MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   47 / 67

138K to 141K   out of 198.3K words

ƙofar fita suka ci karo da Musa ya fito saga ɗakinshi da yake hanyar waje saɗab_saɗab da budurwarshi yana riƙe da ƙugunta.
"Hiye ba shakka Musa. Kai amman wannan yaro kwai kwashasshe. Wato so kake ka cika mun gidannan da yaran shegu ko?" Ta dubi yarinyar data yi tsuru_ tsuru ta nunata da yatsa tace.
"Ke kuma inna kuma ganinki a cikin gidannan. Wallahi saina sa Sagiru yayi gunduwa_ gunduwa da namanki ya watsar dan ubanki. Ku kuke lalata mun yaro ko? Fice ki bani waje, kai kuma muje ka rakani wajan malam" Da sauri yarinyar ta fice a gidan. Musa kuma ya bi Mama suka jera.
"Musa da kai da Sagiru so kuke in faɗi in mutu ku huta. Jiya_jiyannan fa ƴan sanda har cikin ɗaki suka zo neman Sagiru. Zarginsu ake wai sun shiga Kasuwa sun fasa shagon Alh muttaƙa sun yi sata. Tun jiyan rabon da in sashi a idanuna, ƙila ma yana police station. Shi nemo jafa'i kai nemo fitna. Gashi gobe zan tafi Ghana Zubaina ba lafiya ta samu karaya. Inna dawo zamu zauna ka faɗa mun yarinyar da kake so, sai inje da kaina in nemo maka auren, ko in tura kawunku"
"Ni Mama har yanzu ba'a ma haifi matar da zan aura ba. Ki barni kawai aure ba yanzu ba. Kiyi haƙuri zan shiryu. Sagiru kuma ko ɗazu na ganshi a saman katangar gidanmu, harma yace in gaisheki, dama lafiyarki yazo dubawa." Da wannan hira har suka isa gidan Malam, kai tsaye akai musu iso suka shiga. Malam yana zaune a kan buzunshi. Ta kwararo mishi bayani akan Zubaina da mijinta. Da kuma Musa da ɗabi'unshi.
"Jummai babu matsala, akwai rubutu mai zafi da zanyi mata a allon ƙarfe, za'a wanke da ruwan gawa. Da daddare ki turo Musa ya karɓa miki, sai ya karɓi nashi shima." Mama na yashe baki tace.
"Godiya muke Malam Allah ya ƙara girma. Sai dai malam kafin alƙalamin sai in na dawo zan bayar dai."
"Haha Jummai ai babu komai an riga da an zama ɗaya" Sallama su kai mishi, suka fito, daga ƙofar gidan Malam kowa ya kama gabanshi dan ba gida zasu ba dukkansu.








BULAMA BABBA:
Tunda mu kai sallama muka shiga cikin gidanmu. Matan gidan su kaita tambayata yanda na baro mai jiki. Gunsum kuwa sai ƙarema gidan kallo yake yi yana faman jijjiga kanshi.
Tsaya bari in shinfiɗa mana tabarma, ko in ɗakko mana katifa muyi kwanciyarmu a tsakar gida, ɗakin ba shiguwa yake yi ba. A tsaye cike da ta'ajibi na bar Gunsum. Ahmad ma ya wuce ɗakinshi, ina jiyoshi yana rangaɗama Hajara kira. Leƙowa cikin ɗakin namu Gunsum yayi. Hawaye naga yana sharewa. Ni kuma na ɗaga katifa zan fitar mana. Hannuna Gunsum ya kama cike da rauni yace.
"Bulama Babba, yanzu a cikin irin gidannan da ɗakinnan kuke rayuwa harda yaranku. Dama haka rayuwa tayi da ku Bulama Babba, aikin gandirobar da kake yi ka dena ne, naji Ahmad yace ɗan sahunnan naka ne kake tuƙawa ka nemi kuɗi? Meye amfanin zumuncinmu, meye amfanin dukiyar da muke dashi? Dukkanmu muna cikin rufin asiri, amman jibeku a cikin damuwa da ƙunci, da talauci. Bayan mu ka bamu kulawa da soyayya, ka bamu kariya dukkanmu. Me yasa Ba Bakura ya ɗauki zafi da kai haka har ya kasa yarda mu tallafa muku?" Idanuna na ƙura mishi ina nazarinshi. Ni kaina kukan nake son dama da hali inyi ko zan ji daɗi amman ni babba ne. Dafashi kawai nayi nace.
