MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   60 / 67

177K to 180K   out of 198.3K words

shiga dan su nuna mun kemis ɗin, yana can cikin ƙauyan ne. A nan na ɓata lokaci sosai, bani na baro wannan ƙauyen ba sai wajajen sha biyu da arba'in na rana. Sai da na kai Baba har gidanshi, kuma a ƙauyen gaba yake kuma can ciki, kasuwa ce yaje ci a ƙauyen dana bigeshi. Nera dubu goma na danƙa mishi, yai ta bina da adda'a har sai da na ɓace ma ganinshi. Misalin ƙarfe biyun rana na shiga cikin layin mu. Ina shan kwana na hango motar Ba Modu a gabana. Suna tafe, gabana ne ya sake tsananta bugawa, ina jin nauyi da kunyar ganin Yahanasu da shi kanshi Ba Modu ɗin, uwa uba Ya Innana. Motarsu na shiga cikin garejin tawa na biye a bayansu. Jim nayi a cikin motata, har sai da naga fitowar Ba Modu da Ya Innana, ban gushe ba sai ga Wakil da Yahanasuna suma sun fito. Sai murmushi take tana kallona. Babu guiwa na fito daga mota, ƙurama juna idanu mu ka yi na wasu lokuta. Kifiyoyin so sai sossoke mun zuchiya take yi. Idanu na lumshe tare da ɗaga hannuna sama.
Allah na gode maka daka bama Yahanasu lafiya, ubangiji ka kareta daga faɗawa wata fitna, ka kare ƴan baya." Da Ameen dukka suka amsa. Da murmushi na ƙarasa garesu, Yahanasu ta kalleni tana murmushi, nima murmushin nake mayar mata, tayi muguwar rama bata wasa ba, Yahanasu abar a tausayama ce.
"Bulama sai yanzu kake tafe, me yasa baka zo tun wuri ba" Cewar Ba Modu daya katse mana hanzari ni da Yahanasu wacce ta cike ni da kallon soyayyar nuna yabawa. Kai na sosa nace.
Wallahi na ɗan samu hatsari a hanya ne na bige wani dattijo. To hidimar kaishi kemis ne ya tsayar dani. Amman ba wani rauni bane yaji mai yawa ba. Ya Innana barkan ku da dawowa" Wakil ya matso yana tambayata.
"Amman Bulama Babba baka ji ciwo ba kai ko?" Murmushi nayi na dafa kafaɗarshi kawai. Ba Modu yace.
"Allah ya taƙaita ka dinga kula sosai Bulama, rayuwa ita ba lalle bane farin ciki ya ɗore ba. Dole yau aji sanyi gobe kuma a busa zafi. Muje ciki mun kwaso hanya." Gaba su Wakil su ka yi da Ya Innana, Ba Modu ya mara musu baya, Yahanasu na shirin bin bayan Ba Modu, na jawota ta dawo da baya. Idanu na zuba mata, ina jin sonta da tausayinta na nunkuwa a cikin zuchiyata. A jikina na mannata dukkanmu muka sauke ajjiyar zuchiya. Mun jima a haka, har sai da muka soma jiyo kororoton ƴan cikin gida, masu murnar dawowarta, ala dole na zareta daga jikina ina kallonta.
Har gaban abada bazan mance alkhairinki ba, kuma bazan dena sonki ba, da sonki zanta rayuwa" Gunsum ne ya shigo cikin garejin motar yana kiran sunan Yahanasu. Dole muka fito zuwa cikin gidan. Yanyame Yahanasu mata su kai a tsakar gidan, su Dala sai washe baki suke yi. Ya gaji ta kamo hannunta tana.
"Ya'isa ku barta ta huta tukunna, sannu Yahanasu an sha jinya" Ni kuma bin bayan Ba Modu nayi da naga ya nufi hanyar turakarshi.
"Bulama Babba, maza jeka ka cika umarnin mahaifiyarka, in ka dawo mayi magana ka same ni a ɗaki. Ka zama mai juriya da dangana Bulama Babba, ka zama mai gaggawar bin umarnin iyayenka kaji ko?" Je ka maza Allah yayi ma albarka A sanyaye na juya na nufi hanyar falonmu."


