MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   41 / 67

120K to 123K   out of 198.3K words

mijinta ya sake ta yai mata korar kare, har da yaran ya hadota suka tawo. Bari dai in musu iso su shigo waƙa a bakin mai ita yafi daɗi" Murmushi Alh kiti yayi yace. "Ai saki ba mummunan abu bane masalahane akan duk namijin da yayi saki, dama ita macen da aka saka. Yaranne dai ubanshi yayi kaɗan in ciyar mishi dasu, ita kanta uwar yaran ina mai takaicin sanwarta da za'a ƙara." Ni dai ina raƙuɓe ina kallon ikon Allah, zazzaɓine kau a jikina, zafin zazzaɓin sai hawa kaina yake sake yi. Yara da matasa, maza da mata, ne su kaita tittiɗowa babban falon Alh Liti, sunfi rai talatin, harda magidanta, ga wasu yungu_yungu suma daga gaba gaba abun tausayi. Dukkansu babu mai kyan shiga, da gani rayuwa matsarsu take sosai, duk wanda ka gani a komaɗe.
"Am da fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya ko?" Cewar Alh Liti. Nan suka shiga rige_ rigen gaisheshi, hayaniyar muryarsu duk ya cika falon na ɗan lokaci. Wasu ƴan mata ne su su biyar kansu ɗaya suka miƙe tsaye, da halama magana zasu yi.
"Baba mu dai akan batun makaranta ne. Dan Allah Baba kar kayi mana aure mu karatu muke son muyi, ko dan mu taimaki kanmu da iyayen mu mata" Wacce ta wakilcesu take magana Alh Liti ya kafama idanuwanshi yana kallonta ƙur, har sai da ta dasa aya sannan ya numfasa yace.
"Batun aure babu fashi, yanda ban ɗauki nauyin ko wanne yaro a cikin gidannan yayi karatu ba, haka kuma ba ku isa kunyi karatu ba. Aure babu fashi magana ɗaya nake yi. Nan da sati guda duk wacce maneminta bai fito ba, to zan aura mata wanda raina yake so. Masu jawabi na gaba" Wasu gungun maza ne riɗa _ riɗa su takwas suka miƙe, mutum guda ya wakilcesu, kamar yadda ƴan matannan su ka yi, shima ina tunanin wata doka ce, tunda ko kotu na lura bata kai gidan bin doka da oda ba.
"Mu Baba aikin yi muka rasa, ɗan dakon kaya da muke yi a kasuwar Nima kuma, jama'a sun sa ido da yawa, surutai tako ta ina tashi suke yi a cikin kasuwar. Baba shagunanka sunfi goma a kasuwarnan, banda store_store ka taimaka ko yaran shagunanka ka mayar damu, wallahi daga mu har iyalanmu, da sauran ƙannenmu maza muna cutuwa, ya kamata ka taimaka ka dubemu da idanun rahama ka samar mana da abun yi. Ka tsundumamu a harkar kasuwancinka, mu kula da harkokin tunda dukiyar dan mu kake tarawa. Azabar dake cikin gidannan tayi yawa. Duk gari sai zancan matsolancinka ake yi, wasu kuma sunce kuɗin lukudi kake dashi......."
"Kace ubanka Sani, nace kaci gidanku. Wannan maganar sama da shekaru goma sha, duk sati sai kun zo mun da'ita gabana, nine zan ɗaura ku akan kasuwancina ku karyani, kunsan ma da yaya na tara dukiyar nan kuwa? Da kunsan irin yawon fataucin da nayi baza ku ɗauka zan rayu har in kai yanzu ba. Ku ma maza ne, ku fita ku nemo, ku shiga ƙasashen duniya ku samar ma kan ku mafita" Cikin ɗaga murya da buyagi yake maganar tamkar zai cinye wanda ya kira da Sanin. Wani daga bayan sanin yace.
"Wai Baba kuma da gaske ne kai ka haifemu dan Allah? Ni naga muguntarka tayi yawa, baka jin tausayin kowa." A zabure ya miƙe ya nufi wanda yai maganar da nufin rufeshi da duka. A guje ya fice, Alh Liti ya rufa mishi baya shima a guje, ko nauyin cikinshi da jikinshi baya yi. Sani da yasan Alh ya fice a falon yace.
