Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
ruɓewa ka yanke a kar. Ana iya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. Daga cikin ku wasu sun kai ma Yahanasu ziyara, sun dawo da kuka, wasu an basu labarin irin rama da duhun da Yahanasu ta sake yi, duk kowa ya shiga tashin hankali. Wallahi _ wallahi tashin hankalin da nake ciki yafi na ku, yafi na Innana, yafi na Bulama. Ban sake yin bacci mai kyau ba tun ranar dana yi tozali da Yahanasu a Dawanau. Wannan hukuncin dana yanke a kanta shine hukuncin daya dace da'ita. Kuma shine zai faru akan duk wanda ya kasa rungumar ƙaddara ya faɗa hidimar shaye_shaye mace ko Namiji. Babu ragiya a tsakanina da duk wanda zai ɓata mana suna ya lalata rayuwarshi, ya saɓi Allah domun wani biyan buƙatarshi. Tun wancan watan malam Rilwanu yace zamu iya dawowa gida da Yahanasu aci gaba da sa mata idanu. Ni kuma nace ya barta ta sake dakuwa tukunna. Iya duka Alhamdulillah ta daku, tasha rubutu, ba dare babu rana adda'a nake mata dan samun lafiya. Jiya malam Rilwanu ya sake kirana yace Yahanasu ta warke sumul kamar ba wannan Yahanasun ba. An kawo mata laka mis ɗin ma, ta fashe da kuka tana ambaton Allah. Alhamdulillah zuwa ƙarshen wata Yahanasu zata dawo cikin iyalanta." Idanu na lumshe ina jin wani irin farin ciki na fisgata. Sai hamdala ƴan uwana suka shiga yi, suna jinjina maganganun Ba Modu.
"In da mai abun faɗe ya faɗa ni kam na gama, ƴan ɗaurin aure suna jirana a waje" Cewar Ba Modu. Hajja ce tace.
"Ina da maganar da nake son isar muku nima, naso ko da babu taronnan in haɗa iya taron cikin gida." Tunda ta soma magana gabana yake faɗuwa.
"Sati biyu masu zuwa in sha Allah ɗaurin auren Bulama Babba, rana irin ta yau. Zai auri ɗiyar wajan Bature Yalewan gidan" Gabaki ɗaya falon babu wanda wannan batu bai jijjigaba, ni kaina na kaɗu da jin wannan batun. Mu yaran gidan mu kai tsuru_ tsuru, matan gidan kuwa kowa ya saki baki .
"Akan wanne dalili zaki ce Bulama Babba ya auri Yalewa, yarinyar data riƙe ita zaki haɗa da Yahanasu su zauna tare? Yarinyar da ta kasa zaman gidan Bature, tana can Yobe tana yawonta kwararo_kwararo. Wallahi baki isa ba Hajja. Ohh yanzu na gano ki shi yasa kike ma mutane gani_gani ko? To wallahi bazai yiwu ba. Modu kana jin abunda wannan matar take cewa ko?" Mama Gana ce ke magana cikin zafi. Ranta har ya gama hargitsewa ta miƙe tsaye. Ya Bagulaji tace.
"To duk da dai baki sanar damu meye manufarki na son haɗa auren Yalewa da Bulama Babba ba. Amman da dukkan halamu yaron ba so yake yi ba. Ni ina ganin in dai baya so da anyi haƙuri an bar yaronnan da matarshi" Ya Innana uwar kawaici tace.
"Akan me zaku ce haka? In akayi haka ai tamkar ba'ai ma Hajja adalci bane. Tana da damar bama Bulama Babba duk matar da take ganin tafi dai dai da rayuwar ɗanta. Fatanmu Allah ya basu zaman Lafiya." Nan fa Mama Gana ta dire a ƙasa tana kuka.