Haba Gunsum, ai baku bane gaba dani, nine gaba daku, ni yafi cancanta in tsaya muku ba ku zaku tsaya mun ba. Batun aiki kuma, mun jima da aka sallamemu a aiki, lone muka ɗauka na ɗan sahu muna fita aiki, muna cin abinci. Yahanasu tana zuwa aiki, sannan tana sana'ar sai da kayan ruwa kaga firjin dana siya mata. Kusan ita tai ta ɗaukar nauyin komai na gidan, har sutura ita ke siya mini. Ni kuma saina koma makaranta nayi mastas ɗina, yanzu haka jarabawar ƙarshe muka zana. Kuma harna samu gurbin koyarwa a Jami'ar Bayero. Dai_dai lokacin da na samu nutsuwar da zan kula da Yahanasuna wannan abun ya kunno kai. Gunsum Ba Bakura yana da gaskiya kuma ya fiku sona. Nayi imani a hanya yake son ya ɗaurani mai kyau, ba gashi munata rayuwarmu ba. Ai ni iyakar yafemun kura_kuraina da yayi wallahi Alhamdulillah" Gunsum yace.
"To amma Bulama Babba!.
La kar kace amma, fitar da katifarnan bari in ɗakko maka kunun zaƙi" Katifar ya ja ya fitar, ni kuma na ɗebo mana kunu gora biyu na fito. Hayaniyar Ahmad na dinga jiyowa daga ɗaki yana rikici da Hajara. Ba shiri na isa ƙofar ɗakin nace.
Ahmad kaima Allah ka rabu da'ita kayi haƙuri haka nan ya isa." Leƙowa yayi yana kumfar baki yace mun.
"Daga shigowata dan nayi mata maganar me yasa tai ta yayata lalurar data samu Yahansu. Sai fa kawai ta dirarmun, har tana mun tafi sai kace muna Lagos, bansan me yasa surutun Hajara yayi yawa ba munafukar yarinya" Kai na girgiza nace
Bai kamata ka biye mata ba. Kayi haƙuri maganar ta wuce hakanan kar ku tashi yaran a barci." Hajara ta iso inda muke tana sababi kamar zata ari baki.
"Baka isa wulaƙantani akan wata banza ƴar shaye_shaye ba. Waye bai san shaye_shaye take yi ba. Kullum cikin narka ƙwayoyi a lakasera take. Ahmad ni na gaji da aurenka ka sake ni in huta." Shiru nayi ina nazarin maganganun Hajara. Sai naji take na gasgata maganarta kullum Yahanasu a cikin shan lakarera take, babu ranar da bana ganin gorar lakasera a jakarta, kenan Hajara tasan Yahanasu tana shaye_shaye kenan? Jikina a mace na dubi Ahmad wanda yake shirin marin Hajara. Ga matan gida har sun soma zuwa ban haƙuri.
Haba Ahmad ka rabu da yarinyar nan dan Allah, karka damu da abunda take faɗa." Wucewa nayi na barsu nan na shige ɗaki. Nan na shiga binciken kayayyakin Yahanasu, ban samu komai ba, jakunkunanta na bincikesu babu komai a ciki. Jiki ba ƙarfi na fito na samu su Ahmad a waje yana zuba musu miyar tuwo. Kallona Ahmad yayi yace.
"Ya dai kar dai maganganun Hajara ne yayi tasiri a jikinka? Zo ka zauna kar kace komai kaci tuwonnan kasha magani tukunna" Zama nayi Ahmad ya tusani a gaba sai da naci tuwonnan da yawa, ya bani magani nasha. Gunsum dai baya cewa komai in banda tagumi da yayi yana kallona. Ahmad yace.
"To Alhamdulillah naji daɗi daka daure kaci abincin. Gunsum muci tuwo, abincin namu sai haƙuri babu kifi ba nama, sai daddawa da tafarnuwa."
"Yaya Ahmad baku kyauta mana ba, da kuka ɓoye mana halin da kuke ciki. Yanzu munanan cikin wadata ku kuna cikin rayuwar ƙunci. Jibi gidan da kuke zaune, da anguwar da kuke shi kaɗai tashin hankali ne mai girma." Dariya Ahmad yayi ya saka lomar tuwo a bakinshi, sai da ya tauna ya haɗiye, yana lasar baki yace.
