Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
dubiya, Allah mai iko kenan. Gashi a cikin gida ina ji ana batun an sake matso da bikin Bulama Babba, yanzu haka saura kwana huɗu a ɗaura aurenshi da Yalewa, harma an fitar da angon milk ɗin lafaya na ƴan cikin gida, da kamfalar kanuri wacce take sananniya a ko ina. Da waɗannan tunanin muka iso Yobe, kai tsaye muka wuce babban asibitin na Yobe, ɓangaren maza. A baranda muka tarar da Mama Gana, Hajja, Aissa ta ɗakin su Bulama Babba, Wakil, da Mainam yaron Mama Gana. Sai Ba Bature da Yalewa Amarya suma da halama isowarsu kenan. Idanu na zuba mata lyakkyawa da'ita san kowa ƙin wanda ya rasa, gata doguwa jiki duk madara. Wani zazzafan yawu na haɗiye mai ƙuna, tsugunnawa nayi na soma gaishesu ɗaya bayan ɗaya. Hajja a daƙile ta amsa mun, tunda na dawo ban sake ganin sakin fuskarta ba, ta'aziyya da na shiga ɗaki nayi mata ma, ƙarshe zageni tayi tas, ta kirani da fasiƙa. Amman ban faɗama kowa ba, ɗaki na shiga nayi kukana sosai."
"Uwar masu gida, zo uwata ki zauna ki sha Mama?" Cewar Mama Gana, tana magana tana yatsina, nasan da Hajja take yi. A kusa da ita na zauna, muka haɗa idanu da Yalewa ta yi wuf ta ɗauke idanunta daga kaina.
"To mu je mu duba jikin na Bulama Babba, mu kam ba zama zamu yi ba hanya zamu sake kamawa" Ba Modu ne yake Magana. Tare dukka muka ɗunguma zuwa ɗakin da Bulama Babba yake kwance. Ɗakin gado ɗayane a ciki, da bayan gida, ga tv da firji. Ahmad da Ba'a Kaka ne a cikin ɗakin. Bulama Babba yana zaune ya jingina bayanshi a fullo yana cin ayaba. Idanu ya zuba mun, nima shi nake kallo ina mamakin ramar da yayi tashi guda, da ganin yanayinshi kasan yana cikin jinya sosai. Hawayene suka cika gurbin idanuna suna shirin zubowa, kai ya girgiza mun halamar kar inyi kukan gashi ya cike ni da kallon soyayya.
"Bulama Babba ya jikin da sauƙi dai ko?" Ba Modu ne ya katse mana kallon ƙudan da muke ma juna.
"Da sauƙi Ba Modu, gobe ma zasu sallame mu suka ce. Sannunku da zuwa" Nan aka shiga gaishe_ gaishe.
Yaya jikin naka Bulama Babba?" Bai ji kunya ko nauyin su Ba Modu ba yace.
"Bazan amsa ba, sai yau kika ga damar zuwa dubani, bacin kinsan sabida ke nake kwance a nan wajan" Kai na sauke ina jin kamar zan fashe da kuka. Hajja na kalla, naga ta sake murtuke fuska. Ahmad ma yace.
"Gaskiya kam umman Maryam muna fishi kuma ba zamu amsa wannan gaisuwar ba. " Murmushn ƙarfin hali nayi musu kawai.
"Yalewa zuba mishi burabiskon da ki ka yo mishi ya samu ya ci" Cewar Hajja kenan. Ni dai bance komai ba. Duk a tsaye muke, Ba Modu yana kusa da Bulama Babba sai kallonshi yake yi, cikin so da nuna kulawa." Yalewa kuwa kiciniyar zuba burabisko take ta yi. Tana buɗe burabuskon ƙamshi ya cika ɗakin. Burabiskone mai hanta da kayan lambu a ciki, sai farfesun kaza mai ɗan kaurin romo. Zuba mai tayi ta ƙarasa kusa da Ba Modu, tana son cewa ya matsa, amman naga ta kasa.
"Yau ga tsiya da wasali ƙasa. Baiwar Allah tureshi zaki yi sabida fitsara ko yaya? Ko da yake kin saba da fitsara da goyayya a cikin ƙattai" Cewar Mama Gana wacce ta isa inda Yalewa take ta fisge plate ɗin abincin.
