MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   37 / 67

108K to 111K   out of 198.3K words

su katon katon na sweet, biskit, cingam, ruwan gora, da lemun roba, sai da suka kusa cika falon Goggo Safiya. Dubu ɗari Mama ta zaro ta miƙa ma Goggo Safiya ta basu a matsayin tukuici, domun hausawa suka ce yaba kyauta tukuici, tuwon girma miyar nama" Zuwa bayan Isha suka yi musu sallama suka fita. Da sauri na fito daga cikin uwar ɗakin Goggo Safiya. Baki na kama da naga yawan kayan abun ya matuƙar bani mamaki. Ban tsure ba, sai da aka buɗe akwatunan naga nagartattun haɗaɗɗun tsadaddun kayan da Alh liti ya loda mun. Sai son barka ƴan uwa suke yi mun. Ana cikin haka Hajiya Mabaruka ta shigo da sallama da ɗan ƙaramin cikinta daya ƙara yi mata kyau. Dubanta nayi naga ta sake zama wata Hajiya, da gani hutu da nutsuwa sun samu waje a jikin Hajiya Mabaruka. Baki ta shiga washewa da ta ga irin kayan da Alh Liti ya lodo mun, da irin dukiyar daya narkar. Ita kanta da Salisu ke ji da ƙuruciya da tashen dukiya, bata samu rabin abunda na samu ba.
"Ƙawata kinyi goshi gaskiya, irin wannan kayan alatu haka. Kiyi haƙuri naso zuwa tun tuni ayi komai dani. Amman Salis ne ya ɓata mun lokaci yace sai na jirashi shi zai kawo ni." Dariya nayi nace
Ai babu komai ƙawata, baga ki kin zo yanzu ba" Kawu Tanko da Musa ne suka shigo da sallamarshi. Waje ya samu ya zauna a sama ya yi gyaran murya.
"Jummai ga sadakin Zubaina nan nera dubu ɗari da hamsin nan na karɓa. Kamar yanda wanda ya ba da sadakin ya faɗi yace shi ƙanin mahaifin Alh Liti ne" Kuɗin ya miƙo ma Mama, tana washe baki ta karɓi kuɗin ta adana a jakarta. Kawu Tanko ya ɗaura da cewa.
"Sati mai zuwa in Allah ya nuna mana juma'a da safe misalin ƙarfe bakwai safe za'a ɗaura auren a ƙofar gidannan. Zuwa ƙarfe goma da rabi jirginsu zai tashi zuwa Ghana in sha Allah, kuma ta Lagos zasu tashi, daga nan zasu hau jirgi zuwa Lagos. Duk wani biki a can za'a gabatar dashi tare da danginshi wanda su kai tsaye Ghana zasu wuce. Yaso daga shi sai Zubaina zasu tafi. To ganin rashin dacewar hakan yasa na roƙeshi akan za'a tafi da iyaye ko da mutum biyu ne, dan bai dace ace daga shi sai ita zasu kama hanya ba. Kuma tunda yace acan za'a gabatar da biki tare da danginshi ai ya kamata ace itama wani nata yana kusa. Da Safiya, da Rakiya sai ku shirya daku za'a tafi. Ƙawayenta sai su yi haƙuri waje ba kusa ba." Ni dai haushi ma Kawu Tanko ya bani, naso ace mu yi tafiyarmu mu mu biyu daga ni sai Alh Liti, sai Mabaruka da mijinta zai biya mata kuɗin jirgi. Amman sabida shishshigin ace matarshi ta taɓa hawa jirgine yasa ya roƙeshi. Mama tace.
"Ashsha Tanko naso da ka bar Alh Liti yayi yanda yaso ɗin ya tusa matarshi sun tafi ni ina ganin da zaifi. Amman yaya zanyi tunda ka roƙeshi ya amince maka mutum biyu zasu bisu ai shikenan" Kawu Tanko yace.
