MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   26 / 67

75K to 78K   out of 198.3K words

ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*


















murmushin ƙeta nayi ma Mabaruka, duk da zuchiyata zafi take yi mun nace.
Habawa Mabaruka ai kowa yaci tuwo dani miya yasha. Duk hukuncin da zan ɗauka a kansu, ai a bayan wannan layar da boka ya bani ne. Babban burina shine inga Bulama tsiya na binshi, ya lalace rayuwarsu ta tagayyara ai shine kawai. Ƙaddara da rabon ƴaƴa shi ya haɗani da Bulama, da kuma ƴan canjin hannunshi, da maiƙon gidansu. In bacin wannan me zai haɗa kifi da kaska, baƙi mummuna dashi, fuskarnan tashi kamar tuwon dare, muni kuwa tamkar a yanka a ɓoye wuƙar. Yanzu kuwa ya bani damata da zan cashi zawarcina yanda yai mun, miji kuwa sai wanda ya isa zan aura, inda zan shiga in baza mulki na. Babban cutar da Bulama yai mun shine daya sake ni da ɗanyan jego sharab. Bansan ma ya idda ta zata kasance ba, tunda ni bana jini har sai nayi yaye ma." Mabaruka tace.
"Tabb ai kuwa Bulama ya gama dake, dan wallahi naji fatawa akan haka a karatun Malam Aminu daurawa, cewar duk macen da aka saketa, sai sakin ya zamana tana da ɗanyan goyo, kuma in tana goyo bata jini, bazata ce ta ƙirga wata uku shikenan ta fita daga iddarta ba. Har sai ta jira ta soma jinin nan tukunna tayi jini uku sannan ne zata iya yin aure. Harma yayi bayani akan wata mace da ta rubuto mishi tambaya akan mijinta ya saketa, to ita kuma a shekara sau ɗaya take jinin al'ada, tana tambayar ne dan tasan ya iddarta take. Ya tabbatar mata dole sai ta jira wannan jinin tayi shi sau uku, shekara uku kenan sannan ta yi aure. Kinga kuwa Bulama ya cuceki, aini sona shine da zaran wata ukun iddarki ya cika sai yaji kinyi aurenki, amman kash, amman fa ƙawata gara da kika yanke hukuncin barin Bulama ." Dariya nayi.
Haba Mabaruka ai babu komai a hakan ma, ƴan watannine ko shekara da da ɗoriya ai, kamar yaune. Tsugunne ai bata ƙare ba, tunda zanje wajan malamai su sanar dani hakkina daya rataya a wuyan Bulama a matsayina na mai shayarwa daya sake ni, inta kama ma sai in kaishi kotu in dai zai mun gardama. Ɗan tasha fa ɗaukar kaya kawai zai nuna mini." Haka mu kaita faman tattaunawa har muka fito daga wannan ƙungurmin dajin. Sannan kuma muka nufi tashar mota, sai magriba motar mu ta ɗauki hanya.




Bulama:
Da sallama muka shiga cikin gidan maƙotanmu, bisa jagorancin yaron gidan. Da Hajara mu ka ci karo tana zaune tana ba Anisa, da Maryam tuwo a baki, suna saye da kayan makaranta daga su har Zulai. Bawa da Mustapha suma tuwon suke ci.
"Sannunku da shigowa ƴaƴannan" Cewar Baba tsohuwar gidan. Cike da girmamawa muka gaisa tare da yi mana jaje. Ni tunanina da burina bai wuce inga Yahanasu ba, idanuna suna kwaɗayin ganinta. Maryam ta miƙe ta faɗo jikina bakinta duk miya, sai ta saka kuka tana kiran sunan mamanta. Ƙur na ƙura mata idanu tausayinsu na huda ni.
"Ina Yahanasu Hajara, ya kuma yanayin jikin nata?" Ahmad ya tambaya. Idanuna na lumshe a hankali.
"Da sauƙi sosai, ai wani bala'in ya kan kori wani bala'in da gudu. Ta fita shago siyan magani, aron kuɗinma tayi a wajan Baba, kai Yahanasu bata jin daɗi, har tangaɗi take yi fa kamar wata mai shaye shaye." Muna cikin zancan sai gata tayo sallama a tsanaki. Idanu muka haɗa naji wani abu ya shigeni yar.
