MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   49 / 67

144K to 147K   out of 198.3K words

labarin kab abunda ke faruwa. Kar ki yi gangancin ɓoye mun komai. Dan ko baki faɗa mun ba Alh Liti yaudararki yayi da kalamai na ƙarya. Na firgita da yanda na ganki a wannan ƙazamin ɗakin mara daraja." Hawaye ya soma zubo mun.
Labarin halin dana tsinci gidan Alh Liti, da halinshi kab babu wanda ban ba Mama labari ba. Kai ta jijjiga tace
"Ciɓiri nannagi azumi ta dahu. Ai wallahi kinji na rantse ba zata saɓu ba bindiga a ruwa. Ƙafata ƙafarki dole mu koma gida najeriya, wallahi sai ya sake ki. Kuma saina yaga mishi rigar rashin mutumci matsiyaci. Ashe kallon kitse mu kai ma rogo. Ke kuma dan ubanki dana tambayarki asirin yaci, sai kika ce mun E. So kike kici gaba da yi mishi bauta kome?"
"Mama wallahi Alh Liti hatsabibine, wayar gari kawai nayi naji na jarabtu da matsananciyar soyayyarshi. Kuma shakkarshi nake yi Mama. Bana jin zan iya rayuwa ba tare da Alh Liti ba. Shi yasa na ɓoye ma kowa komai. Wallahi Mama ina sonshi. Ni dai kisa ya sake mun gida kawai."
"La'ilaha illallah mahammadun rasulillah sallallahu alaihi Wasallam. Zubaina kece da bakinki kike faɗar kina sonshi a hakan, da mata huɗu da bataliyar yaran? Ohh kin fi son har sai layi yazo kanki yayi miki sakin wulaƙanci sannan zaki dawo Najeriya baki ga tsuntsu baki da tarko ko?, ke wallahi Alh Liti ɗan tsubbu ne, in ba tsubbaceki yayi ba meye abun daɗi a gidanshi da har kike mafarkin kici gaba da zama har sai yayi miki korar kare, irin yanda yaima sauran matan daya saka ko, ko kuma yaranshi su kasheki a banza da wofi, tunda da badan nazo da hanzariba yanke miki hannu za'ayi ki zama nakashashshiya. Kuma ya danna miki saki. To wallahi baki isa ba. Mama na cikin sababinnan Alh Liti yayo sallama ya shigo ɗakin, sai muzurai yake yi. Ƙamshin turarenshi na mallaka ya daki hancina, muka haɗa idanu dashi. Fararen idanunshi sun sha kwallin idonki idona na ƙifil. Take naji na sake jarabtuwar da soyayyar Alh Liti, tsoronshi ya kuma shigata. Hatta Mama da suka haɗa idanu sai da ta shiga taitayinta. A madadin ta jira ya gaisheta, itace ta gaisheshi tana washe baki. Sai da yai mata wani kallon ƙasƙanci, da rashin girma sannan ya soma magana cikin cin magani. Ba tare daya kalli inda Mama take ba yace.
"Lafiya Jummai kece dama, to maraba lale." Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna. Naji zafi da raɗaɗin yanda Alh yake ma Mama magana cikin rashin daraja. Mama ta saki bakinta tana kallonshi, kalmar Jummai sai nanata kanta take yi a kunnuwanta.