"Jummai kenan. Ai ni abunda duk kika ga nayi, ko nayi magana akai yana da matuƙar mahimmanci ne. Gani nayi in dai Zubaina da gatanta ai bai dace ace an ɗaura aurenta ta bi miji sun tafi wata ƙasar su su biyu ba. Ko banza yana da kyau ko da mutum ɗaya ne su bisu domun ganin muhallinta dan gudun afkuwar wani abun. Ni dai ta ɓangarena banyi bincike a kan Alh Liti ba. Amman ai ke kince ba'a buƙatar bincike sabida abokin mijin Asiya ne. Kinga dani da ku du bamu san halinshi ba, abun hannunshi kawai aka duba. Toh yace matarshi baza tayi aiki ba, tama ajjiye aikin ɗan doka da take yi. Amman akwai albashi da zai dinga biyanta duk wata na kimanin nera dubu ɗari biyu a kuɗinmu na najeria. Inaga iyakar abunda zance kenan. Allah ya nuna mana lokacin, zan je ƙauye gobe in sanar da su, zamu dawo tare da Isiya ma, da jama'ar ƙauye da zasu zo ayi biki tare. Sai Zubainar ta kasance a nan gidan da safe, dan daga nan zasu wuce." Haka dai mu kai ta shirye_shiryen biki. Ni da Mama mun so ayi bikin a sabon gidana dana zuba haya. Dan akwai ɗakina dana Mama a cikin gidan dana ware mana babu kowa a ciki. Amman kawu Tanko ya buƙaci ayi bikin a gidanshi kamar yadda aka saba. Ƙawayena kowa na son zuwa, wasu nisan ke kashe musu jiki amman ba dan basu da kuɗin jirgi ba. Wasu kuma basu son tafiya mai tsayi sosai. Haka dai naita aikin gyaran jiki da gyaran gashi, na tsawon kwana huɗu. Supplement na kamfanin G H T nasha na gyaran fata, nasha na gyaran al'aura duk wani na gyara babu wanda ban sha ba. Na sai majakani ma, da wani supplement mai ɗankaren kyau na matsi nera dubu tamanin na siye shi, na sha pesona ma shima ƙarshe ne. Maman Amal ita ta haɗamun kayan kamfanin G H T Cikin ƙanƙanin lokaci na canja na sake, ni kaina ina jin sha'awar kaina sosai. Kaya kala goma na ɗinka daga cikin kayan akwatina na cin bikin da za'ayi a Ghana, ɗinkuna masu tsadar gaske na sa akaimun sosai. Ran alhamis na yi taron bikina ni da Mama. Ƴan uwa da abokan arziki duk sun halarta, babban fili na kama akaci aka sha, aka yi rabon sobeniya na kasko da turaren wuta wanda MRS BUKHARI ke yi domun aure, ko bikin suna. Washe gari da sassafe muka kulle gida zuwa gidan Kawu Tanko. Dangin mahaifinmu cike da gidan maza da mata anzo daga ƙauye. Ɗaki guda aka ware mun ni da ƙawayena. Ina zaune nasha kwalliya da wani dafaffen farin lace, wanda yasha ɗinkin doguwar riga, stone work akai mun a jikin lace ɗin sai walwali nake yi. Takalmin ƙafata ma fari ne sol, haka fashion ɗan kunne da sarƙa na suma fararene sol. Sai ƙamshi nake ta fitarwa tamkar fulawar Queen of the night. Su Hajiya mabaruka sai zuba akeyi da kawayenmu. Nafisa ce ta shigo cikin shigar atampa super tasha adon gwalagwalai tace.
"Anti Zubaina Mama na nemanki, tana wajan bayan ɗakin Kawu Tanko. An ɗaura auren ma yanzunnan" murmushi nayi wani farin ciki ya saukar mun, tare da faɗuwar gaba, da sanyin jiki wanda bana ce ga dalili ba. A sanyaye na bi bayanta muka fito, nan take sanar dani itama zata bimu ita da Asiya. Naji daɗi sosai, ko ba komai nima aga ƴan uwana suma masu kuɗine. Mama na samu a can bayan ɗakin Kawu Tanko ita da Mama Rakiya. Kasancewar nan ɗin shine ba jama'ar biki.
