MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   3 / 67

6K to 9K   out of 198.3K words

da rai, da ɗanye zasu cinyeshi." Mahaifin matashin da yayi ma Yahanasu fyaɗe yace.
"Ranka shi daɗe, maganar gawar yaron, a taimaka mana muje asibiti mu ɗauka, ayima yaronnan sutura. Ko a yanzu yaga aya, tunda da yanzu yana cikin makwancinshi, mutuwar wulaƙqnci da ƙasƙancin da yayi ma ya'isa, mu kammu dama ya riga ya zame mana ƙarfen ƙafane, ni bana jin takaicin mutuwarshi sam, na dai fi son ayi mana alfarma a bamu gawar mu binneta, abunda ya shuka shi zai girba ba, kuma duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka." D P O yace.
"Zaku iya ɗaukar gawar ɗanku, tunda likitoci sun gama bincike, maniyyin da aka samu a jikin yaron, maniyyin ita yarinyar da yaima fyaɗene, ƙwararru sun auna. Da ƙyar aka samu yarinyar ta tabbatar ma mai jinyarta, cewar ita ta kashe yaron. Babu wata doka da zata yi aiki akai, sabida a cikin ɗimuwa da fitar hayyaci take, babu wata doka da zata hau kanta, domun a hanyar ceton nata ran ne ta kashe taƙadarin ɗanku dake neman tata rayuwar, kuma duk mutumin da yayi kisa domun kuɓutar da kanshi daga kisa, bashi da laifi, kamar yadda ba'a shari'a da mahaukaci, haka ba'a zartar da hukunci akan ire_iren su Yahanasu. In kuma kuna ganin a turaku kotu to" Cikin sauri iyayen wannan mamaci suka ce, babu wani kotu da zasu je, su sun yafe, kuma a ta ya su roƙon gafarar iyayen Yahanasu. Haka suka fita harda godiya a hakanma.Da haka wannan zancan ya mutu mus, ba'a ƙara tado dashi ba. Lokaci yaita tafiya cikin damuwa da zulumi. Babu laifi Yahanasu tana samun sauƙi, kuma ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai ta zama shiru_shiru bata son magana sam. Ranar da iyayen Nasiru suka zo dubata, kasa magana tayi dasu sai hawaye, Nasiru ya tausaya mata ganin yanda tai wata iriyar muguwar rama, kamar ba Yahanasu ba. Kwananta goma a asibiti aka sallameta, suka dawo gida, da jikin nata ya ɗan yi ƙwaɓi sai ta soma yin azumin daya wajabta a kanta na kisan kai da tayi.


Wannan kenan.




