in zan dawo ne? Naso in zauna in yi jinyarki ma, amman zama ba aiki bai taso ba. Sannan ka da ki sake ki sanar ma kowa rashin aikina, kar mu ɗaga musu nasu hankalin, Allah zai mana mafita." A raunace na kalleshi, gurbin idanuna tab da ruwan hawaye nace.
Ubangiji Allah ya baku abunda kuka fita nema, Allah ya bada nasara. Babu abunda nake buƙata face kayan kunun zaƙi da meat pie ɗina babu, kuma ya kamata ayi, sabida kasuwanci bai gaji yau akwai gobe babu ba. Zan kira ma'aikatarmu in sanar dasu halin da nake ciki, ko sati guda ne su bani in zauna a gida in yi jinya. Sallama yayi mun suka fice da yaran, bayan ya karɓi kuɗin kayan haɗin kunun zaƙi da meat pie. Cikin sati guda yawon neman aiki su Bulamana suka share suna yi. Amman ba wani labari, hatta koyarwa a makaranta, sun nema a makarantu da dama, amman aikin bai samu ba. Masu digiri da damansu da koyarwar suka ta'allaƙa, samun koyarwar a wannan lokacin shima sai sa'a. A cikin sati na biyu ne suka yanke hukuncin karɓar hayan ɗan sahu, zasu dinga kabu_kabu. Shima da ƙyar suka samu wani bawan Allah mai bama samari lon ɗin ɗan sahu, ya siya musu ta hannu ko wanne ɗaɗɗaya, zasu dinga kai balans ɗin dubu biyu da ɗari biyar kullum har su gama biyan kuɗin ɗan sahun, sai ya zama nasu. Ni kuma shaguna biyu yanzu nake kaima kunun zaƙi da meat pie, banda wanda nake tafiya dashi wajan aiki, ga kuma masu shigowa saye a gida. Har kunun aya da ƙanƙarar madarar kuka nake yi yanzu. Al'amuran sai dai godiyar Ubangiji, ni nake biyan kuɗin haya duk wata, hatta kuɗin makarantar yaran kusan ni nake biya, ga gini a hakan ina taɓawa duk wata ina warar wasu kuɗaɗe in zuba a ginin, adashe nake yi hannaye birjik. Ana cikin wannan rayuwar Bulamana ya samu gurbin karatun mastas a jami'ar bayaro dake Kano, ni kuma na samu ƙaramin ciki. Al'amuran suka sake ɗaure mana sai hamdala kawai, iyaye da ƴan uwa babu wanda yasan halin da muke ciki. Cikina na da wata uku na sake yin ɓari, a sakamakon shaye _shayen muyagun ƙwayoyin da na kasa dena shansu. Ban fi wata ɗaya da yin ɓari ba na samu wani cikin. Watan shi biyu shima yabi rariya. Nayi kuka kamar raina zai fice, nayi nadamar soma shaye _ shaye a rayuwata. Haka lamuran rayuwa su kai ta gudana. Munje gida mun yi zumunci, mun zagaya dangi, har gidan Hajja Fati Bulamana ya kaini. A cikin halin matsanancin ciwo na je na iske Hajja Fati. Ta lalace ta komaɗe in banda sambatu babu abunda take yi. Bata ma iya gane ni ba, shaye _ shayen miyagun kwayoyi ya jirkita mata ƙwaƙwalwa. Ranar na kuma jin tsoron Allah, gami da buwayarshi. Kwana nayi ina kuka tun Bulamana yana rarrashina, har abun yaci tura, ya juya bayanshi yayi watsi dani. Nafi sati guda a cikin tunanin hanyar da zan bi dan ganin na dena shaye shaye, amman duk yanda nayi tunani abun yafi ƙarfina, da naji ina shirin zaucewa dole na sake komawa ruwa tsundum.
