Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
da daddare har yanzu bai sake ni ba, da ƙyar nake iya riƙe kaina. Naji tausayin kaina sosai, yanda naga Ahmad ne kawai ya damu da kukan da nake yi, amman wanda nake zamanshi, kuma ɗan uwana ko kallon inda nake baiyiba, ta matarshi kawai yake yi, da yaranshi. Allah sarki ni, ban taɓa tsanmanin rayuwa zata iya juya mun baya haka ba, banyi tunanin Bulama zai iya watsi dani haka ba. Inna tuno da nasihar Ba Modu da Ya Innana sai inji jikina ya kuma mutuwa. Kukana na tsagaitar na dinga ragargazo adda'a tunda muna hanyar tafiya ne. Zuchiyata tayi zurfi wajan roƙon Allah yai mun mafita. Awa huɗu mu kayi a hanya kafin muka isa Kano. Ahmad yace
"Bari in kira Musa agent inji me sunan anguwar, direba ka tsaya tukunna." Direba ya nemi waje ya tsaya. Ahmad ya kara wayarshi a kunnenshi, jim kaɗan ya soma waya.
"Gamu mun shigo Kano musa ageint inane unguwar take?" Dake a hands free ya saka wayar muna jiyo abinda Musa Ageint yace.
"Ƴan lemo zaku zo, bayan layin mai kalwa primary school, sai mu haɗu a dai dai mai kalwa, ni kuma sai inyi muku jagora zuwa gidan. Ahmad yace.
"To shikenan ba matsala" Mai mota ya koma kan titi, sai gamu a ƴan lemo, ta cikin kasuwar ƴan lemo muka shiga. Anata sauke lemo da mangoro a tirela, ga lemo nan buhu_buhu a jibge, ga masu kashin, lemo, gwanda, abarba, a ƙasa sunata cinikayya tsakaninsu da jama'a. Ni dai sai baza idanu nake yi. Wayata ce ta shiga kuka, ina dubawa naga Ba Bakura ke kirana, da sauri na ɗaga.
Ba Bakura ina wuni?" Da sauri Bulama Babba ya dubeni muka haɗa idanu, idanun nashi kallo ɗaya zaka yi musu kasan cewar bai da lafiya. Ba Bakura yace.
"Uwata ya hanya, kun isa kanon ne?"
E yanzu muka iso, ko gida bamu shiga ba ma, ya jikin Ba Baana?"
"Alhamdulillah sai yanzu hankalina ya kwanta, dan inata kiran wayarki bata shiga. Mamanku Hajja Gana ma ta kiraki bata samu layin naki ba. Amman zan sanar mata kun isa lafiya. Jikin Baana sai godiya, India ma su Bulama ƙarami zasu fita dashi domun a dubashi da kyau. In kun isa gida Maman naku zata kira." Hawaye na share, mu kai sallama da Ba Bakura dai dai isowarmu mai kalwa primary school. Wani mutum ne a mashin yai mana jarora yana gaba, motarmu na biye dashi har muka tsaya a bakin wani madaidaicin gida marar fenti. Yawancin gidajen anguwar ma babu fenti. Anguwace mai cike da yamutsi da hargowa, anguwace mai cike da tulin yara, kasancewar anguwace ta masu ƙaramin ƙarfi. Firfitowa mu kayi, Wannan bawan Allah shi ya buɗe mana gidan muka shiga. Ɗakuna huɗu ne a cikin gidan falle falle, sai ban ɗaki da kitchen, da ƴar rijiya a gefe, sai famfo da akayi a wani ɗan waje kamar wajan wanke_wanke. Gidan yasha tails tun daga ƙasa har rabin bango, fari sol, ba ƙaramin haska gidan yayi ba, tsakar gidan bata da wani girma.
"To kunga gidan, sai dai ku kama dukka fa, ku raba biyu biyu tunda ku biyu ne, ga yara maza da mata. Bulama Babba yace.
