MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   38 / 67

111K to 114K   out of 198.3K words

ɗinkin riga da zane, sai wani ɗan mitsitsin gold a kunnenta, mayafin jikinta na nera dubu huɗu ne, takalmin ƙafarta bazai haura nera dubu uku ba. Fuskarta ba kwalliyar komai sai kwalli, duk da ta manyanta kaɗan. Baki na taɓe, naji wani sanyi a raina. Ita Maryam ɗin da akace ɗiyarshi ce, wani ƙoɗaɗɗen tsohon lace ne a jikinta, wanda tuni aka daɗe da dena yayin irinsu, in ba idanuna ke mun gizo ba ma, har ƙuraje leshin jikinshi yayi, hatta gyalen jikinta tsohon yayine irin na gyatumarta. Wani kallon banza na watsa musu kuma dukkansu sun gani. Goggo Safiya tace.
"Dama muma yanzu muke shirin ɗakko Amaryar mu kawo muku ita, sabida gobe zamu juya in Allah ya yarda. Hajiya Kubra tace.
"Ai Babu komai Baba kar ku wahalar da kan ku wajan kawota ma, Alhn zai kawota da kanshi, haka doka da tsarin gidanshi yake. Kuma da ace kun kawota ba tare da sanin nashi ba, ranshi ka iya ɓaci da hakan, mu janku ko?" Tana gama faɗar hakan suka fita ita da Ɗiyarta. Bayansu muka bi, tiryan_tiryan har zuwa ƙofar gidan. Inda ya cika ya batse da maza da mata, ana zazzaune a kujerun robar da suke cikin rumfar da aka kafa ƙatuwa. Ga makaɗa a fili sai tattakawa tsirarun mata suke yi. Wani irin biki ne wanda mu dai bamu gane kanshi ba sam, haka dai akaita abu ɗaya, gashi ba abinci, ba ruwa har aka tashi ba'a bamu komai ba. Iya ƙula na gama ƙumewa sosai. Muna dawowa na siga aikin kiran wayar Alh Liti dan in sanar mishi ba'a bamu abinci ba a wajan biki, kuma ba'a kawo mana abinci ba. Amman nayi kiranshi yafi sau goma, dana sake gwadawa ma sai naji wayar a kashe. a cikin jirgi Alh Liti ya bani sim na ƙasar Ghana na sanya a wayata .Mama Rakiya tace.
"Kar ki ɗaga mishi hankali Zubaina, duk wannan abun bazai wuci sharrin uwar gidanshi ba. Amman tunda ba wata yunwa muke ji ba, ki bari mu tari gobe, sai ki yi mishi bayani cikin lumana bayan mun tafi." Haka na kwana cikin zafin zuchiya, da tunanin dalilin da yasa Alh Liti yaƙi ɗaga wayata. Washe gari da sassafe shi ya tashe mu. Ina buɗe ƙofar muka haɗa idanu dashi, kallona yayi ƙur kamar mai nazari, rannan nashi a murtuke, sai naga duk ya sauya mun, fuskarshi ta zama kamar ba tashi ba.
"Kice ma su Goggo su shirya ƙarfe takwas zamu kai su filin jirgi" Tunda nake dashi ban taɓa jin muryarshi a kaurare haka ba, nayi mamaki sosai, amman sai na ɗaura alhakin hakan akan ƙila uwar gida ce ta murɗa kambunta, nace dashi.
Dama suna so, su shigar dani cikin gida wajan Hajiya Kubra kafin su tafi"
"A'a ni da kaina zan kai ki, bama sai sun wahala ba, ke dai kice su shirya." Yana gama maganarshi ya wuce. Ni kuma ina tsaye ina ganin ikon Allah, ban bar wajen ba har sai da na ga ƙulewarshi sama, sannan na juya cikin ɗakina jikina a sanyaye sosai. Kafin takwas kowa ya shirya tsab. Amman babu abinci ba dalilin abinci, har Alh Liti ya zo yayi mana sallama akan su Goggo Safiya su fito. Mabaruka ta ɗan jani gefe guda
"Ga layunnan gudun kar a samu matsala, in zo in saka su a ɗakinnan, ya zamana ba a ciki zaki zauna ba, kyayi aikin da kan ki kawai. Kinga sharrin kishiya ko? Harta kaɗa miji mijinki ya sauya miki, tun jiya da yamma rabonmu da abinci" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Ni gabaki ɗaya naga Alh ya canja mun, kinga yanda yake harhaɗe fuska kuwa, yanzu yana nufin ba zaku karya ba zaku tafi?" Mabaruka tace.
