Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
a haka har gari ya waye, da nayi Sallah kuma muka koma falon Alh Liti da zama.
MRS BUKHARI CE
[21/08, 3:16 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 59
Muna zaune a babban falon ƙasa da masu zuwa gaisuwa, aka soma shigo da dumamen tuwon shinkafa da miyar Egusinnan, mutane sai ci suke ana hira kamar ba gidan mutuwa ba. Auwal ne ya leƙo yake sanar mana dangin Alh Liti suna hanyar zuwa daga Sokoto, tsofaffin matan Alh ma sunata kiran ƴaƴansu suma fa suna hanya. Shaguna da store_store na kayan masarufi na Alh dake kasuwa duk aka bada umarnin a rufe. Da rana taliya da bushasshen kifi akayi ma baƙi, mu kuma akayi mana jallof rice mai daɗi taji soyayyen naman saniya. Da misalin ƙarfe ukun yamma naƙuda taci ƙarfina dan ko iya tashi na kasa yi. Ana cikin wannan halin su Mama suka iso. Sai mata_ matan da suka cika falonne suka firfice, su Mama da Hajiya Kubra suna kaina, ni kuwa sai kwakwa nake faman ci, cikin ikon Allah a cikin awa guda na haihu, tunda kwana biyu kenan ina naƙudar a tsattsaye dai. Ai kuwa sai ga ɗana namiji sunkucecen gaske na haifa. Mama ce tayi ma jaririn komai, Asiya kuma ita ta kwashe ƙazantarnan ta haihuwa ta zuba a bokiti ta fita tsakar gidan. Ni kuma Hajiya Kubra ta raka ni ɗakina. Ni dai ina kwance ƙwalam sai ga Mama ta shigo da jaririn a hannunta ta naɗeshi da hijabinta.
"Zubaina ashe ciki ne dake shine ƴannan baki faɗa ma kowa ba? Iko sai Allah, wai Alh Liti naji anata zancan wai ɓarayine suka shigo har ɗaki suka kasheshi. Kwana ya ƙare ya bar baya da ƙura wannan bataliyar yara daya tara haka, amman zaku kwashi dukiya. Hmmmm ni dai naji daɗi da Allah ya yanke miki wannan wahalar, ya sake dubanki ya yanke miki takaba kuma. To Allah yasa ƙarshen wahalar kenan, Zubaina muna ganin rayuwa wallahi, abinci fa wannan da ba dan kawunku Tanko ba wallahi da bamu isa munci ba. Sai Asiya da take son ta soma aiki a gidan wata mata, dan mu rufa ma juna asiri. Matar Musa ta gama mallakeshi nera biyar Musa sai dai ya bamu a ɓoye, ke wata rana sai dai ya siyo mana dafaffen abinci ya zuro mana ledar abincin ta taga fa." Hawaye Mama ta shiga sharewa kawai tana jin zafi a zuchiyarta na rabata da ɗanta da suruka tayi. Haƙiƙa na cuci mahaifan Bulama dana raba su da ɗansu, irin wannan kukan da Mama take yi a gabana Hajja tayi irinshi da yawa a gabana.
Mama kiyi haƙuri, a hakan ma mun samu da sauƙi, fatanmu Allah ya yafe mana dukkan kura_kuranmu. Zan je in samu Bulama da iyayenshi, da Yahanasu su yafe mun cutar dasu da nayi ko zanga haske a gaba." Asiya ce ta shigo da bokitin ruwan zafi a hannunta.
"Mama ga ruwan wankan yaron, Anty Zubaina Hajiya tace kije kiyi wanka an kai miki ruwan wankan. Kuma wai dangin mijinku sun iso, in kin gyara jikinki sai kije ku gaisa" Da ido na bita, ta rame sosai, idanta zuru_zuru dasu, kamar ba Asiyar dana sani ba. Amman naji daɗin ganinta akan ƙafafuwanta. Fita nayi tsakar gidan. Kai tsaye ban ɗakin na nufa na gargasa jikina na fito. Na fito na samu su Mama sai cin haɗama suke ma taliya. Wasu siraran hawayene suka surnano akan kuncina. Koɗaɗɗiyar goduwar rigar wani lace na zura, na fito da wani koɗaɗɗen hijabina na saka.