"Ohh sabida anga BaKura baya nan ƙasa ta rufe idanunshi za'a kawo mana rabe_raben kai? To a matsayina na ya a cikin gidannan ina da ƙarfin faɗa aji dole wallahi ko kuna so ko bakwa so. Nari ga na gane take _ taken ki. Tun lokacin da Yahanasu ta faɗa jarabawarnan kike cikin fishi da kowa. Ke kin mance sanda naki ɗan wata ƴar iska ta raba ku dashi ko waya baya iya muku. Ince ba Yahanasun bace tayi uwa tayi makarɓiya wajan dawo dashi saiti ba? Duk abunda ya faru da Yahanasu Bulama Babba da tsohuwar matarshi su su kai mata sila, ita kuma tsantsar biyayya yasa ta ci gaba da zaman. Yanzu daga yaro ya samu dukiya shine Bature yake ƙoƙarin ganin ya shiga tsakaninmu? A lokacin da shi Bulama Babban yace cikin ukun da tsohuwar matarshi ta sashi. Ai a lokacin ya dace Bature ya sadaukar ya ba Bulama Babba Yalewa su je su gwabza da Zubaina, tunda dama duk ƴan duniyane dukkansu" Duk wannan maganganun cikin zafi Mama Gana take fesar dasu. Dukkannin abinda take faɗa gaskiya ne kuma. Hajja ta miƙe tsaye tace.
"A hir dinki Mama Gana, dan kina ƙanwar mijina ai baki isa kin taka ni na ƙyaleki ba. Yahanasun ba sai da ta rasa darajarta bane aka liƙa ma Bulaman ba? Me yasa tun da darajarta ba'a aura mishi ita ba. Sannan da kike zancan Yalewa ƴar iska ce, amman kinsan ba'a taɓa kamata tayi ma iyayenta ƙaryar anyi mata fyaɗe ba ko? Yahanasu kuwa shaye_shayenta taje tayo, ƴan iska abokanta ƴan iska suka tare ta su kai mata fyaɗe. Modu yasa BaKura ya rurrufa aka ba Bulama ita. Dan haka a wannan karon sai ya auri Yalewa ko kuma ya saki Yahanasun" Ƙasa tamkar ta tsage in faɗa nake ji tsabaragen kunyar Ya Innana da Ba Modu. Hawaye sosai Ba Modu yake zubarwa kuka kuwa harda shessheƙa. Abinda ya ja hankalin kowa kenan har hayaniyar ta lafa. Sautin kukanshi ya cika falon tab. Dukkanmu mazan muka isa gareshi muna rarrashinshi, amman sai ɗaga mana hannu yake yi akan mu barshi yayi kukanshi. Mama Gana tana kuka tana faɗin
"Ku barshi ya koka Bulama Babba. Hajja Gana na son kawo rikici da gaba a tsakanin iyalan Modu da BaKura. Kinci amanar ɗan uwanmu, ashe lumbu_lumbu kikai mishi sabida kinsan zai iya haƙura da ke sabida farin cikin danginshi." Hajja ta shigewarta ɗakinta tana fesar da maganganu masu kaifin gaske. Ba Modu ya daure yace.
"Kar kowa ya ɗauki wannan abinda ya faru a matsayin komai. Wannan nasan shine na farko daya taɓa faruwa a wannan zuriyar. Ina mai baku haƙuri. Hajja Gana tana nan a matsayin uwa a cikin wannan gidan. Kuma matsayinta yana nan dam. Aikhairanta zamu kalla ba wannan abun data aikata ba. Nasan a cike take da zafin mutuwar BaKura ta dalilin halin da Yahanasu ta jefa rayuwarta. Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka. Kai kuma Bulama Babba da kaina zan kai kuɗin aurenka zuwa wajan Bature. Allah yayi muku albarka. Mama Gana ki dena kukan ya'isa kiyi haƙuri kar ki sake cewa komai."
"Wallahi tallahi Modu baka isa ka tursasa Bulama Babba ya auri Yalewa ba. Akan wannan lamarin zan iya yin fito na fito da kowa. Na faɗa ma, wannan shine karon farko da mukai gaddama da juna. Kar ka bari in hassala in yi abunda zan ƙarashe rayuwata a firzin." Miƙewa tayi ta fice tana share majina. Komar kowa jira yake yi sai aka soma firfita. Matan duk suka yi shashen iyaye mata, su Aissa kuma suka shiga ciki wajan Hajja. Mu kuma ƙofar gida muka nufa, dan gudanar da ɗaurin auren Ba Modu.
MRS BUKHARI CE[19/08, 9:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 53
YA INNANA:
Sunturi take yi a farfajiyar falonta. Kanta yayi matuƙar ɗaukar zafi sosai. Taji zafin maganganun Hajja Gana matuƙa gaya, har tana ji kamar ba zata iya mancewa da wannan lamarin ba. Wannan ranar ranace wacce ba zata gogu a tarihin rayuwarta ba. Kuma tana ji kamar ƙarshen zaman Bulama Babba da Yahanasu yazo. Ya Bagulaji ce ta shigo jikinta a sanyaye ta dubi Ya Innana wacce idanunta ya kaɗa ya zama jawur dashi.