Sannunku Yaya Ahmad kun dawo?" Ta faɗa a sanyaye, muryarta a dashe sosai.
"Mun dawo Yahanasu, sannunmu fa, Allah ya auna mana arziki babu wanda ya jikkata, sai asarar dukiya da akayi kawai, wannan kuma dama nemota akayi, za'a nemo wasu da izinin Allah" Waje Yahanasu ta samu ta zauna kanta a ƙasa, da kyar na buɗe baki nace.
Dukkannin wata ƙaddara da take samun bawa a rubuce take, wayo ko hikima ba zasu kuɓutar da bawa ba. Kuyi haƙuri a bisa yanda kuka tsinci kanku baku da ko zanen ɗaurawa, wata rana sai labari. Dole zuwa gobe zamu tattara mu je gida, ko da ku ɗinne mu kai ku, sai mu mu dawo, ɗan abinda aka gagganɗa muka kama muku haya sai kuma ku dawo. Karatun yaran ma dole zai tsaya tukunna." Babawo ne ya dawo inda muke a tsaye yace.
"Bulama akwai ɗaki biyu a zaure na samarine zaku iya amfani da ɗakunan ku da iyalan naku, in yaso su yaran akwai ɗakin yara a cikin gida sai su kwanta, kafin kuma ku gama shawarwari a tsakankaninku. Muje ku ga ɗakin kafin mu wuce masallaci." A baya muka bi Babawo ya nuna mana ɗakunan harda katifu a ko wanne ɗaki, sai ɗan karen datti abunka da ɗakin samari. Komawa cikin gidan yayi ya sanar da iyalinshi ta taya su Yahanasu gyaran ɗakunan, mu kuma muka wuce masallaci. Bayan mun idar da sallar magriba kuma jama'a suka taru akaita mana jaje, masu taro masu sisi sai bamu suke yi. Harda masu suturu namu dana mata, da yara. Haƙiƙa musulunci akwai daɗi. Haka zalika zama da maƙoci cikin aminci da amana akwai daɗi, munga haɗin kai da soyayya irinta malam bahaushe mai ɗaukar damuwar wani tamkar tashi. Har bayan isha muna ta karɓar jaje daga manya da matasan anguwa, ni kuma zuchiyata tana wajan Yahanasu babu abinda nake son ji ko gani sama da muryarta, da ganinta a kusa dani. Tara saura muka samu shiga cikin gidan niƙi_niƙi da ledojin kayan da aka bamu.
"Ahmad kai ka riƙe na hannunka ɗin, wannan ya ishemu."
"Ah ba'ayi haka ba Bulama ai" Ban ce mishi komai ba na soma sallama a ɗakunannan dan sanin inda matayen namu suke. Ɗakin dake kusa dani shine ɗakin da na jiyo amon muryar Hajara tana amsa sallamarmu. Can inda Ahmad yake kuma kenan a nan Yahanasu take, duk da banji amon muryarta ba. Har zan shiga ciki Ahmad yace.
"Aff ni na mance, iyayen Zubaina sun nemeka danjin ba'asin abinda ya faru har ta kai ku ga saki kuwa?" Tsaki naja nace.
Ana ta kai wa yake ta kaya? Bana tunanin ko a mafarki zasu kira danjin me ya haɗamu, karfa ka mance ni gandirobane yanzu, mai ƙaramin albashin da bai taka kara ya karya ba. Akan me zasu kirani? Alhalin yanzu daga iyaye har yaran auren kwaɗayi kawai suke yi. Ahmad ni wallahi bana buƙatar da wasa iyayen Zubaina su kirani a waya ma, dan zan iya zaginsu" Dariya Ahmad yayi har yana girgiza kai.