DAMATURU.
BULAMA BABBA:
Da misalin ƙarfe goman safe muka isa Damaturu. Tun daga kwanar layinmu muke cin karo da motoci, layin cike da mutane, wasu na alwala wasu kuma isowar tasu kenan kamar ni. Ganin jama'ar ya sake rikita lissafina. Dam Ahmad ya riƙe hannuna mu kaita kutsa kai cikin mutane. Waɗanda suka Sanni sai nuna ni suke yi suna faɗin.
"Wannan ai shine Bulama Babba, babban ɗanshi kenan" Ni dai bana ko iya ɗago kaina a haka muka shiga cikin gidan. Koke_ koken mata na al'ada ya sake firgita tunanina. Take hawaye ya soma wanke mun fuskata. Ƙannena maza da mata naita cin karo dasu. Ko wanne cikin zubar da hawaye. Wakil ne ya riƙe hannun haguna suka shiga dani falon Ba Bakura. Inda na tarar da Ba Modu, da yurom, da Ba'a Kaka. Ba Bakura yana shinfiɗe a cikin makara an gama suturceshi. Hajja tana gefe tare da sauran ƙannena waɗanda suka samu damar shigowa. Naga ƙannena da muke ciki ɗaya dukkansu. Gefen Ba Modu naje na durƙusa jikina na rawa, hawaye ya kafe a idanuna, bakina sai ambaton Allah kawai yake yi. Adda'ar samun rahamar Allah nayi ma Ba Bakura. Na shafa jikinshi ina jin zuchiyata na ɗaci. Gawar muka cicciɓa muka fito. Mata nan suka shiga kururuwa. Allahu Akbar Ba Bakura mutum na mutane, baya goya marayu. Ya samu jama'a sosai. A tsohuwar maƙabarta aka birneshi, maƙabartar da aka birne Hajja Yahanasu, da Ba Baana da sauran danginmu da suka kwanta dama. Bayan mun kai Ba Bakura gidanshi na gaskiya, sai muka ɗinguma zuwa cikin gidan dan yima iyayenmu ta'aziyya. Ba Modu kuma ya tsaya tare da jama'a yana shaida musu Ba Bakura ya daɗe da yin wasiccin in ya mutu kar ayi mishi zaman makoki. Kowa yayi gaisuwa ya kama gabanshi kawai. Nan jama'a su kai ta ma Ba Modu gaisuwa suna watsewa. Biyo bayanmu yayi zuwa cikin gidan.
"Innana a sanar ma maƙota dan Allah ko wacce tayi gaisuwa ta koma gidanta. Marigayi baya son zaman makoki, ko a rasuwar mahaifinmu, da Hajja bai bari anyi makoki ba. Suma yara yaran zuwa yamma ko wacce ta ja hannun ƴaƴanta su koma ɗakin mazajensu. Bulama Babba sai bayan uku zasu goma, domun a tattare kan dukiyar Bakura a rabe musu. A sauke mishi nauyin dake kanshi." Ni dai ina bayan Ba Modu ina jinsu. Falon Ba Bakura muka nufa. Mu kai ma Hajja ta'aziyya sai faman kuka take yi. Ƙannenta nata bata haƙuri. Zuwa yamma gidan kamar ba gidan mutuwa ba, kowa ya watse sai surukan cikin gidan kawai. Sai da na samu ƴar nutsuwa na kira su Ya Bagulaji dan inji jikin Yahanasun. Amman sai naji labari mara daɗi, cewar da ƙyar aka taro Yahanasu taso ta fice daga asibitin, tana ihu da kururuwar zata sha lakamis. Wannan labari shi ya sake susutani. Ambaton Allah kawai nake yi. Take na ɗauki karatun Qur'ani na soma rerawa domun samun nutsuwa. Ba Modu kuwa sai faman ganawa yake da manyan baƙi, masu hulɗar kasuwanci da Ba Bakura. Ni dai ina ɗaki ni da Ahmad, bana ƙaunar son ganin kowa. Damuwar dake kaina ma ta isheni."


MRS BUKHARI CE[14/08, 9:54 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
41