"Ai babu damuwa Musa dama mu biyun zamu kama. Zubaina ku shiga daga ciki, ko wacce ta zaɓi nata ɗakin. Mu kuma bari muje mu zo. Fita su kayi dukkansu. Zubaina ta lalleƙa ɗakunan ta zaɓi ɗaya. Hajara ma ta ɗauƙi ɗaya, ni kuma na faɗa na kusa da Hajara, dama a tsaye nake a wajan. Gudan daya rage su zulai ne da yara suka shiga. Kayayyakinmu suka jibge mana a tsakar gida, suka fice. Hijabina na rataye a igiya na shiga aiki, kowacce ta ɗauki tulin buhun kayanta ta shigar ɗakinta, ina jiyo ihun kofur Zubaina, ƙanwarta Asiya ce ta shigo da abinci da drinks niƙi_niƙi. Labulaye na kafa, bayan na goge ƙasan tails ɗin ɗakin da tsumma da ruwa. Sai na shinfiɗa babban bargon da nake kwanciya a kai, na shinfiɗa dadduma wacce taci rabin ɗakin. Akwatunana na jera a gefe, kayan kitchen kuma na fita dasu, na jibge a kitchen Alwala na ɗaura tukunna, nayi salla, sannan muka gyara kitchen ni da Hajara, Zulai kuma ta wanke tsakar gidan tas. Zubaina suna ɗaki da jama'arta suna gyarawa, yara sai tsalle tsallensu suke yi a tsakar gidan, abunka da yaro ba hankali. Sai yamma lis na samu kaina, har zuwa lokacin su Bulama basu dawo ba, har yaran Hajara sun soma kukan yunwa, dan ina gani Zubaina ta kira yaranta cikin ɗaki, yaran Hajara da suka shiga ta korosu. Dab Magriba sai gasu sun shigo kici kici da katifu.
Bulama:
Ina shigowa da Yahanasu na soma haɗa idanu. Tausayina fal gurbin idanuwanta, jikina sai yayi sanyi, a hankali nace.
"Yahanasu zo ga katifarki ki kai ɗaki" A sanyaye ta karɓi katifar ta shigar ɗakinta. Na miƙa mata take away ɗaya da ruwan gora. Na shiga da ɗayar katifar ɗakin dana ga Zubaina a tsaye a bakin ƙofar ta ƙume kamar zata dakeni, sai jijjiga jikinta take yi. Ahmad kuma ya shigar da katifar hannunshi ɗakin Hajara, tasu da suka tawo da'ita aka saka a ɗakin yara."
Umman Maryam ya dai naga ranki a jagulene?" Cikin ɗan ɗaga murya tace.
"Ba dole kaga raina a jagule ba. Naga sai wani kallon waccan yarinyar kake yi, ka duba sai da fa ka sallameta sannan ka shigo wajena fa. Wato kafi damuwa da'ita kenan fiye dani da ƴan yaranka da tun tuni suke damuna da tambayarka" Murmushi nayi tare da girgiza kai.
Haba uwargida sarautar mata, waya isa yaja dake a birnin zuchiyata? Ai babu. Kawai dai dan naganta a tsakar gidanne, amman me zan kalla a jikin Yahanasu, yarinyar da a bayana nake goyata, har wanta na goya. Ayi haƙuri a sakko. Yaran fa?"
"Suna ɗakin ƙarshe, sai kuka Maryam take yi mun, sai da na aika Zulai ta siyo musu chixi shine tayi shiru, Mama Rakiya kuma ƙamshi
Asiya sun tafi gidanta." Ledar dana shigo dashi na buɗe, na ware abincin yaran dukka da ruwa nace.
Gashi to a basu nasu suci ko?" Yamutse fuska tayi.
"Ba daɗi nake ji ba, ɗan miƙa musu mana Abban Maryam, su Maryam a ƙoshe suke, sai dai su Anisa da Zulai" Ledar na ɗauka na fice. Yaran na ganina suka shiga tsalle. Maryam na ɗauka nace.
Yaya? Zulai ga abincinkun kuci maza." Na miƙa mata ledar, na ɗan zauna inata sauraren shirmen yaran. Daga bisani na fito. Ahmad da Hajara na samu a zaune a tsakar gida sun shinfiɗa taburma, sai fifita suke yi. Sabida akwai zafi sosai.
Mrs Bukhari ce gidan ƙamshi
[28/07, 12:57 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
15
Zafine ya fito daku ko Ahmad? Yanzu na fito daga ɗakin yaran, akwai zafi gaskiya a Kano, Kaduna tafi daɗi. Kafin in rufe baki sai ga wutar nepa ta haske tsakar gidan tanwar, sai dai kash bamu da fanka."
