Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
ce ta soma kururuwa, ina dubawa naga Ba Modu ke kirana, gabana ya takarkare ya faɗi, ji nake tamkar ya kiranine dan ya tsine mun akan rayuwar dana jefa kaina, da in ina na soma gaisheshi, bayan na ɗauki wayar na kara a kunnena.
"Uwata kina lafiya, yaya mai gidan naki?" Muryata na rawa nace dashi.
Lafiya ƙalau Ba Modu, ya su Ya Innana da su Wakil?" Murmushinshi na dattawa yayi, kana yace.
"Gashi nan a kusa dani, zamu je asibiti Baana ba lafiya jikin nashi yayi tsanani sosai, sai ki kirasu iyayen naki mata ki ji jikin nashi. Kuna zaune lafiya da Bulama ko, kuma ina fatan kina bin umarninshi akan dukkan abinda ya umarceki dashi, in dai ba saɓon Allah bane?" Hawayen da nake kireƙewa ne suka zubo.
E Ba Modu" Abunda na iya furtawa kenan. Ya ɗaura da cewa.
"Allah yayi miki albarka, kiyi haƙuri da dukkan abunda zaki fuskanta, rayuwa a cike take tab da ƙalubale iri daban daban, musamman a gidajen aure. Biyayya da haƙuri shine babban jari, da makamin da ko wacce mace ya dace ta riƙa. Ki sani babu abunda yake dauwamamme face ƙudura da mulkin ubangiji Allah. Yahanasu na horeki da yima Bulama biyayya irin biyayyar da bazai taɓa mancewa da alkhairinki ba, ko da a bayan ranki ne. Hakan shine kaɗai zai sani farin ciki, dukkan wani abu da zaki buƙata na kuɗi ki tambayeni zanyi miki Yahanasu. Dake da Bulama baku da banbanci, nafi son Bulama fiye daku, kamar yadda nafi son Bakura fiye da kaina. Kuma yanda nake ji akan Bakura da iyalanshi, hakan yake ji akan nawa iyalan, kinga kuwa ya zame miki dole kiyi ma mijinki biyayya" Jikina ya mace mus, sai da ya ɗaureni da duk jijiyoyin jikina Sannan yai mun sallama. Kiran gidan nayi, duk matan gidan iyayenmu, sai da na kira kowa na yi mishi ya jikin Ba Baana, shine kaɗai ban samu damar yin magana dashi ba. Ya Innana itama nasiha tai ta ragargazomun, tare da lallamina, Allah sarki uwa, burinta ta faranta ran iyalanta kowa yaji daɗinta, har ya shiga inuwarta ya fake" A hanzarce Bulama Babba ya shigo ɗakin.
"Yahanasu, ki tashi kiyi girkin da za'a kai asibiti, ƙanin Zubaina bai da lafiya. Sannan Ahmad yana hanya da iyalanshi, suma ayi musu girki, sannan ki gyara musu ɗakina, anan zai sauka da iyalinshi."
To Bulama Babba, akwai abunda kake son a girka ne, ko kuma in girka ko meye?" Zama yayi a kujera tare da dafe kanshi yace.
"Ki dafa koma meye kawai" Nan da nan na shiga aikin girki, Awa sama da huɗu, nayi ina abu ɗaya. Tuwon shinkafa da miyar taushe nayi, naman rago nayi amfani dashi, kafin in yi girkin ma sai da na shiga kasuwa nayo cefanen miya dan ba komai muke dashi a firji ba, dana dawo ne na shiga aikin, ni ce har bayan isha ina abu ɗaya, sabida babu kuzari a jikina sam, nasha magunguna sun kashe mun jikina sossai. a gaggauce Na jera kulolin abincin baƙi a falo, wanda za'a kai asibiti kuma na fita dashi, mai gadi yasa a bayan mota. Bulama Babba yana zaune shiru, yayi wani irin mugun zurfi a cikin tunani, sai numfashi yake saukarwa. Abubbuwan dana ɓata na wanke, na kunna turaren wuta, sannan na dawo wajan Bulama Babba nace.
Na gama komai, wanda za'a kai asibitin yana mota" Kai kawai ya gyaɗa mun, sannan yace.