Ba Modu:
Bayan Bulama Babba ya bi da kallo, ya na ji da yana da iko da ya hana afkuwar wannan saki. Tuno ɗan uwanshi gudan jininshi yayi. Hawaye suka gangaro daga idanuwanshi i zuwa kuncinshi. Yana jin kamar ya dawo da agogo baya, amman ina abunda ya riga ya wuce ya wuce kenan" Turakarshi ya buɗe ya shiga. Amman ya kasa zama tamkar wanda ya haɗiyi taɓarya. Yanzu shikenan Auren Yahanasu mutuwa zaiyi? Ita kanta ya zata ji wannan lamarin, da wacce siga za'a sanar mata da wannan mummunan labarin? Zama yayi a kan gado, ya zare malum malum dinshi, tare da cire kularshi zanna. Kai ya dafe yana tuno fuskar Bulama Babba a lokacin yana da shekaru goma a duniya. Da irin tsantsar so da kulawar daya dinga bashi, har Ba Bakura yana ganin kamar son yayi yawa kar yaje ya sangarce. Da kuɗinshi Bulama Babba yayi karatu, a ƙarƙashin kulawarshi Bulama Babba ya girma. Dan wajen Ba Modu kaɗai Bulama Babba ya ke kai buƙatarshi. Kowa a cikin family ya shaida soyayya da shaƙuwar dake tsakanin Bulama Babba da Ba Ba Modu. Shi kanshi Ba Bakura ya yarda Bulama Babba ya fi son Ba Modu fiye dashi mahaifinshi" lumshe idanuna Ba Modu yayi wasu hawaye zafafa suka zubo mishi. Take kanshi ya ɗauki ciwo, zazzaɓi ya lulluɓeshi sosai.






MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CEGAWURTATTU UKU
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 55






















BULAMA BABBA:
Jikina na ɓari na shiga falon, bakina da sallama. Tana zaune a kan kujera, Gunsum da Aissa suna ƙasa a gabanta. Aissa hawaye naga tana zubarwa, Gunsum kuwa jikinshi duk yayi sanyi. Waje na samu a gefe na zauna. A sanyaye na gaisheta, bata amsa gaisuwar tawa ba. Gunsum da Aissa ne suka shiga rige_rigen gaisheni. A sanyaye na amsa.
Ya jikin naki Hajja " na faɗa a hankali. Cikin dakiya tace.
"Ciwo ai kaine sale_salin tayar mun dashi. Amman tun a jiyan da saƙonka ya iso gareni na samu lafiya. Kazo mun da takaddar sakin a rubuce?" Numfashi naja nace.
Na rubuta amman kafinnan Hajja ki rufa mun asiri ki barni in rayu da Yahanasu, yarinyarnan ba ta yi komai ba, kuma ta samu lafiya gata can an dawo da'ita ma. Ina gudun lalacewar zumuncinmu ta dalilin wannan sakin. Nayi imani da Ba Bakura yana da rai wannan maganar ma ba zata taso ba. Ki mun rai" Hawayen dake shirin zubo mun nayi kokawar mayar dashi.
"Ka gama, nace ka gama dai ko? Kaga ƙannenka sunfi awa ɗaya suna mun magiya. Babu wani sauyi da zaku samu. Miƙon takaddar in gani " Hannu nasa a aljihu na ciro takaddar na miƙa mata. Hannu tasa ta karɓa. Murmushi naga tana yi.
"Allah yayi maka albarka bisa umarnina da ka bi. Ungo ka kai mata takaddarta maza, sannan ka dawo zamu yi maganar kuɗi dangane da batun aurenka da Yalewa".
"To Hajja" Abunda bakina iya furtawa kenan. Fita nayi a ɗakin ina gauraye hanya. Dala yana hangoni ya iso inda nake.
Dala kira mun Yaha kace ta same ni a ɗakin ka na da, ka bani key ɗin ɗakin" Dala yace.
"Bari in ɗakko key ɗin tukunna." Har zai wuce nace.
Dala in ka buɗe ka kirata kace ta jirani, zanje in ga Ba Modu" Ina faɗar haka na wuce, mota na koma na ɗebo takaddu na wuce ɗakin Ba Modu. Sallama nayi yai mun izinin shigowa. Da ganin fuskarshi kasan yana cikin damuwa. A gabanshi na zube ina kuka kamar mace. Duk na gigice kunya nake ji sosai. Takaddar hannuna Ba Modu ya zare ya ajjiye a gefe.