"Mai da wuƙar goga na kofur Zubaina ba da kan ka a sare kaje gida kace ya faɗi, sai da safe, ka gaishe da Yahanasu da jikinta"




Yahanasu:
Ina kwance shiru ina karanta wasiƙar jaki, duniya tayi mun ɗaurin lemar minti, al'amura sai caɓewa suke yi daga ɓangarena, bala'i ina cikin wannan sai wannan ya faru. Na yarda da ƙaddara, amman kuma ban isa ince bana cikin damuwa ba. Ba abu bane mai daɗi ace kayi gobara ka rasa dai dai da zanin ɗaurawa. Ni ina ganin bakin da Ba Bakura yai ma Bulama Babba akan dukiya da duniya shi yasa wannan abubbuwa suke faruwa damu a jejjere, dan fishin iyaye da zubar hawaye su masifa ce babba a garemu. Sallamar Bulama Babba na jiyo da sauri na shasshare hawayen dake zuba a idanuna. Yana shigowa ya zuba mini idanu cike da kallon tuhuma. Ni kuma da sauri na tashi naje zan karɓi ledojin hannunshi.
"Ki barshi Yahanasu ke da baki da lafiya" Naji ya faɗa da wata muryar da bansan ya mallaketa ba, dan nasan muryarshi girma da kauri gareta. Dan bana mance sanda yake daka mana tsawa duk mu furgice tsabar kaurin muryarshi. A hankali na juya na koma inda nake. Shi kuma ya tattako ya zauna a kusa dani daf, jikinmu yana gugar na juna.
"Kin samu kinci abincin, ko kuma akwai abinda kike buƙatar in nemo miki ki ci?"
A'a bana buƙatar komai, naci abinci"
"Maganin me kika fita siyowa da kika kasa bari sai na dawo na siyo miki? Ke da baki da kafiya haba Yahanasun Ba Bakura " Ɗan Murmushi nayi mishi kawai. Na jawo kwanon tuwonshi na dure a gabanshi.
Ga abinci kaci" Kai ya girgiza mun
"Abinci bazai samu gurbi a cikina ba Yahanasu. Bari ina zuwa kinji" Bai jira na amsa ba ya fice. Bai wani daɗe ba sai gashi da leda ya shigo. Balangu ya miƙo mun a ƙunshe a leda, shi kuma kunu naga ya ciro a leda ya soma sha. Da ganinshi a cikin tsananin damuwa yake sosai, idanunshi sun kuma rinewa sosai. Tsoka biyu naci balangunnan na ƙunshe shi, na adanashi a gefe guda. Kowa yayi shiru yana tunanin rayuwa, kowa da abinda yake saƙawa. Bulama Babba sai jan carbi yake yi daga zaune inda yake. Sannu hankali bacci ya gagari idanuna, a hakan ma na shanye kwalba guda na maganin tarin yara, na haɗa da ƙwaya guda biyu na haɗiye, amman idanuna tamkar an soya gyaɗa, kaina sai shirin tarwatsewa yake yi. Ina kwance Bulama ya ɗauki Qur'ani mai girma da ya gani a ajjiye, nan ya soma karatu da ƙira'ar alaramma Sulaiman sa'ed. Bashi da niyyar bacci, nima Allah nake ta ambato ina ta hailala. Ƙarfe ɗaya ƙarfe biyu, nima ba shiri na miƙe zan fita waje, yana kai aya yace
"Ina zaki a cikin darennan Yahanasu?" Cikin rauni nace mishi.
Alwala nake son in ɗauro, zanyi sallah. Bacci ya gagari idanuna, gashi kaina kamar zai tarwatse." Ƙur ya zuba mun jajayen idanunshi yana karantar yanayina.