"Gunsum kenan, ai rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki sai dai muce Alhamdulillah. Tunda bamu taɓa barin iyalanmu cikin yunwa ba. Yaranmu kuma suna zuwa makaranta ta dai_dai ƙarfinmu. Gunsum ita rayuwa ai juyi_juyi ce, mu kanmu bamui tsammanin zata juya damu haka ba, khairan in sha Allah. Bismilla kaci tuwo da zafinshi kasha kunu. Mijin tace ne yayi kunun zaƙin fa. Har goruna shi yake wanke mata a tsakar gidannan, mata suita zinɗensa. Murmushi kawai nayi musu, Allah sarki Ahmad aminin arziki kenan ( KAMAR AMINU DA SAMINU) Bayan sun gama cin tuwon Ahmad yace.
"Ya batun kwanciya fa Bulama, a ɗakin zaku kwanta ko a tsakar gidan? Naji cikin da zafi, ga ba wuta"
A tsakar gidan zamu kwanta Ahmad. Shi ya kwanta a katifar, ni wannan daddumar ma ta isheni." Ni dai a cikin wannan daren, babu wani bacci dana samu damar yinshi. A sallaya na kwana ina nafilfili da adda'ar samun lafiyar Yahanasu. A cikin kunnuwana akayi kiran sallar farko na assalatu. Ahmad da Gunsum na jira su kai alwala muka nufi masallaci. Bamu muka baro masallaci ba, sai da rana ta fito mu kai nafila raka'a biyu, mu kai addu'o'i sannan muka fito.
Ahmad kayi ƙoƙari ka tafi aiki yau, ni kuma zan kai kekena wajan parking. Nagode matuƙa gaya."
"Bulama ka wuce haka a wajena. Akwai abinci a gidan wanda zasu ci yau. Zan tsaya tare da kai zuwa gobe, muga yanayin farkawar tata. Kuma kaga yau ƴan Damaturu zasu iso, nasan dole kana buƙatata a kusa da kai. Muje wajan mai waina mu siya ko?" Gunsum yace.
"To muje sai a siya harda yaran. Wainar dubu biyu Gunsum ya siya mana. Muka koma gida, Ahmad ya kaima su Hajara da yaran nasu. Mu kuma muka ci namu. Ni da Ahmad ne mu ka yi wanka, muka sake kaya. Gunsum yaƙi yin wanka, nasan bazai iya ba dan yana da ƙyanƙyami.
"Yaya Ahmad ga dubu biyar ɗinnan aba Anti Hajara tayi ma su Mama Gana girki dan Allah. Karɓar kuɗin Ahmad yayi ya koma ɗaki. Mu kuma muka fita dan jiranshi a cikin motar Gunsum. Bai jima ba, sai gashi da filas ɗin ruwan zafi. A hanya Gunsum ya saima su Ya Bagulaji lafiyayyen abinci a restaurant muka kai musu. A barandar kusa da ɗakin da Yahanasu take ciki muka samesu. Ya Bagulaji tana kwance a tabarma. Aissa tana waya ganinmu yasa ta kashe wayar ta miƙe ta karɓi ledar hannun Gunsum na take away ɗin su, da filas ɗin tea ɗin hannun Ahmad.
"Sannunku da zuwa Yaya Ahmad, Bulama Babba, Gunsum. Kun tashi lafiya?" A tare duk muka amsa mata. Jin muryoyinmu yasa Ya Bagulaji ta tashi. Cikin ladabi muka gaisa tare da tambayarta mai jikin.
"Hmmm jiya munga tashin hankali sosai Bulama. Yahanasu ta farka misalin ƙarfe ukun dare. Tai ta bige_bige tana dariya, da wasu irin sambatu marasa daɗin ji. Tana ta batun cikinta wai bai zube ba ko, tana tambayata. Bafa ta dena surutai ba, har sai da akayi mata allura bacci yayi awon gaba da'ita. Ko abinci bata samu taci ba, sau biyu Aissa na zuba mata abincin tana ɓararwa. Haka ɗai ɗakin ya kasance, kowa naji da ƴan uwansu marasa lafiya. Kai wannan yarinya ta bani tausayi. Yanzu haka zamu zuba idanu muita kallon Yahanasu a asibitinnan?" Kaina ne ya sara mun, dama ciwo yake yi mun kamar zan zauce ni kaina. Wannan mummunan labarin ya sake rikirkitani ainun. Magana wannan na kasa. Sai binsu da idanuwa nake, suna ta mai da zance.