Mama ko zamu je tare mu gaishe da dangin Alh?"
"To sai mu je ai Zubaina, Asiya taso muje." Tare muka fita zuwa falon Alh. Ƴan uwanshi daka gansu ba sai an baka labari ba, sun yi kama kusan su takwas su ka zo. Maza huɗu mata huɗu. Nan muka shiga gaisuwa, tare da ma juna ta'aziyyar Alh. Na dubi Mariya nayi mata barkar haihuwa, itama taimun. Kafin mu fito tsofaffin matan Alh Liti suka soma hallara suma Allah yayi yawa dasu, kuma ko wacce da ƙwanta a gida gadon ɗanta tazo ma. Bani na samu kaina ba sai bayan isha. Ina zaune ina cin abinci a ɗaki, muna taɓa hira dasu Mama. Asiya sai ƴan biyu take ba abinci a baki. Haka dai zaman makokinnan yaci gaba da gudana, sai tattaro dukiyar Alh Liti aketayi, dan ance ranar sadakar arba'in za'a raba gado. Ranar sadakar bakwai Amaryar Alh Liti ta haifo ɗiyarta mace itama. Ranar da Alh Liti ya cika kwana goma kowa ya saki jikinshi, har ana taɗin yanda za'a fantama in anyi rabon gado. Duk yaran Alh Liti sun dawo gida, har da waɗanda suka tafi karuwanci duk sun dawo domun karɓar gado. Tsofaffin matan Alh da danginshi ba wanda ya tafi, kowa ya kafa ya tsare, Nabeela kuwa hannu da hannu na danƙa mata ɗanta da yake mun kallon uwa, sai godiya take zuga mun. Ranar ko da Alh Liti ya cika arba'in a ranar malamai suka soma rabon gado bayan anyi adda'ar arba'in da sadakar su cincin da waina. Rabonnan aketatayi, har zuwa la'asar kafan aka kammala, a ranar naga wasu irin mahaukatan kuɗi da suka sa tsigar kaina su kai ta tashi, gasunan buhu_buhu jaka_jaka. Mu matanshi mu aka soma cirema kasonmu, aka kididdiba mana bayan an cire bashin da ake bin Alh Liti wanda ya kusan lashe rabin dukiyar daya mallaka, amman fa duk da haka dukiyar batai rawa ba, dan akwai gidaje, filaye, garke_garken shanu duk suna rubuce a hannun malamai. Bayan an raba mana namu, Sannan aka raba ma yaran gidan ihu maza da matan suka saka sabida tsabaragen miliyoyin da suka samu, burin mazajen yaran gidan ya cika, dan dama ance duk dan sabida dukiyar Alh Liti suke zaune da yaran, irin wannan ranar suke jira. Dangin Alh dake jahilaine suma jira suke ace ga nasu. Da ba'ace ba, nan tarzoma ta tashi sai waje aka fitar dasu. Mu mata_matan Alh duk mun yarda a siyar da kadararmu data yaranmu a bamu kuɗaɗenmu. Amman mata_matan da suka yi aure an basu shawarar kar su siyar suci gaba da juyawa. Dama maza_maza ba'a maganarsu dan zasu ci gaba da kasuwancin da mahaifinsu yake yi ne. A cikin sati guda aka siyar mana da komai aka danƙa mana kuɗaɗenmu, naga miliyoyin kuɗi cike da jaka. Washe gari ni da Mariya muka fito dan tafiya gida. Hajiya Kubra zata ci gaba da zamanta tare da yaranta a Ghana amman ba'a wannan gidan ba, dan gidan bai fito a gadon yaranta ba. Ni dai nai ma kowa sallama muka kama hanya. Kuɗaɗennan muka samu jakunkuna muka rarraba kuɗin muka bisu da tsummokarai a sama. Mama na goye da Hassana, Asiya ta goya Usaina, ni kuma ina goye da mai sunan Alh a bayana, babu abunda na ɗauka a gidannan duk tsummakaran kayana da su kai ragowa anan na barsu. Motar wani malamine ya rakomu har Airport yai musu bayani ni dai bansan mai yace musu ba, anan yai mana sallama. Sanda na zauna a kujerar jirgi kuwa idanuna a rufe suke ina kukan farin ciki, wani irin daɗi nake ji. Da muka sauka a Lagos sai daɗi ya kuma shigata ina jiyo ƙamshin arewa. Kai tsaye tashar mota muka nufa dan muna tsoron kar a tuhumemu dangane da kuɗaɗen da muke tafe dasu, Najeriya macuta sunyi yawa. Motar tare muka faɗa abinmu. A mota muka kwana cur,. Da na ganni a ɗakin Mama sai da nayi sujudur shukur, ina ɗagowa na yanke da kukan da ni kaina na kasa tantance na daɗine ko akasin hakan. Nayi farin cikin ganin dangina sosai, har kawu Tanko shima yazo yi mun ta'aziyya da shi da Goggo Safiya. Su Mama zakiya duk kowa yazo. Bayan na nutsa ne yau na shirya inason zanje in duba Mabaruka a asibiti. Liti na saka a baya na fito. A tsakar gida na samu Mama a zaune tana gyara kayan miya, Asiya kuma tana hura gawayi. Matar Musa kuma tana tsakar gidan tana wanki sai yarfo ma Mama ruwa take yi. Ayi magana ta nemi zagin mutane, ko Mama tace mu barta duniya ce.