BAYAN SHEKARA GUDA
Abubuwa da dama sun faru. A ciki akwai samun ƙaruwa da akayi a can Damaturu. Kusan kab surukan gidan sun sake haihuwa, Aissa kuma ta gama iddarta. Ba Modu yayi ciwon da har an cire rai da ci gaban rayuwarshi, amman daga bisani ya samu lafiya. Ciwon siga ne yai mishi mummunan kamu mai zafi. An ɗaurashi akan magani, sannan su Ya Innana suna ƙoƙarin su wajan bashi abincin masu irin lalurarsu. Dangin wake, jar dawa, alkama, acca, tamba, basmati rice, marvel madarar masu ciwon siga, Tropicana silm (suger shan tea ta masu ciwon suger) da duk wani abinda masu ciwon siga suke ci. Duk wata ana mayar dashi asibiti dan a duba yanayin hawa da saukan sigar. Ta ɓangaren mu kuma rayuwar sai sake tsauri take mana, duk ƴan kuɗaɗen aikina dana sana'a ƙarewa suke yi tas a hidimar gidan. Bulamana kuma yanata aiki da ɗan sahunshi, ɗan kuɗaɗen da yake samu, dasu yake ɗaukar jigilar karatunshi. Kullum a cikin bani haƙuri yake. Ni kuma kullum a cikin ƙarfafa guiwarshi nake, domun babu abinda yake dauwamamme face ƙudurar Ubangiji, bayan wuya sai daɗi. Muna cikin wannan halin kwatsam wata ranar lahadi da misalin ƙarfe takwas na dare. Ina zaune a tabarma ni da yara a tsakar gida, Bulamana ya tafi aikin kabu _kabu, bai dawo ba, sai goma da rabi yake shigowa gida. Wayarshi daya bari a gida ake kira. Ina jawowa naga sunan Zubaina ɓaro _ɓaro ya bayyana akan kwalbar wayar. Sai da gabana ya faɗi, dakewa nayi na ɗaga wayar.
Assalamu alaikum wake magana?" Jim muryata yasa tayi jim kafin daga bisani ta saki tsaki.
"Kwatancen inda kuke zaki yi mun, inason in zo ganin yarana tsohuwar munafuka algunguma" Cije leɓena nayi nace.
Za'a turo miki adireshin a rubuce" Ban jira naji me zata ce ba, na datse wayar. Adireshin gidan na tura mata. Naci gaba da shige da ficen ɗakko kunun zaƙi ma masu saye. Kamar minti goma sha biyar da kiran waya da Zubaina tayi. Sai ga Bulamana ya shigo gidan, ya nemi waje ya zauna a taburma. Tagumi ya zuba. Na dubeshi jiki a sanyaye nace.
Lafiya meke faruwa Bulamana, wani abunne ya faru na ganka haka, gashi yau ka dawo da wuri?" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Ai kasuwar sai godiya, tun fitar da nayi nera ɗari biyar kacal nayi. Gashi jiya ban bashi balans ba, yau kuma ga yanda abun ya kasance. Gashi zazzaɓine ma yake damuna sosai Yahanasu" Bance mishi komai ba, na shige ɗaki, na buɗe bankina na ƙirgo dubu biyar na fito. Bayan na zauna ne na miƙa mishi kuɗin. Ƙin karɓa yayi ya bini da jajayen idanunshi.
"Wannan kuɗin na meye kuma Yahanasu? Ina bazan ma karɓa ba. Komai na nauyin gidannan kan ki ya dawo fa, ke kike yin komai. Balans kuwa na biya da kaina, sai kace mara tausayi" Murmushi nayi nace.
To in banyi maka ba wa zan yi ma to? Kai dai ka karɓa kawai ka je ka kai mishi. Wata rana sai labari, kar ka mance karatu kake yi, in sha Allah da zaran ka kammala zaka samu aikin yi. Muna fatan kafin ma ka kammala ɗin. Ai ko a gidan wani nake aure, zanyi ma duk wannan abubbuwan, ballantana kai nake aure, dan Allah karɓi ka kai mishi" Karɓa kuɗin yayi, ya dinga shi mun albarka.
"Kai in nayi kuɗi sai kin soma hawa mota kafin in hau, ke zan soma siya ma. Banda suturu da zan ta jibgo miki, duk shekara kuwa a Saudiyya zaki yi Azumi. Dariya mu ka yi dukkanmu, har muna tafawa duniya tayi mana daɗi.
Ban da dai cika baki, azo kana yin kuɗi ka danƙaromun Amarya, ƙila ma ta riga ni tarewa a cikin sabon gidan da zaka gina mana" Dukan wasa ya kawo mun. Nayi wuf na kauce. Kiran wayarshi ce ta katse mana nishaɗin da muke ciki
"Zubaina ce yau take kira na? In ma batun kuɗine bani dashi gaskiya nima" Sai da ya gama surutanshi kana ya kara wayar a kunnenshi.
"Ina bakin layin naku, ko za'a iya zuwa ai mun jagowa zuwa gidan, in fa da hali kenan?" Da mamaki ya zare wayar a kunnenshi dan ya tabbatar shin ko gizo idanunshi ke mishi, amman daya duba sai yaga itance, kafin ma yayi magana ta katse wayar. Da yake wayar tashi na da ƙara sosai, raɗau abinda Zubaina ta faɗa a kunnena.