"Yauwa dalilin da yasa na kira ki Zubaina shine. Aure an ɗaura yanzu, har ma Alh Liti ya turo a sanar muku nan da minti talatin za ku tafi filin jirgi. Ga wannan hayaƙin, da kun shiga ga Rakiya ta turare miki ko ina da shi. Ga gawayin kanti tafi da gidanka, dan nasan ko a maƙota ba zaku samu gaushi ba. Zubaina sai fa kin tashi tsaye sosai akan kishiyarki da yaran mijinki. Ki dinga turo kuɗi ana kaima bokanku tunda Mabaruka tana nan, kar ki je ki miƙe ƙafa, in ba haka ba zaki dawo najeria dan wallahi matarshi ba zata zauna ta miƙe ƙafa ba ke kin fi kowa sani ai. Kuɗin hayar gidanki kuma ya za'ayi miki dasu?" Dariya nayi guntuwa.
Ku dinga amfani dashi. Zan turo kuɗaɗe ɗan abun da zan wawuro na amarci a sake sayen wani filin a rangaɗa ginin gidan sama babba. Amman kafin nan ina samun kuɗi zan sa a rushe gidanku a gina gidan sama mai lafiya,yanda ƴan anguwa zasu san e mai kuɗi nake aure. Zan sa Alh ya zuba muku komai sabo. Kuma zamu aikin Hajji harda Mama Rakiya da Musa da Sagiru ma in sha Allah. Nan mu ka yi sallama, ina fitowa naga su Mabaruka cirko cirko a tsakar gida.
"Yauwa dama yanzu zan zaga in kira ki sai ga ki. Alh yace mu fita waje, zamu tafi Airport tun yanzu." Sallama na shiga yi da ƴan uwa da ƙawayena. Mu bakwai muka fita zuwa waje. Alh Liti yana jingine a motarshi muka fito, ya dube mu yace.
"Ya nagan ku har ku bakwai, duk ina zaku je?" Mabaruka ce ta soma yi mishi bayani.
"Ni da su Nafisa mun biya ma kanmu kuɗin jirgin. Su kuma iyaye su biyu kai zaka biya musu" yace.
"To babu laifi muje ko?" Mota biyu ce ta kwashemu ƴan uwa sai hannu suke ɗaga mana. Kai tsaye muka wuce Airport mu ka hau jirgin Lagos. Ƙarfe goma da minti goma muka shiga Airport na na Lagos. Kai tsaye bayan an gama bincikar kayanmu, muka sake shiga layin da zai sada mu da harabar filin, dan shiga bus da zata ƙarasa damu wajan jirgin. Ƙarfe goma da rabi muna zazzaune a cikin jirgin ko wanne ɗaure da bell, na'ura sai magana take yi akan, kowa ya gyara zamanshi, nan da minti biyar jirgi zai ɗaga. Lokacin na cika jirgi ya shiga haramar tashi, cikina take ya bircike, dan ji nake kamar kaina zai fita a jikina. Bani na dawo dai dai ba har sai da jirgi ya dai dai ta a sararin samaniya, ajjiyar zuchiya na sauke mai ƙarfi. Na dubi Alh Liti yai mun Murmushi yace.
"Matsoraciya, a haka zaki tafi yawon buɗe idanun kina shirin sume mun a jirgi gimbiyar mata. Yau gamu a matsayin ma'aurata, na tabbatar gidana zai baki farin ciki da nutsuwa, yanzu ne zaki san kin yi aure." Murmushi na mayar mishi nace.
Ni kaina na san yanzu ne nayi aure. Kuma na tanadar maka farin ciki da nishaɗi a cikin wannan rana mafi girman daraja"
"In kuwa hakane, na tabbatar daren yau babu abunda zai zo ya ture miki shi a zuchiyarki. A shirye nake dan dandalar zuma mai garɗi, wadda na daɗe ina tanadi, sai yau Allah yasa ta zama mallakina" Haka mu kai ta musayar narkakkun kalaman soyayya mai daɗi. Haka jirginmu yai ta gudu a sararin samaniya. Awa ɗaya da minti hamsin da huɗu jirginmu ya sauka a KOTOKA international Airport Accra" A hankali muka sakko daga cikin jirgin, zuwa cikin wata ƙofar glass. A cikin wannan falon muka jira akwatunan kayanmu da suke tawowa cikin wani abun sulu. Mu kuma duk muna tsaye, in akwatinki ya sulo sai ki ɗauka ki fice ta wata ƙofa, in da anan masu jiran ƴan uwansu suke jiransu, masu motoci da babura ma duk iyakarsu wajan. Wasu manyan motocine suka ɗebemu zuwa gidan Alh dake Nima anan cikin Accra.