"Innana kinga wani sabon al'amari da ya ɓullo cikin gidan kuma. Daga rasuwar Ba Bakura al'amura sun soma jagulewa. Ga can Mama Gana ta sake komawa ɓarayin Hajja Gana sai rikici suke yi. Kinsan mama Gana ba ƙanwar lasa bace. Gashi mazan gidan duk suna wajan sha'anin ɗaurin aure. Su Fanna dai da surukan gidan nasa suke kwashe tuwon ƴan ɗaurin Aure. Muje dan Allah mu same su gudun kar ayi ɓatacciya. Gashi hankulan surukan gidan duk ya koma falon Hajja Gana. Ya Innana bata ce komai ba tasa kai ta fita. Ya Bagulaji tabi bayanta har zuwa cikin falon.
"Waye bai san Innana ta gama mallake Modu ba? Hatta Bagulaji sau nawa tasha kawo ƙarar Modu kan fifita Innana da yake yi. Ai barewa ba za tai gudu ɗanta yai rarrafe ba" Itace kalmar data dira a kunnen Ya Innana. Ji tayi data sani da bata shiga falon ba balle har ta ji wannan kaifaffar maganar. Mama Gana tace.
"Amman kin cika butulu Hajja Gana. Zaki sha mamaki kinsan Allah sai Bulama Babba ya saki Yahanasu tunda bashi bane autan maza ba. Ni sai yanzu naji daɗin yanda Zubaina ta dinga hanaki bacci, ke da ɗanki baki da matsayin da zaki kira wayarshi ya ɗauka. Allah ya bamu lafiya" Fuuu Mama Gana ta fita tana ihun kuka. Ya Innana ta ƙura ma Hajja Gana idanu tana mai cike da mamakin yanda dukiya ta rufe mata idanu, har take ƙyashin Yahanasu ta ci wannan dukiyar. Har ta buɗe baki zata yi magana, sai ta tuno maganar bata da amfani kwata_kwata fita kawai tayi. Ya Bagulaji ta biyo bayanta. A tsakar gida suka iske Mama Gana tana burgima. Shigowar su Ba Modu kenan suma, an gama ɗaurin aure, ana kan yin walimar cin abinci. Fanda ta je ta kirawosu, zuwa wannan lokacin surukan gidan sun fahimci inda aka dosa. Sai dai mazajen nasu sun musu umarni da ko wacce ta wuce ɓarayinta.
"Modu Bulama ya saki Yahanasu shine abunda nake so. Wallahi ba zata ci gaba da zama dashi ba, yaje yai ma uwarshi biyayya. "
Bulama Babba:
Dam naji gabana ya faɗi jin furucin Mama Gana. Ba Modu yace.
"Ki dena wannan maganar Mama Gana a tsakar gida gaban yara. Ke sai yaushe zaki girma ne? Ni kaina da kika ga nayi shiru zan ɗau matakin da zai kwanta ma kowa a rai. Ko wacce ta shirya ta koma gidan mijinta. Bulama ka ɗauki Mama Gana ku koma ka kwashi yaran." Wakil ka je gareji ka fito mana da mota zamu yi wata ƴar tafiya. Kai Dala ka je ka sallami jama'ar dake waje." Ni dai gabaki ɗaya sun gama rikirkitamun lissafina. Na ma rasa yanda zanyi. Gashi Ba Modu ya tsorata ni dangane da batun matakin da zai ɗauka, tunda bansan wanne mataki bane. Sannan ina zasu je yanzu? Innalillahiwainnailaihilrajiun Allah ka kawo mun ɗauki ya iyali. Mama Gana ce tace.
