MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   12 / 67

33K to 36K   out of 198.3K words

Yanunu, Bagulaji ku tawo mu tafi." Fita su ka yi duk rayukansu a jagule ba daɗi, Fanda ta dafani taji jikina kau.
"Subuhanallahi Yahanasu naji jikin naki da zafi sosai ai" Ina sharar hawayen da ya zame mun jiki nace.
Babu damuwa zan lallaɓa in sha magani, in naji jikin babu daɗi zan yi ma Bulama Babba magana ya kaini asibiti." Allah ya ƙara sauƙi tayi mini ta fita, Kuɗi na ciro nera dubu goman da Alhaji Munka'ilu ya bani, na danƙama Hajja Fati.
Gashi nan ki kama sana'a kuma da zaran sana'arki ta kafu, sai ki yi ƙoƙarin komawa makaranta ki kammala karatunki, da zaran kin soma aiki, wasu matsalolin sai su kau" Karɓan kuɗin tayi tana godiya. Takaddar magani fara ta miƙomun cike da magunguna, nasa hannu na karɓa.
"Yahanasu, karki bari kaɗaici da tunani, da takaici ya haifar miki da ciwon hawan jini, ko ciwon zuchiya, ki kashe rayuwarki a banza da wofi. Ciwon rashin bacci shi kanshi yana iya haukata mutum, wannan maganin baccine, da zaran kin kasa bacci ki sha guda biyu kawai, dan ki samar ma kanki da ƙwaƙwalwarki hutu da sauƙi. Bazai gusar miki da hakali ba sam, zaki yi normal bacci daga dare izuwa safiya, kuma duk cunkushewar da zuchiyarki tayi, zakiji nauyin yayi ƙasa wanda in a sikeli za'a ɗaura a auna bai wuce nauyin kwalin omo ba" Hannu nasa na karɓi maganin na ja durowar gefen gado na jefa. Tare da Hajja Fati muka fita, nayi sallama dasu, Ba Bagulaji sai hawaye take yi, ina tsaye a wajan har suka fice mai gadi ya rufe get ɗin gidan. In ɗaga ƙafa in koma ɓarayina abun yaci tura, kuka kawai nake yi, ina tuno mahaifana da dangina. Ƙannen Zubaina ne suka zo suka wuce ni, hannunsu jaye da yaran. Sai habaice_ habaice suke yi, suna zage _zage. Juyawata nayi na koma ɓarayina, a kujerar falo na kwanta, nan jikina ya shiga rawa, gashi bani da mataimakin da zai taimakeni.






Kofur Zubaina:
A ɗakin Mansa mu ka rama sallolin da ake binmu, dan ni dai kam sun riƙe mun wuya sosai. Anan muka ga irin mulkar abokan zama da Mansa take yi, dakama kowa tsawa take yi harda mai gidan, hakan ya ƙara mun ƙaimi sosai. Anan mu kai musayar number waya, muka kama hanyar Kaduna. Muna shiga Kaduna wayata ta soma ring, Bulama ke kirana.
Allah ya taimaki mai taimakona, barka da safiya ango mijin amarya. Wato ko ɗan kiran da ka saba mun in zanyi aikin night jiya ba kai mun ba ko, harma na soma fuskantar canji kenan Bulama, duk ƙoƙarin danne kishina da nayi dan samun nutsuwarka? Ina kaiwa ƙarshe na fashe da kukan makirci har ina wani jan majina. Gabaki ɗaya na gama rikita kan Bulama, dama abu kaɗan ke ruɗashi, bashi da jumurin shanye abu, murya a raunace kamar mai shirin yi mun kuka yace.
"Haba rayuwata, uwar ƴaƴana kiyi haƙuri ki share hawayenki, ni wannan yarinyar bata sani a idanunta ba wallahi, dan ko su Mama Gana ban bari mun haɗu ba." Jin ya furta haka sai nayi cak da kukan da nake yi mara hawaye, na karya murya nace.
