Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
waya.
"Duk abinda kika girka mun ai mai daɗi ne, na baki wuƙa da nama ki yi duk yadda kike ganin kin soni dashi. Rayuwata da taki a waje guda suke. Zan kira ki dana shiga Lagos I love You" ƙit ya kashe wayar ya barni da sakakken baki, hawaye sai makanta ganina yake yi, ni kaina bansan kukan me nake yi ba.
"Ke ki shiga ki fito da kwanukan dana karya, sannan ki fito da ledar kayanki, ki jirani a bakin get zaki buɗe mun, inason in shiga cikin gidan." Nan ya fito daga cikin mota ya nufi cikin gidan ni kuma ya barni da sakakken baki.
Alh Liti:
Yana tafe yana wani murmushin mugunta, hannu yasa da karfi ya tura ƙyauren da zai sada shi da barayin iyalan nashi. Kasancewar gidan tabkekene mai yalwar tsakar gida babu ma wanda yasan da shigowarshi. Tun daga nesa ya hango Jamilu ya cukume Fa'iza suna rikici Hajiya Kubra ce a tsakankaninsu tana ta kiciniyar kwatan Fa'iza a hannun Jamilu. Nabila tana gaban murhu tana haɗa wuta, Zakiya kuma wankin kayan yaranta take yi, da goyonta a bayanta. Ƴan matan gidan kuma sun fita jidon ruwan da ya zame musu tamkar idaba domun babu fashi kullum sai sunyi, wasu daga cikin ƴan matan suna waje suna taɗi da samarinsu, wasu kuma suna zazzaune a tsakar gidan a hautsine. Matasan gidan kuwa masu fita nema sun fita, masu fita bin yawon majalisa suna can, ƴan maula sun tafi sana'ar tasu. Halifa ya fita kasuwa saida maganin basir.
"Jamilu ka saketa nace dan ƙundun ubanka baka da hankali ne zaka cukumeta kana tuhumarta?" Cewar Hajiya Kubra kenan. Jamilu yace.
"Tare da abokina suka kwana a ɗakunan hotel ɗin cikin lingun gidansu Mafi fa, waye bai san Zazu ɗan iska bane bashi da aiki sai na ɓare mata. Dan ubanta tun a wajan nayi mata maganar meya kaita ɗakinshi shine take mun rashin kunyar data saba." Hajiya Kubra data saba da irin wannan kes ɗin in dai akan yaran gidanne tace.
"Yanzu Fa'iza kema bin mazan kika soma bakya ko jin tausayin mahaifiyarki kullum in tayo kiran waya a cikin yi miki nasiha take, ashe bata isa dake ba ko?" Cikin rashin kunya da tsiwa irin ta yaran da idanuwansu ya buɗe suka san maza tace.
"Kashe kaina zanyi to Hajiya, a gidannan ko asibiti ba'a kai mutum a duba lafiyarshi, zancan abinci ma ba'ayi sam dan wallahi abincin gidannan bashi da maraba da guba. Sutura daga shekara sai shekara akeyi mana, wanne namijin ne zai kulaka a wulaƙance, ga kuɗi a gidan ubanmu amman kuɗin lukudi" Alh Liti yace.
'"Kinci abu kazan ubanki shegiyar yarinya" Take kowa ya sha jinin jikinshi, takalmin ƙafarshi ya cire ya nufo su, daga ita har Jamilun darewa suka yi, suka ari na kare. Da mugun gudu ya bisu har ƙofar gida yana kutuntuma manya_manyan ashariya.
"Ƴan iskan yara, na haifa sun zame mun masifa da jaraba" Yafi minti biyu yana ƙunduma zagi. Harya juya zai shige cikin gidan, ya hango su Barira da Aina'u suna taɗi a dakalin kusa da gidan nasu. Faram_fararam ya isa wajan da takalminshi a hannunshi. Da samarin da yaran nashi duk suka miƙe tsaye.
"Aurensu kuka zo yi, ko rage lokaci kuke yi?" Mai ƙarfin hali daga cikinsu yace.
"Aurensu muke son yi Alh" Alh Liti yana zazzare idanu ya mazarin tsire yace.