"Kar ki damu da wannan, ke dai ki shawo kan mijinki Zubaina, irin wannan gidan zaman cikinshi sai anyi da mugun gaske yake yiwu fa." Muryarshi muka jiyo yana kwaɗamun kira da sunana.
"Ke Zubaina Zubaina ku fito mana" Tsurewa na kuma yi. Da sauri muka fito falon suna tsatstsaye mu suke jira.
Amm Alh basu karya ba fa, kuma jiya da daddare ba'a kawo abinci ɗakinmu ba, inajin Hajiya Kubra ta manta ne." Agogon hannunshi ya kalla yace.
"Yanzu in suka ce zasu tsaya cin abinci zasu iya rasa jirgi. In sun isa lagos sa ci abinci." Mama Rakiya tace.
"Ai babu komai Alh" Goggo Safiya tace.
"Amman munso mu miƙata cikin gida, wajan uwar gidan. To amman hakan bai samu ba. Alh dan Allah ayi haƙuri da duk halayen Zubaina. Kaga Zubaina yarinya ce, duk abunda tayi ba dai _ dai ba, a dinga nusasheta dan Allah " Murmushi yayi ya kwantar da murya yace.
"Wannan ba komai Goggo, za'ayi ƙoƙarin hakan. Muje mu kaisu filin jirgin ko Zubaina?" Tare mu ka kaisu filin jirgin, muka yi sallama da juna, sai naji lokaci ɗaya jikina yayi laushi, har nake jin tamkar in bisu mu koma. Amman babu dama, mota na shiga mu ka bar filin jirgin izuwa gida. Tunda muka soma tafiya, babu wanda yace da wani uffan, kowanne da abunda yake saƙawa a cikin ranshi. Taka maimai in za'a shaƙeni bana ce ga abinda nake tunawa ba. A get ɗin farko muka dakata, Alh ya dube ni yace.
"Fita ki buɗe mun get in shiga da motata." Kallonshi nayi cikin tuhuma, shima ni yake kallo, sai zazzare idanu yake yi.
"Dallah fita ki buɗe mun get in shiga da mota, dan bura'ubanci kin kakkafeni da mayun idanunki" Wata uwar tsawa ya daka mun, sai da hantar cikina ta kaɗa, ba shiri na ɓalle murfin motar na fito a hargitse. Da sauri na tura ƙaramar ƙofar dake jikin get ɗin, na shiga cikin gidan. Turus na tsaya cak, ina ƙarema gidan kallo, wanda nake gani kamar mafarki nake yi, in kuwa ba mafarki bane, to tabbas wannan shafar aljanune"


Mrs Bukhari ce
[08/08, 11:24 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR
(,DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
31
























YAHANASU:
Sai da na shafe kusan kwana huɗu ina fishi da Bulamana. Shi kuwa yaƙi sam yayi fishi dani, sai lallaɓani da yake faman yi. Yusuf kuwa rashin sabo yasa kullum a cikin ɗan karen rikici yake, musamman in dare yayi, sai yai ta kuka, wata rana in na bashi ruwa ya karɓa yasha, wata rana ya botsare mun. Yau kwanan Yusuf biyar da dawowa hannuna, Bulamana ya siyo mishi ƴan kayan gwanjo kala uku. Nima yau na ɗan biya kasuwa bayan na tashi aiki na tsinto mishi kala uku, na ƙaro ma su Bawa kala bibbiyu. Bulamana ma na siya mishi wandon jins guda biyu da ƴan t shirt kala biyu, dan kayan nashi duk sun soma jemewa, gashi har zuwa yanzu ƴan Damaturu basu san halin da muke ciki ba. Kullum muna kiransu a waya a gaggaisa, amman muna sa ran zuwa sati mai zuwa bikin Wakil. Ina zaune a tsakar gida sai faman aikin kunun zaƙi nake yi, yara sai shigowa saye suke yi, a yanzu a iya cikin gida ma ina yin dubu biyu da ɗari biyar, banda wanda nake kaiwa shaguna, ga meat pie shima yanzu ina cinikinshi a gida, banda wanda ake kaiwa shaguna. Uwatale ce ta shigo wajena, baki na washe mata.