"Na saki girki wuni guda ki kai kina abu guda tun rana har bayan isha, ƴan Lagos har sun shigo Kano. Amman lafiyarki ƙalau kuwa, ko kuwa raini ne da iskanci yasa ki kai haka, ko kuma ƴan uwan Zubaina ne bakya so su ci abincin?" Kaina na ƙasa bance mishi komai ba, har sai da ya gama na bashi haƙuri. Miƙewa nayi na wuce ɗakina, ina jiyoshi yana waya. Ina zama a bakin gado na jiyo sallamar Ahmad da iyalanshi. Dole na saka hijabi na fito falon.
"Malama Yahanasu Amaryarmu, kai masha Allah naji daɗin wannan al'amari sosai" Kaina na sinne na zauna aka shiga gaggaisawa. Hajara tace.
"Yahanasu ya Fandau yaranta nawa yanzu kuwa? Rabona da'ita tun tana goyon wata baƙar ƴarta" Dariya nayi nace.
Yaranta uku yanzu, ya hanya?"
"Hanya an shata, wani irin wawan dereba mu ka samu mai mugun gudu ya dinga wasa da rayuwarmu a titi, ai da sai irin 12 na dare ko 1 ya kamata ace mun shigo Kano." Dariya tayi tana kallon Bulama Babba ta sake cewa. "
" Masha Allah, Bulama lallai anyi gyara, gida ya fito yayi fes." Dariya yayi mata yace.
"Hajara mutanen Ikko an dawo arewa, an baro cikin yarbawa masu kolokolo" Dariya suka yi shi da Ahmad, Ahmad yace.
"Kai dai bari, Ikko ko wahala Bulama? Ai wallahi ina mamakin yaranmu matasa da suke zuwa Ikko ƙwadago, duk arzikin dake Arewa, har sai sunje Lagos zasu nemi kuɗi. Ka gansu a wulaƙance, basu da wajan kwana, ita kanta sana'ar basu da guda ɗaya, duk abinda aka samu yi akeyi kawai. Wasu sun zama ƴan ɓata gari, wasu basu da aiki sai shaye_ shayen muyagun ƙwayoyin da zasu kassara musu tunaninsu" Kaina na sinne ƙasa, nace da Hajara.
Mu shiga daga ciki ku samu ku watsa ruwa, kuci abinci, ku huta" Jakunkunan kayansu mu ka shigar ciki, na ja yaran muka shige ciki. Duk su kai wanka, sannan su ka ci abinci. Hajara macece mai hira da son jin ƙwaƙwab, a fahimtata irin matannanne masu dukan cikin mutum dan suji abinda suke so. Bata san ko a gida, ƴan uwana suna saramun wajan zurfin ciki ba. Har Dala yakan kirani da munafuka in yaso jin gulma ni kuma na ƙi bashi haɗin kai. Allah sarki Dala nayi kewarsu sosai"
Bulama Babba:
Bayan Ahmad yayi wanka yaci abinci, sai muka fita dan kaima su Zubaina abinci.
Kai meye shawararka Ahmad, wallahi ina cikin damuwa sosai, a hakanma daurewa nake yi Ahmad.
"Ni shawarata anan shine. A gaskiya kar ka jira banki suzo su yi gwanjon kayanka, hakan tonon sililine. Ni a shawarce ka siyar da gidanka da duk abinda ke cikin gidan, da kayan shagonka dai dukka, a haɗa musu kuɗinsu akai musu, yafi rufin asiri, fiye da ace banki sunyi gwanjon gidanka. In wani abu ya saura, sai ka ɗan siya ma su Zubaina ɗan kayan ɗaki, ka kama haya kuma, sai kuma mu haɗu mu shiga neman sana'a"
Gaskiya ne maganarka Ahmad, zamu tattauna hakan da Zubaina yanzu in muka je asibitin. Amman wallahi bansan ta inda zan soma neman aiki ba ma" Ahmad yace.