Nayi haƙuri uban ƴaƴana kishine ya motsa mun raina, kai kasan ina sonka, kuma kaine gatana, gatan dangina ma."
"Nasani Zubaina ta, ina sonki, babu wani abu da zai iya taɓa sonki a zuchiyata, ni kin ganni a office ma. Dan da asuba na fice a gidan, yau zasu tafi, na dai ba da saƙon dubu hamsin ma mai gadi, nace in sun fito zasu tafi ya basu" Wani tuƙuƙin baƙin cikine ya turniƙe ni. Amman sai na shiga jero mishi adda'ar buɗi a bisa ƙoƙarin da yake dashi.
"Babu komai matata, da daddare sai mu je mu dobo atampopin in mun dawo aiki ko? Sannan zan turo miki dubu ɗari ki riƙe a hannunki kya biya kuɗin ɗinki dasu. Far nayi da idanu nace.
Godiya nake yallaɓai Allah ya ja kwana. Cikin taushin murya yace.
"Ameen matata, bari inyi aikina, dan inna biye miki ke da zaƙin muryarnan taki, sai jikina duk ya mace" Dariyar da nasan in nayi ina motso mishi da duk wata sha'awar kasancewa tare dani nayi, kana nace.
Ka shirya, domun yau zan kai ka ɗakin amarya ni da kaina, dan har kazar Amare ni da kuɗina zan siya ma, kai dai ka sha kuruminka. Ƙit ya datse wayarshi. Dariya muka saka ni da Mabaruka harda tafawa, tace.
"Ƙawata bakya wasa da maza, ƙawata yanzu fa da ba dan kin cabki Bulama ba ko? Hmm yau da zai yi kwanan ɗakin Amarya wallahi da kinga kumumelesi. Ke ni fa ranar da Adam ya kwana a ɗakin Sagira kin san dan munafurci na maza har wani ihu ya saki, mutumin da ko nishi bayayi sai gashi ya ɓige da ihu. Jin wannan ɗan ƙara da Adam ya saki sai naji zuchiyata kamar zata tarwatse, banyi ƙasa a guiwa ba na fito saɗab saɗab na laɓe a tagar uwar ɗakinsu. Hmm takaici wallahi Zubaina ashe sambatu Adam ya shiga yi ma Sagira har yana ce mata yanzu yasan yayi aure, ashe mata suna suka tara. Ke haukatani fa Adam yayi, kiga yanda na fige na rame ni da gidana fa a lokacin" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Amman lallai maza basu da mutunci akan son ransu, yanzu yana nufin kenan Sagira ta fiki komai kenan a wajanshi,mu da muke aika kuɗin magungunan mata har togo. Hmm ai ni bazan lamunci ganin takaici ba, yanzun ma ji nake kamar bazan iya barin Bulama ya dinga yi mana wani rabon kwana ba"
"Ƙawata wai ashe har yanzu tantama kike yi a aikin bokannan, duk abinda kika gani a gidana, da wanda kika gani a gidan Mansa, dana bakunan mutanen da muka haɗu duk baki gamsu ba wai? Hmmm ranar da nayi duk abubbuwan da bokannan ya sani, daga ranar har rana mai kamar ta yau Adam bai sake kusantar Sagira ba. Ɗan data haifa ma Allah ya ƙaddara zai zo duniya ne, tun a ciki nake aika mishi da boma bomai, shi yasa kika ga yazo ba lafiya, aikinane fa" Baki na washe ina dariya nace.