"Ai gaskiya Dauda ya faɗa, mutum sai rashin mutunci, Allah ya ɗau ranka uban kowa ya huta. Mutum ya tara uwar dukiya, yaƙi ci ya hana kowa yaci, sai auro ƴan shila, daga tattaraba sai kanari" Cikin masifa Alh Liti ya shigo.
"Ɗan nema, dana kamashi da yaji tsohon hannu. Sani ku fice mun a falo, kuma kar ku sake halartar wannan taron daga yau sai yau. Kamar yanda su Nasiru suka zuƙe jikinsu suka dena shigowa nan kuma haka nake so kuyi" Sani yace.
"Baba kayi haƙuri dai, sannan su Yaya Nasiru da Yaya Rabo ba zuƙewa su ka yi ba. Basa ƙasar ne, sun shiga birkinafaso ci rani. Su kan dai yi ma iyalansu aike"
"To kaji, kuma ku fantsama mana da zai fi muku, kun tsaya jiran dukiyar ubanku. Kai ka sani inajin duk surutan ku akan cewar in mutu ku huta. Wallahi duk mai jiran saina mutu zai yi arziki, to walaha da yunwa su zata riga halakawa" Ficewa su kayi suna ƙunƙunni, ragowar matasan da basu tashi sunyi nasu jawabin ba, suka mara musu baya, suna surutan banza. Ɗakin ya rage sai yaranshi mata, da kuma ƴan yungu _ yungun yaran gidan.
"To Rashida tayi kiyi naku jawabin ina jinki, shegiya kulllum in kika zo taronnan a cikin kuka kike." Wacce ya kira da Rashida ta tashi tsaye tana sharar hawaye.
"Baba mu kukanmu ɗaya ne ko da yaushe. Shine dan Allah ka rufa mana asiri ka dena wannan auri sakin da kake yi. Wallahi Baba ko ina a gari zaginmu akeyi harma da kai ɗin. Hatta mai gidana motsi kaɗan sai ya zagar mun kai, a dalilin haka ne ma ya sake ni, nima na gaji da cin zarafinka da yake yi...
"Ya isa haka ƴar ƙundun uba kai. Ku tashi ku fice mun da gani. Babu uban da ya isa ya sani in dena auri saki, ko yau na samu wacce ta yi mun, saina saki wata cikin waɗannan na auro wata. Ai ni gidannan in kinga na dena aure da saki, to rayuwata ce ta zo ƙarshe, amman ko a gadon mutuwa nake zan iya saki in auro kuma. Tunda mata in dai kana da kuɗi ba cancanta suke nema ba" Suma haka ya kaɗasu suka fita, duk yawancinsu kuka suke yi. Ɗakin ya rage daga mu sai yungu_ yungun yaran gidan.
"Kubra su kuma fa waɗannan?'
"To su kuma duk basu da lafiya, wasu ƙurajene suka fiffito musu a jikunansu, jikinsu da zazzaɓi dukkansu." Kallonsu yayi yace.
"Ke Hauwa, da Ummu Kulsum ku tawo inji jikin naku" Na yi matuƙar mamaki da naji ya ambaci sunan yarannan. Wallahi ko kusa banyi tunanin zai iya tantance sunayensu ba, naga yaran nashi yawa garesu kamar fari. Jikin yaran daya kira ya tattaɓa. Ya girgiza kai yace.
"Kubra kenan, ke wato a kullum baki da hankali, haka kike tunda na sanki. To me kike son ayi ma yarannan dan Allah?" Hajiya Kubra ta yi Murmushi, yanzu ne na gane murmushin da take yawan yinshi meye ma'anarshi. Na baƙin ciki ne da tsantsaryar takaici, gami da dana sani maras amfani.
"Na ɗauka za'a kaisu asibiti, tunda abun yazo da ƙurairaji. Kuma Alh ko bacci ma yaran basa iya yi. Kwana biyunnan Zakiya ke kwanciya dasu a ɗakinsu. Yarannan ka tausaya musu, su yarane sosai, gashi babu iyayensu a gidan balle su su tallafesu"
"Uwar zaƙin baki kenan Kubra. Magana kamar wacce ake rubuta mata ta haddace. To kiji da kyau, ni in ba magashiyan naga yaro rai a hannun Allah ba, bafa za'a sani asarar dukiya ba. Ku basu sabara su sha, zan shigo da ganyen gwanda a dafa musu. Ƙurajen jikinsu kuma a shafa musu toka zasu baje" Ɗayar daga cikin matan Alh mai goyannan tace.