"Ni kam daga Kaduna Kano na nufa acan zanje in ya da zango, zan nemi aiki inna samu to, in ban samu ba, sai in shiga aikin ƙarfi duk wanda na samu sai inyi, kuma kanon tafi kaduna sauƙin rayuwa. Na kira Safiyanu a waya yana kan duba mun waje, ranta mun kuɗinma zaiyi. Cewa fa yayi ana samun gida sukutum na dubu hamsin, ɗaki biyu da bayan gida da kitchen, da ɗan tsakar gida. Ai ya ishi talaka rayuwa muita adda'a Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar, nasan halin da kake ciki kafin ka ɗanɗana nina soma ɗanɗana, a cikin shi ma nake ni." Shiru nayi ina wani nazari a zuchiyata, a haka har muka iso asibitin. A wajan parking ɗin motoci muka haɗu da Zubaina da Asiya Amarya. Tayi ƙyau ta zama jawur, tana ganina ta soma washe baki.
Asiya Amarya kece a gari? A lalle maraba da zuwa" Cikin wasa da dariya muka gaisa. Zubaina suka gaisa da Ahmad, Asiya sai ta ɗan ja gefe tana jiran Zubaina.
Madam ina zaki je haka a cikin darennan?"
"Ai da abinci zanje mu siyo, nace kar aikin yai ma Yahanasu yawa, ga hidimar su Ahmad, kuma mu na da baƙi a ciki sai tea muka wuni sha, ni aikin ma ban samu zuwa ba." Daɗi naji sosai a raina da Zubaina bata ji zafin Yahanasu ba, lallai ta cika mai sauƙin hali.
A'a ai ta jima da gamawa, kin ganshi shi ya tsayar dani" Na nuna Ahmad.
"Zubaina yaya mu ka ji da haƙurin abunda ya faru, ya mai jikin kuma?" Wani ɗan murmushin damuwa da tashin hankali tayi, dan har faɗawa Zunaina tayi, tace.
"Kai dai bari Ahmad, tunda wanna labarin ya riskeni gabaki ɗaya babu abunda yake yi mun daɗi, ni Kadunan ta fice a kaina, wallahi da da hali garin zan bari, dan kaucema masu son ganin faɗuwarka suyi dariya" Carab na tari hanzarinta da cewa.
Ni kaina garin nake son bari. To Ahmad yai mun magana Kano zai koma da zama, in kina ganin babu wata matsala, kuma zaki samu transpa a wajan aikinki ai sai mu kutsa Kanon ko, kinga gaki ga ƴar uwarki Asiya ma ko ya kika ce?" Ajjiyar zuchiya ta sauke ta lumshe idanunta, nima idanun nawa na lumshe ina jin sonta na nunkuwa a zuchiyata, ga tausayinta da nake ji.
"Abban Maryam wallahi mu je, ni ko yanzu kace mu tafi ai da gudu zan bika, ai duk inda kake anan nake. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Sagiru yaron da suka je suka haɗu su kai faɗa, iyayen ɗaya daga cikin yaran sun zo har asibiti sun samemu. A gaskiya sunyi ma mahaifin yaron ɓarna sosai. A shagon mahaifinshi suka same shi, suka ɓarnatar da dukiyar shagon. So suke a biya su, kuma kuɗine kusan million uku. Kasancewata ta ƴar sanda ne yasa iyayen yaron su kai haƙuri basu shigar da ƙara ba, da kotu za'a shiga. Amman na basu haƙuri nace gobe zan kawo musu million ɗaya da rabi tunda su biyu ne su kai ɓarnar. Nasan baka da kuɗi kai kan ka taimako kake nema. Shine nace ko zaka amince in siyar da motata in biya kuɗin?" Ahmad yace.
"To Zubaina Bulama dai yana buƙatar taimako bafa lallai bane in an siyar da dukkan kadarorinshi su biya mishi bashin da ake binshi ba. Ni ina ganin maganar siyar da motarki ki biya kuɗin da Sagiru suka je su kai ɓarna, baima taso ba. Sannan ai da kin bari an hukuntasu, in yaso ƴan uwa su haɗu a gagganɗa a biya waɗannan kuɗaɗen sabida shi kanshi Bulama yana buƙatar kuɗin motar ki a halin yanzu, tunda dole ku siyar da komai naku ku biya banki kuɗaɗensu."
"Ahmad nima hakan naso. Amman mama ta ɗaga hankalinta har hawan jininta ya tashi, dole yasa nima nayi maganar motar. Amman tunda hakane abar zancan motar, ita Mama zan bata haƙuri, Sagiru kuma in danƙashi da kaina, ƙila a shiga kotu, kaga in bamu samu wannan kuɗin ba, sai a rufeshi a gidan yari har zuwa sanda zamu biya wannan kuɗaɗen." Kai na girgiza nace.