Mrs Bukhari ce
[08/08, 9:04 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
30


















.
A hankali na buɗe idanuna ina kallon ƙasar Ghana, farin cikin dake cikin zuchiyata ba abu bane wanda zai musaltu ba. Babu abunda nake yi sai Murmushi. Cikin wata anguwa naga motarmu ta sulale ta shiga. Anguwace wacce take cakuɗe da masu kuɗi da talakawa. Amman gidajen masu kuɗin kamar yafu yawa, dan manya manyan gidajen sama su suka fi yawa ma a anguwar fiye da gidajen ƙasa. A wani katafaren gidan ƙasa muka tsaya gari guda. Gidan yasha zane irin na gidajen sarautun Arewa, amman gidan ya fi mun kama da irin zanen gidan sarkin Bauchi. Get biyu ne a gidan, tsakankanin ko wanne get akwai tafiya. Wani matashi ne mai tsantsar kama da Alh Liti ya taso ya nufo motar mu. Alh Liti ya sauke kwalbar jikin tagar motar ya dubi wannan saurayi ko magidanci zance yace dashi.
"Buɗe mana get ɗin ɓarayina can, ta can zamu shiga." Yaron Alh Liti cikin hausarshi irinta hausawa mazauna Ghana yace.
"Su Hajiya Kubra suna ta wanga ƙofa suna jiran isowarku Baba" Idanu Alh Liti naga ya runtse yace.
"Nace ka buɗe mun wancan get ɗin ko Adamu, shin ko kayi hauka ne ban sani ba" A zabure wannan yaro ya wuce zuwa ɗayan get ɗin gidan. Mu kuma muka bi bayanshi da mota, mun yi tafiyar kimanin minti uku kafin mu iso bakin ɗayan get ɗin. Tura hancin motar mu muka yi zuwa cikin gidan, wanda yake cike da shukoki kala daban daban. Gidan nake ƙarema kallo sosai. Babban gidan sama na hango a ware a gefe ɗaya, anyi mishi gini irin na alfarma. Tsakar gidan an shinfiɗa intalok tako ta ina, ga wata baranta da aka ƙawata ta da kujerun kaba masu kyawun gaske. Jibga_jibgan motocin Alh Liti guda uku suna adane a rumfar adana motoci na farfajiyar gidan. Daga hannun dama na na hango wata ƙatuwar ƙofa wacce da dukkan halamu itace ƙofar da zata sada mutum da ɗayan ɓarayin, ba sai mutum ya fita waje yayi doguwar tafiya zuwa get ɗin farko ba. Da dukkan halamu ɗayan ɓarayin na uwar gidan Alh Liti da ɗiyoyinta ne, in kuwa hakanne zanci karena babu babbaka kuwa" firfitowa muka yi daga cikin motar. Alh Liti yana gaba muna biye dashi a baya. Key yasa ya buɗe wata ƙofa. Falone gabjejen gaske, wanda ya lamushe kujeru kusan saiti biyu da rabi. Ga wasu tum tum da aka barbaza a kafet ɗin dake tsakiyan falon, kalan kujerun, falon ya tsaru iya tsaruwa. Hotunan mata na hango cike da wani bango, ciki harda hotona, hoton Alh Liti yana tsakiya yafi na kowa girma.
"Goggo Safiya ku shiga can ɗakin, zan sanar ma da mata isowarku a kawo muku abinci." Cewar Alh Liti kenan. Ni kuwa tsabar daɗi kamar in tashi sama haka nake ji. Ɗakin da ya nuna mana muka shiga, shi kuma ya haura matattakalar dake cikin falon dan hawa sama." Ɗakin baccine mai kyan gaske, komai na cikin ɗakin baƙi ne da ratsin silver, tun daga kan gado, wadrope, santa kafet, labulaye, komai da komai dai. Ɗakin babu wani kayan hayaniya, amman dake kayan ciki masu tsada ne, sai suka fito da ɗakin sosai. A bakin gadon na zauna, su Goggo Safiya kuma su ka yi rashe rashe a ƙasa suna ta kallon waje. Mabaruka da su Nafisa suka ɗane tsakiyar gadon suna yabon kyau da tsari, gami da girman gidan Alh Liti. Mabaruka tace.