"Ya Bagulaji ga abincin kari nan ku karya. Su Wakil sun taso ne?" Cewar Ahmad. Ya Bagulaji tace.
"Ai hankula yaƙi kwanciya, tun kafin asuba tayi suka ɗakko hanya, sallar asuba ma a hanya zasu tsaya suka yi. Ku je ku ga Yahanasun. Ya kamata ka kawo mata kayan sawa ko?"
To Ya Bagulaji za'a kawo. Miƙewa nayi su Ahmad suka mara mun baya. Da wata nurse muka ci karo, kamar wajensu Ya Bagulaji zata je.
"Yauwa bawan Allah kamar kaine mijin Yahanasu ko?" Cikin sauri na ɗaga mata kai.
E nine lafiya?"
"E lafiya dama ta farka ne, ya kamata tasa wani abun a bakinta, kuma za'ayi mata allura da bata magunguna, dole sai da nata a kusa, dan duka take yi sosai. Juyawa tayi muka bi bayanta. Tun daga bakin ƙofa nake jiyo ihun Yahanasu tana.
"Ku rabu dani, juna biyu ne fa dani, ku barni ni bazan sha komai ba, banason nayi ɓari. Sauri_sauri gudu_ gudu na isa bakin gadon da Yahanasu take nasa hannuna na riƙeta, na kalleta ta canja kamar ba ita ba. Sai surutai take yi, can kuma tayi shiru hawaye na kwarara a gurbin idanuwanta. Sai da ta samu nutsuwa nace
Gunsum kira Aissa ta tawo da abincinta maza. Tashi ki zauna Yahanasuna" Tana kuka tace.
"Nifa lafiyata ƙalau me yasa aka kawo ni nan?" Tambayata take yi.
Zasu sallameki yanzu. Kici abinci tukunna." Kai ta ɗaga mun halamar to. Aissa ce ta iso da take away da kofin tea mai madara. Zama nayi na dinga bata jallof ɗin shinkafar wacce taji kayan lambu. Tas ta cinye, shayinma tas ta shanye shi.
"Na gama a sallameni to?" Ta faɗa tana ƙara kafe ni da idanu. Sai kuma ta fashe da kuka. Maganin na narka a cikin kofi na ɗura mata. Nurse kuma tayi mata allura guda biyu. A hannuna tayi bacci, na gyara mata kwanciyarta, na rufeta. Tsuru nayi ina sauke ajjiyar zuchiya, baccin magani take yi mai nauyin gaske. Kowa yayi shiru da abunda ko wannenmu yake ƙissimawa a zuchiyarshi. Haka nursses ɗinnan su kai ta bi gado_gado suna bama marasa lafiya magani, wasu da allura wasu babu allura. Sai da suka gama tsab, suka ce mu fita mu basu waje, su samu su huta a tsanake, basa son hayaniya. Haka muka dawo wajen Ya Bagulaji muka zauna. Gama karyawarta kenan.
"Yanzu nake son in biyoku, Yaya akayi, taci abincin kuwa?"
Taci Ya Bagulaji, ni sha'anin jikin nata ya tsorata ni. Ni ina ganin a sake mata asibiti zaifi. Amman bari su Ba Modu su iso muji wanne hukunci Ba Bakura ya yanke a kan lamarin." Ya Bagulaji tace
"Hakane nima zuwan iyayen naku nake jira, inji me zasu ce. In sunce a barta ai shikenan, in kuma suka ce mu sake mata asibiti shikenan. Suma Dawanau suna iyakar ƙoƙarin su, tunda daga gari_gari suke amsar marasa lafiya. Da dama sun warke an sassallamesu. Yanzu jiya wata baiwar Allah da take jinyar mahaifiyarta gadonsu na kallon namu. Cemun tayi sanda ta kawo mahaifiyarta daga Jigawa har ɗaɗɗaureta akeyi a jikin ƙarfen gado. Makarai ke damunta. Amman baka ga jikin nata yanzu yanda yayi kyau ba. Watansu huɗu yanzu suna jinya. In kaga uwar ba kace ma marar lafiya bace. Sai in hira kuka soma zaka ji tana sakin layi a wasu wajajan. Mu yi ta adda'a." Haka mu Kai ta zama a asibitin. Ana dab da azahar su Ba Modu suka iso. Muna zaune sai muka gansu tafe. Ba Bakura da Ba Modu suna gaba. Ya Innana da Hajja, da mana gana suna biye dasu. Sai su Dala da wakil, da da Yanunu da Fandau, da Yurom babban ɗan Mama Gana. Da sauri muka tashi muka nufesu. Ko wanne ka kalla a cikinsu suna cikin damuwa. Musamman Ya Innana idanuwanta duk sun koɗe. Ba Bakura ya sauke ajjiyar zuchiya yace.