Ɗazu ta kira, ni na bata adireshin gidanma. Ka je ɗin ka shigo da'itan" Ran shi a dagule ya fice a gidan. Ni kuma wani irin kishin mijina ne naji yana nuƙurƙusar raina, ji nake tamkar in bishi in ce inason raka shi, dan gani nake kamar biko Zubaina tazo , ba wani ganin yara. Shekara ɗaya da wata biyu da rabuwarsu, sai yau ne ta tuno da akwai yara a tsakaninsu da zata tawo ganinsu.






BULAMA BABBA:
Ina tafe ina mamakin zuwan Zubaina wai ganin yara. Shekara ɗaya da wata biyu ta kwashe ba tare da tazo duba yaran ba, sai yau ne zata zo.
"Malam Bulama Bakura Bukar bismillah shiga gidan baya mu ƙarasa gidan ko?" Zubaina ce a kame a gaban wata jibgegiyar baƙar mota. Tayi wani irin kyau da mugun haske, fuskarta sai sheƙi take yi. Tsanarta naji ta kuma yi mun dirar mikiya a zuchiyata. Kallon shirgegen mutumin dake tuƙa motar nayi, shima ni ɗin ya zuba ma idanu, yana wani irin murmushin da shi kaɗai ya barma kanshi sanin dalilin yin shi.
Kar ki damu, ku bini a baya kawai gidan ba nisa." Ina faɗar haka na shige gaba ina tafe ba guiwa. Ni kaina bansan dalilin daya sarar mun da guiwata ba. Gabana sai faɗuwa yake yi. A ƙofar gidanmu na tsaya, ina jiran su gyara tsaiwar motarsu. Tafi minti biyar kafin ta fito daga cikin motar nan. Idanu na zuba mata ƙur.
Mrs Bukhari ce
[08/08, 7:26 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
29


















Ƙamshinta ya daki salansar hancina. Sanye take cikin shigar atampa ɗinkin doguwar riga, ya kamata tsam, duk wani diri da cikar halittarta ya bayyana. Ga wasu takalma masu tsinin gaske a ƙafafunta. Tasha kwalliya tamkar wacce ta fito dan zuwa wajan zaɓen sarauniyar kwalliya. Sai wani annuri fuskarta ke fesarwa, ta yi mul_ mul abunta. Yusuf ta fito dashi daga mota, shima yaci uban ado yayi kyau ainun. Kamarshi sak da Zubaina har ma ya zarce ta fari da yake yarone. Tana takowa inda nake, na tsugunna na ɗauki Yusuf a jikina, na lumshe idanuna na buɗe su a kan Zubaina dake tsaye a gabana tana dariya.
"Malam Bulama Bakura Bukar, a wannan ƙazamar anguwa da ƙazamin gida kuke rayuwa haka? Wow kace talauci yaci uban na da, ko da yake ba abunda ya kawo ni ba kenan." Murmushin cusa haushi na mata nace.
Mu je ki aiwatar da abunda ya kawo ki Zubaina, kin bar bawan Allah shi kaɗai. Wucewa ta nayi ciki, tana biye dani har ƙofar ɗakinmu. Yahanasu na kalla muka haɗa idanu, murmushi ta sakar mun, nima na mayar mata da murmushin.
Ga baƙuwar mu, ki bata wajan zama, ga kuma ɗanki Yusuf. Na tsugunna na ajjiye mata shi a jikinta. Yahanasu ta nuna ma Zubaina kujerar tsugunno tace
"Bismillah Kofur ga waje, maraba da hanya, bari a kawo abun sha." Da sauri Yahanasu ta miƙe ta shiga ciki. Sheƙeƙe Zubaina tabi bayanta da kallo. Yaranta ta zuba ma idanu suna kwance a tabarma, duk sun rame sun yi duhu, sun dawo yaran malo. Kai ta jijjiga kawai. Ahmad da Hajara ne suka fito tsakar gidan. Zubaina ta buɗe bakinta data gansu. Hajara ta iso wajan da saurinta tana yashe baki.
"Kaga manya_manya maganin ƙanana ƙanana. La'ilaha_illallahu Zubaina kece kika zama babbar mace haka, kinga yanda kike haske kamar wata ɗan daren sha biyu? Tubarakalla kai farar mace alkyabbar mata, Kai ya sa, ji Yusuf yanda yaro ya zama ɗan turawa wallahi ba kya ce Bulama Babba bane gyatumun shi ba" A yatsine Zubaina ta dubi Hajara tace.