Mama zanje asibity in duba mabaruka bazan daɗe ba"
"To Zubaina dan Allah ki gaisheta da jiki" Sallama nayi musu na fice. Ganin Mabaruka ya ɗaga mun hankalina sosai, tana kwance da robar lumfashi a fuskarta da wasu na'urori suna aiki a jikinta. Bata sanin ma wanda yake kanta. Ina sharar hawaye sai ga Adam ya shigo shida yaran Mabaruka da matarshi Sagira. Sun zama masu kuɗi gasu nan gwanin sha'awa. Ni kuwa a mugun kunyace na gaishesu, Sagira kuwa da fara'arta ta gaisheni, ina bani da guiwa anan suka tafi suka barni jikina a mugun mace. Dubu ɗari biyu Adam ya ajjiyema mamansu Mabaruka suka fice."
Yobe:
Yahanasu
Fitowata daga ma'aikata kenan inason zan nufi shago akwai Amaryar da zan yi ma gyaran jiki. Sanye nake cikin wata baƙar abaya wacce take daga ire_iren kayan da Bulama Babba ya sai mun. Sabida son Bulama Babba yasa na soma ƙaunar baƙaƙen kaya nima. Motata na shiga ina sauke nunfashi, na sa hannu zan murza keyn motar kenan Alh Nura ya ƙaraso bakin tagar motar.
"Haba Yahanasu yanzu kenan ba da ban ina hangoki ba da shikenan tafiya zaki yi ki barni kenan? Na ɓata lokaci sosai ina jiranki, kwanana nawa ina baro office ina zuwa wajanki, amman kin ƙi bani dama" Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Alh Nura nayi jim. A zahiri yana da kamala gashi yana da kyanshi dai_dai shi gashi da haske. Ni har mamaki nake yi to mai yake nema haka wai a wajena da har ya nace mun? Duk da ni kaina nasan munina ya ragu, sabida gogewa babu abinda bata ɗaukewa kuma ina yin gyaran jiki ka'in da na'in, girman shekaru ya sake murje munina, kuma ina gaye fiye da yanda nake a baya, dan shima yana shafe munin ɗiya mace, kwalliya wani babban jigone na ɓoye munin mace mata ku kula da wannan, baƙar fatata har wani walƙiya take yi tamkar jikin kulɓa sabida tsabaragen gyaran da nake yi duk sati, da wata irin haɗin dilka ta bare bari mazauna sudan ( nima ina da ita duk mai buƙata ya tuntuɓeni, in kina amfani da'ita babu ruwanki da shafe_shafen mai, ko wani sabulun gyaran fata mai so ta tuntuɓeni) Ajjiyar zuchiya na sake saukewa, ni tsoron bama wani namiji dama nake yi, gani nake kamar zan koma ɗakina. Duk da naji labarin Yalewa matar Bulama Babba ta kusan haihuwa, kuma na ji labarin yadda take azabtar da su Bawa, duk abinda yake faruwa dasu ina jin labari a bakin Mama Gana.
Alh Nura kayi haƙuri wallahi har ga Allah na mance kana jirana. Kuma gashi sauri nake yi ana jirana a shago ko zamu bari gobe ma yi maganar?" Da sauri Alh Nura ya tari nunfashina yace.