Gaskiya ƙawata baki da dama, kinci dubu sai ceto." Ƙaran kiran wayata ne ya katse mana hirarmu A S P ke kirana, nasan akan case ɗin ɗan luwaɗinnan ne yasa ya kirani, ni nama sha'afa. A ƙofar gidan Mabaruka na tsaya, sannan na ɗaga wayar. Adam ne ya zo ya buɗe ma Mabaruka ƙofar mota ta fita, ya amshi jakarta suka wuce, suka barni da sakakken baki. Daga nan aiki kuma na shiga, naje na gabatar da duk binciken daya dace, a hanyar zuwa office na tsaya na sai waina da miya, lokacin har azahar tayi, ni nama mance ko karyawa bamu yi ba, in banda shayi da mu ka sha a gidan Mansa. Daga nan na wuce office na soma gudanar da aiyukana. Da yamma na fito na tafi gida. Duk a gajiye nake tulus sosai. Harara na doka ma BQ ina jin wani tururin kishi na rufe ni. A guje Maryam da Bawa suka tare ni, sunata murnar ganina. Kawunansu na shafa, ina jin farin ciki sosai. Babu abunda yake burgeni sama da kasancewa a cikin iyalaina. Asiya ta amshi jakata, Nafisa tace.
"Anty tun ɗazu fa Mama take zaune tana jiranki."
Ah da gaske Nafisa?" Nafisa tace.
"Ai ta jima sosai a ciki" Da sauri na shiga cikin falon. Na tarar da Mama tayi baje baje a ƙasa tana cin shinkafa da miyar kaza, ga lemon kwalba da ruwan faro a gabanta. Wani daɗi naji sosai. A ko da yaushe in Mama tazo gidana tana santin irin daɗin da Bulama yake bamu, sai inji na tausaya mata, a lokaci guda kuma sai inji daɗi dana samu damar mallakar Bulama, dan ya tsamoni daga cikin ƙangin talauci, dama dai dani kab ƴan gidanmu suka dogara, ni kaɗaice nake aiki, su ko karatun kirki basui ba, in banda yanzu da Bulama ya ɗauki nauyin karatun nasu har zuwa jami'a.
"Zubaina kin dawo? Ke zauna inna gama fasa ƙashinnan mayi maganar" Dariya na saka mata nace.
Mama amman muje can ɗakina, dan Bulama ya kusan shigowa, kinga biyar ta gota, duk yanda akayi go slow ya samu a hanya ma." Abincin na ɗaukar mata muka shige ɗakina tare da banko ƙofar. Anan na labartama Mama duk halin da ake ciki, da magungunan da aka bani.
"Da kyau ƴarnan ai ba'a bori da sanyi jiki. Jiya banyi baccin kirki ba, sai mafarkai nake yi, wai Bulama ya sakeki yayi miki korar kare yayi miki kafirin duka." Bakinta na toshe.
Haba Mama wannan mafarki yayi tsauri da yawa. Aini da Bulama tamkar takone da ƙafa, mutuwa kaɗai ke iya rabasu." Magunguna ta sunto a bakin zaninta tace.
"Kinga wannan, a cikin abun sha zaki zuba mishi, yai ta sha. Wannan kuma da jinin al'ada ake haɗawa a kwaɓa, na ranar farko, sai ki gasa naman saniya dashi ki bashi yaci. Shikenan fa ƙurunƙus" Godiya na shiga yima Mama. Haka na shiga store na haɗo musu kayan abinci rigijib, na je na sauketa a gida, a gurguje na dawo. Nako ci sa'a Bulaman bai dawo ba. Wanka na faɗa nayo da wannan garin maganin. Na tsara kwalliya na fito fes dani a cikin goduwar rigar kanti baƙa, na rambaɗa kwallin wajan boka, na fito shar. Daddumar cin abincinmu na nufa na buɗe kular miya na barbaɗa garin magani, miyar kajine zuƙu zuƙu. Ina miƙewa Bulama ya shigo kici_kici da manyan ledojin shagonshi dake kan titin isa kaita, shagon saida dogayen riguna na mata da maza irinna ijib. A guje Bakura da Maryam suka fito daga ɗakin su Asiya, sun riga sun haddace dirin motarshi. Sakin ledojin yayi a ƙasa, ya ɗaga Maryam sama yana ta juyi da'ita suna dariya. Bawa kuma ya kama mishi ƙafafunshi sai tsalle yake yi. Daya sauke Maryam sai ya ɗaukeshi shima.