GHANA
ZUBAINA:
"Lallai Alh Liti, zahiri ka bani mamaki. Ta wanne dalili zaka je har najeriya ka auro mun ƴa ka kawota inda bata sani ba ka shiga gana mata azaba. Nazo na sameta a cikin wani irin hali wanda da banyi gaggawar zuwa ba, da sai dai a yanke mata hannunta, kai ba asararka bace. Yaron da yayi mata wannan aikin ya kamata a ɗauki matakin shari'a dashi dan kasheta yayi niyya. Alh Liti maganar gaskiya ni bana son tashin tashina, ka saki Zubaina kawai mu kama hanyarmu, bazan iya barinta a cikin wannan halin ba." Kallon Mama nayi ta gefen idona a tsorace nake sosai da Alh, in na ganshi gabana har kakkatsewa yake yi. Gyaran murya yayi yace.
"Hummm Jummai lashe money kenan. Kin ɗauka rabuwa da Zubaina wani kayan gabas ne a wajena? Bari kiji na auro ƴan mata waɗanda ni na yage ledarsu, ma'ana ni na karɓi budurcinsu, na sauwaƙe musu, ballan tana wannan fankon da ko ɗanɗano bata dashi. Rabuwa da'ita kamar in tuɓe takalmin ƙafata ne, kinga kuwa cire takalmi ai ko yaro baya yima wuya balleni da a girme na girme miki. Amman bari kiji in so kike da gaske in rabu da Zubaina, sai kun biyani dukkan kuɗin dana narkar muku dashi, komai da taci tun daga farkon haɗuwarmu kawo i yanzu yana rubuce. Itace mace ta farko a cikin rayuwata data lashe kuɗi tsabarshi sama da million bakwai, dan ko a ƙarashen ginin gidanta da kayan dana zuba mata a cikin gidan yayi million biyar. Ke karan kanki nawa kika ci? Million ɗaya da rabi na kashe miki babu amfanin kuma da zaki yi mun. Kuɗaɗena sun kama jimilla million tara da dubu ɗari huɗu da ashirin da biyar. Banda kayan maƙulashe fa da nake siyo muku ku lashe, A cake mun su, kuga aiki da cikawa. In kuwa ba'a cake mun ba, ni da Zubaina mutu ka raba dan bata cikin jerin matan da suke jiran layin saki ya zagayo kansu. Sannan Jummai inason in ja kunnenki karki kuma yi mun kutse cikin harkar data shafi iyalina, abinda yasa bazan yi ƙararki kotu ba sabida wannan shine karon farko, amman ina mai gargaɗinki da ki kiyaye gaba. Ke kuma Zubaina, ki shirya da yamma za'a baku sallama sai Jummai ta mayar dake tunda dai ita ta ɗakko ki. Yana dasa aya ya juya ya fice yana saɓa malum_malum ɗin shi. Idanuna na tsiyayar hawaye nabi bayanshi da kallo. Mama na kalla jikinta yayi sanyi ainun idanunta sun cicciko da ruwan hawaye.
"Ni Jummai wannan mutumi kwai tambaɗaɗɗe, Zubaina dama haka Alh Liti yake, ashe gogaggen baduniye ne bamu sani ba ƙwallon shege?, kallon kitse mu kai ma rogo ashe? Tabɗi jan ni Jummai tawa ta ƙare." Ni dai sai hawaye kawai nake zubarwa, ina tuno lokacin da Bulama yake gurfana guigowinshi a ƙasa, kanshi na kallon ƙasa yana gaishe da Mama cikin girma da karamci. Na sake tuno yanda yake ganin girmana da girman ƴan uwana. Nayi imani da Allah da ace a gidan Bulama na samu wannan karayar da yanzu yana gefena yana aikin yi mun sannu da jiki. Muryar Mama ce ta katseni tana faɗin.
"Dole zaki bar gidan Alh Liti in kina son ki tsira da rayuwarki. Zan haɗa kan ƴan uwanki su samo wannan kuɗaɗe a biya Alh Liti ya sauwaƙe miki. Tunda matsiyacine shi. Da sauri na dubi Mama kaina na saramun nace.
A'a Mama karki nemo kuɗi a wajan kowa ki barshi kawai" Shessheƙar kuka naci gaba dayi. Mama ta riƙe ƙugunta tace.
"Me kike nufi da kar in nemi kuɗi a wajan kowa Zubaina, baki da hankali ne, ko kuwa asiri Alh Liti kema yayi miki ne?"
Wallahi Mama ban sani ba. Amman ko asirinne sai yayi mini. Ni dai kawai inason in zauna a gidan mijina, sabida bana jin in na rabu da Alh Liti rayuwata zata ɗaure. Mama wallahi ina sonshi." Kuka mama ta saka tana salati tare da kutuntumama Alh Liti ashariya iri _ iri akan ya rabasu dani. Ni dai ina kwance ina kukan baƙin ciki da takaici, tare da tambayar kaina me yasa nake son zama a gidan Alh Liti ne? Sai dai kash bani da wannan amsar, wanda zai bani amsar ma ban sanshi ba. Haka mu kai zaman kurame ni da Mama a asibitinnan, ina ji Asiya tana cema Mama ta bani wayar zamu gaisa, amman Mama fur taƙi sai ce ma Asiyan tayi ina baccine. Kallonta nayi, itama ni take kallo, harara Mama ta sakar mun tana ƙwafa. Da yamma aka bamu sallama muka tattaro muka dawo gida. Nan su Hajiya Kubra suka shiga tambayar jikin nawa. Mama kuwa tagumi tayi tana kallonmu dukkanmu, hawaye take ta aikin sharewa da gefen mayafinta. Da daddare aka kawo mana dukunu da miyar tanƙwa da soyayyun kayukan kifi.