"Ƙawata a gaskiya gidanki yayi kyau babu ƙarya, kuma da halama ɓarayinki da ban, na uwar gida ma daban, in kuma ba a saman da Alh Liti ya hau take ba. Amman falonnan naki shararshi da tsabtaceshi sai ƴan aiki ba ma ƴar aiki ba, naga yana da girma sosai. Murmushi nayi mata nace.
Gida kam yayi kyau, abun ma ba'a cewa komai gaskiya. Haka zanyi kane_ kane a cikin gidannan inta zazzage ƙwayayan da suke mahaifata a cunkushe, in giwa ta faɗi mu ci nama" Hannu ta miƙo mun muka tafa, tare da yin dariya ƙasa ƙasa, dama cikin raɗa_raɗa muke maganar daga ni sai ita.
"Yanzu in Alh Liti ya tabbatar miki nan ɗakin shine naki, sai in sassaka miki layun da boka ya bayar ko?" Hakan data faɗa yasa na tuno da hayaƙin da Mama ta ba Mama Rakiya. A hankali na isa gareta a kunne nayi mata magana dan gudun kar Goggo Safiya taji mu. Ba shiri Mama Rakiya ta miƙe tsaye, nan ta shiga binciken ashana ko laita. Kab ɗakin dai bata samu ba, falo ta fita bata jima ba sai gata da laita ta shigo. Gawayin ta kunna, ta saka a ƙaramin kaskon ƙarfe da yake jakarta. Nan ta yi ma gidan hayaƙi har zuwa falo." Ina sallah na jiyo sallamar mace. Su Goggo Safiya ne suka amsa sallamar, ta turo ƙofa ta shigo.
"Sannunku da zuwa lale. Ina yininku, kun zo lafiya?" Kafin su amsa na sallame, Amman ban juyo ba. Har suka gama gaisuwarsu.
"Ni ɗiyar Alh ce, nazo ganin Amarya ne, sannan Hajiya tace in sanar muku a shirya Amarya, zuwa bayan la'asar akwai biki a ƙofar gida da za'ayi, in kun ci abinci, Ni sunana Hadiza" Gaggo Safiya tace.
"To madallah Hadiza, kinga Amaryar gata can akan sallaya tana sallah ne. Zuwa dare ma zamu zo cikin gidan mu kawota, sannan zaku ganta a wajan bikin." Dariya tayi ta fice, naja guntun tsaki na takaici. Hadiza bata daɗe da fita ba, aka kawo mana abinci. Jallof ɗin shinkaface da kaza, sai coslo, da lemon gora da ruwan gora. Kowa yaci abinci ya goge wuyanshi. Daga bisani kuma, muka shiga shirin biki. Zuwa bayan la'asar kowa ya shirya tsab dashi. Ina sanye cikin wani net mai duwatsu masu walwali orange, ɗinkin riga da siket wanda suka ainihin zauna a jikina das, nayi kyau sosai, takalmin ƙafata mai ɗan karen tsini na saka mai ruwan madara, sarƙar wuya na itama mai ruwan madararce, na fito shar dani. Ƙarfe biyar dai _dai wasu mata su kai sallama a ƙofar ɗakin da muke. Mama Rakiya suka amsa musu, suka shigo. Su biyu suka shigo. Wata matace fara sol mai haƙorin makka a bakinta na azurfa dan sai ƙyalli yake faman yi, ita ta soma magana da cewa.
"Sunana Hajiya Kubra nice uwar gidan Alh Liti. Wannan kuma ɗiyarshi ce, Maryam. In Amarya ta shirya zaku iya biyo bayanmu mu je." Kallonta nayi da kyau, itama ni ta saki baki galala tana kallona. Siririyace sosai, fara sol da'ita dan ta kereni fari, amman bata da hanci, kuma idanuwanta fici fici suke kamar fincen ƙuma, gata da ƙaton leɓe, duk da nima laɓɓana suna da girma, amman nata sunfi nawa girma. Atampa Chiganvy ce a jikinta

37 / 67