"Bulama kuka ba naka bane. Duk inda aka samu biyayya akwai nasara. Yahanasu kayi mata fatan alkhairi ina ganin zaifi. Kaima ina maka fatan alkhairi, Allah ya haɗaka da mata ta gari. Ka share hawayenka" Hawayena na shiga sharewa, da ƙyar na auro jarumta na yafa.
Ga takaddun ɗaya daga cikin gidajen dana gada Ba Modu na mallaka ma Yahanasu duniya da lahira. Kuma zan tara ƴan uwa su zama shaida. Wannan key ɗin motar ma gashi. Motar tatace dama da sunanta na siya, a baya motar dana karɓa a hannunta tafi wannan ma tsada. Sannan na tura maka da million ɗaya kuɗin gidanta ne da take gina mana kafin lalurar data sameta ta same ta. Ba Modu ka yafe mun, ka taya ni ba Yahanasu haƙuri."
"A'a Bulama Babba shi gidan da motar na meye kuma haka? A'a ka ɗebe kayanka, babu buƙatar hakan, kana buƙatar gidan da motar dukka, Yahanasu maccece gidan wani zata je."
A'a Ba Modu, ko ubangiji yace in zamu yi sakin mu kyautata sakin. Haka kurum ma ana sakin mace a haɗo ta da mota ko check. Wannan na bata duniya da lahira" Sai da Ba Modu yayi jim ya ƙura mun ido kafin yace.
"Allah ya saka da Alkhairi. Yahanasun tasan me ke faruwa kuwa?" Da sauri na girgiza mishi kaina halamar a'a"
"Kar ta ji a bakin ka. Zan sa a kira mun ita, dole da sigar lallashi da hikma za'a yi mata bayani. Kana da damar da zaku zanta a tsakaninku. Tashi kaje Allah ya baku haƙurin rashin juna. Allah bai ƙaddari Yahanasu zata haifa maka ɗa ko ƴa ba, sakamakon muyagun ƙwayoyin da tai ta ta'amali dashi." Bance komai ba na fita. Sai haɗe hanya nake yi, da ƙyar na isa ɗakin Dala. Yahanasu tana zaune a bakin katifa na shigo. A jikin bango na jingina ina daga tsaye nake ƙare mata kallo, ina jin wutar sonta da kewarta na ruruwa a zuchiyata. Tasowa tayi tana shirin shigewa jikina. Idanu na runtse da naji ta rungume ni ƙam, sai nunfarfashi nake fitarwa.
Sake ni muyi magana " Jin kaurin muryata ne yasa ta ɗago kanta a firgice. Idanu da muka haɗa ne ta fahimci ina cikin matsala. Hannuna ta jawo ta zaunar dani a gefen katifa, ita kuma ta zauna a ƙasa.
"Haba Bulamana, menene yayi zafi haka wanda har ya sa idaniyarka zubar hawaye, kaddai a bisa laifin shaye_shayen da nayi a baya ne, ko a bisa cikin jikina da yai ta zubewa ne? To in ma a kanshi ne, da izinin Allah an sha ni kuma na warke. Yanzu nake shirin zuwa ɗakin Hajja, ita da Ba Bakura ne kaɗai ban gani ba." Idanu na lumshe kawai bance komai ba.
"Meke faruwa ka sanar dani dan Allah"
Babu damuwa Yahanasu. Ki koma ciki ki huta, dan kina buƙatar hutu sosai. Zanje in samu Hajja tana jirana."
"Wanne hutu, ai in hutun akeso in yi, sai a kaini ɗakin mijina kai tsaye ai dan nayi kewarka sosai, kuma kaima nasan kafi son mu kasance a tare. Ɗazu na ganka a mota kuma ba motar gida bace ta wanene?" Miƙewa nayi da kuzari nace.
Zan je in dawo zan neme ki kinji, ki kula da kan ki Yahanasu ƴar lukutar Bulama" murmushi mu ka yi dukka, jikinta dai a sanyaye ta fice. Ni ma na nufi ɓarayin Hajja. A falon na tarar da Ba Bature suna tattaunawa da Hajja.
"Gashi nan ma ya shigo" Cewar Ba Bature. Gaisheshi nayi, ya amsa cikin fara'a. Waje na samu na zauna. Hajja ta shiga mun lissafin maƙudan kuɗin da bikin zai lashe. A sanyaye nace.