"Ga yaranka Bulama wuce mu tafi ka mayar dani gida. Amman kafinnan zaka kaini gidan Bature. Ni dai ko magana wannan na kasa yi. Ina gani su Ba Modu suka fice a mota shi da Ya Innana sai wakil dake tuƙi. Fita motarmu tayi a cikin gidan muma. Na baro yan uwana a cikin tulin baƙin ciki da damuwa. Kai tsaye gidan Ba Bature muka nufa. A ƙofar gida naso tsaiwa amman Mama Gana ta tusani a gaba muka shiga. Abinda muka tarar yana faruwa a gidan yai mun daɗi. Yalewa ce riƙe da akwati tana rantsuwar in suka matsa mata dole sai ta aureni zata iya shiga duniya a nemeta a rasa. Ita me zata yi dani mummuna baƙi dani. Mama Gana dake tsaye a bakin ƙofar shiga ko sallama ba tai ba sai jin maganarta suka yi a bayansu.
"Kinyi dai_dai yarinya. Wake yayin auren dole a wannan zamanin. Kai kuma Bature wallahi ka faɗi ƙasa tim babu nauyi. Oh sabida Hajja Gana ta miƙa maka dukiyarta a hannunka shine kake son ka haɗa auren ɗiyarka da Bulama Babba ko? Kaga in Hajja Gana ta mutu dukiya ta zama ta Bulama Babba shi kuma Bulama Babba sirikinka ne, kaga kuɗin ya koma hannunka. In lissafina yayi dai_dai to kaine kai ma Hajja Gana famfo, ta sauke mana atilarar rashin arziki a gida." Nan sa in sa ya ɓalle a tsakankanin Ba Bature da Mama Gana, sai ni ne na zama mai rarrashinsu. Sai da tayi ma kowa tas sannan ta fita, matan gidan da Yalewa babu wanda yace komai.
"Ba Bature ayi haƙuri. Rikicine sosai ya ɓalle a gidan, ni kuma tace in rakota bani da ikon yi mata musu. Kuma Ba Bature tunda Yalewa bata son aurennan, nima ba so nake yi ba. Ni ina ganin ayi haƙuri kawai zai fi alkhairi. Sannan Ba Bature dan Allah ka samu Hajja ka tausheta, yau tayi maganganu a gidan marasa daɗi".... Katseni Ba Bature yayi ta hanyar cewa.
"Fice mun a gida kaji Bulama Babba, ba dai kafi fifita ƙanin mahaifinka sama da ƙanin mahaifiyarka ba? Ka fifita ƴar shaye_shaye sama da Yalewa" Ban bari ya ƙarashe ba na fice da sauri a cikin gidan, idanuna cike tab da ruwan hawaye, na fahimci so suke su haukatani, kowa sai garani take yi kamar tayar mota. Mota na shiga muka kama hanyar Yobe" Tun daga Damaturu Mama Gana take jaraba har muka iso gida na sauketa. Ban ko shiga ba na juya na nufi gida. Ɓarayin Ahmad na isa dan in karɓi key. Hajara ce ta miƙa mun key ɗin na wuce ɓarayinmu ba tare da yaran sun biyo ba. Sallah nayi da shigata, ɗakin dana rufe na Yahanasu na buɗe na shiga ina ƙare ma ɗakin kallo yanda ya tsaru sosai. Ba tarkace aka cika a ɗakin ba, amman komai yana kan tsari da matsuguninshi mai kyau. Bakin wadrope na isa na wangale murafan wadrobe ɗin na shiga kallon kayayyakin dana siya na loda mata a cikin wadrope ɗin. Tun daga kan atampa zuwa leshi, material shadda, lafayoyi, dogayen riguna ƴan yayi iri iri. Wasu kayayyakin ma ɗikkakku na sai mata irin ɗinkin hajiyoyinnan. Naci burin Yahanasu ta samu lafiya ta dawo mu shimfiɗa sabuwar rayuwa mai ni'ima in riritata taji daɗin aure, wahalar hidima dani da yara da tai ta yi in fanshe mata. Duk a cikin wannan hidimar da tai ta fama dashi, har muhalli take ta ƙoƙarin taga ta gina mana duk dan asirinmu ya rufu. Na tuno sanda take shiga ƴan gwanjo ta tsinto kaya ta siyo mun dani da yara. Na sake tuno sanda nace mata in nayi kuɗi zata ji daɗi ita zan soma siyama mota kafin ma in hau. Kuma na cika mata alƙawarinta wannan motar da nake hawa tatace, da sunanta na siya, kamar ta san mai zai faru tace. "Allah yasa in kayi kuɗin ka barni in mora, ƙila ma tare da Amarya zamu tare a sabon gida, koma ta rigani tarewa." Ya ilahi ka kawo mun mafita. In sha Allah in ta dawo ta samu lafiya, zan kaita umara in kaita aikin Hajji ta sauke farali itama. Kuma aurena da Yahanasu babu wanda ya isa ya kashe mun shi, ni da ita mutuwa ce kaɗai zata iya rabamu. Wayata ce ta shiga kuka a ajjihu. Ina zarowa a ajjihuna naga Hajja Gana ce kira na. Sai da gabana ya faɗi ras kafin na ɗauki wayar. Kuka take yi sosai, kukan da take yi a yanzu bata yi kwatanshi a rasuwar Ba Bakura ba. Cikin shessheƙa tace.
