Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
kuwa take yanayinshi ya sauya, daga farin ciki izuwa baƙin ciki. Idanunshi suka kuma yin ja, dama jajayene idanun nashi.
" Kuyi haƙuri, zanyi musu magana. Babu inda zasu je, ina zuwa" Fuu ya fice. Na yi Murmushi kawai na share hawayena, na fita falon nima, dan in kalli bidiri"
Bulama Babba:
Cikin zafin rai na fita falo. Wakil da Bulama ƙarami na gani a zaune suna kiciniyar buɗe gidauniyar abincin da aka dire musu. Ƙofar ɗakin su Asiya ce tayi ƙara. Su Mama Gana ne suka fito, jin ƙaran ƙofar yasa su Fanda suma suka fito, duk suka shigo falon. Zubaina ma fitowarta kenan. Jikina sai naji yayi mugun sanyi, na zuba ma ƴan uwana abun ƙaunata idanu ina murmushin da bansan sanda ya subce mun ba.
"Bulama sa ƴar dokar matarka ta kawo mana babban faranti, yau abincin tare zamu ci, a falonnan.
Allah sarki Bakura yana shiga farin ciki, in yaga wani shashi daga cikin iyalanshi sun haɗe waje guda suna cin abinci a akushi guda. Dariyar farin ciki nayi, ko babu komai na shiga farin ciki jin furucin Mama Gana.
Zubaina ɗakko mana faranti maza" Zama nayi a kusa da Wakil, ina zama Maryam ta dawo cinyata ta zauna. Zubaina ta kawo farantin Fanda kuma ta juye taliyar a faranti, ta kwarara miyar akai. Gabaki ɗaya muka matso tare da yin bismilla dan soma cin abinci. Salab naji abincin a bakina, abunda ban saba ji game da girkin Zubaina ba kenan, gashi miyar tayi ruwa, bata ko kama taliyar ma. Dubanta nayi, tana zaune ta jawo laptop ɗinta tana aikinta.
"Wannan wanne irin girkine haka kamar an wanke kan mahaukaciya, haka kake gasuwa da irin wannan girkin? To ina ma zata iya girki tana aikin police, aikin da a tarbiyya na maza ne aikin, ina matar aure ina kama ɓarawo ko ɗan ta'adda." Da sauri na tari Mama Gana da cewa
Kiyi haƙuri Mama Gana kefa uwace, karki zubar da kimarki a gaban yarinyar nan."
"Dalla rufa mun baki shanyayyen kawai, wa yake neman daraja a wajan marar daraja irin azzalumar matarka? Ahir ɗinku damu wallahi Bulama. Kuma wallahilƙudrat in baka ce baƙar almurar matarka ta fice mun daga nan ba, saina ci ubanka Bakura" Da sauri na juya, muka haɗa idanu da Zubaina wacce fuskarta ta jiƙe sharab da ruwan hawaye. Laptop ɗinta ta ɗauka tare da wucewa kamar kububuwa.
"Haba Mama Gana in hankali ya gushe hankali ake turowa ya nemo shi. Kai kuma Bulama ƙarami kuje ku siyo mana abinda zamu ci yinwa muke ji. Allah ya bamu lafiya, ni dai Bulama bazan sake tako ƙafata da sunan zuwa gidanka ba, ko mai zai faru da kai. Ka zauna da matarka kaita ma danginta hidima." Cewar ya Bagulaji kenan, Yanunu tace.
"A haɗu ayi haƙuri dai, mu iyayene, mu kai zuchiyarmu nesa dan Allah, ke Gana kiyi ma Allah ki dena magana. Sannan shi Bulama Babban yaje ya nemo mana abincin da zamu ci, a bar mata abincinta."