"Ni sai in biki a baya in kin ban dama, inaso yau mu kawo ƙarshen komai" naso in samu in kubce amman fur Alh Nura yaƙi. Ni kuma ban iya musu da babban mutum ba, tsakaninmu da manya girmamawa ce" Motarshi ya shiga ya dinga bina a baya. A hankali na dinga tafiya gabana na faɗuwa nasan ma cewa zaiyi yana sona. Wasu hawayene suka shiga tuntiri akan fuskata. Shikenan abu kamar wasa shekara guda da rabuwata da Bulama Babba, yana ganina ina ganinshi amman sai dai in mai kallon wa, yai mun kallon ƙanwa? Innalillahiwainnailaihilrajiun Allah ka iya mun, ka sassauta mun soyayyar wannan bawa naka, shima ka sassauta mai irin wannan so da yake mun, Bulama masoyine na haƙiƙa. Da waɗannan zantuka na iso shago. A gefen shagon na yi parking motar Bulama Babba na gani a ƙofar shagon, sai da gabana ya yanke ya faɗi, ji nake kamar nayi laifi ina kallon bakin shagon muka haɗa idanu da Bulama Babba mu kai ma juna kallon ƙuda. Alh Nura ne ya buɗe mun murfin motar tawa, harda murmushin shi. Da sauri na kalli Bulama Babba naga yana rarraba idanu a tsakankanina da Alh Nura. Jikina a sanyaye na fito, ya rufe motar. Ƙafafuwana har rawa suke yi sanda nake nufar cikin shagon. Kafin in ƙarasa bakin shagon Bulama Babba ya shige ciki abunshi. Tare muka shiga da Alh Nura cikin in da baƙi maza suke zama, dan wasu su ke kawo matayensu, ko ƴaƴansu, ko budurwayensu.
Bismillah ka zauna ga waje" Na nuna mishi kusa da Bulama Babba. Zama yayi ni kuma cikin dakiyar zuchiya na kalli Bulama Babba da Ahmad nace.
"Yau Bulama Babba kune a shagon nawa, ko madam kuka kawo mun in mata gyaran jiki?" Bulama Babba ya haɗe ranshi tamau, bai ko kalleni ba saima juyawa da yayi ya miƙa ma Alh Nura hannu. Ahmad ne yace.
"Ai Khairat muka kawo gyaran jiki amaryata kenan ai. Ba dai ke kin watsar damu ba, ko irin zuwa duba yara sam bakya yi kin zama Hajiya, ko wanne gida son kasancewa tare dake suke yi a telebijin ɗinsu." Ɗan murmushin yaƙe nayi nace.
Ba haka bane, yanayin aiyukanne basa bani damar in samu lokacin kaina. Ko Damaturu ina jimawa ban shiga ba. Ashe Khairat amaryarmu ce ai ban sani ba." Alh Nura na kalla, shima naga fuskarshi ta nuna rashin jin daɗi, sai kuma naji babu daɗi sam sai nace.
Alh Nura waɗannan yayyenane" Sai lokacin ya saki fuska suka sake sabuwar gaisuwa. Nima na gaishe da Bulama Babba, a daƙile ya amsa, yana gama amsawa ya miƙe tsaye.
"In an gama mata kyaran jikin ma dawo mu ɗauketa, Ahmad muje ko?" Musabaha suka sake yi da Alh Nura kafin su tafi. Shi kuma nasa aka bashi tea kafin in shiga ɗakin aiki. A ciki na samu Khairat harma an soma rage mun aiki. Ban yi wata wata ba, na saka kayan aiki na hau dirzarta ina shafe mata jiki da dilka haɗin ƴan sudan. Bayan na gama na sata a burƙha domun in turara mata jikinta. Duk wannan abunda nake yi, zuchiyata tana wajan Bulama Babba, banji daɗin yanda ya tafi yana fishi dani ba sam. Hannu na wanke kafin in shiga ɗan ofishina naima ɗaya daga cikin ma'aikatan shagona magana nace, ina da baƙo a ɗakin baƙi, ai mai iso office ɗina kafin na wuce. Ban daɗe da zama ba sai ko gashi ya shigo da sallamarshi. Waje ya samu ya zauna a 2 sitter yana fuskantata.