A'a Zubaina mota taki ce halak malak, ni na sai miki. Ki siyar, a rufa wannan asirin, muma in sha Allah zamu tsallake. Sannan akwai shawara da Ahmad ya bamu. Nan na zayyane mata shawarar da Ahmad ya kawo, game da maganar siyar da kadarori in biya banki kuɗinsu, ba sai sun yi mun terereba. Tayi na'am da zancan har da ƙarawa da godiya ga Ahmad. Tare muka shiga ciki dukka da kulolin abincin, a cike ɗakin yake da jama'a. A tsaitsaye aka gaggaisa, mu kai musu sallama muka fita. Bamu zarce ko'ina ba sai inda mu ka san zamu samu dillalai masu siyan gida, da masu siyan tsofaffin kaya. Dillalan dai take suka biyo mu suka zo aka zagaya dasu ko'ina suka gani, dan ance da zafi_zafi ake dukan ƙarfe. Million shidda su kaima gidan kuɗi, ya ƙara daraja har da million guda. Bani da zaɓi take na sallamar. Nan muka ɗunguma wajan mai anguwa dan shaidar, wanda zai sai gidan kuma yazo da lauyanshi. Nan akaita cike ciken takaddu. Ana gamawa suka bani kuɗina a Ghana most go, nan na fitar da dillalai, mai anguwa ma na bashi wani abun. Sannan muka wuce zuwa shagona, dan dillalan sunce suna da masu siye. Kayan dake shagon dai na million biyu ne, amman da ƙyar suka saye million ɗaya kuɗi ya zama million bakwai da ɗauriya. Haka mukaita jigila bamu muka samu kan mu ba, sai sha biyun dare., washe gari masu ganin motoci suka zo su ka ga motata data Yahanasu. Nera million huɗu suka siya, kuɗi ya tashi million goma da ɗauriya. A cikin kwana uku dai muka kammala komai, an siyar da komai na gidan iyakar suturune,da abinci kaɗai suka tsira, sai ƴan tarkacen kayan kitchen, su ma an siyar da wasu manyan, irin su gas kuka, firji, da su oven, rice kuka da dange_dangensu. Amman alhamdulillah kuɗin sun cika harda ɗoriyar dan harda su laptop ɗina guda biyu duk na ɗunguma na siyar. A cikin kwana na huɗu muka mayar ma da banki kuɗinsu, muka shiga shirye _shiryen tafiya Kuma. Zubaina cikin ƙanƙanin lokaci ta zuge ta fita hayyacinta, kuka kuwa tayi shi ba iyaka, ana gobe zamu tafi taje gida tanason kwana a gida dan tayi ban kwana da su mama"
Yahanasu:
Tun sanda na fahimci abunda ke faruwa hankali yayi matuƙar tashi. Hajara ce ta ƙara fashe mun baƙin abinda ke faruwa. Nayi kuka sosai, har zazzaɓi saida nayi na kwana biyu. Na sanar ma Ba Modu halin da ake ciki. Hankalinshi ya tashi ainun. Washe gari Ba Bakura ya kirani, yai ta mun nasiha akan sabuwar rayuwar da zamu tsinci kanmu. Na dinga roƙonshi ya taimaka ma Bulama Babba ko da da hanyar da zai samu aikine, amman sai ya ce mun.
"Yahanasu ko da zaku rasa abinda zaku ci, bazan iya taimakama Bulama da gumina ba. Muddin in yana amsa sunan mijin Zubaina. Kuma wallahi babu wanda zai taimaka mishi, na kuma jama kowa kunne. In kun nutsa ki roƙeshi ki zo ki duba Baana jikin nashi yana ta tsananta, ko magana bayayi" A daren nayi shaye _shayen da ban taɓa yinshi ba. Dan ni kaɗai nake jin inata surutan dana kasa tantance, shin mafarki nake yi ne ko ido biyu. Rufin asirina ɗaya ranar Hajara basu kwana a gidan ba, a gidan ƙawarta ta kwana. Tausayin Bulama Babba nake ji sosai. Cikin ɗan lokaci ƙanƙani ya fice a hayyacinshi. Asibiti ma Ahmad ya kaishi ya ga likita, sabida baida lafiya, damuwa da zafin karayar arziki sun haɗu sun zame mai ciwo sosai."