"Kai dai bari kawai, amman Lagos tafi Kano zafi ai. Munyi sabo da zaman tsakar gidanne dai." Miƙewa yayi, dan har an soma kiraye kirayen sallar Isha. Leƙawa nayi ɗakin Zubaina. Shinfiɗa take a katifa.
Zamu je masallaci, sai mun dawo ko?"
"To sai kun dawo." Tana faɗar hakan taci gaba da aikinta.
Zunaina:
Ina jin fitarsu, na saɓi hijabi har ƙasa na saka, tik nake daga ta ciki babu ko kanfai a jikina, na fito wuf, shigar Hajara ɗaki kenan. Kitchen na shiga na ɗauki wuƙa na fice da sauri. Sai karo nake ci da maza masu zuwa masallaci. Bayan windon ɗakin Yahanasu na tsaya, na shiga waige waige, ƙafa dai bata ɗauke ba, amman babu mutane ta wajan, kasancewar babu kofofin gidaje ta wajan, banga mutum ko ɗaya ya gibta ba. Tono na soma yi da sauri, gabana na faɗuwa, sai da na gama tono tsab na sa hannu na cire hijabina, ba kunya ba tsoron Allah, sai dai cike zuchiyata take da taraddadi layar da boka ya bani na tura a ciki, na miƙe tsaye da sauri na mayar da hijabina. Da ƙafa na tsure ƙasar wajan nasa ƙafa na dandaɓe wajan. Da sauri na zagayo na shiga cikin gida. Hajara na tarar a tsakar gida tana sallah, sai da nayi ras, dan banso kowa ya ganni ba. Wuceta nayi na shige ɗaki, na kunna gawayin kanti, na banka hayaƙin magani, ina jiyo Hajara na tari, na tabbatar Yahanasu itama ta shaƙa, dan sai da na saurara na jiyo tarinta. Sai nabi hayaƙin da turaren wuta, na feffesa turare. Na saka kwalli, na cusa wanda boka ya bani a gabana. Sannan na zuba na abinci. Saina fito da ƙatuwar daddumata tsakar gidan.
"Yanzu nake shirin leƙawa ɗakinki ni naga hayaƙi sai fitowa yake yi. Sai tari muke yi, hayaƙin meye?" A zuchiyata nace.
Kajimun mata da shegen tambayoyin tsiya. A fili kuma nace mata.
Hayaƙin maganin saurone, ɗan kaɗanne ya saura shine na bunka, kafin mu tashi yin bacci sun mutu" Shinfiɗa daddumar nayi a gefen ɗakina na zauna. Hajara ta muskuto tace.
"Wai ni Zubaina wannan Amaryar taki bata son jama'ane? Ni naga ta ƙunshe kanta a ɗaki duk wannan zafin. Kamar tana da wuyar sha'ani ko?" Baki na taɓe na dubi Hajara da take jiran me zance.
Ƙila Bulama ne ya ɓata mata rai. Ai tunda karayar arzikinnan ya sameshi take fishi da kowa. Yanda kika san dan kuɗinshi aka aura mata shi. Amman da lafiya lau muke zaune, yanzu zamannan da kika ga nayi, kiranta zanyi muci abinci ma." Zama Hajara ta kuma gyarawa gulma na cin takashinta, tace.
"Uhmmm ai da yake duk matan gidan nasu masu arziki, da rufin asiri suke aure. Ai yarta ƙawatace Fanda. Nifa nuna mun tayi bata san ma da zancan rashin aikin ba, balle wani karayar arziki. Makira sai ni nayi mata bayani. Nan ta dinga runtuma kuka. Dariyar mugunta na kwashe dashi, harda shewa nace.
Hajara baki da dama. Kema kinsan yana aurenta, gata ƴar uwarshi, saita iya rigani sani ma, kindai san halin mazan. Bakii ji ɗazu tana waya da Baban Bulaman ba muna mota? Duk abinda ke faruwa a gidan ita ke kai musu gulma" Miƙewa nayi naje ƙofar ɗakin Yahanasu nayi sallama. Sai naji tana kusurkusur kamar mara gaskiya, labulen na bangaɗa. Muka haɗa idanu tana tattare wani abu da sauri a baƙar leda. Ƙur na zuba mata idanu, kai da gani kasan bata da gaskiya. Basarwa nayi nace.