"Rashin kunya, a baki kike so ki bashi ko me? Ko da yake ba mamaki ai tunda an saba cuɗanya da masu buɗewar idanu"
"Ya'isa Mama Gana. To mu kam zamu wuce Allah ya ƙara lafiya Bulama Babba. Mama Gana ki zo mu tafi gidanki mu ɗan zanta mana" Da dariya yayi maganar. Nan mu ka fice mu ka bar su Hajja da Ba Bature, da Ahmad dan ba'a kaka ma biyo mu yayi. Mu muka shiga motar Ba Modu da mu ka zo a ciki. Su Mama Gana kuma suka shiga motar Mainam, muka nufi gidan Mama Gana. A falo mu ka ya da zango. Ita kuma ta shige ciki sai gata da alkali da nakiya cikin faranti. Da tuwon shinkafa miyar taushe a ƙaton tran silver. Gwanin sha'awa dukkanmu mu ka sa hannu a cikin abincin muna ci. Dana ɗago sai in ga Mainam na kallona. Hakan ya mugun takurani sosai, ba shiri na tsame hannuna a abincin nace Ni na ƙoshi. Dama ba wani na azo a gani na ci ba. Ganin Bulama Babba ya fama mun mikin dake cikin zuchiyata. Ɗakin Mama Gana na wuce da akwatina. A kan gadonta na kwanta ina sharar hawaye tausayin kaina da tausayin Bulama Babba ya kamani.
Ba Modu:
"Mama Gana ga Yahanasu nan ni da kyatumarta mun yanke hukunci ta dawo wajanki ta kammala iddarta. Ni kuma zanyi ƙoƙarin ganin na nemo mata aikin gidan TV in sha Allah, tunda nasan tana so. Na tura miki kuɗi wadatattu ki kula da'ita sosai, kin san dai halin da take ciki da wanda ta fito a ciki, kar a sake a barta ita kaɗai a ɗaki. Bana son kowa yasan tana gidanki. Ki tuntuɓeta ya take son yi da kuɗinta da Bulama Babba ya bata? Ga waya nan Wakil ya siya mata. Mu kam zamu koma sai kun zo biki."
"Wa babu wani biki ni kam da zanje. Su je su yi biminsu can da su gada." Cewar Mama Gana tana magana tana huci. Ba Modu yace.
"Assha Mama Gana, ai wannan bikin mune akan gaba gaba. Ita kanta Yahanasu ya zame mata dole ta halarci bikinnan. Abunda ya faru ya riga da ya faru kuma ya wuce ai. Fatanmu Allah ya haɗa kowa da abokin zama na gari. Mu kam zamu wuce." Nan suka tattara suka kama hanyar komawa Damaturu. Ba Modu yana zaune a mota yana tunanin al'amuran da suka faffaru."
BULAMA BABBA:
Kaina na sauke ina jin zuchiyata babu daɗi sam. Hajja kuwa ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
"Ka kiyayeni akan Yahanasu wallahi Bulama Babba, kar ka bari in yi fishi da kai. Yalewa ki zauna ki bashi abincin har sai kin tabbatar ya ci tukunna. Muna jiranki a waje, in kin gama sai mu tafi. Bature mu basu waje" mamakine sosai ya kama ni jin Hajja tace a bamu waje, sai kace mata da miji. Ina gani suka fice a ɗakin har da Ahmad, ɗakin ya rage daga ni sai Yalewa da take zaune a kujerar roba tana fuskantata. Ƙur ta zuba mun idanu tana karantata. Abincin ta ɗebo a cikali ta nufo da cokalin bakina. Carab na riƙe cokalin ina kallon ƙwayar idanunta nace.
Al'adarmu da addininmu sun koyar damu kunya. Ita kunya adone a gun duk wata ƴa mace. Sabida wayewa jibi shigar jikinki, gashinki da ƙirjinki a bayyane. Kayan jikinki sun kama miki jikin ki, kin bayyana ma mazan waje adonki, kina tallata musu surarki, dan Allah ya baki kyau, da kyan fata, da kyan diri ta hanyar daya dace kiyi amfani dashi kenan....?"