"Nan da kwana bakwai ku tawo da sadakinku a hannu, bayan sallar isha za'a ɗaura muku aure dasu. Sai ku sanar ma magabatanku ku yi shiri. Ba'a akwatin aure a gidana, a madadin akwati zaku yi musu kayan ɗaki, da gara. Ni su zan baku gayatan ɗinsu da an ɗaura aure su fito ku tafi. Su waye iyayen naku?" Suna soshe_soshe suka yi mishi bayanin kansu, duk yasan iyayen nasu. Yarane na talakawan anguwa masu lallaɓowa suna son haɗa zuriya da Alh Liti ko banza komai daren daɗewa zai mutu, kuma za'ayi rabon gado, matayensu Allah kaɗai yasan abinda zasu mallaka. Alh Liti ya kora yaranshi gida suka shiga ya rakasu da gudu har ciki. A cikin wannan zage_zagen ya saki Zakiya.
"Ayirirririiiii Alhamdulillah Allah na gode maka daka kawo mun ƙarshen wannan wahalar, ku kuma inai muku fatan alkhairi. Yara Allah shike riƙe dasu dama. Yaron bayanta ta kwance ta kwantar dashi a ƙasa ta shige ɗakinta tana kukan da ya zame ma mata al'ada, duk yanda su ka kai da son saki, da zaran anyi musu sai su fashe da kuka.
"Aikin banza aikin wofi, tunda baki da mutunci ki tattare inaki inaki ki bar mun gidana. Ke Kubra ɗauki yaronnan ya rayu a tsakankanin cinyoyinki da kafaɗun Nabila. Yarannan ƴan matan su goma ne cib ko?" Hajiya Kubra tana kuka ta ɗauki yaron Zakiya ta rungume, tama kasa amsa tambayar da Alh Liti yayi mata, har sai da ya daka mata uwar tsawa.
"Ba magana nake yi dake ba, kike faman yi mun kukan iskanci ba"
"E e su goma ne" Ta amsa a kiɗime dan tasan ba ƙaramin aikinshi bane ya tsinkata a gaban yara ba.
"Duk su fito da mazaje sati mai zuwa zan aurar dasu, in basu da samarin kuma, zan bada su kyauta ga ƴan ciranin da muke sallah dasu, na faɗa muku dan haka su zauna cikin shirinsu daga yanzu zuwa sati guda." Cikin kuka Hajiya Kubra tace
"Alh kaji tsoron Allah ina jiye ma ƙarshen rayuwar......."
"Dakata Kubra, baki faɗama iyayenki suji tsoron Allah ba, sai ni kike faɗama jin tsoron Allah? Da kina jin tsoron Allah bazaki butulcema mai ƙaunarki da gaskiya kibi son duniya ki zaɓeni ba. Alhalin dashi nazo na tarar kuna soyayya. Duk matar da zan auro son duniya ne yasa ta aureni ai" Yana gama faɗar haka ya wuce fu ya barsu a wajan suna jimami.
Zubaina:
Ina tsaye naga shigowar Alh Liti fuu kamar kububuwa da sauri na buɗe mishi get ya fice da mugun gudu fuuu" kwanuka da ledar kayana na ɗauka na shiga cikin gidan. A tsattsaye na samesu suna ta jimami. Tambayarsu nayi meke faruwa. Rashida ce tace.
"Anty Zakiya Baba ya saki. Kuma nan da wata uku zaki ga ya sake auro wata matar. Wannan abun kunyar mu da wanne zamu ji?" Tana kaiwa nan ta fice a gidan tana faɗin.
"Gara naje gidan abincin Mari in huta da takaicin cikin gidannan namu, Allah ya ɓullomun da bazawari dana gama idda ya aureni. Jikina a sanyaye na ajjiye kwanukan abincin Alh a wajan wanke_wanke har zan shiga ɗaki Nabila tace.
"Ga abincinki can a rufe ki je ki ɗauka. Sannan ki dinga fitowa cikinmu kina ɗan hira kar ciwon zuchiya yai ajalinki ba tare da kowa ya sani ba. Muma da haka duk muke zaune a gidannan. In kaje ganin gida aita ma tambayar ciwo kayi ne. Ciwon cikin gidannan ai baya warkewa har sai ranar da zaka karɓi takaddar sakinka a hannunka. Ni dai bance komai ba na juya na ɗakko kokkona da kulikuli na shige ɗaki. Kaina na haɗa da guiwa na shiga rera kuka, ina cikin kukan sai ga kiran Mama ya shigo wayata"
Bulama Babba:
Ina tsaye a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Yahanasu, babu nutsuwa a tattare dani sam. Nafi minti talatin a tsaye, jama'a sai kai kawo suke yi a cikin ɗakin, wasu su shiga, wasu su fito, a haka Ahmad ya dawo. Ledar kayan ya miƙo mun
"Ka kai musu kayan a samu a sake mata ta rabu da wannan kayan dattin?. Bance mishi komai ba na shiga ɗakin a katange gadon Yahanasu yake, da halama har zuwa lokacin dubata akeyi, a gefe na tsaya nayi musu magana.
