MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   57 / 67

168K to 171K   out of 198.3K words

tazo bakina cabkarta nake yi. Bin bokaye masifa ne, da badan naƙi bin Allah a baya ba, da yanzu ina rayuwa dai_ dai data mutane. Wannan bala'i da mai yayi kama ace mijinka ya mari mahaifiyarka yasa ƙafa ya shureta, ya zageta. Innalillahiwainnailaihilrajiun, Allah ka kawo mun agaji, haka nasa Bulama yai ta wulaƙanta iyayenshi. In yaga wayarsu sai yayi tsaƙi ya dubeni yace.
"Su Ba Bakura sun fiye naci kamar ni kaɗai ne ɗa a cikin gida" Ni kuwa a lokacin ji nake yi kamar an yi mun bushara da gidan Aljanna dan tsantsar daɗi. Ina zaune daga ni har Mama a inda Alh Liti ya turemu. Kawai sai muka ganshi a mugun fusace hannunshi riƙe da igiyar wuta. Ihu muka shiga yi ni da Mama, Alh Liti ya shiga zane ni ciki da waje. In mama ta miƙo hannu dan ta tareni haka zai zuga mata bulalarnan. Da mama taga dai da gaske kasheni zaiyi gadan_ gadan ta nufoshi ta cukumeshi. Cizo ta gasa mishi a kumatunshi. Zafin cizon ne yasa ya fyaɗar da Mama a ƙasa ya taka mata ƙafarta. Idanunane suka rufe ruf dukkansu na dena ganinsu ma, sai sautin ihunta kawai nake ji. Sai farkawa nayi naga Hajiya Kubra a kaina. Mama kuma ban ganta a ɗakin ba.
Hajiya Kubra ina mahaifiyata take, ba dai tafiya tayi ba ko?"
"Bata tafi ba Zubaina. Nabeela da Rashida sun raka ta gidan ɗori, kamar ta samu tsagewar ƙashi ne a ƙafa. Abinda nake so dake shine. Muje in raka ki ɗakin Alh yana sama yana jiranki. Sannan zan faɗa miki in kina son kan ki da arziki karki sake tankama Alh balle har yai miki irin wannan dukan." Kaina na sauke hawaye na shatata a kuncina. Da taimakon Hajiya Kubra, da taimakon Nasiba ɗiyar wajanta muka isa ɓangaren Alh. Naci sa'a yana falon ƙasa. Yaran Hajiya Kubra ta bashi yasa hannu ya karɓesu. Rannan nashi a murtuke, ni dai ina ƙasa na ƙume da haushi kallonshi ma bazan iyaba. Ina ji yana mis mis da baki yana ma yaran adda'a. Can ya miƙa ma Hajiya Kubra da Zainab yaran.
"Nasa musu suna Fatima da Aisha. Wannan itace Fatima, wannan Aisha, ai musu inkiya da Hassana da Usaina. Sannan gobe ina da zama da ku a cikin gidannan. Dan naga raini da rashin ɗa'a ya soma damunku ina son zanyi ma tubkar hanci. Ke kuma ki ƙara jaddada ma uwarki, gobe ta tattare ta bar mun gidana. Duk ranar dana sake ganinta a gidannan, saina zauna a ruwan cikinta nayi mata fitsari. Ƴar iska maras tarbiyya, wacce bata gaji tarbiyya ba, masu abun faɗe. Ko Alh da ƴar uwarki ta dabainayeshi da asiri, Asirinku ya tonu, ya sake ta saki uku ya huta, ga lalura data kamu dashi, wallahi baku ga komai ba ma. Ni kaina da ɓarnar da zaku yi mun sai tafi ta Alh tunda na fishi ƙumbar susa, ke da kwanciyar hankali har abada, aurena dake ba saki, babu yaji. Na zame miki ɗuwawu dole ki zauna dani. Ku fice mun da gani." Hmmm da taimakon Hajiya Kubra muka bar shashen Alh Liti. A tsakar gida muka tarar da Zarah tana hararwa, tunda na haihu Zarah ko barka bata leƙo tayi mun ba. Yanzun ma tana ganina ta saka dariya.