"Ai wallahi har in bar gidannan bazan sake cin abincin matarshi ba, ya san yanda zai yi damu, shashsha wanda baison mutunci ba. Albasa dai batai halin ruwa ba" Fuu Mama Gana ta shige ɗaki tana gama magana. Su Ya Bagulaji suka mara mata bayanta. Kaina ya ɗauki caji sosai, na dubi ƙannena duk ransu a jagule, Fanda da Yahanasu har hawaye suke zubarwa. Inason ƴan uwana bana son ganinsu a wannan halin.
Dan Allah kuyi haƙuri ƙannena, ku dena kuka Zubaina bata kyauta ba, kuma zan yima tubkar hanci. Wakil ku zo muje mu kawo musu abinci, kar yinwa tai musu lahani. Tare muka fita, bamu daɗe ba muka shigo, Kaji gasassu da masa na siyo musu hilimi guda. Muka shigar musu da abun sha. Ni kuma muka wuce masallaci dan gabatar da sallar isha.
Yahanasu:
Bayan fitarsu Bulama Babba da kyar na dena kuka, sai da su Mama Gana sukaita lallashina. Ni tsorona Allah, tsorona su barni a wannan gidan, tare da makirar matar Bulama Babba. Mama Gana tace.
"Dalla ki share hawayennan, tun yanzu so kike su gano logonki, wallahi in kika bari matarshi ta takura miki ke kika so Yahanasu. Kema fa mata ce, kuma bugu da ƙari ƴar uwarshi, kima saki jikinki, kafin in tafi saina tabbatar tsintattun magenan sun bar gidan, dan zasu iya haddasa muku fitina a zamanku." Nan sukai ta bani baki, ana haka su Wakil suka kawo mana abinci. Sai da mu ka yi sallah sannan Hajja Fati ta je kitchen ta ɗakko mana faranti muka baje kaji, da masarnan. Bamu ci ba har sai da su Wakil suka dawo sallah. A ɗaki muka ci, a faranti ɗaya, Bulama Babba sai Murmushi yake yi.
Mama Gana wannan zaman saiya tuna mun da gida, lokacin ina ɗan sakandare, mama Gana kin tuno? Ni sai ince sai da su Wakil zanci abinci. Lokacin suna yara dan in ban mance ba, Su Wakil da Bulama ƙarami da Bulama Fari, da su Ahmada, da Dala duk dai yara yaran maza suna firamare, hanci duk majina. A lokacin su Yahanasu, su Fandau suna yara ƙanana, Fanna da Yabulu, da Ba'a kaka duk goyonsu ake yi su kuma a lokacin. Haka za'a zuba mana Buski da miyar kuka, muita ci. In an aikeni kai niƙa sai na goya Fanna ko Yabulu nake zuwa. Kafin a haifesu kuma su Yahanasu nake goyawa. Akwai wata rana da kare ya biyoni ina da goyon Yahanasu a bayana. Naje ɓarjin Masarar buski. Na ɓarar da masarar naita gudu, Yaha na bayana sai kuka take yi. Muka faɗa kwata, har kanta ya fashe, sai da akai mata ɗinki, bazan mance da wannan lokacin ba" Dariya muka saka dukanmu, Wakil yace.
"Ni ina tuno lokacin da muke tsaiwa a bakin get muna jiran dawowarka, ka bamu biskit ko abincinka daka rage. Ahmada gashi da shegen kwaɗayi. Kai kuma kana zuwa sai ka tsugunna a gabanmu ka rarraba mana biskit guda guda" Bulama Babba yace.
Lokacin sabida ku saida na dena kashe ko sisi a makaranta, biskit ɗin ku nake siya ma. Abincina kuma, rabi nake ci in kawo muku rabin. Abokina Jabir Dauda da mun sha kwanar layinmu, zai ce Bulama Bakura ga mayun ƙannenka can masu nacin tsiya suna jiranka" Dariya dukka aka kuma sakawa. Mama Gana tace.