Zan turo da kuɗin in sha Allah. Sannan inaso ku shaida, na mallaka ma Yahanasu ɗaya daga cikin gidajen dana gada, sai motar da nake ja na mallaka mata a madadin motar ta da Ba Bakura ya siya mata, wacce na kwace a baya, suturu dana loda a wadrope da sunanta na siya, zan turo mata dasu suma Domun Allah subuhanahu wata ala shi ya faɗa cewar in zamu yi saki mu kyautata" Hajja kamar zata ari baki dan masifa, dukanane kawai ba ta yi, amman har tana kukan wai Ba Modu ya cuceta. Ni dai sallama nayi musu na bar garin ma baki ɗaya"




YAHANASU:
Ina fitowa kaina ya shiga sara mun. Da ganin Bulama Babba nasan akwai gagarumar matsala sosai. Da Ya Innana naci karo, hannuna ta ja mu ka shiga turakar Ba Modu. Rabona da shiga wannan ɗaki tun ina yarinya ƙarama. Zaunar dani tayi a ƙasa a kusa da ƙafarshi. Tana ajjiyeni ta fice ta barmu.
"Wanne irin darasi kika koyo a duniyar masu taɓin ƙwaƙwalwa?" Kalmar ɗaya soma jifana dashi kenan. Jikina na rawa, muryata na sarƙewa nace.
"Na koyo darrusa masu tarin yawa. Hakan ya ƙaramin tsoron Allah, da kuma tsoron duniya, ya koyar dani ilimin rayuwa wanda ba'a aji ake koyo ba. Nayi nadama, na sake gode ma Allah a bisa ni'imar lafiyayyar kwakwale daya bamu har muke tunani. Haƙiƙa na tabka kuskure mai girma, kuma nayi nadamar dukkan abubda na aikata, na ɗaukeshi a matsayin ƙaddarar da bawa bai isa ya shure ba." Ƙur Ba Modu ya zuba mun idanunshi. Ni ko ɗari _ ɗari nake yi dashi. Domun nasan sai ya hukunta ni, a bisa ɓata mishi suna da nayi"
"Toh zan ɗaura miki sa nasiha" Nan ya shiga yi mun nasihu da kalamai masu sanyi. Yafi awa biyu yana nuna mun yadda rayuwa take da yanda ake kore damuwar duniya. Nayi kuka sosai. A cikin wannan nasihar tashi ne ya sanar dani rasuwar Ba Bakura. Nayi kuka sosai, dan Ba Bakura jigo ne. Ba Modu ya sanar dani aurenshi da su Ya gaji, da abubbuwa da suka faru ban sani ba. Bayan ya samo nutsuwata ta hanyar karanto mun wasu hadisai sai yace.
"Shi aure, rai ne dashi kuma ina so ki rungumi dukkan jarabawar da Allah zai jarabceki dashi. Ki sani gwajin imanine, kuma hakan nasara ne ga duk wanda ya cinye, ubangiji yana kallo. Yahanasu na yarda na gamsu Bulama Babba yana tsantsar sonki. Kamar yadda ƙaddara ta ƙadarto miki shaye_shaye da taɓin ƙwaƙwalwa, kuma haka ƙaddara ta ƙadartoma Aminiyarki Hajja fati ajalinta a sakamakon ta'amali da miyagun ƙwayoyi. Haka ƙaddara ta ƙara ƙadarto miki mutuwar aurenku da Bulama Babba. Ki sani wannan baya nufin ƙarshen rayuwarki ne, ki ɗauka yanzu zaki soma rayuwa, kuma kice Allah yasa hakan shine alkhairin, ki rungumi ƙaddara kinji ko uwata? Dole akaima Bulama tare da barazanar tsinuwa kar ki kama shi da laifin komai" Jikina babu ta inda baya rawa, Allah na shiga ambato a fili, idanuna naji suna mun yaji_yaji. Ba Modu ya tare ni da hadisai masu kashe jikin ɗan Adam. Ajjiyar zuchiya na shiga saukewa, a hankali ina ambaton Allah sai naji na samu salama, idanuna basu zubo da hawaye ba. Labarta mun dalilin sakin da Ba Modu yayi, yafi sakin girgiza ni, kuma yafi sakin bani mamaki. Murmushi kawai nayi nace.
Babu komai Ba Modu, Allah yasa rabuwar mu shine mafi alkairi. Ka kwantar da hankalinka, bazan sa komai a raina ba, kuma bazan riƙe kowa ba." Yawu na haɗiye, wani malolone ya tokare mun maƙoshina, bai wuce ba, bai fito ba.