"Ahayye, an dai yi abun kunya. Faɗa da mijin ƴa har da cizo, kila dangin mayu ne ku wa ma ya sani" Damuwar dake damuna tafi ƙarfin in tsaya tanka ma Zarah. Jikina har rawa yake yi, maganganun Alh Liti akan saki ukun da mijin Asiya yayi mata ya gigitani. Na shiga tambayar kaina. To ya ma akayi Alh yasan Asiri akayi mishi?" Ina zama a bakin gado Mama suka dawo ita da su Rashida. Ƙafarta tayi suntum, gefen idanunta ya tara jini, ga ciwo a bakinta. Ajjiar zuchiya kawai na sauke, na dinga bin kowa da idanu, kaina kuwa riƙewa yayi gam, jirine ya kwasheni na faɗa gado luu. Dole haka Mama tasa aka kwasheni zuwa asibiti, gado suka bani dole, sabida jinina ya hau sosai. Washe gari Mama ta kama hanyar Najeriya, ko sallama da juna bamu samu damar yi ba. Rashida ke zaune dani a asibiti.








KADUNA:
Misalin ƙarfe shidan yamna Mama ta sauka a tashar mota daga Kano zuwa Kaduna, dan jirginta na Kano ne. Da sallama ta shiga ɗakin ta iske, Rakiya da Naja'atu ɗiyarta. Asiya kuwa tana kwance a ƙaramin gado kamar babu rai a jikinta. Wuyanta ya kumbura yayi suntum dashi himm.
"Rakiya haka jikin na Asiya ya tsananta? Innalillahiwainnailaihilrajiun, Alhn kuwa ya dawo ko tunda yazo ya ajjiye mun ita bai waiwayo ba?" Rakiya tace.
"Yaya haɗarin mota kika yi ne, naga kin shigo harda sanda, ga fuskarki duk ciwo" Zama Mama tayi tace.
"Ke dai Rakiya bari. Mijin Zubaina ne ya haɗa ni da itan yai ta jibgarmu, kinga ƙafata targaɗe da tsagewar ƙashi na samu. Ita kanta fa Zubaina ciwo take yi mai tsananin gaske. Amman wallahi yaƙi ya barni in zauna da'ita, tana asibiti babu mai kulawa da'ita sai kishiyoyi. Ni rayuwarma ta fice mun a kai" Salati Rakiya ta shiga rabkawa ita da Naja'atu.
"Yaya duka fa, yau ni naji tsiya da wasali ƙasa, amman wannan miji na Zubaina kwai tambaɗaɗɗe. Ki duba yanda Bulama yake haba_haba damu, in munje gidansu, ya hadomu da goma sha tara na arziki, ya ɗakko mota ya kawo mu har gida. Abinci da Azumi muma sai dai mu taimakawa maƙota, sallar laiya fa ki duba Yaya har ni yake yi ma laiya, ga atamfar sallah da takalmi da yake aikoqa Zubaina dashi. Ohh duniya kenan, ni na ɗauka yanzu ne Zubaina zata huta ashe kallon kitse mu kai ma rogo?" Mama ta share hawayenta da yake zuba tace.
"Ke dai bari tuna mun wannan yaro Bulama Rakiya." Rakiya tace.
"Kinga Naja'atu ma uwar miji ta hanata zaman auren fur, tasa mijin ya korota gida, amman bai bata takadda ba. Yaya Alh fa ya saki Asiya saki uku. Hmm Yaya da yazo ma ƙin shigowa yayi wallahi, kishiyarta ya turo uwar gidanshi kenan da takaddar ta shigo ta kawo, tana wani taƙama. Ni bama wannan ba, gidajen da yarinyarnan ta giggina aka zuba haya, duk ya ƙwace gidajen, sannan yace duk wanda ya taka gidanshi da sunan kwasar kaya, ko ganin yara to kotu ce zata rabasu. Shi yasa nake zargin kishiyarta ce ta tabka mata wani asirin." Mama kuka wi_wi ta fashe dashi har tana birgima, sai faɗi take ta shiga uku ta lalace, asirinta ya tonu.
"Yaya bafa kuka bane mafita, yanzu meye abun yi? Wajen wanne mai magani zamu kai yarinyarnan?" Mama ta miƙe da ƴar sandarta a hannu tace.
"Rakiya mu soma zuwa gidan Malam Babba. Naja'atu ki fita ki taro mana Ɗan sahu, tunda gidan ba wani nisa." Naja'atu ta fita ta dawo da me ɗan sahun. Ita da Mama Rakiya suka kinkimi Asiya zuwa ɗan sahun. Mama ta rufe ɓarayinta ta biyo su. A bakin ƙofar gidan Malam Babba suka tsaya, sun kuwa ci sa'a yana ciki, dan sun hango layin mata. Mai ɗan sahun suka sallama, aka sake tarairayo Asiya zuwa rauren gidan malam Babba. A benci suka zauna suna riƙe da Asiya. Mama da mama Rakiya kowacce tayi jigum abun duniya ya ishi waɗannan bayin Allah. Mama ta ɗaga wayarta ta kira Musa.