"Ai kaso ƙannenka sosai, mu a lokacin har mamaki kake bamu. A kwai lokacin da aka haifi Yahanasu, to tunda aka haifeta sai aka haifeta da shawara, ko idanu bata iya buɗewa. Ganin hakan sai aka riƙeta a asibitin. A lokacin kana wajena ni kuma nazo Damaturu sabida haihuwar Innana ɗin. Muna shiga da kaga Yaha da ƙarin ruwa a hannunta, sai ka fashe da kuka ka ƙanƙame Modu kana cewa. Ba Modu a cire mata tana jin zafi. A lokacin munyi mamaki sosai bana wasa ba, yanda ka tausaya matan shi ya bamu manaki" Ya Bagulaji tace.
"Ai Baluma yayi abubbuwa sosai, tun yana yaro ƙannenshi suke jin maganarshi. Sabida duk abunda aka bashi su yake rabewa shi ya haƙura baki ɗaya ma. Ko wanne yaro ɗan gatan Bulama ne. Kullum a cikin saima su Dala tamaule yake. Kullum kuma in aka fita sai an ɓatar, amman bai taɓa gajiyawa ba" Munyi hira sosai, irin hirar da aka jima ba'ayi irinta ba. Sai kallon Bulama Babba nake yi. Sai nihaɗi da jin daɗi yake yi, tausayinshi ya kamani ainun. Gashi yanzu ya ware kanshi da danginshi, ko kira iyayenshi basa cin albarkacin haihuwa ya kira su, in ma suka kira, sai yayi ra'ayi zai ɗaga. Na ci alwashin da ƙarfin adda'a in Allah ya amince zai dawo da Bulama Babba ainihin Bulaman da kowa ya sani. Iyayenshi sai sun yi alfahari da wannan haɗin da suka yi. Ko banci ribar komai ba a zamana da Bulama. Inason inci ribar dawo da tunaninshi cikin iyaye da dangi, nayi wannan alwashin, ko da hakan zai zame mun ƙarshen numfashina. Zan sa Hajja gana farin ciki, da Ba Bakura. Domin su ɗin mutanene na gidi, kuma su suka tsaya ma rayuwarmu har muka kai matakin da muke kai. Ba Modu ya bamu labarin irin faɗi tashin da Ba Bakura yayi dan ganin ya tallafi rayuwarsu, ya ɗaurata akan turba ta gari. Alhamdulillah ya ɗaurasu bisa tartibiyar tarbiyya, ya basu ilimi, ya aurar dasu, ya basu wajan zama, ya ba ƴaƴansu ilimi. Madallah da babban wa irin Ba Bakura. Sai wajajen ƙarfe sha ɗayan dare Bulama yace zai je ya kwanta, gobe monday yana da zuwa aiki. Tare muka fito harda su Wakil. Muna shiga ɗakin Bulama Babba mu ka ga Zubaina a zaune akan wani teburi tana danna laptop.
"Kun gama hirar ne? Cike da fara'a tayi maganar kamar ba ita bace ɗazu ta shige cikin gida fuu da hawaye a fuskarta ba.
"Bulama bai faɗa muku zaku kwanta a BQ ba ne? Ai an riga an gyara muku ɗayan ɗakin" Fanda ta riƙo hannuna muka fita. A falon muka tarad da su Wakil, a tsayenma hira suke yi.
"Lafiya kuma kuka fito Fanda?" Wakil ke tambayarmu.
"Zamu je BQ ne ɗayan ɗakin mu kwanta acan kawai, mu jenku ko?" Fanda ta bashi amsa. Bulama Babba baice komai ba, mu kai mishi sallama a wajan mu dai muka barshi, yana bin bayanmu da kallo"
Bulama Babba:
Ajjiyar zuchiya na sauke, ban gushe ba har sai da suka fice a falon. Na rufe ƙofar falon, tare da kakkashe wutacen gidan. Ɗakina na nufa kai tsaye. Tana kan table ɗin da nake aiki, itama aikin take yi. Jin shigowata ne, yasa ta ɗago ta zuba mun idanu, tana mun kallon sai yanzu ka tuno dani. Sai tausayinta ya kamani, ta bar falo ɗazu tana kuka, Mama Gana taci mata fuska, amman ban sake waiwayarta ba.