"Me zan gani ɗuwawu ya mutu ya bar zani ni jummai, Zubaina meye wannan haka a ɓawon masara?" Ajjiyar zuchiya na sauke na kalli Mama itama ni take kallo tana tsaye a kaina.
Dukunu ne Mama, wani irin tuwone na gargajiya anan Ghana."
"Kuma ake cinshi da romon attaruhu da kayukan kifi, sai kace wasu kuliyoyi? To bada ni ba gaɗa a makwantai, inci zawo ya hanani tafiya gobe. Tashi zaki yi ki kira mun wata yarinya nan in aiketa ta siyo mun abunda zan iya ci." Cikin ɓata fuska nace.
Haba Mama ni da ba lafiya gareni ba shine zan tashi in kira miki yaran aike? Yaran gidannan ma ba aikuwa suke yi ba Mama." Ai daga faɗar haka Mama tace ina wuta ta sani. Ta inda take shiga ba tanan take shiga ba, zagi kuwa a wannan ranar nasha zagi iri _ iri. Matan gida na jinmu, sai kuka nake yi. Fuuu mama ta fice abunta ina kiranta ma tayi banza dani. Bata jima ba ta dawo da take away na indommie da soyayyen ƙwai sai coke mai sanyi. Ina kan gado na soma cin dukunu kenan ta shigo, ko kallon inda nake batai ba. Nima bance mata ci kanki ba. Har dukkanmu kowa ya gama cin abincinshi. Alwala na fita na ɗauro na dawo na rama sallolin da ake bina. Mama kuwa ni take kallo ƙur da halama tunani take yi mai zurfin gaske.
Mama kiyi haƙuri in nayi wani abun daya ɓata miki ranki. Wallahi Mama inason inci gaba da zama a wannan gidan. Kuma Mama ni ina ganin kamar alhakin Bulama da iyayenshi ne ya soma bibiyata tun kafin aje ko ina. Mama wanne surƙuƙune bamu shiga mun gurfana a gaban bokaye ba? Mama kin taɓa ba da jikinki ga boka duk dan sabida biyan buƙatarmu. Mun samu komai a yadda muke son ya tafi mana. Amman aurena da Alh Liti ina ganin kamar shine sakamakon dukkan aiyukan sharrin da muka shuka a baya. Ni dai Mama na zubar da wasu makaman yaƙina. Kuma zan ta yin istigifari Allah ya yafe mun kura_ kuran dana aikata a baya. Wallahi Mama Alh Liti yafi ƙarfinmu ne shi yasa kika ga na sallama." Kallona Mama take yi sosai tana nazartar yanayina tare da jujjuya kalamaina. Ajjiyar zuchiya Mama ta sauke ta kira sunana da sassauƙar murya.
"Zubaina dukkan maganganunki akan hanya suke. Tun kafin in yi aure nake biye_ biyen bokaye, gashi har yanzu aikin kenan guda ɗaya sama da shekaru talatin da doriya. Ban huta ba kuma har yanzu bata sauya zani ba. Kuma har gobe a cikin matsaloli muke, daga wannan sai mu faɗa wannan. Yanzu haka ko jarabar Musa da Sagiru aka barni dashi wallahi ta isheni. Ƴan uwanki dai ko wacce lafiya sumul take zaune a gidan mazajensu. Ke da kika faɗa jarabawa sai dai ince miki Allah ya fitar dake, zan ci gaba da taya ki da adda'a. Amman ni kaina yawon bin malamannan ya gama isata wallahi, na riga dai na shiga ne, in banje ba sai inga kamar rayuwar tawa ba zatai dai _dai ta ba. Amman a hankali zan dinga rage zuwa har in dena. Kici gaba da zaman haƙuri in ki kai ta adda'a Allah zai kawo miki mafita." Cikin muryar kuka nace.
Dama Allah ya barmu ne da iyawarmu, yanzu kuma sai yaso ya nuna mun ikonshi ta hanyar jarabtata da Alh Liti. Mama nayi kaicon barin gidan Bulama Kamar yadda nayi kaicon cutar da mahaifanshi da nayi. Nayi kaicon biye _ biye bokaye maƙaryata da na dinga yi Mama. Mama ki nemi Bulama ki dubo mun su Bawa dan Allah, nayi watsi da yarana da yawa. Ina gudun kar dangin mahaifinsu su rabani dasu baki ɗaya." A daren ranar munfi ƙarfe biyun dare muna tattaunawa da Mama. Dukkanmu tsoron Allah da dana sani ya ratsa jikkunanmu sosai. Washe gari sassafe Mama taimun sallama ta tafi. Ta barmun ragowar kuɗaɗen Ghana data canja anan. Haka naci gaba da jinyar hannuna, hannu dai kullum babu daɗi kwata _ kwata, ina cikin jinyarnan akayi bikin yaran gidan su goma, bikin daya tara tarin jama'a, dan ko wacce yarinya mahaifiyarta ta samu halartar taron, a bisa jagorancin dangi. Maƙotama sun cika gidan fam, bikine dai akayi shi kadaran kadahan, dan iyayen amarennan kusan su suka ɗauki nauyin abincin ranar yinin biki, Alh Liti na ranar ɗaurin aure kawai ya bada cefane, tuwon shinkafa da miyar kabewa, babu ishasshen kayan miya, balle nama ko kifi haka akayi bikinnan aka kai amare gidajen aurensu. Sati biyu na zagayowa na koma asibiti dan a kunce mun hannuna kamar yadda suka ce. Tashin hankali wai hannun bai ɗauru ba sai an kuma mun sabon ɗori. Haka aka kuma karya hannuna akaimun sabon ɗauri, sai da nayi kashi tsabar azaba.
BAYAN WATA UKU