YAHANASU:
Ina kwance akan gadon Ya Innana ina karanta littafin addu'o'i, Ya Innana ta shigo da sallama, ita da Fanna. Waje ta samu ta zauna a kan gadon, Fanna kuma ta zauna a kujerar dake cikin uwar ɗakin.
"Yahanasu, abunda zan sake somawa dashi shine. Haƙuri da yarda da ƙaddara. Bana jin daɗin ganinki a cikin wannan yanayin. Sai ciwon damuwa ya kamaki ai. Jiya Yaguji har ɗakinnan ta shigo ta sameki, amman kinƙi ce mata komai. Kiyi haƙuri abunda zai faru ya riga ya faru, saimu rungumi ƙaddara baki ɗayanmu, ni na fiki jin zafin yadda rayuwa tayi dake, amman ki sani hakan ba wai yana nufin ƙarshen rayuwarki ba ne. Jibi akwai taro da Ba Bakura ya tara, duk ƴan uwa za'a taru. Abunda ya tsayar da Mama Gana kenan bata koma ba. Maganar janye aure da iyayen Nasiru suka yi, suka ce a dakace su kuma. Karya baki tsoro, rayuwarnan cike take tab da ƙalubale, kiyi haƙuri, hakan karya dame ki, in ma rasa Nasirun ki ka yi, Allah zai ɓullo miki da mafiyinshi, kuma in dai har ya gujeki, ki sani dama ba masoyinki bane, sai ki gode ma Allah da ya sa akai walƙiya." Murmusawa nayi na dubi Ya Innana. Ni dama aure da sha'anin maza duk ya fice mun a raina. Inason ni kaina a bani lokaci in samu cikakkiyar nutsuwa tukunna. Mikin dake zuchiyata dai har abada bazai gogu ba nasan wannan.
Ya Innana, na karɓi dukkan ƙaddarar da rayuwa zata zo mun dashi a gaba ma. Allah shike tsara mana rayuwa ba mu ba. Duk yanda kuke so haka zanyi. Maganar dakatar da maganar biki da iyayen Nasiru suka yo aike kuma. Ya Innana, ni a tawa fahimtar iyayen Nasiru basa son ya Aureni ne, shima kanshi ya dena sona, ƙila dama ba son gaskiya yake yi mun ba, gangar jikina kawai yake so. Sun mance cewar babu wani bawa dazai iya tsallake wani abun da kanshi, face wanda ubangiji buwayi gagara misali ya tsallakar dashi ba. Ni a sanar da iyayen Nasiru cewar na haƙura na janye gabaki ɗaya. Tun kafin su su ce muku hakan, dan nasan zaku ji ciwo gaya. Ku taya ni da adda'a Ya Innana, ina cikin damuwa mai yawan gaske, zuchiyata zafi take yi mun" Ya Innana ta dubeni da kyau tace
"Naji daɗi da kika fahimci inda surukanki suka dosa, janyewarki, da danganarki ta matuƙar faranta mun. Kuma nasan lallai turbar haƙuri da juriyar dana ɗauraku akai, lallai kun hau. Na sani na baku tartibiyar tarbiyya da akeson ko wacce uwa ta baiwa ƴaƴanta. Mun baku ilimin Arabi da Boko. Yahanasu ni kaina zanfi son ki manta da Nasiru ki shiga sabuwar rayuwa. Allah yayi muku albarka duka" Da Ameen" muka amsa ni da Fanna. Haka dai lamurana suka ci gaba da tafiya. Duk wani jin daɗi da ake ganin jin daɗine, ni bana sonshi, bana kallonshi ma a matsayin jin daɗi. Bana son hayaniyar kowa, kuma ban cika son fitowa in haɗu da jama'a ba, tsoron kowa nake ji, gabana faɗuwa yake yi, ko da ƙaramin ƙara naji a gefena, ko wata sowa. Wayata ma kashewa nayi, na tura a jakata. Yau gidan namu an tashi da shirin gudanar da taron da Ba Bakura ya haɗa. Har munyi wanka, mun karya Ba Modu kawai muke jira."






Ba Bakura:
Waya ce a hannunshi, yana ta faman kiran wayar Bulama Babba. Amman tana ringin ba'a ɗagawa. Sunturi ya shiga yi a babban falon nashi. Idanunshi sun kaɗa sunyi jawur. Ya rasa meya canja mai tunanin ɗanshi, da har ya gujesu haka. Aita kiran wayarshi bazai ɗaga ba, kuma shi bazai kira ba. Zuwa duba iyaye da dangima sai ya bushi iska yake yi. Zama yayi akan kujera, yana kallon lokacin da Bulama Babba yake rarrafenshi a falon. Da kuma lokacin da yake raba dare yana aiki a falon. Yarone mai ƙulafacin iyaye da ƴan uwa sosai. Ko lokacin da ya tafi Kaduna karatu, ba'ayi tunanin zai iyaba ma. Amman a haka ya daure, sai dai fa kullum sai yayi kiran waya. Lokacin da ya soma ɗaukar albashi kuwa, ƙannenshi mata sunji daɗi sosai, mutum ne wanda abun hannunshi sam basu dameshi ba. Wani irin jiri Ba Bakura yake ji daga zaune, sanadiyyar damuwar juya musu baya da Bulama Babba yayi hawan jini ya dokeshi, ko da yaushe a cikin shan magani yake. Sabida shaƙuwarshi da Bulama Babba ta dabance, dan aboki ya ɗaukeshi ba ɗa ba. Hajja Gana ce ta shigo cike da sallama, tana sanye da lafaya mai kalar baƙi da fari, tasha ƙunshi baƙi, ga ƙamshi na tashi ta ko ta ko ina a jikinta. ( Kunsan kanuri ma ba baya ba wajan ƙamshi da ƙunshi) Kallon me gidan nata tayi, kallon shari'a, kawar da damuwarta tayi ta nemi waje ta zauna, sannan tace.
"Bulama ya ɗauki wayarka kuwa, ko har yanzu matarshi bata bashi izinin ɗaukar wayarmu bane?" A raunace take maganar muryarta tana rawa tamkar mazari. Kallonta Ba Bakura yayi, yace.
"Tun jiya nake faman kiran wayarshi, har yau bai ɗaga ba, yanzu na gama kiranshi amma ina. Bana neman dukiya a wajan Bulama Babba dan da dukiyata yaci yasha, yai karatu, har ya zama mutum, yayi aure. Tunda matarshi da yaranshi yana ganin sun isheshi rayuwa, ai shikenan. Bazan sake ɗaga waya in kira Bulama ba, ko zuwa yayi karki sake ki kawoshi gareni, in kuwa ki ka yi Hajja Gana zaki ga fishin Bakura. Duniya ce ai mai ido a tsakar ka, akwai ranar da zai gane babu abunda yakai Ahali daɗi." Tari ne yaci ƙarfinshi. Hajja Gana kuwa, sai haɗiɗiyar zuchiya kawai take yi, ta rasa me zata ce. Iya damuwa da tunani, harma da kukan babu wanda bata gaji dayi ba. Tana ji tana gani, ɗanta data ɗauki ragamar kula da rayuwarta, yau an wayi gari ya fifita wata mace sama da'ita mahaifiyarshi. Sallamar Ba Modu da iyalanshi ne ya katse musu damuwar da suke ciki. Sun zauna ba'a jima ba, Mama Gana ta shigo. Ba Baana da nashi iyalan suma sun shigo. Falo ya cika dam da iyaye da yara. Kowa ya saurara yana jiran Ba Bakura.