Ashe kina ciki, su Nafisa sun kwanta a ɗakinki, da su Maryam ko?" A ido a ido nake kallonta, tare da karantar yanayinta, Murmusawa tayi kawai, bata ce komai ba."
Mrs Bukhari gidan ƙamshi ce.
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
[26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
6
takowa tayi har inda nake ina kwaɓe rigata, ta kama rigar ta taimaka mun na cire, kamar yadda ta saba yi mun a ko da yaushe. Ina samun kulawa fiye da tunani, Zubaina bata rageni tako ina ba. Zamanmu mai daɗine, kuma abun koyi, amman muna samun saɓani kamar yadda rayuwa take tafiya, kuma tana da yawan fishi sosai, da zaran wani abu ya haɗamu mara daɗi, take ƙaurace mun akan shinfiɗa, sannan duk tarairayar da nake samu a wajanta, ajjiyewa take yi a gefe, hakan ba ƙaramin galabaitamu yake yi ba dukkanmu, dan a ranar da muka shirya komawa muke yi tamkar mayu a shinfiɗa. Tunanina ta katse mun da cewa.
"Ka shiga ka samu kayi wanka, na haɗa ma ruwan wanka, in ka fito ina da magana da kai."
To Zubaina ta na gode, ina kuma ƙara gode miki" Ban ɗakin na shiga nayi wanka, tare da yin brosh, na ɗauro alwala. A zaune na fito na same ta, agogo na kalla, sha biyu saura kwata na dare.
Wai kaddai wannan case ɗin ɗan luwaɗinnan kiketa faman yi har yanzu?" Kallona tayi taja dogon tsaki.
"Kai dai ka bari, har yanzu bamu gama tattara bayanan daya dace mu tattara a kan mutumin ba, gashi A S P ya bamu lokaci, D P O ɗinmu gani yake kamar bama ƙoƙari akan case ɗin. Amman gobe zani kaciya ni da yara, zamu ziyarci gidan wasu yara biyu da shi mutumin yai musu fyaɗe, suna ƙarƙashin kulawar asibiti, sai ɗayan yaron dake anguwan dosa, sauran yaran sun mutu, amman mun tattauna da iyayensu. Ni bama wannan ya ɗaga mun hankali ba. Wallahi damuwata shine wannan kayan dake cikin mota, wanda ƴan uwanka suka zo dashi, amman Bulama ziyara kawai suka kawo mana kuwa, ni naga sunyi yawa ne ace ziyarace wannan kawai fa, sannan ga kaya cikin mota, duk da naga ba'a taɓa kayan ba, amman duk da haka na kasa samun nutsuwa" Zama nayi a kusa da'ita, na jawo hannunta ta dawo kusa dani.
Ziyarace kawai, a gidanmu haka muke yi, in dai gidan ɗaya daga cikin dangi zamu je. Maganar kaya da kike yi, ni kaina bansan kayan meye ba maganar gaskiya, amman bai kamata kayan su ɗaga miki hankali ba ai, koma na meye, ko na waye dole zasu faɗa mun, zaki ji. Sai dai banji daɗin abinda ya faru ɗazu a falo ba. Kiyi haƙuri da dukkan maganganun Mama Gana, kuma kiyi taka tsantsan da ɓacin ranta, naso in taso in rarrasheki gudun fitinane yasa na zauna, amman zuchiyata tana tare dake. Amman Zubaina garin Yaya abincinki ya zama haka?"
"Ni kaina ban sani ba, su Asiya na bari akan miyar, sabida an kirani daga wajan aiki kan maganar case ɗin ɗan luwaɗinnan, to kafin in fito sun gama miyar, kayi haƙuri bansan haka suka yi ba. Sannan ka bata haƙuri su ci abincina hakan ba zata sake faruwa ba" Murmushi nayi.