"Hajara kina nan a yanda na sanki. Ya yaran kema a cikin jagwalgwalon gidannan kuke, aminci daɗi?" Ahmad ne ya ja ni gefe can.
"Me ya kawo wannan maras tarbiyyar gidannan kuma Bulama?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Tace dai ganin yaran tazo. Ita da wani ne ya kawota." Kai Ahmad ya jijjiga. Muna jiyo Hajara sai ɓarin zance take yi, har abinda ba'a tambayeta ba sai da ta faɗa ma Zubaina. Hatta rasa aiki da mu ka yi, sai da ta fesa mata. A fusace Ahmad yayo kan Hajara rai a dagule, ba shiri ta gudu ɗaki tana tambayarshi ita me tayi. Yahanasu ce ta fito da kunun zaƙi jiki a sanyaye, ranta a dagule bazai rasa nasaba da surutan Hajara ba.
"Yaronku na kawo muku dama, domun na kammala iddata har an sa mun ranar aure. To ba'a ƙasar zan zauna ba, shine nace bari inzo in ga yaran shi kuma Yusuf in dawo dashi gidansu" Baki na washe mata nace.
Kai masha Allah, Allah ya sanya alkairi, Allah yasa gidanki ne. Ina taya Yusuf murnar dawowa cikin ahalinshi. Yahanasu tashi su Bawa su ga mamansu." Tashinsu Yahanasu tayi, Bawa ne kaɗai ya gane mahaifiyarshi, amman Maryam ta mance da'ita. Ɗan jim tayi ta saka hannu a ajjihu ta zaro dubu ashirin ta ajjiye mana
"Ga wannan a yima shi Yusuf ɗin siyayya, tunda banzo da kayanshi ba. Sunan Asiya nazo sai kuma nayi amfani da damar kawai nace bari in kawo muku shi kawai. Tana kaiwa nan ta miƙe ta tafi. Bayanta nabi da kallo, ina juyowa Yahanasu ta gallamun harara tace
"Ka mayar mata da kuɗinta, bata isa raina mana arziki ba, tunda gidanmu yafi nasu nesa ba kusa ba." Ran Yahanasu ya ɓaci ainun, ga kishi ina hangowa ƙarara a idanunta. Ba shiri nabi bayan Zubaina, tana shiga mota, ni kuma ina isa wajan. Ƙwanƙwasa ƙwalbar tagar motar nayi. Tana yin ƙasa da kwalbar na ajjiye mata kuɗinta a cinyarta, bance da'ita komai ba na juya na dawo wajan ƴar matata me kishina. A daren ranar naga rikicin Yahanasu, dan da ƙyar ta ba da kai bori ya hau, nasan ta wannan hanyar kaɗai zan rarrashi abata. Ahmad kuwa muna jiyo rikicinshi da Hajara, sai tafi da ɗaga mishi murya take yi, kamar wata ƴar tasha, duk da a hakan ma ta rage abubbuwa da daman gaske.






KOFUR ZUBAINA:
Bayan Bulama na bi da kallo, na dawo da kallona ga kuɗin daya ajjiye mun a cinyata. Alh Liti yace.
"Amman wannan tsohon miji naki akwai shi da girman kai, da ganinshi talauci ya gigita rayuwarshi, ni tausayin Yusuf ne ma ya kamani. Jikina a mace na dubi Alh Liti nace.
Su kansu su Bawa kar ka so ganin yanda duk suka lalace, cikin gidan ma kaɗai ya isa ka tausayama Yusuf da yayyenshi. Amman ni naji daɗin ganin Bulama cikin rashin daraja, da kasan wulaƙancin da yayi mun sabida dukiyar daya samu ai kare bazai ci ba ma alhakina ne ya talautashu." Motar shi yai ma key muka koma gidan Asiya. Washe gari da safe Alh Liti ya ɗauke mu zuwa Kaduna. Kwanan mu biyu da dawowa daga Kano, Alh Liti ya tura magabanshi zuwa gidan Kawu Tanko. Mazan su kai sadakin, matan kuma suka shiga cikin gida da akwatunan aure na alfarma. Mama ma tana gidan tare da Mama Rakiya ƙanwarta da Mama Zakiya, Musa yana waje tare da su Kawu Tanko. Kaji goma Mama ta soya musu akai musu pepper kickhen, sai kayan fulawa dangin cincin, meat pie, fish roll. Abun sha katon biyu, ruwa katon biyu. Dangin Alh Liti sun samu tarba ta mutunci. Ina daga ɗakin Goggo Safiya ina leƙensu. Tsofaffine, amman ƴan gayu cikin sutura mai daraja. Kayan akwati da

36 / 67