Uwatale baki yi fishi dani ba, wallahi naso in shiga miki jiya, amman sai naga mashin ɗin Baban Maryam a ƙofar gida, nasan yana ciki, kinji dalilin rashin shigowar tawa. Ga kujera zauna mana" Zama tayi tana hararata tace.
"Har akayi azumi, aka sallace bamu haɗu ba, ke da an taɓa ki kice bakya zama aiki, ni nama gaji da wannan ƙawancan gaskiya." Dariya mu ka yi duka, meat pie da kunun zaƙi na kawo mata.
Bismillah ƙawata, muna hira kina korawa ko, kin ganni girki nake son maza maza in kammala, zamu je dubiya ni da Abban Bawa ne asibitin murtala, shi yasa kika ga inata sauri" Uwatale ta kalli Yusuf dake zaune a bakin ƙofa yana cin meat pie tace.
"Ƙawata wannan yaron fa, baƙi kika yi ne?"
Au Yusuf wai? A'a ƙanin Maryam ne, mamanshi zata yi aure ne shine ta kawo shi" Zama Uwatale ta gyara tace.
"Ƙawata ashe jita_jitan da nake ta ji a cikin layi gaskiya ne, cewar su Maryam ba yaranki bane, yaran mijinki ne?" Baki na riƙe nace.
Tsegumi daɗi, wato har wani jita_jita akeyi a anguwa? Zancen duniya baya ɓuya"
"Hmmm ƙawata, Hajara ce take ta yaɗa zancan duk inda ta ɗaura ɗuwawu ta zauna, sai ta yi hirar. A wajan matan gidanmu nake ji, suma itace ta fesa musu." Take jikina yayi sanyi kamar an watsa ma kaza gishirin, rashin samun haihuwa ya sake dukan zuchiyata, nayi shiru na wasu daƙiƙu. Uwatale tace.
"Ƙawata ina adda'ar kema Allah ya baki naki yaran ki rainasu da hannunki. Kuma dole a yaba miki yanda kika riƙi su Bawa, duk da dai kince auren zumunci kuka yi ke da Abbansu. Daɗin auren zumuncin kenan, ai duk kishinka baka cutar da yaran ɗan uwanka ba" Haka dai mu ka yi hirar inata daurewa, sai da na gama girki na zuba mata, da taci ta ƙoshi ta mun sallama. Magriba na gama duk aikace _aikacena, har nayo wanka. Abinci na zuba ma yaran, ni kuma na ƙule ɗaki abun duniya duk yabi ya isheni, kwaɗayin son samun ciki ya sake shigata. Doguwar riga ƴar kanti na zura a jikina, wadda Bulamana yai mun da ƙaramar sallah. Sallar magriba nayi, ina zaune a kan sallaya na zuba tagumi bulamana ya shigo da sallama. Ciki _ ciki na amsa sallamar tashi, dan tun ranar da Zubaina ta tako ƙafafunta zuwa cikin gidannan nake ta aikin fishi dashi, yayi rarrashin, yayi magiyar, amman fur naƙi daina fishi. Tun ranar ban sake bashi hakkinshi ba, duk da inna kalleshi yana bani tausayi, domun nasan baya iya zura mun idanu na kwana biyu ba tare da ya huta dani ba, sai dai in al'ada nake yi, shima kwana uku nake yin wanka. Amman yau kwana biyar rabonshi dani. Wannan shine karo na farko da nayi fishi mai tsawo dashi, tun bayan daidaituwar zaman aurenmu. Nima kuma ina kewarshi sosai.