Ba Bakura:


"Modu ka buɗe mana wannan taron da adda'a domun kawar da shaiɗan, da naiman albarka." Ba Modu ya tashi tsaye ya gabatar da adda'a mai tsayin gaske, aka shafa ya zauna. Falon ya sake ɗaukar shiru na wasu daɗiɗu kowa da tunanin dake cikin zuchiyarshi. Ba Bakura kawai ake saurare ya soma magana......✍🏻












Mrs Bukhari ce GIDAN ƘAMSHI. Hajiya in kina neman turaren wuta, turaren kaya, turaren tsugunno, turaren wadrope, turaren mopping, turaren labule, humrori nau'i daban daban, KULACCHAM masu ɗan karen daɗi dan gyaran fatarki, Room freshner masu ƙamshin daɗi. To ki nemi Mrs Bukhari in dai harkar ƙamshine kin samu. Turarena na manyan mata ne, ba daku ake yi ba kucakai.













_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023






_1-NIHLATUL-KHAIR_
👇🏽
*(Ummu Affan)*




_2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*




_ZULFA_
👇🏽
*Ummu maher(miss green)*




_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_


Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank


Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽


08104335144


Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽


08104335144




*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽


08104335144
07068606171
08179523215


Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽


2K
sati biyu
3k


idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.






Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
[26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)




3


Ina miƙa saƙon godiya a gareku masoyana na haƙiƙa, naji daɗi sosai da yanda kuka so littafin mai ido a tsakar ka duniya. Ina alfahari da masoyana na faɗin duniya.


Masoyana na niger ban barku a baya ma, ni da ku son so fisabilillah.




Saƙon gaisuwata a gareki.
Fatima Sulaiman, nagode da soyayya.


_*YADDA ZAKI BURGE MIJINKI*_


_1⃣-Garin Nahal_ babban cokali 2.
_2⃣-Garin yayan bagaruwa Qaramin cokali 2._
_3⃣-Garin kanimfari cokali 1._
_4⃣-Garin almiski ko ruwan almiski._
_Zaki kwabasu gaba daya, yayin da zakije gun mai gidanki sai kiyi turarensu ki tsuguna ya shiga gabanki, Insha Allah maganar birgewa gun mai gida kin gama dashi ko harararki ake daga sanan an daina......_