"Halo Musa, kazo nan gidan malam Babba ka same ni, mun kawo Asiya ne" Musa ya amsa mata da cewar shi baya ma garin, yaje wajan wata yarinya a Jigawa. Da tsaki Mama ta datse wayarta tana tsine ma Musa" Mama Rakiya dai bata ce komai ba tana riƙe da Asiya. Sannu kan hankali har layi yazo ya iskesu. Haka suka kuma tattagar Asiya zuwa cikin ɗakin malam Babba. A gefen wata tabarma ya nuna musu yace ta a shinfiɗe Asiyan. Umarninshi suka bi suka shinfiɗeta.
"Jummai lafiya wannan ba Hajiya Asiya bace?" Mama na share zufa tace.
"Itace ka ganta nan kishiya ta sabauta mun ita, miji ya saketa, duk wasu kadarorin data tatsa a jikinshi komai ya kwace. Malam kai mun rai" Miƙewa malam Babba yayi ya tsugunna a gefen Asiya ya kama kanta yana dubawa. Ya daɗe yana nazari kafin ya ɗago da kanshi yace.
"Jummai an fa yanka ta tashi. An samu gagarumar matsala dangane da aikin da nayi ma Hajiya Asiya. Dan kinga wannan ciwon nata? Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya aka turo mata, da yanzu kishiyarta ce a cikin wannan lalurar" Mama tasa hannu a ka tace.
"Shikenan Jummai ƙaryarki ta ƙare alkadarinki ya karye Jummai. Malam to yanzu menene abun yi, sannan wacece tayi mata irin wannan mummunan aikin" Kasar da yake duba da'ita ya soma zanawa, ya jima yana zanawa yana gogewa, daga bisani yace.
"Ƙasa bata nuna mana wanda yayi ƙaiƙayi koma kan masheƙiyar ba. Babbar matsalar shine, maganin makarinshi ne babu Jummai. Yarinyar nan ku mayar da'ita gida mutuwa zata yi. Aljanu sunfi dubu a jikinta. Jummai ku tashi ku tafi." ( Tashin hankali wanda ba'a sa mishi rana. Dama ƙarshen masu bin bokaye ba ƙarshe bane mai kyau. Komai daren daɗewa wata rana zasu zama ababen tausayi) Nan su Mama suka ɗauki Asiya suka nufi gida. Washe gari suka kuma zazzagaye bokaye da ƴan borin da suka sani, duk inda suka je cinye musu kuɗi kawai akeyi a banza amman babu wani canji wuyan Asiya sai kumbura yake sake yi, Mama bata da zaɓi dole taje gidan kawu Tanko ta zayyana mishi halin da Asiya take ciki da kuma wulaƙancin da Nafeesa take fuskanta a wajan mijinta dama danginshi, da irin yanda suka kwashe da mijin Zubaina,tana yi tana kuka. Shiru Kawu Tanko yayi yana nazari tare da jinjina ƙudurar Allah da yanda yake kama mai laifi duk abinda ya shuka ya girbe abunshi. Ya ji daɗin faruwar hakan ba dan baya son su Asiya ba, sai dan ya zame musu izina dama masu karatu baki ɗaya. kwatancen wani ƙauye yayi musu a Bauchi yace su tafi can ko Allah zai sa a dace. Sai dai fa babu kuɗi a hannayensu. Haka dole su Sagiru suka sa gidan gadonsu a kasuwa suka siyar, aka tarkaka kuɗin Mama da Nafisa da Goggo Safiya, ne aka shirya tafiyar dasu, Ita kanta nafisa a cikin tsangwama da hantara take a wajan mijinta, ya ɗauke mata wuta, bata jin daɗin zaman dashi sam. Tayi baƙi tayi muni, duk ƴan kadarorinta sun salwanta a hanyar bin malaman tsubbu da bokaye, da komai nata ya ƙare ne tayi haƙuri ta zuba ma sarautar Allah idanu zanen ɗaurawa wannan bata da na kirki,ga ciki na biyu a jikinta. Halin da Mama ta bata labarin Zubaina tana ciki, da halin data ga Asiya a ciki, da irin yadda Mama ƙafarta take mata mugun ciwo shi yasa ta saduda tabi Allah ta bi koyarwar ma'aiki arrasul Sallallahu alaihi Wasallama. Ko wannan malamin da zasu je wajanshi. Malamine na gaske ba mishiriki ba. Zubaina kuma suna waya da'ita babu laifi kwananta uku a asibiti aka sallamesu suka koma gida.