"Gashi, zaki ga ƙunshin naki yafi girma, ƙaramin na yara ne, ki shirya ina dawowa masallaci zamu tafi" Yana gama faɗar haka ya fita, dan kiraye kirayen sallar isha aketa yi. Sai da nayi sallah, sannan na buɗa ledar da Bulamana ya turo gabana. Balangune gashin ruwa ruwa, yaji kayan ƙamshi sai turiri yake yi. Murmushi nayi, dan nasan so yake yi dai in sakar mishi mu dawo yanda muka saba, ni kaina duk na bi na takura, amman wani sa'in ɗan adam yakan wayi gari cikin jin haushin kowa da kowa ma, wannan ɗabi'ace ta ɗan adam. Musamman ma'aurata sunfi shiga irin wannan yanayin. In ba'a kai zuchiya nesa ba, akan iya samun gagarumar rikici akan ɗan abun da bai taka kara ya karya ba. Kiran yaran nayi suka shigo. Kasafta musu nasu balangun nayi, na ba kowa nashi. Kunun zaƙi na ɗakko mai sanyi inaci ina korawa. Kai Allah kai mana arziki mai albarka. Rabi naci na ƙunshe mishi rabin. Da sallama ya shigo. Na amsa mishi. Cikin yaranshi ya shiga ya zauna, sai biyema shirmensu yake yi. Wasu siraran hawayene naji suna surnanowa daga gurbin idanuna. Ni sai yaushe zanga nawa jinin Bulamana yana wasa dashi, kamar yadda yake wasa dasu Bawa?" Bansan Bulamana yana kallona ba, ji nayi ya riƙo hannayena yana murzasu a hankali. Jikina murza yatsun da yake mun yake shiga sosai, kasancewar nayi kewar hakan.
"Menene ya saki kuka Yahanasu na, haba masoyiyata. Me nayi ne kike ta faman azabtar mun da ruhina?" Da sauri na fisge hannuna na tashi a guje, na shige wajan katifarmu dana raba da labule.ina shiga na kife a katifa sai na raushe da kuka, wanda nake jin ciwonshi daga ƙasan zuchiyata" Da sauri ya shigo. Ji nayi ya kamoni gabaki ɗaya ya sani a jikinshi yana rarrashina. Jina a jikinshi yasa na kuma rushewa da kuka mai taɓa zuchiya"
"Wani abunne ya faru bayan fitata ko menene Yahanasu? Dan Allah kiyi shiru ya'isa haka yara suna jiyo kukan ki fa" Haɗiye kukan na shiga yi, amman hawaye bai dena sunturi a kumatuna ba. Zaunar dani yayi muna fuskantar juna.
"Menene yabi ya dameki Yahanasuna, yau tsawon kwana biyar kina ƙunci, ko zuwan Yusuf ne baiyi miki ba? In kina ganin hidimar tayi miki yawa sai in kai shi wajan Hajja, ko Ya Innana, zuwa kafin ya soma......" Da sauri na katseshi.
Ko kusa in yaran daka haifa da Zubaina sun kai goma, ni zan riƙe maka su, in basu tarbiyya har suyi aure. Kawai kishinka ne ya dinga nuƙurƙusan zuchiyata, ganin Zubaina ya famamun abubbuwa da suka faru a baya. Sai idanuna suke nuna mun kamar kallon so kake yi mata, zuchiyata tai ta rura mun abun. Wannan shine abunda yasa nake ta ƙunci, amman ba dan zuwan Yusuf ba. Yau kuma na shiga damuwa a sakamakon rashin samun haihuwata, ko Ya Innana abun yana damunta ko da yaushe a cikin yi mun magana take" Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya dubeni cikin zolaya yace.
"Au kishina ashe kike yi, ɗan duƙununu dani, mummuna dani?"
Kafi mun ko wanne ɗa namiji kyau a duniya. Ka sani kyawun zuchiya shi ake biɗa, ba kyawun fuska da zubin halitta ba. Wannan baƙar fuskar, da wannan jan idon su ke sa in sake jin lallai kana da wani matsayi babba a zuchiyata." Dariya mu ka yi, na faɗa jikinshi, ina share hawayena da bayan hannuna.
"Kai yau naji daɗi, sai yau na samu nutsuwa. Amman zan rama, irin wannan wuya da kika bani, in na kamaki anjima a shinfiɗa, sai na fanshe duk ƙullewar marar da kika haddasamun, dan yau fyaɗe nayi niyyar yi miki" Kalmar data dakatar da nishaɗi da walwalar dake shinfiɗe a fuskata, na sake rikicewa da hawaye. Shi kanshi na lura yayi nadamar furta wannan kalmar. Da ƙyar ya shawo kaina nayi shiru. Kwalli na murza ma idona, na naɗa lafaya ta muka fito.