BA BAKURA:
"Da farko inaso in soma da ku mazan gidan. Masu iyali da waɗanda suke shirin ɗauko iyalin. Yarane ku masu ilimi, kuma masu taimakon iyaye da ƴan uwa. Duk kun haɗe kawunanku, ku ke ciyar da gidan, mu ƴan kuɗaɗenmu in mun samu sai dai muyi ma kanmu hidimar da muke so, da matanmu, da taimakon masu buƙata. Kune kula daci da shanmu, kune kula da abun hawanmu, sutura, kula da ƙannenku, kula da iyayenku matan duka. Alhamdulillah ko a yanzu na faɗi na mutu, na cika wasiccin da iyayenmu suka bar mun, cewar in kula da ƙannena. Na kula dasu, na kula da matansu, na kula da yaranmu duka. Gashi kuna kulawa damu a Yanzu, dama duk ɗan daya samu tarbiyya daga wajan iyayenshi, da izinin Allah, Allah zai dafa ma iyayen ta hanyar shiryar musu da wannan yaron, domun ya kula da tsufansu, mu kam Alhamdulillah shine abunda zance. Abinda zanja kunnenku akai shine, kar kuyi sake da adda'a kamar yadda ɗan uwanku Bulama Babba yayi sake da yin adda'a, har Matarshi taci nasarar rabamu dashi. Yau shekara biyu bansa Bulama Babba a idanuna ba, a wannan shekarun baifi sau huɗu mukai waya ba, shima wayar da muka yin, ni na ke soma kira, sannan saiya kirani. Babu ciwon da yafi wannan, ka haifama duniya ɗa, ya tare a jikin matarshi da danginta, yasa ƙafa yayi fatali damu. Mahaifiyarshi, kusan kullum saita zubda hawayen damuwar rashin ɗanta. Ta ɗauka ban sani bane, ina sane, kuma ina gani. Kuyi ƙoƙari karku yi sake a raba mu daku. Ku kuma matan, da masu auren da waɗanda suka ɗaura ɗambar shiga gidan aure. Kuji tsoron Allah ku mutumta mazajenku ku mutumta iyayen mazajenku, ku mutunta dangin miji, kar ku bari muyi kuka daku. Duk da nasan kab ɗinku babu wanda yake auren bare, acikin ku masu auren. Marasa aurenma babu wanda ya zaɓi bare, duk ƴan uwan junane, aurene na zumunci wanda aka haɗa da kyakykyawar niyya, dan ganin mun haɓaka zuri'a da kuma haɓaka zumunci. Wanda a wannan lokacin zumunci yayi ƙaranci, badan komai ba, sai dan dena auren zumunci da akayi. Yara kansu ya waye, sunfi ƙarfin ace musu suyi, suyin. Zamani yazo da sauye sauye, waɗannan dalilan su suka rushe mana zumunci, mu kuma in Allah mun ɗaura ɗambar haɓaka zumuntarmu. Yahanasu itama tabi sawon Bulama Babba, Nasiru dai Kanuri ne, amman ba danginmu bane. Duk da dai auren ma reto yake yi, dan gane da abunda ya faru, gani nake yi kora da hali iyayen yaronnan suke son suyi mana. Ni kuma na yanke hukuncin cewar mun haƙura, zamu mayar musu da kuɗin gaisuwar da suka kawo. Sannan babban maƙasudin wannan zaman dana tara yau, sabida Yahanasu ne, da kuma tunatar daku girman zumunci, da girman kula da iyaye da ƴan uwa. Allah ya isa akan duk wanda yayi yunƙurin rushe mana farin cikin gidannan. A matsayina na uba a gidannan, ba a wajan Yahanasu ba harma a wajan Innana da Modu. Zan ɗaura auren Bulama Babba da Yahanasu, za'ayi biki irin wanda ake yima duk wata ƴar gata. Amman bana fatan wani daga cikinku ya sanar da Bulama Babba wannan lamarin. Mama Gana, kece zaki kai Yahanasu Kaduna ɗakin mijinta. Ki faɗa mishi ban yafe mishi ba, in yabar ɗiyata ta zubar da hawaye, ban yafe mishi ba in ya bari sanadin aurenshi da Yahanasu ya kawo rabuwar kan zuriyar Bulama Bukar. Me magana yayi, dan ina ganin dukkan abunda zan faɗa, ya ƙare kuma, ina mai ba Yahanasu da Innana haƙuri a bisa wannan hukunci dana zartar, amman wannan aure babu makawa."