"Dakata Bulama Babba. Kar ka ɗauka aurennan da za'a ɗaura mana ko ina sonka ne, balle ka samu damar ci mun fuska. Ka dubi kyau da tsarina wallahi nafi ƙarfin talaka irinka. Kuma jikina haramun yake a wajanka baka isa ko yatsan hannuna ka taɓa ba. Ka ɗauka zan zauna a gidanka ne a matsayin baƙuwar da ka ba ma wajen kwana" Tana kaiwa nan ta ja tsaki tare da dangwarar mun da plate ɗin abincin a saman cinyata rabi ya zube. Ta kama hanyar fita, na bi bayanta da kallo, babu shiri na kawar da kaina. Dan duk wani lafiyayyen namiji in yai tozali da irin shigar da Yalewa tayi, dole kwaɗayinshi sai ya motsa, balle irinmu da mu kai tsatsa. Idanu na lumshe fuskar Yahanasu ta shiga yi mun yawo, ina hango tausayina da kewata a tsakiyar idanunta. Shigowar Ahmad da Ba Bature ne yasa na buɗe idanuna.
"Bulama Babba Allah ya ƙara sauƙi sai ka zo taron ɗaurin auren Allah ya ƙara lafiya"
Ameen Ba Bature nagode sosai. Yana fita Ahmad yace.
"Wallahi Bulama Babba Yahanasu tana cikin tashin hankali da damuwa mai tsanani. Ina tausayinta sosai. Yanzu likitan ma yace zamu iya tafiya gida ya sallame mu, na gama komai. Sai ka taso mu tafi Dala yana waje yana jiranmu, wannan abincin fa zubewa yayi?." A sanyaye na sakko muka wuce gidan ba tare da na iya cewa komai ba. Amman kullum a cikin kewa da tunanin Yahanasu nake, ashe haka soyayyar gaskiya take, jibi yanda duk girmana soyayya take sani fitar hawaye, da kasa bacci, rashin walwala da rashin sukuni. Oh ya Allah, ban taɓa mafarkin Yahanasu zata iya zamewa sanyi ga idanuna ba, sai gashi a kanta nake fama. Haka dai lokacin yai ta tafiya ana gobe ɗaurin Aure na shiga shirin tafiya Damaturu da safe dan Hajja ta dame ni da waya akan ya kamata in zo, anata gudanar da bukukuwan al'ada babu ango. Babu yadda zanyi haka na shirya na fito. Ina fitowa Mama Gana ta kira ni a waya.
"Bulama Babba kana Yobe ko Damaturu?"
Ina Yobe yanzu kinga fitowata kenan zan je can Damaturun."
"Yauwa shikenan ma. Biyo ta gidan ka ɗauke mu a sabuwar motarka muma mu ɗana" Ɗan murmushi nayi nace.
Ke da waye Mama Gana?" Ɗan dariya tayi mun itama tace.
"Ni da Uwata ne." Dam naji gabana ya ba da wani irin bugu. Idanuna na ɗan rintse kaɗan, ina jin motsin son Yahanasu wanda nayi imani dashi zan game rayuwata.
Gani nan zuwa Mama Gana" ƙit na datse wayar wajan motata na nufa. A wajan na tarar da Ahmad da Hajara da yaran suma sun fito tsab Damaturun suka nufa, amman a tashi motar daya siya zai tuƙa su.
Zan biya gidan Mama Gana in ɗaukosu ita da Yahanasu sai dai mun haɗu a Damaturun kawai"
"Ohhh Yahanasu tana cikin garinnan shine ko ta ɗan leƙo mana. Kuma Bulama itama bikin zata je? Allah sarki Yahanasu" Kallonta nake yi kawai Ahmad ne ya daka mata uwar tsawa.
"Dalla shige mota jo. Baki ba matari duk maganar data fito bakin ki sai kin fesar" Da sauri taja yaran suka shiga mota. Ahmad ya dafani yace.