MRS BUKHARI
[18/08, 9:45 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 52














BULAMA BABBA:


Yau ya kasance ranar asabar, wanda yai dai_dai da ashirin ga watan da Ba Modu ya tsaida ranar meeting na gida. Tun sassafe na gama shirina a gurguje, dan Mama Gana tun asubar fari take jaddadamun in zo ta gidanta mu tawo tare, domun su Ya Ari basa nan duk sunyi tafiya. Ina fitowa na samu Bawa a falo yana aikin gida wanda makaranta ta basu, domun kar a barsu a ranakun hutun haka.
Bawa ina Maryam take, me yasa baka je ɗakin karatunku kayi karatun a can ba, ina su Aneesa fa?" Bawa yace.
"Suna ɗaki dasu Maryam Abba. Yanzu umman Aneesa tayi mata wanka."
To maza tashi zamu je Damaturu yanzu."
"Abba muna da islamiyya, kuma jarabawa zamu zana" kai na dafe dan na sha'afa da batun jarabawar sam. Hannunshi naja zuwa ɗakin yaran na hado kansu muka fito, sai da na kulle shashen, sannan muka nufi Shashen Ahmad muka nufa, a guje suka shige suka barni a tsaye. Hajara ce ta leƙo.
"Bulama ina kwana"
Lafiya Hajara, ya hidima, amma Ahmad fa?"
"Ai ya fita tun safe, yace akwai aikin da zai gudanar a kamfani." Sallama nayi mata kawai na wuce, bayan na bata key. Ko da naje gidan Mama Gana ta gama shiri ta jima tana jirana. Ai kuwa ina shiga ta dirarmun da masifa. Ni dai sai haƙuri nake bayarwa. Muna hanya ne Mama Gana tace.
"Wai ni Bulama Babba baka ji halamar sauyi a muryar uwarka ba tunda Bakura ya rasu ba?" Gabanane ya faɗi ras na dubi Mama Gana nace.
A'a wani abun kika ji Mama?"
"O'o kawai dai ni inna kirata sai in ji tana sha mun ƙamshi. Duk da nasan mutuwar miji akwai ɗaci, amman ai ba mu muka kashe BaKura ba, sa'inshine ya cika. Ni naga kamar ta sauya."
To ƙila dai sabida rashin mijinta da tayi ne, kinsan Ba Bakura da barkwanci." Mama Gana ta taɓe bakinta kawai. Ni kuma na shiga tunanin me yasa Hajja zata ɓullo da wannan ɗabi'un a yanzu da gidan babu abunda suke buƙata sai haɗin kai, da sake riƙo da zumunci. Lallai ta ɗakko hanyar wargaza zumuncin cikin gidan. Amman in sha Allah ba zata samu wannan nasarar ba. Haka nai ta aikin tunane_tunane, hirar ma jifa_ jifa muke yi da Mama Gana, daga baya ma bacci ne yayi awon gaba da'ita." Kai tsaye falon Ba Bakura muka harhaɗu kamar yadda aka saba. Wannan taron shine taro na family na farko da aka gudanar babu Ba Bakura. Kowa ka kalla da ɗan guntun hawayenshi a idanunshi. Mama Gana ma na shigowa ta fashe da kalan nata kukan. Ni dai hawaye kawai nake sharewa da bayan hannayena. A kusa da Gunsum na zauna. Ba Modu ne ya yafito ni da hannunshi ya nuna mini kusa dashi. Dawowa nayi na zauna a kusa dashi.
"Allah ya gafartama iyayenmu, da ƴan uwanmu. Ya gafartama dukkan muminan duniya baki ɗaya, in tamu tazo Allah yai mana cikawa da kyau da imani. Bulama Babba a matsayinka na shugaba kuma jagoran gidannan tashi ka buɗe taron da adda'a domun mu gudanar da abunda ya tara mu a nan, wasu nasan suna da uziri." Umarnin Ba Modu na bi ta hanyar miƙewa na buɗe taron da adda'a mai tsayi daga bisani na zauna kaina a ƙasa.