Ki fito da abincin naki waaje kici, kema kya sha iska, ga zafi ma a ɗakin. A daburce ta amsa mun da '"To" Na saki labulen na dawo na zauna shiru ina nazarin. To me yarinyarnan take yi haka? Da dukkan alamu wani asirin take ƙunshewa, daman nasan ba banza aka aura mata Bulama ba. Amman sun makara, dan na rigata tashi a bacci, da ita da Bulama duk a ƙarƙashin ikona suke. Fitowa tayi da ƴar daddumarta itama ta shinfiɗa a ƙofar ɗakinta ta zauna, sai janta da hira Hajara take yi, suna cin abinci har su Bulama suma suka shigo. Nan hira ta ɓalle a tsakaninmu, Yahanasu tana gefe tsulum da'ita, ta kasa sakewa, sai Ahmed ke ɗan janta da taɗi jifa jifa, sai dai tayi Murmushi kawai, ni kuma fsrfesun kazar dana baɗe da garin magani na miƙa mata. Hannu biyu tasa ta amshi kwanon.
"Babu dai yawa, abun ɗaukani. Hajara ga naku ke da yara. Asiya ce ta kawo mun." Hajara tace.
"Muna godiya, bari mu dangwali arziki muma." Yahanasu dai murmushi kawai tayi. Ta ci kazar ta sha romon, ta na dai gefe a takure. Daga baya ma tayi mana sallama ta shige ɗakinta. Muma kowa ya watse. Bayan Bulama ya fito daga wanka ne, muka lula duniyar ma'aurata,a ɗakin Yahanasu ya kamata ya kwana, amman sabida maganin da boka ya bani inyi amfani dashine, yasa na riƙeshi a wajena. Muka wayi gari a cikin wannan gida. Gabaki ɗaya daren jiya bacci ya ƙaurace mana sabida jarabar zafi ga sauro. Bayan sun dawo sallah Bulama ya dawo ya kwanta yana ta rawar ɗari, kafin kace mai, sai amai sai suma. Cikin kururuwa na fita tsakar gida ina faɗin
A taimakamun Bulama ya mutu ya barni da marayu, na shiga uku na lalace" Gabaki ɗaya kowa ya fito. Bamu tsaya wata wata ba, Ahmad ya nemo mai ɗan sahu, ni dashi muka wuce asibitin Murtala, shine mafi kusa damu. Cikin gaggawa da taimakon ma'aikatan kiwon lafiya aka shiga dashi ɗakin jinya na maza.
"Zubaina ki samu waje ki zauna. Bari in tsaya a kanshi, kiyi haƙuri" Ahmad ya shiga cikin ɗakin da aka shiga da Bulama. Ni kuma nai masauki a kujeraun dake ajjiye a dogon falon dake kallon ɗakin jinyar maza, ga jama'a nan tsiraru a zazzaune. Kaina na dafe, ni wannan bala'e _bala'en wallahi sun isheni. Dame mutum zaiji da talauci ko da abubbuwan da suke ta faruwa?"
Yahanasu:
Cirko_ cirko aka barmu a tsaye a ƙofar gida. Hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, yanda naga an fitar da Bulama Babba ranga_ranga. Sai Hajara ce ta riƙo hannayena ta shigar dani cikin gida.
"To amman ko babu komai ya kamata ace an tafi dake, tunda ba Zubaina bace kaɗai matarshi ba. Ke bafa a raga ma kishiya ko a ɗaga mata ƙafa. Sai kin tashi tsaye zaki ƙwato ƴancinki bawai ki zauna kishiya na juyaki ba, Zubaina ba daɗi bane da'ita mara mutunci ce wallahi. Bari kiga in kira Abban Anisa inji wanne asibitin suke, in yaso sai ki tafi musu da abun kari in an gama. Kema kya ganshi ki samu nutsuwa, ke inma gado aka bashi, kamata yayi in yau wannan ta kwana gobe wannan ta kwana." Ni dai sai kallon Hajara kawai nake yi yanda take tsara magana. Ita ta kammala kayan karyawa, tea da biredi da wainar ƙwai. Ta zuzzuba komai ta haɗa a basket, sannan ta kira Ahmad ya tabbatar mata suna asibitin Murtala. Ta sanar dashi gani nan zuwa, hankalina ya kasa kwanciya. Ina dai jinsu yanata mata kwatancen ɗakin, daga bisani su kai sallama.