"Bulama kayi haƙuri ka cire Yahanasu a cikin rayuwarka ko dan ka zauna lafiya. Kayi ta adda'a in da rabon ku sake yin zaman aure a gaba wallahi sai kaga komai ya zama kamar tarihi. Kaje ka ɗakkosu suna jira"
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE[20/08, 10:01 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 56
GHANA:
Kofur Zubaina:
Kwanan mu uku a asibiti aka sallamomu muka dawo gida. Matan gida sai sannu su ke yi mun, ni kuma ina binsu da um hum. A bakin gado na zauna ina ba ƴan biyu nono ko wanne ya kama sai ja suke yi abinsu. Idanu na zuba musu hawaye na shatata a kuncina yana ɗiga a kayansu. A haka Nabeela ta shigo cikin ɗakin da kofin ruwan zafi a hannunta. Ganin halin da nake ciki ne yasa ta zauna tace.
"Sai yaushe zaki dena zubar da hawayenki a game da lamarin Alh da gidanshi ne Zubaina? To wallahi gara ma ki dena dan Alh yana nan yana dakon dawowarki cikin gidannan ya sauke miki buhu_buhun ɗiban albarka sabida katsalandan da mahaifiyarki take yi mishi akan ki. Ni dai babu abunda zance damu duka sai haƙuri. Duk abunda ya samu shamuwa watan bakwai ne, in da kwaɗayi da wulaƙanci, motar kwaɗayi a tashar dana sani take tsaiwa. Kuskure ne mun riga mun tabka, jarabawa kuma bamu isa tsallakewa ba, sai mu yi haƙuri mu rungumi ƙaddara. Ga ruwan zafi nan na ɗebo miki ki dan kukkurɓa ya warware miki hanji tunda kunu ko shayi bazai samu ba. Nima a haka nake nawa jegon. Ke bama ni kaɗai ba harda waɗanda zasu shigo gaba ma." Hawayena na share jikina ya sake yin laushi, dama ashe haka sakayya take, ashe haka ƙaddara take juya akala? Allah na tuba ka yafe ni ya Allah. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Nabeela nace.
Nagode ƙawai Nabeela" fita tayi ta barni a zaune ina karanta wasiƙar jaki. Muguwar yunwa nake ji, ji nake uwa ana yashe mun hancin cikina, ga ƴan biyu sai tsotso suke yi, ruwan nononma guda nawa ne. Bayan sun yi bacci na shinfiɗesu, sai na shiga buɗe buɗe ko zanci karo da wani abun ci. Ledar da Mabaruka ta bani na hango a can ƙarshen gado, hannu nasa da ƙyar na zaro, na zazzage ko Allah zai sa in dace. Amman wayam babu komai a ciki duk na cinye komai, ala tilas na kafa kai na kwankwaɗi ruwan ɗuminnan, ina sha ina jin ƙarar gangarawarshi cikina tamkar ana zuba ruwa a buta. Abun duniya ya game yai mun yawa, hankalina ya dawo kan ƴan uwana da halin da Asiya take ciki. Gashi bani da ko sisin kobo balle in kira in ji yadda ake ciki. Mun dai yi waya da Mama kafin a sallamoni daga asibiti take sanar dani zasu tafi wani ƙauye domun nemama Asiya magani ko Allah zai sa a dace. Nayi kuka kamar fitar rai, tausayinmu da tsoron Allah ya sake shigata ainun. Jiƙewar da ƙunzugun jikina yayi da jini shi ya tilastamun tashi domun neman fallen zanin da zan yayyanka in yi ƙunzugun dashi. Wata atamfar chiganvi na kakketa na ɗauki falle ɗaya na fito tsakar gida da zummar zuwa banɗaki in gyare jikina. Ina fitowa wani sanyi ya shiga kaɗani jirin yunwa da rashin ƙarfin jiki na jinya suka saukar mun. Alh Liti na hango buguzun_buguzun yana tawowa ɓarayinmu. Sunana ne a bakinshi yana rakaɗa mun mahaukacin kira. Tsumman hannuna babu shiri ya faɗi ƙasa jikina babu ta inda baya rawa. In kada baki in amsa kiran nashi na kasa. Yara da manyan gidan kowa ya shiga taitayinshi sun zuba idanu suna shirin kallon ikon mai sama. Da ɗan yatsa ya nuna ni.