Sannu da dawowa Yallaɓai, yau me ya tare ka ka makara?" Ɗagowa yayi ya dubi tsakiyar idanuna:




BULAMA:
Kallon Zubaina nayi cike da so da kulawa, gabana ya bada wani bugu mai ƙarfi, take kaina ya sara mun, har sai da na ɗan kanne idona na gefen hagu. Sannan na sauke ajjiyar zuchiya, na kuma dubanta, sai Murmushi take zabgawa tayi kyau sosai, sai ƙamshin turaren Dubai gold take yi.
Ke dai bari, kece kika sani makara, dan naje shagone na ɗebo miki wasu dogayen riguna da aka kawo su yau, wannan ledar kuma ki miƙa ma su Asiya suma ƴan mata su saka. Wow kinyi kyau fa gimbiyata" Dariya mu ka yi duka. Ɗakina na nufa, ita kuma na barota a tsaye tana kiran Asiya. Wanka nayi da ruwa mai zafi, kaina naji yana ta tsananta ciwo sosai, ga zazzaɓi da ke shirin kamani. A daddafe na ɗauro alwala na fito. Baƙar jallabiya na zura, ina kan fesa turarena mai suna one million sai ga Zubaina ta shigo. Gabana tazo ta tsaya, ta ƙura mini idanu, yau idanun nata sai naji kaifinsu tamkar yana kekketamun jikinane.
Yallaɓai mun fa gode sosai da irin wannan ɗawainiya da kake yi, ubangiji Allah kar ya gajiyar dakai wajan kula damu." Hannu nasa a ƙugunta na hankaɗota jikina ta kuwa rumgumeni. Kaina wani irin saramun yake yi sosai, ba shiri na sake ta, na zauna a bakin gado dafe da kaina wanda nake jin kamar zai tarwatse.
"Lafiya kuwa Abban Maryam naga ka dafe kan ka?" A hankali nace mata.
Kai nane yake wani irin ciwo, sai sara mun yake yi. Kwakwalwar tawa kamar zata huje haka nake ji" Take Zubaina ta ruɗe ta shiga yi mun aikin sannu, gashi sai kiraye_kirayen sallah ake yi. Amman bana jin zan iya zuwa masallaci. Magani ta ɓallo ta bani da ruwa.
"Gashi kasha, sai ka ɗan kwanta, inya lafa maka sai kayi sallar." Baki na buɗe ta zuba mun ƙwayayon maganin guda biyu, ta bani ruwa na kora. Sai taga na miƙe kuma. Da zafin nama ta zaunar dani.
"Ina kuma zaka a cikin wannan halin?"
Sallah kina ji har an shiga Masallaci, kinsan ita Magriba lokacinta ƙanƙanine" Kai ta girgiza mun tace.
"Ina sai dai kuwa kayi sallarka a gida, komai sai da lafiya ake yi ai." Dadduma ta shinfiɗa mun, sai da na tada sallah sannan ta fita. Raka'ar ƙarshe sai a zaune na kawota, dan ciwon kan sai tsananta yake yi. Ina idarwa na kwanta a kan sallayar. Da sallama Zubaina ta shigo, hannunta ɗauke da babban farantin silba, da kuloli biyu a kai, da sauran tarkace.
"Sannu ya kan?"
To gashi nan dai. Zazzaɓi ma nake ji dai" Jikina ta taɓa, ai kuwa ta same shi kau.
"Subuhanallahi ko asibiti zaka taso in kai ka ne, jikin naji da zafi kau? Janyota nayi jikina, na ƙanƙameta tsam sam bana fatan abunda zai sa ta motsa, ɗan dama dama na soma ji. Da ƙyar dar na daure naci abinci, dan kar in ɗaga mata hankali sosai.