"Muje in raka ki to" Banyi jayayya ba, muka fito a tare, ya raka ni har ƙofar bayan gida na shiga bakina da adda'ar shiga ban ɗaki. Ina fitowa na ɗaura alwala, muka koma ciki. Hijabin matar Babawo data bani kyauta na saka, na ta da sallah, shi kuma yaci gaba da rera karatunshi a hankali cikin nutsuwa. Haka muka raya darennan da ibada, har zuwa asuba. Hannu na ɗaga na dinga ragargazo mana adda'a, mafi yawan adda'ata akan Bulama Babba take. Dan har ga Allah, tausayinshi na shirin fin ƙarfin zuchiyata, ni da na zauna tare dasu, nasan cewar ba banza haka Zubaina ta barshi ba, duk abubbuwan da yake yi baya cikin hayyacinshi domun ba haka halayyar shi take ba sam. Nutsuwa sam bata tattare dashi, wani irin suru_suru ta mayar dashi. Amman alhamdulillah Allah ya share mana hawayenmu, kuma ba zan gushe ba, wajan riƙon Allah ya shiga takaninmu da zubaina, da mugaye irinsu. Ina roƙon Allah ya kuɓutar dani in dena wannan shaye_shayen, nima ba a son raina bane. Amman nasan su ummu naheeba ba zasu fahimci halin da nake ciki ba. ( Note BARI IN YI MUKU TUNI, YAHANASU A CIKIN DEEPRETION TAKE KAR KU MANCE, SHI KUMA SHAYE_SHAYE BA KAMAR SHAN RUWA BANE DA ZAKA SHA A SANDA KA GA DAMA KA ƘI SHA A LOKACIN DA KA GA DAMA BA. WANNAN YANA DAGA CIKIN JARABAWAR YAHANASU, MATSI DA TSANANI YANA JEFA MUTUM A CIKIN MUMMUNAN YANAYI. KUMA MU SANI DEEPRETION CIWO NE WANDA YAKE IYA JUYARMA DA MUTUM ƘWAƘWALWA, KUGA MUTUM YA KASHE KANSHI, KO YA KASHE MIJI KO ƘAWA, KO YA FAƊA SHAYE_SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI. KUMS ABUNE WANDA IN AKA SHIGESHI FITARSHI YANA DA MATUƘAR WUYAR GASKE KUYI MATA UZIRI, NAJI ƘORAFE ƘORAFENKU)






Kaduna


Kofur Zubaina:
Bamu muka iso Kaduna ba sai wajajen sha ɗayan dare. Mabaruka ta nufi gida, nima na dawo gida. A tsakar gida na samu Mama a zaune, ita kaɗai, cikin muryar bacci tace .
"Zubaina kece da darennan me yasa baku kwana acan ba?" Zama nayi a kusa da'ita nace
"Mama ke kiji ashe ɗan akuyarnan sakina yayi? Sai da muka je wajan boka yake faɗa mun. Ita kuma matsiyaciyar matarshi ta bunka ma gidan wuta, komai ya ƙone ƙurmus. Amman ina zuwa tunda akwai wuta bari in jona chaji in kunna wayar, inason ganin sakin ne" Nan na bar Mama tana ƙunduma ruwan zagi, tana tafa hannaye. Ɗakin babu kowa, da halama ma Nafisa bata gidannan. Wayata na saka a chaji, na sauke Yusuf dake ta faman bacci, a gado na shinfiɗeshi. Na dawo gaban wayar na kunna. Tana gama kunnuwa kuwa, sai saƙon Bulama ya shigo. Karantawa nayi, na ɗanyi Murmushi.
Bulama kenan, zaka gane kuranka, sai kayi ɗan daka ce baka sake ni ba." Wajan Mama na dawo"
"Hmmm Zubaina saki fa kika ce, yanzu abinda ja'irin yaronnan zai mana kenan, zawarci bagatatan haka?. Amman to ya kuka yi da bokan?"
Ni bazan koma gidan Bulama ba dai na farko. Gara in yi zawarcina Allah ya ɓullo mun da wani mai maiƙon yayi wuf dani. Ni zawarci bazai bani wuya ba, ina aiki fa. Babban baƙin cikina goyon da nake dashi ɗanye ne, amman dai gobe zan shiga layin dutse makarantar sha rubutu, in mishi bayani ko akwai wata fatawa da zan samu mai sauƙi. Mama Bulama tunda ya rabu dani, ya dinga ganin masifu kenan, aikin da boka ya bani inyi, ban shigo gida ba sai da na aiwatar dashi tukunna." Mama tace.
"Ina baki kina roƙa. Yanzu da wanne idanu zan kalli munafukan anguwarnan Zubaina in har suka fahimci zawarci kike yi? Gashi zawarcinma na tsiya tunda ko kayan kirki baki dashi, muguwar kishiya ta bunka miki wuta. Ga jarabar iyayen yarinyar da Musa yai ma ciki. Ko ɗazu sai da na kai kuɗin abincinta nera dubu ɗaya suka yanke za'a dinga biya kullum , in ba haka ba kotu ta raba mu. Na nemi ragi ma wallahi sun ƙi. Ga iskancin Sagiru abun ya'isheni kullum a cikin gaggayamun maganganu yake, ga Nafisa itama ko da mu ka je asibiti ɗazu cikine da'ita. Amman har an zubar mata, amman kinga harta fice yawo tana jinin raɓe raɓe. Yanzu ya zamanki zai kaya tsakaninki da Sagiru?" Ana cikin haka kuwa sai gashi ya shigo yana fito, hannunshi riƙe da adda tsirararta. Wani mugun kallo ya watsa mun yace.