"Malam ko zaka taimaka mana wajan sake mata kayan nata nauyi gareta tun ɗazu muke kiciniyar saka mata mun kasa, dan transpa zamu rubuta muku ma yanzu, mu mun gama namu. A rikirkice na isa bakin gadon da Yahanasu take kwance, fuskarnan tata tayi fiyau da'ita, taji ciwo sosai a fuskarta, har gefen hancinta naga bandeji. Da taimakon wannan likitar mace na sake ma Yahanasu kayan jikinta, sauƙinta ma gashinta bai jiƙe ba. Wannan likitar ta dubeni tace.
"Ina mai baka haƙuri cikin dake jikinta an rasa shi. Sannan nayi maka batun Transpa ko? Zamu turaku asibitin DAWANAU ne, ka biyo ni muje zan ɗanyi ma bayani kaɗan." Dam naji gabana ya yanke ya faɗi, zargina ya sake tabbata cewar da jinnu Yahanasu taci karo suka jirkita mata ƙwaƙwalwarta. Take zufa ta shiga yayyanko mun, ƙafafuwana da harshena su kai mun nauyi, na kasa tafiya, haka zalika na kasa furta ko wacce kalma, idanuwana suka kawo ruwan hawaye, sai ambaton Allah nake yi kawai a cikin zuchiyata wacce take bugawa"
"Bawan Allah kayi haƙuri, ka biyoni inyi magana da kai, kafin ka karɓi takaddar transpa" Naji wannan likitar dana manta ma ni take jira tace. Bance komai ba na bi bayanta ina waigen Yahanasu har sai da na fice a ɗakin tukunna. Ahmad yana ganinmu ya taso ya riƙe hannuna. Baice mun komai ba, nima bance mishi komai ba, mu kaita bin likita a baya har izuwa ofishinta.
"Ku zauna ga waje" Ta nuna mana benci, bani da guiwa haka na daure na zauna na ƙurama ƙasa idanu.
"Kamar yadda dai na faɗama shine, cikin dake jikinta ya zube, sannan tana cikin wani irin hali a sakamakon shan miyagun ƙwayoyin maye ta samu taɓin hankali, kuma bincike ya nuna mana magani tasha mai ƙarfi ya salwantar mata da cikinta. Amman bai kamata a matsayinka na mijinta ka kasa kula da'ita ba harta faɗa ƙangin shaye_shaye. Ko ma naga shaye_shayen ya zama tamkar ruwan dare ga matan aure. A cikin sati biyu mun samu keses ɗin matan aure masu shaye_shaye bakwai harda matarka ta takwas, duk mun aike dasu dawanau, uku daga cikinsu an basu gado, huɗu kuma suna zuwa karɓar magani." Ajjiyar zuchiya likitannan ta sauke, ni kuwa in banda rawa babu abunda jikina yake yi, kaina kamar zai tarwatse haka nake jinshi, duniyar baki ɗayanta juyawa take yi dani.
"A'a likita bana jin Yahanasu zata faɗa ƙangin shaye_shaye kamar yadda kika faɗa, ni nafi alaƙanta wannan lalurar tata da shafar aljanu amman ba shaye_shayen muyagun ƙwayoyi ba, meye matsalar Yahanasu da har zata yi ta'amali da kayan maye? A baya ma da abubbuwa da dama suka faru da'ita bata sha komai ba, sai yanzu da take cikin walwala da farin ciki." Ahmad ne yake wannan maganar a kausashe, har suna shirin yin rikici da likitan.
"Kana nufin zaka nuna mun aikinane, ko kana nufin bansan me nake yi bane, waye ma kai a wajanta da zaka hayayyaƙomun? Kabar mijinta yace wani abu mana" Ahmad ya zabura zai mayar ma da likitarnan amsa, nayi saurin cewa.