Baki san Mama Gana ba ne. Ai bata haƙuri da zanyi shi zai sa ta zazzage kwandon faɗa, kuma tunda tayi rantsuwa ko kin dafa abincin bazata bari kowa yaci ba. Karki damu zan dinga siya musu har zuwa lokacin da zasu tafi. Su Wakil ma da asuba zasu juya kamar yadda suka ce mun. Gobe ƙarfe nawa zaki fita office?" Kuka ta fashe mun dashi.
"Bansan me nayi ma ƴan uwanka suka tsaneni ba Abban Maryam, wallahi ni kuma ina ƙaunarsu sosai, dan Allah in akwai wani halina da ƴan uwanka basa so ka sanar dani in gyara" Rarrashinta na shiga yi, ina jin zafin kukan da Zubaina take yi. Aikin faranta mata rai na shiga, dan nasan shine kaɗai zai kwantar mata da hankalinta.
Yahanasu:
Ɗakin baƙi muka shiga kai tsaye. Katifa ce babba a yashe a ƙasa, sai ban ɗaki, shikenan abunda ke cikin ɗakin. A bakin katifar na zauna, Fanda ta zauna kusa dani, Hajja Fati ta zauna a ƙasa tana ba ɗiyarta nono.
"Yahanasu zaman aure fa haƙuri da juriya shike rayar dashi. Da wasa kar ki sake ki zama mai raki da ƙorafi, sannan ki koyi tursasa zuchiyarki wajan ɓoye sirrin gidan aurenki. Fitar da laifin Bulama Babba ko laifin matarshi, ka iya jawo targaɗe ko karayar aurenku. Mu dukka dangin junane, abinda ya yi ki, shi ya yi Bulama Babba. Ba Bakura tamkar mahaifi yake ga su Ba Modu. Kiyi ƙoƙarin ganin kin sa Ba Modu a cikin farin ciki, ta hanyar tattala musu zumuncinsu. Da zaran kin fitar da magana, a kwana a tashi, za'a iya samun rashin daidaito, ko kuma gagarumin RIKICIN CIKIN GIDA. Bulama Babba bazai cutar dake ba, a hannunshi duk muka girma, tun bai mallaki hankalinshi ba, yake yi mana hidima, ni tausayinshi ma nake ji wallahi. Sabida da kin ganshi, kinga wanda baya cikin hayyacinshi, matarshi ƴar duniya ce, ko a fuska duniyancinta ya fito, ki bi su a hankali, ki kwantar da kai kiyi tsantsar biyayya ga mijinki, ɗan uwanki, dan Allah ki rufa mana asiri. Ki duba sabida halin dattaku irinna Ba Bakura,ya haɗa aurenki da Bulama Babba ne sabida ya sama miki sauƙin rayuwa a cikin ƙunci, duba da iftila'in da ya yi kotse a cikin rayuwarki, muma ya taɓa zuchiyoyinmu, ki dinga tunawa da wannan." Jikina sai naji ya sake macewa mus, har nake jin ko da yankar naman jikina Bulama Babba yake yi, shi da matarshi, zan bishi zan zauna dashi, ko dan in faranta ran mahaifana, kuma in kare dagulewar zumuncinsu mai kyau ta dalilina. Hawayene yashiga zarya a kumatuna, Hajja Fati tace dani.
"Kuka ba naki bane, bai kuma kamace ki ba. Yahanasu ki dage akan adda'ar Allah ya baki yaddar mijinki, ya kare ki daga sharrin dukkannin wasu masharranta. Ki yi haquri, muma da mu kai auren soyayya kina ganin yanda muke fama, ni kaina gudun kar in tsunduma Mama a halin damuwa ne yasa nake zaune da Baban Nasiba. Amman wallahi zaman cutuwa nake yi. To Mama tana da ciwon Suger, ga hawan jini, kullum nasiharta dani shine, in zauna inyi haƙuri a gidan mijina. Shawararki dai kawai zan ɗauka, na komawa makaranta, zan nemi ƴar sana'a in kama dan