"Yahanasu kije ai kinji duk kwatancen da yayi, in kin kasa ganewa sai ki yi tambaya. Ga lambar Abban Anisa ki kwafe in kin kasa gane ɗakin sai ki kirashi. Ki kintsa maza. Tsintar kaina nayi da bin umarnin Hajara, duk da ni kaina a kan kin kaina inason ganin halin da Bulama Babba yake ciki. Ruwa naja a rijiya na shiga na watsa. Sabuwar shadda ta ɗinkin doguwar riga na saka, na ɗauko sabon mayafi da sabon takalmi na saka, banyi kwalliyar komai ba sai kwalli dana zizara a baƙin idona, dan hankalina sam baya ma tare dani. Ina fitowa Hajara ta shiga kambabani tanai mun kirakin Amare. Murmushin takaici nayi mata kawai, dan nasan babu wani abun a kalla a yaba a tattare dani, sai dai ince Alhamdulillah na gode Allah da ya bani rai da lafiya kuma ya yi ni musulma, mahaddaciyar littafi mai tsarki. Ta bani basket ɗin abincin, sallama nai musu na fice. Da tambaya na hau ɗan sahun da zai sadani da asibitin Murtala, bamu da wani nisa ma. Bansha wuya ba wajan gane ɗakin da Bulama yake kwance. Da siririyar sallama na shiga ɗakin jinyar. A hankali na soma gaishe da marasa lafiya, har izuwa gadon da Bulama Babba yake kwance, idanuwanshi suna kallona. Wata uwar harara Zubaina ta sakarmun tare da jan dogon tsaki, ta kawar da kanta gefe can. Leɓe na cije dan naji zafin tsakin da tayi mun, na tsani tsaki sosai. Nan da nan Bulama Babba ya kawar da kallonshi a kaina. Ahmad ya karɓi basket ɗin hannuna, tare da miƙewa a kujerar da yake, ya nuna mun da hannu.
"Zo zauna nan Yahanasu ashe zaki gane ɗakin?" Kai na ɗaga mishi halamar E, bayan na zauna nace.
Bulama Babba ya jikin naka?" Can ƙasan maƙoshi ya amsa mun da cewa.
"Da sauƙi, ai da baki zo ba, dan bana buƙatarki, wa kika barma yaran kuma da kika kwaso jiki kika zo?" Hawaye cike da gurbin idanuna na miƙe tsaye.
Kayi haƙuri Bulama Babba, dama abincine na kawo muku gashinan, Allah Ubangiji ya baka lafiya yasa kaffarane?" Da sauri na fice bana ko iya ganin gabana. Har na kusa da get na jiyo muryar Ahmad yana kirana, ban juyaba naja tunga na tsaya. Gabana ya iso ya ƙuramun idanu.
"Yahanasu na fahimci babu zaman jituwa a tsakaninki da Bulama,da ita kanta Zubaina, duk da nasan dama Zubaina ba lalle bane ta bada haɗin kai a zauna lafiya ba. Bama ita kaɗaiba, mata bakwa son kishiya sam.Ɗan murmushi yayi dan ya ƙarfafani, kafin ya ɗaura da cewar.
"Na lura da hakan Tun ranar da nazo gidanku. Amman ni da shi ba mu zauna mun tattauna akan hakan ba, duba da irin jarabawar data afka muku. Amman ina mai baki haƙuri a matsayina na wanki, da kici gaba da adda'ar Allah ya karkato hankalin mijinki kema izuwa gareki. Akwai wasu addu'o'i da zan baki,muddin kika lizimci yinsu da ikon Allah zaki zama mai soyuwa a zuchiyar mijinki, duk da na san ke ɗin malama ce, ta yiwu kinsan addu'o'i n a kansu kike, ta yiwu baki sani ba. Ni tun lokacin da Bulama ya Auri Zubaina abokarmu ta samu tangarɗa, kullum a cikin raba hali muke. Shaƙuwa ce ke zaune damu kawai, amman da tuni na yar da Bulama, tunda duk abinda zan bashi na shawara, baya ɗauka, sai