A'a dan Allah Ahmad. Muyi haƙuri muje dawanau ɗin a duba ta, amman ba wanna sa'insar ba. Likita kiyi haƙuri, a bamu takaddar transpa ɗin, ni dai a iya sanina in banda lakasera babu abunda Yahanasu take sha Dr, kullum sai ta sha wannan lakasera" Zama Ahmad yayi sai muzurai yake yi, ita kuma wannan likitar ta shiga rubutu a wata ƴar takadda. Takaddar ta miƙomun tare da katin mu.
" Wannan lakasera da kake magana akai, ƙwaya suke narkawa a ciki suita sha hankalinsu kwance, yanzu mai gari ya waya? Ƙwaƙwalwarta gabaki ɗaya ta jirkice. In kuka je DAWANAU ku nemi Dr Halima ta dubata, ku sanar da'ita Dr Ruƙayya Shehu ce ta turo ku. Zan kirata ma in sha Allah kafin ku isa. Zaku biya kuɗin gado, da kuɗin gwaji kafin ku wuce. Sannan ina mai baka shawara kai a karan kanka ka yi tunani da kyau, shin baka taɓa kama matarka da wata ƙwayar magani, ko kwalbar maganin yara ba, iyakar wannan lakasera kawai ka taɓa kamawa tana sha kullum? Da sannu ƙila ka tuno wani abun. Ga takaddar biya nan kuje ku biya" Godiya nayi ma likitannan muka fito.
Ahmad ka je ka biya kuɗin, ni kuma bari in sakata a cikin ɗan sahu kafin ka fito" Ahmad ya bini da idanu yana son ya karanci yanayina. Da sauri na wuce ɗakin da Yahanasu take kwance. Bacci_bacci ido biyu na sameta, tana ɗan surutai sama_sama bana iya gane abunda take cewa.
Yahanasuna kin farka ne? Na faɗa a hankali, kallona tayi da idanuwanta da suka rine suka zama wasu kala.
",Na farka, naganmu a jeji me muke yi ne haka? Ni tsorona ma ɗaya kar zaki ya cinye mu" Da sauri nasa hannu na rufe mata bakinta hawaye na shirin zubo mun, da ƙyar na yaƙesu basu zubo ba, na shiga dube_duben ɗakin ko wasu na jinmu, amman kowa harkar gabanshi kawai yake yi. Miƙar da'ita nayi tsaye na saɓa hannayenta a kafaɗata na tallafi ƙugunta sosai. A hankali muke tafiya, tana sulalewa ina tarota, wata nurse ce ta taimaka mun muka kai Yahanasu har cikin ɗan sahu. A wajan zaman direba muka tarar da Ahmad yana jiranmu. Haka muka nufi hanyar Dawanau babu mai cewa da kowa komai hankali da nutsuwata basa tattare dani sam. Adda'a nake yi Allah yasa ba dai_dai bane abinda Dr Ruƙayya ta faɗa akan Yahanasu. Ɗan sahun mu har cikin harabar asibitin Dawanau muka shiga da'ita.
"Bulama ina ganin ka zauna bari in soma shiga ciki in kira nursses su taimaka mana, ina zuwa ko?" Kai kawai na ɗaga ma Ahmad, ina zaune ina tunani Ahmad suka iso gabana ban sani ba.
"Malam ka fito mu shigar da'ita ciki" Naji muryar wata mace. Sai lokacin na ɗago kaina wanda yake sarawa na kallesu, a sanyaye na sakko daga cikin ɗan sahun. Ni da wannan nurse muka kama Yahanasu ta gefe da gefe zuwa cikin asibitin. Marasa lafiya mu kaita wuce wa, har zuwa wani babban ɗaki na majinyata mata. Babban abunda ya tsoratar dani, bai wuci yanda na ga ɗakin cike da mata ba, wasu ma hannayensu ɗaure da kaca an sagale a jikin gadajen nasu. Wasu na bacci, wasu kuma suna shirme, harda masu zage_zage. Take ruwan jiri ya ɗebeni nayi kata_kata zan zube Ahmad yayi saurin taroni. Gam ya riƙe ni yana faɗin.