"Haba Alh ka ji tausayin yarannan mana. Duk wani jiƙo wallahi an basu, amman da zazzaɓin suke kwana fa. Ya kamata a kaisu asibiti a duba lafiyarsu"
"To in kuna da kuɗi ni ban hana ku kaisu asibiti ba , ai kuma yaranku ne. Amman ni da kuka ga na rayu har zuwa kawo yanzu, babu wata ƙwayar bature dana taɓa haɗiya. Ni a ƙauyenmu ma babu asibitin, da magungunan gargajiya na rayu. Kuna maganar ƙuraje, mu da mu ka yi ƙazzuwa, da sosa gaye tun kafin asan ma zaku zo wata duniya" Shiru kowa yayi a falon. Ni kuwa lamarin Alh Liti ya dena bani mamaki ma, dan na fahimci baduniye ne shi sosai, asalin tantiran ƴan ƙauyannane jahilan da basu san komai ba, Allah dai ya azurtashi ne, ya samu dama shi kuma yake ɓarar da mata makwaɗaita irinmu. A haka dai wannan taro ya watse, suka fita suka barmu a zaune daga ni sai shi. Miƙewa tsaye nayi nace.
Zan iya ɗaukar wayata in ci gaba da amfani da ita?" Dariya yayi ya kalleni yace.
"Kofur Zubaina kenan, har bakin tsiwar taki ta mutu ne haka, naji muryar tayi sanyi gwanin daɗi" Murmushi nayi mishi kawai na wuce ɗakin daya sauke mu da muka zo. Na tattare kayan sawana, na bar mishi akwatunanshi nan. A hanyar fita falon muka haɗu.
"Ni zan fita Nima market, sai takwas zan dawo. Da daddare zaki gyara falo da sama, yanzu ki samu ki huta ke amaryace." Bance dashi ci kan ka ba muka fito tare. Ni na buɗe mishi get ya fice ya barni a tsaye ina cizon yatsana. Barayin matan gidan na shiga, jama'ar gidan sai hada hadar aikace_ aikace suke yi, gidan kuwa ya haɗe yayi kace_ kace, ko ina ruwa. Haka na tsatstsallake na shiga ɗakina. Kwanukan abincin jiya aka turo wata ƴar lukutar yarinya ta fita dashi. Zama nayi a bakin gado, na saki kukan nadama da dana sani, wacce hausawa sukaima laƙabi da ƙeya. Wayata ce ta shiga ruri da sauri na rarumeta na kara a kunne na. Kuka nake yi a hankali.
"Ya'isheki haka kukan mana Zubaina. Ke kan ki kinsan in dai ina numfashi bazan bari ki wulaƙanta ba. Jibi zanzo, yau zanje wajan malam ya haɗo mun wasu magungunan mallaka masu zafin gaske, zan tawo miki dasu, ki kwantar da hankalinki, dukiyarshi wallahi sai fa munci" Da sauri na katseta da cewa.
A'a Mama, karma ki wahalar da kan ki akan wani zuwa wajan boka. Wallahi Allah bazan zauna a wannan gidan ba. Sannan wanne irin maganin mallakane banyi amfani dashi ba? Bokan daya raba Bulama da iyayenshi, ya haɗa Mabaruka da mijinta na yanzu shi yayi aikin fa. Kuma yanka wuƙane, ni gani nake Alh Liti ba'a zaune yake ba, yana biye_ biyen muggan malamai. Ni dai kixo ki tafi dani kawai, kuɗinshi ba masu cuyuwa bane kuɗin cizo ne dashi. Wallahi yaranshi ma taimako suke buƙata, abun a taimakesu ne. Mama asibiti wannan na fahimci sai Alh Liti yaga mutum na gargarar mutuwa yake bari a kaishi asibiti. Katseni Mama tayi da cewa.