"Kuyi mana jagora zuwa ɗakin da Yahanasun take." Ahmad yace.
"Ba Bakura da saura kaɗan kafin aba masu zuwa dubiya izinin shiga. Ku zauna ku huta kafin lokacin yayi. Da zaran anyi azahar zasu buɗe ƙofa." Zama matan su ka yi a tabarma. Mazan kuma muka zazzauna a benci. Nan aka shiga gaggaisawa. Ba Bakura yace.
"Naji duk abunda Dr tace akan Yahanasu. Nayi mamakin yanda Yahanasu ta tsinci kanta a cikin wannan yanayin. Shaye_shaye a cikin zuriyar gidanmu. Kuma ma ba namiji ba mace. Ina ɗumbun ilimin da muka ba Yahanasu ya tafi? Qur'ani shine maganin dukkan wata damuwa, me yasa bata riƙe kanta ba. A kanta aka fara fyaɗe ne ko a kanta aka soma shiga ƙunci? Ta tabka kuskure babba yarinyar nan, kuma ta kasa sanar ma da kowa halin da take ciki har sai da wankin hula ya kaita dare. Shikenan ai yanzu gashi abunda ta jawo mana ta gama zubar mana da kima da darajar gidanmu." Haki ya soma yi, idanuwanshi na zubar da hawaye duk yabi ya rikice yana shirin fita a hayyacinshi. Ba Modu yace.
"Bakura kayi haƙuri ka dena wannan hawayen ya'isa haka. Ni ina ganin adda'a ya dace mu yi ma Yahanasu, tunda abunda ya faru ya riga da ya faru. Ta shafa mana baƙin fentin da bazai taɓa gogewa ba, wallahi ji nake kamar in haɗiye zuchiyata in bar muku duniyar ko zan samu sassauci. Ka duba duk tarbiyyar da muka bata sai ta ɓige da shaye_shaye. Ace Ɗiyata aka samu da shan miyagun ƙwayoyi masu gusar da hankali?" Ba Bakura ya riƙe hannun Ba Modu gam yana sharar hawaye yace.
"Duk abunda ya samu Yahansu wannan yaron shine silar komai daya kwaso mana bare ya cakuɗa mana ita da zuriyarmu. Da ace sanda muka hanashi auren Zubaina ya haƙura ya janye duk haka ai bazata faru ba laifin Bulama Babba ne, ya azabtar da Yahanasu ainun. Yarinyar da muka aura mishi ita tana cikin ciwon damuwa, da ace ya kula da'ita da mance komai zata yi. Allah kaɗai yasan irin azabar daya gana mata harta tsunduma kanta harkar shaye_shaye, ya ba zata shiga mummunan hali ba? Muma fa yaronnan sai da yasa mu rama da rashin bacci, ballantana Yahanasu yarinya muma harda laifinmu Modu da muka ɗau dokin zuchiya." Ƙasa nayi da kaina nayi shiru gabana na dokawa. Mama Gana ta sake ruruta lamarin ta hanyar dawo da bara bana.
"Shine kam sila. Muma ya wulaƙantamu balle Yahanasu. Zubaina waye bata mulkaba a cikinmu. Yaronnan a ranar da zamu dawo Damaturu sassafe ya fice a gidan ya barmu. Ya ba mai gadin gidanshi kuɗi ya bamu. Tunda ya ɗaukemu ƙwaɗayayyu kamar dangin shegiyar tsohuwar matarshi mai idon cin nera. Bulama ka cucemu mu kam gaskiya. Aurenka da Yahanasu bai amfana mana komai ba, sai baƙin ciki da ci baya da aka samu." Kuka ta fashe dashi har tana buga ƙafa. Da idanu kawai na dubeta an rasa wanda zai rarrasheta. Hajja naga ɓacin rai sosai a fuskarta amman bata ce da kowa komai ba. Ya Bagulaji tace.
"Haba ku tausayama yaronnan kar kusa ya zauce mana. Ku duba yanda ya rame ya fice a hayyacinshi. Ku dubi shigarshi mana. Wancan abinda ya faru ai ya farune a bisa ƙaddarar

47 / 67