Yahanasu:
Gabana sai dukan uku_uku yake yi. Tunda Ba Bakura ya furta zai haɗani Aure da Bulama Babba. Hantar cikina ce ta soma disko, wani irin jiwa na ɗibana daga zaune. Ta ina zan soma da namijin da matarshi ta rabashi da mahaifanshi, ni wanne irin zama zanyi dashi kenan? Innalillahi wa'innailaihil rajiun, rana zafi ina ƙuna, ni Yahanasu da wanne zanji? Haƙiƙa Ba Bakura ubane, kuma ba'a taɓa ƙetare umarninshi ba, tunda ya haɗa aurennan nasan kamar anyi an gama ne. Amman nasan rayuwata zata dawo abun tausayi da kwatance ne. Sai dai Ya Innana ta horar damu, juriya da haƙuri, da ɗaukar dukkan wani abun da zai samemu na tashin hankali, ya zama ba komai ba. Lokaci ɗaya, manyan al'amura suka sameni masu girman gaske. Na rasa darajata, gashi za'a aurad dani ga mijin tace. Hawaye tuni ya gama wanke mun fuskata. Satar kallon Ya Innana nayi. Itama hawayene ke fita da ga idanunta, tana yi tana sharewa da hannun lafayarta daga ganin fuskarta bata so wannan haɗin ba. Dan tasan cutuwa zanyi sosai. Ba Baana ne yayi gyaran murya yace.
"Ni abunda nake gani shine, ko za'a tambayi Bulama Babba tukunna aji ra'ayinshi dangane da hakan? Sabida gudun kwaɓewar zumuncin. Kunga dai yaronnan fa sai abinda matarshi hamshaƙiya tace, kar mu zo ayi abunda daga baya za azo ana cizon yatsa. Bakura kayi haƙuri bawai ban girmama umarninka bane, face gudun abunda ka je ka zo" Yana cikin jawabi Mama Gana tace.
"Zancan ɓur kenan inji tusa. Baana baka gane inda aka dosa ba ga dukkan halama. Ni abunda na fahimta shine. Zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne . Zamu haɗa auren Bulama Babba da Yahanasu sabida zumunci, sannan shi ɗan uwanta ne zai fi bare riƙe ta da daraja, duba da asarar budurcinta da ta yi. Zamu haɗa auren Yahanasu da Bulama Babba sabida ta shiga rayuwarshi wala Allah ta sanadiyyarta shima ya samu rangwame, Allah ya kuɓuto dashi daga hannun azzalumar matar da yake aure, sannan zai kare mutuncinta a matsayinta na wacce ta rasa darajarta ta ɗiya mace, sai yafi kowa sanin kimarta, tare da taya ta jin ciwon abunda ya farun da'ita. Kuma shine kaɗai yake da nisa, kuma shi kaɗai yake auren bare, wannan aure da Bulama Babba yake yi da kofur Zubaina, kowa yasan tun fil azal babu wanda yaso haɗin, kanuri sai kanuri." Ba Modu yace.
"Koma dai sabida menene. Ba Bakura shike da iko akan kaina, dama iyalan nawa. Ni bani da ja akan duk abinda zaka zartar. Kaine da wuƙa da naman, Yahanasu taka ce Bulama Babba naka ne, tuwo na mai na. Fatanmu shine Allah yasa ayi damu. Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garemu baki ɗaya." Ba Bakura, ya fashe da kuka shi da Hajja Gana. Haƙiƙa kukansu ya bayyanar da zafin da zukatansu suke yi akan ɗansu ƙarara. Take a wajan naji cewar zanyi biyayya irin biyayyar da iyayenmu sai sunyi alfahari dani. Da yardar Allah zan share ma Ba Bakura hawayenshi, in sashi farin ciki da walwala." Alkhairi akaita sanyawa haɗina da Bulama Babba. Daga bisani Mama Gana ta rufe taron da adda'a. Mu yara da iyayenmu mata, duk muka fito. Su kuma su Ba Modu suna wajan ɗan uwan nasu, suna ƙoƙarin kwantar mishi da hankalinshi. Jikina a saɓule na zauna a kujera. Ya Innana ta zauna a kujerar dake fuskantata. Bulama ƙarami yana zaune a kujerar da nake, Wakil yana jogane a hannun kujerar da muke. Fanna, da Fanda suna ƙasa. Kowa jikinshi a mace, duk wanda na kalla, sai in ganshi cikin damuwa. Ya Innana uwa ta gari wacce bata nuna sarewarta tace
"Ina horanki da yima iyayenki biyayya. In har kina son rayuwarki tayi albarka, to kibi iyayenki. Ki riƙe adda'a da tsaiwar dare,ki lizimci karanta Qur'ani mai girma ba dai mutum ba sai dai Allah, ki dinga haɗe saukar

3 / 67