"Yanzu ba zaki bari mu sake jarabawa ba, ko Allah zai sa mu yi dace uhm? Ki duba fa bawan Allahn nan irin miliyoyin daya kashe a kanki, dan ya mallakeki kawai. Ni ina ganin in da zaki bi sannu _ sannu, cikin laluma da kissar mu ta mata, kamar zaki iya shawo kanshi ko? In kuma kina ganin inje in samu Mabaruka ta raka ni wajan bokan naku ai sai inje mu tafi tare. Ki daure mu jaraba, in yasan wata ai bai san wata ba. Ki bar mun komai a hannuna, ko tsirara zanyi yawo ni kuwa sai na samar miki da fada a wannan gidan, sai kin mulki kowa, mukullin taskarshi sai ta zama a tafin hannayenki. Maza kira Mabaruka kice mata gani nan zuwa gidan nata" Da waɗannan kalaman Mama ta shawo kaina, har na ɗanji nutsuwa ta faɗa mun. Kiran Mabaruka nayi a waya.
"Ƙawata ta kaina. Yanzu nake shirin kiranki ai, amman sai nace bana kira Amarya da safe ba." Tsaki naja nace.
Wacce Amarya kuma? Hmmm Mabaruka ai ina cikin tashin hankali mai girman gaske. Alh Liti fa kallon kitse ashe nai ma rogo. Mai kuɗin lukudine, kab ƙasar Ghana kowa yasan hakan, gashi da auri saki. Mabaruka matsalolin Alh Liti sunfi ƙarfin in tsaya faɗa miki duka, sai dai in tsakura miki kaɗan." Labarin kaɗan daga cikin hali da gidan Alh Liti ya kasance na bata.
"Ni ai tun daka kan abincin da aka tare mu dashi. Wallahi na san akwai matsala gagaruma. Amman kinyi amfani da waɗannan layun da boka yace ki saka a ƙarƙashin gadon baccinku, da pillow?" Kai na dafe nace .
Na sha'afa shab tsabaragen tashin hankalin da nake ciki. Sannan Alh Liti turaka yake dashi, a ɗakina zan sa ko a ɗakin nashi?" Mabaruka tace.
"A ƙarƙashin gadon da kuke hawa kuyi kwanciyar aure zaki saka, da pillown da yake ta da kanshi. Ki kula sosai, wannan maganin da kinyi amfani dashi tun jiya ai da kakarki ta yanke saƙa." Ajjiyar zuchiya na sauke wani daɗi ya ratsa zuchiyata.
Mabaruka ai wallahi na mance shab da wannan layu, zan yi duk ƙoƙarina inga na aiwatar da wannan aikin. Ni da harfa nace mama tazo ta tawo dani ni bazan iya da wannan ƙaddararren auren ba. Da har tace zata zo gidanki ki rakata gidan boka fa. Bari in kirata in sanar da'ita tayi zamanta, ba sai ta zo Ghana ba, kuma ba sai ta je gidanki ba."
"Gaskiya kam, kema dai Zubaina kin mance da aikin boka ne. Ya taɓa yi miki aiki bai ci bane?"
Mabaruka ke bazaki gane irin halin dana shiga tsakanin jiya zuwa yau ba. Wai ke kinga yanda Alh ya hayeni kamar wata doki, ya shiga sukuwa kuwa? Ga matsaloli masu tayar da hankali, yaranshi da matanshi duk a yamutse, ga wani abinci da suke ci kamar a firzin" Mun dade muna tattauna maganganu da Mabaruka, daga baya muka yi sallama. Na kira Mama na sanar mata abunda ke tafiya, itama taji daɗi sosai. Jigum nayi a zaune ina karanta wasiƙar jaki. Anya kuwa wannan hanyar zata ɓulle dani kuwa, matan Alh kab da ya dinga aura yana saki, su basu san hanyar gidan boka bane, ko su ba sa son dukiyar tashi ne? Tsorona kar in je garin neman wajan zama a gidan Alh Liti, inje ta zaune mun, sai dai inji kiɗa a magwan. Na ɗau lokaci mai tsawo ina aikin tubka da warwara. Zakiya ce ta yi sallama a ƙofar ɗakina ta ɗaga labule.