"Ki yima Hajara magana ta ɗan dinga jiyo miki motsin Yara, da masu zuwa neman kunu" Tsaƙi nayi guntu na harari wajen da Hajara suke zaune da Ahmad"
Dan Allah daure ka faɗa ma Ahmad ɗin, ya sanar mata" Ana cikin haka Ahmad ya taso ya iso wajanmu.
"Sai yanzu zaku je dubiyar, aini na ɗauka tuntuni kunje har kun dawo" Cewar Ahmad" Bulamana yace.
"Kaga ƴar rigimar data tsai damu nan, amman yanzu zamu je mu dawo. Ƙofar a buɗe take madam ta dinga duba mana yaran, sai mun dawo" Sallama su ka yi, ina jiyo Hajara na ce mun sai mun dawo, banza nayi da'ita. Nayi kamar ma bansan me take cewa ba. Muna cikin ɗan sahu ne nake ba Bulamana labarin abinda Hajara take ta yaɗawa a anguwa a game da yara. Shima ranshi ya ɓaci sosai yace.
"Ai Ahmad bai yi sa'ar matar aure ba sam. Yarinya ba kamun kai ba nutsuwa sam. A hakan ma ai ruwa ya daki babban zakara, a lokacin da Ahmad yake da abun hannunshi, meye Hajara bata yi ba. Rayuwar ƙarya iri iri. Yanzu ne fa ta nutsu talauci ya saitata." Har muka isa asibitin Murtala muna ɗan taɓa hirarmu. Alhn daya basu lon ɗin ɗan sahu ne ba lafiya, shi muka je muka duba a asibiti. Daga nan ya wuce dani sahad mu ka siyo chocolate nawa dana yara, a gajiye muka shiga gidan tulus. A cikin wannan dare, mun murji junanmu sosai, Bulamana zame mun yayi tamkar mayunwacin zaki. Rungume da juna muka yi baccinmu mai daɗi. Haka mu ka wayi gari cikin walwala da farin ciki. Takwas Bulamana ya fita, suna da jarabawa a makaranta. Ni kuma dai a hankali yau na kammala komai, sai wani jiri da tashin zuciya nake ji. Sai wajajen tara da rabi ma na isa office. Haka dai wunin na yi shi sukuku. Kamar wasa da zan shiga gida na sai p t. Ai kuwa ina gwadawa ya bani ina da ciki. Jan layi biyu suka fito ɓaro ɓaro. Murna a wannan ranar ba'a cewa komai, duk da a kwance na wuni, amman ina Allah _Allah Bulamana ya dawo in yi mishi albishir. Girki ma na kasa, sai inji amai na taso mun. Sai Uwatale na kira tazo ta ƙarashe mun, ta yi mun wanke_wanke. Hajara sai suntiri take yi mun, so take taji abunda ke damuna, ni kuwa nace mata mura ke damuna, hancina yoyyo yake yi, shi yasa na kasa yin girki. Sai Magriba Uwatale ta yi mun sallama ta tafi. Ina kwance Bulamana ya shigo da ƴar guntuwar sallama ɗauke a bakinshi. A hankali na amsa mishi ina kallon idanunshi, wanda suka ƙanƙance tsabaragen wahalar aiki, ga kuma karatu ma.
"Ba lafiya ne na ganki a kwance a ƙasa?" Hannu yasa ya ɗauki Yusuf daya tawo wajanshi, amman hankalin shi yana wajena.
Lafiya lau, ciwon daɗi da farin ciki ne ya kwantar dani" Zama yayi yana murmushi yace.
"Inna canka dai _ dai ciki ne dake kenan ko?" Dariyar da nayi ta bashi tabbacin abinda ya faɗa dai _ dai ne. Hamdala yayi tare da kallona yana dariya.
"Kuka ya ƙare kenan ko? Sai ki nutsa ki kula da kanki, meat pie da kunu ni zan dinga yi miki, aiki kawai na yarda kije, kuma in muka tafi bikin Wakil, ina tunanin zan ajjiye Yusuf a wajan Ya Innana, ke ma ki kula da kan ki,

38 / 67