"In dai ni na tsugunna na haifeka, to inci darajar naƙuda da rainon ka da nayi. Zan baka umarni ka saki Yahanasu, kar ka ce zaka yi mun musu dan zan iya yima baki a kanta. Naji ɗiban albarkar da ka raka Mama Gana tayo a gidan Bature. Ashe zaka iya rakota ta zazzageni nima? To yayi, ka sani aurenka da Yalewa babu fashi. Ina jiran ka ka kawo mun takaddar sakin Yahanasu"" Kaina ya shiga jujjuyawa dani, duniyar tai mun zafi da duhu. Allah kawai nake ambato dan shine abun ambato. Idanuna na lumshe wasu hawaye suka zubo mun mai zafin gaske. Sallama na jiyo anata dokawa, da ƙyar na lallaɓa na fito falon. Ahmad na gani a tsaye da basket na abinci. Ganin halin da nake ya girgizashi ainun. Da sauri ya iso inda nake.
"Lafiya Bulama rasuwa akayi ko me?"
Ahmad rayuwata Hajja take neman ta raba ni dashi. Ahmad kaji fa wai sai na saki Yahanasu. Kuma umarni take bani. A cikin masifa take son ta jefa ni Ahmad, tace zata mun baki in na ƙi sakinta. Wannan jarabawar da nauyi take." Zaunar dani Ahmad yayi a kujera yace.
"Bulama ka kasance mai dauriya. Ka nutsu kai mun bayanin menene yake faruwa. In yaso sai mu je mu samu Mama mu yi mata bayani. Ni da ita zamu je mu samu Hajja mu yi mata magana" Cikin haki na bashi labarin duk abubbuwan da suka faru, na ɗaura da cewa.
Yanzu haka shi kanshi Ba Modu yace zai yanke hukuncin da zai ma kowa daɗi. Bansan wanne irin hukunci bane. Kuka Ba Modu da Ya Innana suke yi suka fita. Ahmad bansan inda zasu je ba. Ita kanta Mama Gana tayi kuka yau sosai. Ba Bature ne yake son wargaza mana kan gidanmu, sabida dukiyar da Ba Bakura ya rasu ya bar mana muka gada."
"Ya'isa haka Bulama, na fahimci abubbuwa sun kwaɓe ba lallai a halin yanzu lallami ko aike yayi tasiri ba. Duk da haka ba zamu zauna ba. Ga shawara me zai hana a halin yanzu tunda a cikin fishi da dokin naƙi take, ga takaba tana yi, ga abubbuwa da suka faffaru a baya. Ka saki Yahanasu saki ɗaya, in yaso daga baya ka mayar da matarka ta dawo maka. Nasan zaka ji nauyin abun. Ina guje maka fishin mahaifiya, ga baki da tace zata yi maka. Yanda Ba Bature ya jagwalgwala al'amurannan zaiyi wuya mu samu abunda muke so..."
A'a Ahmad mu nemi wata mafitar rabuwa da Yahanasu gangancine Babba." Ahmad cikin fishi yace.
"Kamar yadda bijire umarnin Hajja yake da haɗari babba ba. Bulama duk wannan nasan bazai wuce sanadiyyar mutuwar Ba Bakura da Hajja take tunanin halin shaye_shaye da Yahanasu ta shiga shi yai silar mutuwar mijinta. Ai mata uziri ba lallai ta fahimci komai yanzu ba, iyaye ka sani a kullum duk abunda kaga sunyi ba suna yi dan son zuchiyarsu bane, sanmu ne yake sawa su yi wannan abun. Ka saketa kawai ta samu kwanciyar hankali in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Bani wayarka bari in kira Ba Modu mu tattauna ban fito da tawa wayar ba." Wayata