"Amarya ki fito mu yi wanke_ wanke" Dubanta nayi na kuma, ina nanata kalmar a zuchiyata.
Wanke_ wanke, wanke_wanke ina Amarya? Ni da nayi tunanin ƴan aikin ɓarayina zasu fi uku ma, kowa da aikinshi, sai gashi daga yin kwana ɗaya ana jirana in soma bautar bataliyar yaran kishiyoyi. Miƙewa nayi na fito. Wanke_wanken da na hanga himili guda a tsube, shi ya kashe mun jiki.
Kut wai ni ce zanyi dukka wannan uban wanke _wanken, sai kace wata jakar da aka cire kuɗi aka siyo?" A cikin zuchiyata nake maganar, Zakiya ta nuna mun kujera, da ruwan ɗauraya, da kwandunan kife wanke wanken, naga ta shiga aikin iza wuta. Hajiya Kubra tana zaune a ƙofar ɗakinta tana yin sukola. Motsi wannan na kasa yi, sai kallon tarin wanke_wanken dake jirana nake yi"
"Umma zamu tafi, ki bamu kuɗin makaranta" Cewar ƴan matasan da suka fito daga ɗakin dake kusa da kitchen ɗin gidan. Kayan islamiyya ne a jikinsu, kayan duk sun jeme,sun dafe.
"Toh Rauda, kuje ɗin kuce da malamin naku za'a haɗa mishi dana wancan watan a biya." Wacce aka kira da Rauda tace.
"Yace in babu kuɗin kar ma muzo wallahi, ni na haƙura ma da karatun duka, kullum a cikin shan wahala kike Umma, Baba yana da dukiyar da zai iya biyan kuɗin makarantar yara sama da dubu, amman mu yaranshi ko islamiyya yaƙi samu" Wucewa tayi cikin ɗakin data fito tana kuka. Ɗayar budurwar dake saye da kayan makarantar tace.
"Ni na gaji wallahi da rayuwar gidannan, kullum cikin talauci. Ni zan nemi ƴar uwata Jamila in koma nima zaman kaina kawai in huta, ni wallahi bazan zauna ba." Wucewa tayi tana bubbuga ƙafafunta. Duk wannan abin dake faruwa ina tsaye a gaban kwanukan wanke_wankennan ne"
"Hajiya yarannan su fito da miji kawai a aurar dasu muma mu huta. Kina jin abunda Kaula take cewa fa. Zata je ta zauna da Jamila, itama tayi zaman kanta. Wannan masifa da bala'i dame yayi kama. Mun jefa rayuwar ƴaƴanmu, da tamu rayuwar a cikin wata iriyar rayuwa, duk a sakamakon son abun duniya. Ina soyayyata da Jabir kamar mu haɗiye junanmu, lokaci ɗaya Alh ya shigo rayuwata ya yaudare ni, ya yaudari magabata na. Mu kai fatali da maganar Auren Jabir, saurayin daya shafe shekaru goma yana mun hidima, kaico na. Ya Allah ka kawo mun ƙarshen zaman gidannan, ya Allah ka kare mun yarana, Allah na tuba." Hawayene suka ciccika guraben idanuna, na tsaya ƙyam a tsaye ina kallon Zakiya. Hajiya Kubra tace.
"Hmmm ina jiye ma Alh ƙarshenshi, domun ƙarshenshi bazai yi kyau ba. Ya cutar da mata da yawa, ya haifo yara birjik ya kasa ɗaukar nauyin komai nasu, mu ya barmu da wahalar renon mishi yaranshi. Allah zai saka mana. Kuma mu ɗauka auren Alh da rayuwa tare dashi yana daga cikin jarabawar rayuwarmu. Muyi ƙoƙarin cin jarabawar kawai. Rashida gata a zaune, zamanin da suke ƴan matancinsu wanne irin lalacewa ne basu yi ba. Sune hotel, sune shagunan maza, suna ba da jikkunansu ana basu kuɗi, ko sutura, ko abinci mai kyau. Gabaki ɗaya sai da suka gama tambaɗewarsu kafin su kai aure gata. Duk kuma wa yaja in ba Alh ba? Duk da mu matan mu muka fi kowa laifi, bari inje in shawo kan

41 / 67