"Wallahi duk ranar da kika kuma fita da sunan zuwa asibiti a cikin gidannan sai na wulaƙantaki ƴar iska ƴar gidan maras tarbiyya. Bazai yiwu Jummai ta dunga zuwa tana fita mun dake ba. Kin ci sa'a da ba dan nayi alƙawarin bazan sake ki ba wallahi da kinga tsiyar da zan tabka miki da ɗanyan jegon nan. Da sai na birkita ma Jummai ƙwaƙwalwa ta ganku jibge ku biyu a gabanta kuna zawarci." Ni dai tunda na sauke kaina ban dena zubar hawaye ba, har sai da ya gama buyaginshi ya tafi, kana na samu zarafin tsugunnawa in ɗau tsummana. Bayan gida na isa da jan ƙafa har yanzu a kumbure nake ban saɓe ba. Ƙunzugun jikina na cire na mayar da wani. Ba sabulu ba omo haka na wanke tsumman jinin nan, na fito dashi. Ɗaki na koma na kwanta numfashina na fita sama_sama. Haka nai ta wannan jego na wahala ruwan nonon ma baya isar jariran sam. Ranar suna da asuba Alh Liti ya leƙo ya jefo mun wata leda kan gadona ya saki labulen. Ledar na jawo atamface ɗinkin doguwar riga atamfar roba, sai rigar yara guda biyu, sai omo ɗaya sabulun wanki ɗaya, shikenan abunda ke cikin ledar nashi kayan sunan kenan a matsayinshi na uba wanda aka haifa mishi ƴan biyu. Idanu na runtse ina kaico a zuchiyata. Na tuno lokacin sunan Bawa. Irin hidimar da Bulama yayi abun har ya wuce misali. Daga ni har jaririn sai da yayi mana akwati ko wanne da nashi. Kayan fitar suna kuwa kala bakwai na ɗinka tsadaddun kaya haka ma ɗinkin shima mai tsadar gaske. Raguna biyu tiƙa tiƙa ya yanka. Banda kaji guda goma sha biyar da aka yanka, abincin suna kuwa sai da mu kai kala uku, ga sobeniyas da muka raba. Murmushi kawai nayi na ɗakko yaran na saka musu kayan da babansu ya kawo musu. Zuwa goman safe yaran gidan suka soma hallara, tuwon shinkafa miyar kabewa akeyi na suna. Babu wani ko wata daga maƙota da suka shigo da zummar taya mu suna. Mu kaɗai ma gayyane bana jin abincin da ake dafawa ma zai wadaci kowa da kowa a gidan. Kuma a Ghana naga rumfa suke kafawa maza da mata a haɗu ayi bikin suna, ana cin abincina ana raye_raye kamar dai yarbawa. Abun haƙiƙa kuwa Alh bai yanka ba haka mu ka yi sunan mu lami washe garin suna na koma bakin aikace_aikacen gida. Ko bacci bana samu ishasshe sabida kuka da tsotson ƴan biyu, nonon ba issarsu yake yi ba to nima banci na ƙoshi ba balle su samu. Yanayina kuma ya koma na bagidadawa fatata ta dafe ta yamushe, ƙafata kuwa duk faso, kaina harya soma furfura dan masifa bansan da me zan fasalta muku zaman gidan Alh Liti ba, su Hajiya Kubra ne kaɗai zasu fahimceni domun tare dasu muke ɗanɗanawa. Ga Zarah data sakoni a gaba, dan tsabaragen jarabarta na dena fitowa tsakar gidan ma in ɗan sha iska, sai dai in ni ce da girki.
Mama
ƘAUYEN YADAGUNGUME DAKE ƘARƘASHIN ƘARANAR HUKUMAR NINGI TA BAUCHIN NAJERIYA"
Isar su Mama gidan mai magani kenan. Ko a iya hanya sun jigata, jigata bata wasa ba, dan a mashin suka ƙarasa cikin ƙauyen da kwatance suka isa gidan mai maganin kasancewar sanannene sosai a fannin bada magunguna irin na gargajiya, fitar da aljanu, dama fitar da maita wannan dalilin yasa ake mishi inkiya da dodon mayu, maye daya haɗa idanu dashi yake soma bubburwa.
"Sannunku da zuwa maraba baƙi. Ga can ɗakin jira ku je ku kama layi, duk waɗanda ke cikin ɗakin layi baizo kansu bane. Ku shiga bari a kawo muku ruwa" Cewar wata dattijuwa dake bakin murhu tana talge. Mama da Goggo Safiya da suke riƙe da Asiya suka shiga wannan ɗaki da