"Me wannan la'ananniyar Allahn take yi a cikin gidannan da daddarennan bata tafi gidanta ba? Ke dan uwarki me kike yi?" Mama ce tace.
"To nan dai gidansu ne itama, kuma kasan mijinta ne ya siya mana gidan ko? Aurenta ne ya ƙare dan haka ta dawo gida da zama ne." Addar nan ya karta a ƙasa yayi ihu yace.
"Arne Allah ya kuɓutar dashi daga sharrinku kenan? Ke kuma zaki girbe abinda kika aikata, sharri ɗan aike ne, kuma haushin kare ne, bayan mai shi yake bi. Gara ni bana cutar kowa, duk abinda zanyi tsakanina da mahaliccinane. Kuma ki kula da shiga harkata, dan wallahi in kika mun yankaki zanyi in soya" Dan baƙin ciki in yi magana na kasa, kallonsu kawai nake yi shi da Mama suna hargowa ta faɗa ya faɗa, daga ƙarshe ya wuce ɗakinshi ya sake kaya ya fice. Sai lokacin Nafisa ta dawo, ta tulin uban kaya leda leda, sai wani yamutse fuska take yi.
"Ba kui bacci ba Mama, lafiya na ganku cirko cirko Anty Zubaina?" Mama ta taso mata da faɗa.
"Dan ubanki daga cire miki ciki yau yau shine zaki fita ɓel ɓel, baza ki ma bari ki warke ba, so kike a sake yi miki wani cikin ko? Dan kinga ina baki kariya, ai ko babu komai ya kamata ki zauna ki warke ko?" Maganganu Nafisa ta soma yi ma Mama, dama mun saba a haka Mama ta tarbiyyantar damu tun muna yara, sai abinda mu ka ce
"Haba Mama in ban fita ba a ina zan samu kuɗin da zanyi buƙata dashi, ke kanki daɗin da kike ci wa zai baki? Yaushe rabon Asiya data turo miki wani kuɗi ishasshe? Ta kanta kawai take yi. Dama mai ƙoƙarin Anty Zubaina ce, to ita kuma karayar arziki ya same su. Mama ki barni in nemo mana kuɗi kici daɗi in kai ki makka kinji?" Baki Mama ta washe tace.
"Allah ya amsa Nafisa da kuwa naji daɗi, ni fatana ko wacce in ganta cikin farin ciki, dan ku nake yin komai. Asiya kuma ai tana ƙoƙari fa Nafisa, kuma in ita bata ƙoƙarin ai mijinta yana yi. Kuma tayi mun alƙawarin umara da watan azumi in sha Allah." Ni nama kasa ce musu komai, damuwar dake gabana itace a gabana. Ɗaki na wuce na kwanta, sai wasiƙar jaki nake ta faman karantawa, na kasa sa komai a bakina. Bansan sanda ɓarawon bacci ya sureni ba. Sai jin kiran sallar asuba nayi. Tashi nayi zaune wuf dan kwanciyar duk ta isheni dama. Bayan nayi wanka nai ma Yusuf ma wanka. Gari na yin haske na fito da goyo a bayana, na shirya tsab.
Mama ni zan fita, inason inje office in sanar dasu dawowata nan, kwana biyunnan nayi wasa da aikina. Can dai Kanon na kira na sanar musu ina cikin wata ƴar matsala ne. Kafin in shiga office zan duba Malam sha rubutu a makaranta, ina da fatawane"
"Amman Zubaina ba kya tsaya ki karya ba tukunna, ƙaramin goyo ne fa dake, aini nayi tunanin rabuwarki da Bulama bazai jefa ki a ko wanne irin halin damuwa ba. Sai naga saɓanin hakan" Rausayar da kai nayi nace.
Yaran

26 / 67