Zubaina:
Abubbuwa duk sun kacame mun, tun daga ranar da Bulama ya rasa aikinshi kawo yanzu. Gashi da Mabaruka ta raka Hadiza wajan boka, ya shaida mata yana nemana. Dalilin da yasa naima Bulama dabara a kan mota kenan, duk abinda na faɗa mishi ƙarya ce zallanta. Ko da mu ka je wajan boka, ya shaida mun, duk aikin da nayi a tsohon gidanmu, sai an sake yin sabo, tunda mun siyar da gidan. Haka na narka mishi uban kuɗi ya haɗamun komai sabo, harda wasu muggan asiran, muka kamo hanya muka dawo. Hadiza kuwa a washe garin ranar da suka je wajan boka, mijinta ya kamo hanya yazo bikonta, bata kuma sati ba, ta tattara ta koma gidanta. Lallai na yarda da aikin wannan boka, dan yafi ƙarfin a kirashi da yankan wuƙa. Mama kuwa da taji labarin rasa aiki da Bulama yayi, da barin garin da zamu yi, hankalinta duk ya tashi, dan Bulama shine gatanmu, sauƙinta ma Asiya mijinta shima yana hidima dasu Mama yanzu, fiye da Bulama kasancewar shi hamshaƙin ɗan kasuwane. Yau a gida zan kwana, washe gari zamu wuce Kano, tare da rakiyar Goggo Rakiya.
"Oh ni Jummai yanzu gobe uwar haka kuna baƙon waje, yanzu sai kunje zaku tsinci kayan ɗaki irin su gado katifa ko?" Kai na gyaɗa nace
Sai munje tukunna zamu siya, ni ina da kuɗaɗena a ƙulle a marata. Ƙoƙarin da zanyi shine, duk wata zan dinga turo kuɗi ana mun gini kawai, da zaran an gama sai in zuba haya, ina karɓar kuɗaɗena ga wannan dubu ɗari biyun Mama a ƙara a gini, ko ya kika gani Mama shawarata ai tayi ko?" Hannu Mama tasa ta karɓi kuɗaɗen da na miƙa mata, sannan tace.
"Ƙwarai da aniya kin koyi farar dabara, karki sake hidimar gidan ta dawo wuyanki, ita kanta baƙar kadarar ki barta taje tayi aikinta ni ina ganin zaifi. Kinsan dai bazata kaiki yawan albashi ba, sai ku dinga amfana da nata kuɗin, kafin shi Bulaman ya samu aiki, ai yasan manyan mutane komai na ƙasarnan hanya ne, aikin bazai zame mishi matsala ba. Amman naji muku zafi. Ita kuma waccan baƙar kadarar ki sake saka mata karen tsana, ki bata wahala ainun da ƙafafunta zata bar miki gidanki ku zauna daga ke sai ƴaƴanki." Mun jima munata saƙawa da warwarewa, daga bisani bacci ya ɗebeni. Da sassafe sai ga Goggo Rakiya ta iso da shirinta tsab na tafiya. Bamu wani ɓata lokacin ba, mu kai ma Mama da su Nafisa sallama, muka koma can gidan. Ƴan bargunan da muke kwana akwai, da labulaye da suka rage duk su Bulama sun zuzzuba a cikin buhu. Da ƴan kayayyakin kitchen irinsu tukunya, plate da dai sauransu duk an kintsa kayan waje guda. Ƙaramar mota muka ɗauka sharon har ƙofar gida ta kwashe mana kayanmu, mai gadi Bulama ya miƙama keyn gidan muka fice a gidan. Kuka na saka mai tsuma zuchiyar mai sauraro. Bulama kuwa kanshi na sama, ashe shima hawayen yake zubarwa. Yahanasu kuwa dama tunda muka shigo gidan take hawaye. Goggo Rakiya da Hajara ne su kaita rarrashina, Ahmad shi kuma ya riƙe hannayen Bulama yana mishi magana. Murmushi kawai yayi, tare da maido hankalinshi gareni, yaita rarrashina. Ba ƙaramin daɗi naji ba da naga ko kallon inda Yahanasu take baiyi ba, balle ya rarrasheta akan kukan da take faman yi.
Yahanasu:
Tun mankas ɗin dana yi jiya