"Na tara wannan taronne a bisa dalilai. Na farko inaso zan soma da sake jaddada maganar zumuncinmu. Sannan inaso ƴaƴayanku tun yanzu ku zaɓa musu matayen aure, maza_ mazan kenan domun a sake cakuɗuwa, ta hakane zumuncin zai sake yin ƙarko da yardar Allah. Muyi haƙuri da kayukan mu, mu yi haƙuri da ƴan uwanmu. Banda riƙo duk da nasan ba'a yin wannan halin a cikin wannan ahalin. Amman duk wanda yake da abun faɗe yayi bayani. Duk wanda aka yi wani abun da ranshi ya sosu ya sanar kafin in ɗaura daga bayanina." Shiru Ba Modu yayi yana sauraren ko da me ƙorafi.
"To ni dai Modu ƙorafina biyu ne kacal kuma dama irin wannan ranar nake jira in faɗi abinda yake raina. Hajja Gana tunda BaKura ƙasa ta rufe idanuwanshi shikenan mata ta soma cika tana batsewa, in an kirata a waya sai kaji tana magana kamar wata ƴar tauri. To ta fito fili tayi bayanin in akwai abunda yake damunta sai mu ji. In kuma rabon gadon da aka gudanar ne baiyi mata ba sai tayi bayani a gaban kowa. Ƙorafi na biyu akan Yahanasu ne Modu. Ni dai fishi da yarinyarnan da kake yi ya isheka haka nan. Tunda dai tana iya banbance fari......." Ba Modu ya dakatar da Mama Gana ta hanyar ɗaga mata hannayenshi. Gum tayi da bakinta. Kallonshi ya mayar kan Hajja.
"Kinji abunda Mama Gana ta faɗi, kina da abinda zaki ce dangane da wannan tuhumar da take yi miki" Kallonta nayi rannan nata a mugun ɗaure tace.
"Babu wani abun da kowa yayi mun. Damuwar mutuwar mijina itace ta dame ni, ya kamata aimun uzirin. Batun rabon gado ai nasan ba da ka akayi ba. Asalima Bature ne yazo da malaman da suka yi rabon gadon." Ba Modu yace
"To Mama Gana kinji amsarki. Akwai wani mai ƙorafin?" Shiru babu wanda ya tanka, hakan ya nuna babu kenan. Sai Ba Modu ya ɗaura bayaninshi da cewa.
"Sai magana akan Yagaji da Yana iyalan Baana. Ni da su mun dai_daita tsakaninmu zan auresu su zauna a ƙarƙashina, domun faɗaɗa zumuncinmu. Sai ko wacce taci gaba da zama a ɗakinta. Na tabbatar yara zasu yi farin cikin hakan" Nan falo ya ɗau sowa sai hamdala akeyi. Bayan an nutsu yaci gaba da magana.
"Yau za'ayi ɗaurin auren in sha Allah. Sai maganar mata_ matan cikin gidannan surukai da muke da su, da namu yaran da suke gidajen wasu. Na ba ko wacce nera dubu ashirin_ ashirin, ba dan komai ba, ba dan mazajen sun gaza ba, kyauta ce daga baban yaran. Bulama Babba ga kwali nan tun jiya nasa Dala ya wauware dubu ashirin_ ashirin ka miƙa ma matan, surukan gidan in an gama taro sai a basu nasu." Miƙewa nayi na bibbisu da dubu ashirin_ ashirin dinnan sai godiya da washe baki suke faman yi. Sai da falon ya kuma nutsuwa sai Ba Modu ya ci gaba da Magana.
"Na samu ƙorafe_ ƙorafe masu tarin yawa akan gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye_ shayen muyagun ƙwayoyi da na miƙa Yahanasu. Har mijinta yana kai kokenshi wajan mahaifiyar Ahmad nashi. Tazo ta same ni, hatta dattawan anguwa sun tare ni da zancan. Haka dangin Innana su kai ta sintiri duk dai akan batun. To ku sani ba ƙin Yahanasu bane yasa na miƙata wannan gidan ba, kuma ba wai bansan gidan suna azabtar da marasa lafiyar ciki bane. Asalima irin labaran duka da azabtar dasu da akeyi ne yasa na yanke hukuncin kai Yahanasu can. Hannunka baya

57 / 67