Ina jinka Alh Nura, ina bakin aikine na sake nace bari in baka lokaci. Kyaran murya yayi.
"To Yahanasu dama ba goduwar magana bace, ni dai ma'abocin sauraren shirye_shiryenki ne a ko da yaushe bana missing program ɗin ko sau ɗaya. Daga haka sai naji na soma jin kina burgeni. To sai nasa a ka ɗan mun ƙaramin bincike aka tabbatar mun baki da Aure. Hakanne ya bani damar zuwa inda kike. Ba wani abun bane sonki nake yi har ga Allah da Aure. Kinga ni ba yaro bane, aurenki nake son yi in kin amince, ina da mata da yarana biyar" Sai ya yi shiru yana mai da yawu. Nima nayi shiru kamar ruwa ya cinyeni shurun yayi tsayi sosai.
"Kaddai na ɓata miki ranki ne Yahanasu naji kinyi shiru?" Sai lokacin na ɗago raina a dagule nace.
Kayi haƙuri ni ban shirya faɗawa wata soyayyar ba gaskiya, sannan a gidanmu auren zumunci muke yi, bazan iya auren wani bare a waje ba. Nagode da soyayya sosai, amman kayi haƙuri " Tarar numfashina yayi da cewa.
"Mutum baya ƙin ta mutum ance da ɓarawo ya ruga. Abunda nake so dama ce kawai. Ki taimaka ki bani dama in ɗan kutsa kai cikin rayuwarki, in sha Allah bazan cutar dake ba, ba zaki yi kaicon rayuwarki dana shiga ba. Ko gaisuwa ma dinga yi" naso yin musu, danni sallamarshi naso yi baki ɗaya. Amman sai ya dinga magiya sai kunya ta kamani, dole na bashi number wayata ko dan mu rabu lafiya. Cikin jin daɗi ya yi mun sallama. Nima na koma bakin aikina, ina ta tunane_tunane. Kafin yamma khairat ta sake ta sake yin wani irin haske.
Kai Amarya gaskiya kinyi kyau, yau dai mun gama da ke, sai kuma gobe in Allah ya kaimu. Ashe wana zaki aura? Ai Ahmad yayanane, ni bansan kece Amaryar Hajara ba" Ɗan murmushi tayi tace.
"Nagode sosai Anty, barin in kira baby yaxo ya mayar dani gida" Kai na jijjiga yanda naga tana wani irin gwalangwaso nasan za'asha cabta da Khairat da Hajara. Office nayi komawata na zauna, ina duba takadda dan ganin gobe aiki nawa muke dashi. Ina cikin wannan aiki naji an turo ƙofar office ɗin. Bulama Babba ne ya shigo yaima kanshi masauki.
"Wato har kin soma kula samari bakya fatan mu sasanta da Hajja ki dawo ɗakin ki ko, duk fafutukar da nake yi ashe ke soyayyarki kike sha abunki. Banyi tunanin zaki mance dani ba. Jibi yadda na zama duk dan sabida ke, dame kike son inji da jarabar Yalewa ko da kishinki? Kullum fa saina ba Hajja haƙuri kuma ina san zaki goma ɗakin ki" Idanu na ƙura mishi har ya gama maganarshi tsab, nama rasa me zance mishi sabida gani nake yi kamar ma ya raina mun wayau. Shi yana can da matarshi harya ɗirka mata ciki, amman ni so yake in tsofe a gida inta jira har sai sanda Hajja zata ce ta amince mu dawo da aurenmu, taya ma hakan zai yiwu?.
Hmm Bulama Babba kenan. Oh so kake inta zama ina jiran tsammanin zan koma ɗakinka? Ai tuni nayi haƙuri da kai daga lokacin dana ga Yalewa da titsetsen cikin ka a jikinta. Kaga halamu sun nuna kuna shan romon soyayya ni kuma kana son cika ni da romon baka ko? Kaga ina mugun ganin girmanka kuma kana da babban matsayi a rayuwata, ka riƙe wannan matsayin dan Allah, bazan taɓa iya komawa gidanka ba na riga na gama jinyar sonka" A fusace ya mike tsaye yana nuna ni da yatsa kamar zai mare ni.
"To