"Ka mallaki kanka mana Bulama meye haka? In sha Allah ba abunda yake damun Yahanasu daya danganci taɓin hankali, mu basu dai dama su gama bincikensu, zasu sallame mu ne. Zaunar dani yayi a farar kujerar roba, na zuba ma Yahanasu ido tana kwance a gadon, bakinta yana motsi amman idanuwanta a rufe suke.
"Dan Allah muna neman Dr Halima ne. Dr Ruƙayya ce daga Asibitin Murtala ta turo mu nan." Ahmad ne yake magana da wannan nurse data taimaka mana.
"Okey kai ka biyo ni in kai ka office ɗinta, yanzu ma zata tafi gida dan night tayi. Amman muje, shi sai ya zauna da'ita. Ina jiyo su suna tafe tana tambayarshi mun taɓa zuwa nan ne. Ni dai tagumi na gasa ina kallon fuskar Yahanasu kawai. Wayata ce tayi kuka, da ƙyar na zarota daga ajjuhuna. Ba Modu ke kiran wayar tawa, gabana ya faɗi ras. Cikin mazantaka na ɗaga wayar tare da karawa a kunnena.
Assalamu alaikum barka da rana Ba Modu" Ya amsa mun sallamata a sake
"Yaya jikin Yahanasun, Innana ta damu da yawa, na shiga ɗaki na same ta sai aikin kuka take yi, kasan mata da rauni. Shine dai nace bari in kira ka in Yahanasun ta farka a bata wayar taji muryarta" Cikin dauriya na ƙwaƙwalo murmushi nace.
"Bata farka ba, anyi mata allurar bacci ne, sai gobe zata farka. Jikin da sauƙi sosai Ba Modu"
"To to shikenan, su Aissa suna hanya tun wuri duk inda suke ma sun kusan isowa, anata kiran wayar tasu ma bata shiga." Nan dai muka rabu lafiya da Ba Modu. Ina ajjiye wayar Ba Bakura ya kira ni. Shima yadda nace da Ba Modu haka nace dashi muka yi sallama. Ahmad ne ya shigo shi kaɗai, dubanshi nayi nace.
Yaya dai Ahmad, ina Dr Haliman take na ganka kai kaɗai?" Ahmad yace.
"Uhmm Dr Halima ta tashi a aiki Bulama, sai ƙarfe shiddan yamma zata dawo bakin aiki, amman akwai nursses ɗin da zasu kula da ita Yahanasun kafin ta dawo. Ina ofishinta ma Dr Ruƙayya ta kirata tayi mata maganarmu. To ta dai ce zata biyo ta ganta kafin ta wuce." Yana cikin yin magana wata farar dattijuwa ta iso bakin gadon da muke.
"Wannan itace Yahanasun ko?"
"E Dr itace kin ganta" Ƙur ta zaba ma Yahanasu idanu, ta matsa kusa da'ita ta gwale mata idanu, tare da juya kanta ya dawo gefen dama.
"Allah ya bata lafiya, zuwa ƙarfe shidan yamma zan dawo, zan duba ta in sha Allah. Iyalaina suna jirana a gida, tun 8 na safe ya kamata in tafi gida amman nice har goman safe. Amman ƙila har in dawo ma bata farkaba, ƙwayar data sha mai ƙarfin gaske ce, ina tunanin allurar doki ma tai ma kanta gaskiya, dan shi ke zaburar da ƙwaƙwalwa kai tsaye, ba kamar laka mis ba. Ba nan kusa zata sake ta ba. Ni zan tafi, nursses zasu dinga zagayowa dubata. Sannan a samo mace da zata zauna da'ita, sabida ward ɗin mata ne. Ahmad ne yayi mata godiya har yana rakata.
"Bulama bari in je gida in dawo, dan nasa Hajara tayo girki, ta dafo ruwan zafi. To zanje in tawo da abincin, itama Hajaran sai tazo ta zauna da ita Yahanasun" Har Ahmad ya fita sai kuma ya dawo.
Ya ka dawo Ahmad?"
"Bazan iya tafiya in barka a wannan halin bane Bulama, na kira Hajara zata kamo hanya." Wata nurse ce ta ƙaraso inda muke tace.
"Dan Allah ku je daga waje, maza basa zama a ɗakinnan in ba masu dubiya bane" Hannun Ahmad na riƙe muka fita waje.
Mrs Bukhari ce
[11/08, 7:03 p.m.] +234 708 194 6843: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B