MRS BUKHARI CE
[14/08, 9:54 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
42






DAMATURU:






BULAMA BABBA:
Ranar addu'ar uku akayi mana rabon gadonmu. Inda mu mazan muka tashi da gidaje bibbiyu masu ɗakuna goma sha bibbiyu da shaguna uku a jikin ko wanne gida,dama gidajen haya ne. Matan suka tashi da gidaje ɗadɗaya. Muka yi taraiya a kamfanin pure water mallakin Ba Bakura wanda bai jima da buɗewa ba, amman kamfanine babban gaske, akwai motoci goma sha biyu masu jigilar fitar da ruwa, har ruwan gora suna yi a wannan kamfani. Banda kuɗaɗe da aka raba mana masu tsokar gaske da ƴan kadarori dai irin filaye da gonakai. Adda'ar uku akayi, ni da Ahmad muka kama hanyar komawa Kano dan ci gaba da kulawa da lafiyar Yahanasu na. Watanmu ɗaya a Dawanau amman babu wani canji da zan ce mun samu babba. Abu ɗaya ne dai, Yahanasu ta dena ihu da fisge _ fisge. Amman kullum a cikin fargaba muke da damuwa. Wata ranar asabar da yamma na shigo duba Yahanasuna, na tarar da Mama gana tana waya tana.
"To shikenan Modu ni gobe ma sai mu kamo hanya kawai. Kana ji ko Modu? Mu haɗu daku ɗin kawai a Dauran. Yanzu Bulama Babba ya shigo zan yi mishi magana a shirya daga yanxu zuwa gobe kawai. Ka kashe wayarka in muka gama tattaunawa zai kira ka." Wayar ta sauke a kunnenta ta dubeni tace.
"Bulama Babba. Modu ne ya kira ni yake yi mun wani batu. Ni dai na gamsu da batun daya kawo mun, kuma ina fatan ku gamsu domun ko baku gamsu ba babu wanda ya isa ya tanƙwarashi."
Ina jinki Mama Gana me Ba Modun yace ne?"
"Dangane da batun lafiyar matarka ne Yahanasu dama. Yace akwai wani rehab da aka bashi labari a can Daura garin su Baba Buhari. Kuma ya tura Dala ya dubo mishi wannan rihab acan Daura. Duk sun gamsu da wajan shine yake bada umarnin akai Yahanasu can domun a kula da'ita yanda ya dace. ( Bawai dan sun raina ƙwazo da ƙwarewar likitocin Dawanau bane, wannan ra'ayinsu ne) Dan haka sai ka shirya mata kayanta cab gobe in sha Allah sai mu ɗauki hanya. Tunda Allah yasa ka sayi mota ma

49 / 67