"Ga takaddun gidan da Bulama Babba ya baki. Sannan ga mota, kuma ya turo mun da million ɗaya kuɗin gidan da kika soma ginawa a Kano. Gasu." Hannu biyu nasa na karɓi takaddun nace.
Allah ya amfana, nagode sosai. Allah ya jiƙan Ba Bakura. In sha Allah zan shiga in yi ma Hajja ta'aziyya da sauran iyaye." Sallamata Ba Modu yayi yana shi mun albarka. Ni kuwa ina fita naji duniya na juyawa dani. Gefe na samu na dinga ambaton Allah, sai da na samu sassauci sannan na nufi ɗaki. Su Fanna na tarar a ɗakin, suna ta hira. Suna gano ni suka soma murna. Ai ina ganinsu na soma kuka mai gunji, cikin ɗimuwa na sanar dasu Bulama Babba ya sake ni. Ya Innana ta saki kuka itama. Cikin ɗakinnan wakil da Bulama fari ne kawai ba su yi kuka ba, amman sun kasa rarrashinmu. Sai da nayi kuka mai yawan gaske sannan nayi shiru a kan ki kaina. Rarrashin su Ya Innana na shiga yi.
Kuyi haƙuri, wannan duk abubbuwan da suke samu na Allah ne yake jarabtata, ku ƙarfafeni dan Allah. Ku yi mun adda'a dan Allah." Jin na fadi haka ne yasa Ya Innana tace.
"Madallah da tarbiyyar da muka baki Yahanasu. Kin yi biyayya a lokacin da aka aura miki Bulama Babba, kinyi tawakkali a lokacin da Bulama ya sake ki. Allah ya kawo miki sauyi da haske a cikin rayuwarki." Fanna ku je ɗaki da ita." Kafin dare kab ƴan cikin gida sunji labarin abunda ya faru. A kan sallaya na raba dare ina sallah ina roƙon Allah ya cire mun son Bulama a zuchiyata. Washe gari muka wayi gari da labarin rashin lafiyar Bulama Babba yana asibiti. Babu shiri Ba Modu da Gunsum suka kama hanyar Yobe. Mama Gana da Ahmad ne a wajanshi. Ni dai ina ɗaki jigum, da naga shirun yayi yawa, sai na soma karance karance littattafan Hausa, da wasu littattafan addini da ban karanta ba. Wasa_wasa ciwon Bulama Babba yayi mugun tsananin gaske, Ba Modu dai ya dawo, amman Wakil da Ba'a kaka sun tafi jinyarshi. Hajja ma ta je ta dawo, har ta kwaso su Bawa ta dawo dasu gabanta. Sai dai in shiga ɗaki in ci kuka in gode Allah, Ya Innana bata barina in keɓe kaina kwata_kwata tsoro take kadda in koma gidan jiya, kullum a cikin adda'ar samama Bulama Babba lafiya nake. Ranar da ya cika sati guda a asibiti. Da safe ina ɗaki a kwance Ya Innana ta shigo tace.
"Ki shirya zaku Yobe da Babanku ki je ki ga jikin Bulama, ance jikin ya tsananta sosai. Ki ɗan ɗebi kayanki kamar kala goma sai ki sauka a gidan Mama Gana ki ɗan huta. Banda sa damuwa a rai, komai yai tsanani zai yi sanyi da izinin Allah." Jikina a mace na tashi na sake kaya. Na haɗa kaya kala goma kamar yadda Ya Innana ta umarceni. Lafaya na naɗa na zari ƙaramar jakata.
Sai na dawo Ya Innana"
"Allah ya tsare hanya. Ki gaishe da Mama Gana" Kai nasa na fita. Gaisawa na soma yi da matan yayyena, wasu suna haramar tafiya wajan aiyukansu, wasu sun riga da sun tafi tun sassafe, domun akwai likitoci, Nurses, da malaman makaranta. A bayan mota na zauna ni da Ya Bagaji, Ba Modu yana gaban mota, sai Bulama baƙi na ɗakin Ba Baana shi ke tuƙin motar. Ni dai ina zaune lamo a bayan mota ina kallon jejuna da jama'ar ƙauye, masu wucewa da masu cin kasuwa. Ohhh yau nice zanje duba Bulama Babba a matsayin ƴar zuwa

60 / 67