"To abu na farko da za'ayi shine, ya kamata kaje kaga halin da Yahanasu take ciki ko? Sannan sai ku tawo nan taci abincinta. Daga nan kuma ni da kai sai muje mu siyo kazar sayen baki, in kai ka ɗakin Amaryarka." Ƙur nayi mata da idanu cikin ɓacin rai sosai, dan banji daɗin yanda ta dangantani da Yahanasu ba sam.
In hakan kike so ai shikenan, kin nuna mun baki damu dani ba, kuma bankai ki kiyi kishi akaina ba....." Shishsh ta ɗaura yatsanta akan laɓɓana, dole na dakatar da magana.
"Bana son musu, kai dai je ka kirawota ku dawo tare. Wannan yarinyar bazan so ka shiga hakkinta ba. Su Ba Bakura ne fa suka aura maka ita. Ya zamemun dole in tayaka kai musu biyayya, wala Allah sa dena ganin baƙina. Kai dai kayi abunda nace kawai."
Allah yayi miki albarka ƴar aljanna" Miƙewa nayi na fice a ɗakin, na nufi BQ ba don son raina ba, sai don in faranta ran Zubaina. A takure a kan gado na samu Yahanasu sai rawar ɗari take yi. Kaina na kawar nace mata.
Ki taso muje kici abinci" Ban jira me zata ce ba na dawo falo, sai kallon tsarin falon nake yi. Idona ya kai wajan daining da aka mayar mata kitchen yayi kyau sosai. Sanye cikin farin hijabi har ƙasa ta fito. Sai ƙamshin humra take yi. Ina gaba tana biye dani har zuwa falon Zubaina.




Yahanasu:
Ba dan inaso ba na biyo Bulama Babba. Na biyo shine dan bana son yin musu dashi. Da siririyar sallama na shiga falon, Bulama na gabana. Wani hayaƙi na shaƙa mai ɗan karen yaji, take naji na sheƙeshi ya shigemun kwakwalwata, hancina duk ya buɗe. Sai naji kamar kaina na juyawa. Ahankali na soma karanto addu'o'in tsari da kariya. Waje na samu sai da nayi bismillah na zauna.
Ina wuni Anty?" Nace da Kofur Zubaina da take tambayar Bulama Babba ya kan nashi. Cikin fara'a ta amsa mun gaisuwata. Bulama Babba yace.
"Inaga gajiyar aikine, amman sai nake jin sauyi sosai a jikina. Amman ciwon kan da sauƙi, ina yarannanne?" Zama yayi a doguwar kujera, Kofur Zubaina ta zauna a gefenshi tace.
"Asiya tana tsakar gida tana zance, Alhaji ne yazo wajanta. Nafisa kuma tana ciki tana chatting kasan ƴan mata da shegen son chart" Kai kawai ya girgiza ba tare da yace komai ba. Kofur Zubaina ta dubeni tace.
"Bari a kawo miki abinci ko Yahanasu? Kiyi haƙuri bamu daɗe da shigowa gidan ba. Zan kawo miki angonki har ɗaki zuwa anjima" Ni dai kaina na sunkuye bance mata ci kanki ba, sai adda'a nake jerowa dan kaina ji nake kamar zai buɗe. Abinci ta kawo mun a plate da ruwan gora. Ni da nake fama da zazzaɓi bakin nawa babu daɗi sam. Amman gudun kar rashin cin nawa ya jawo wata matsala, sai nayi bismillah na soma ci. Noma baifi biyar nayi ba, na ajjiye abincin nasha ruwa. A hankali nace.
Nagode Anty, ni zan tafi sai da safe" Wani murmushi tayi mai ma'anoni da dama tace.
"To shikenan Yaha, sai na kawo miki angonki. Murmushi kawai nayi na fice abuna, bakina ɗauke da adda'a dan ji nake tsigogin jikina sai miƙewa suke yi. A hankali nake tafiya har na isa ɗakina, ban zauna a falo ba, ciki na kutsa kaina na shiga. Sallar isha na gabatar, sannan nayi azkhar ɗina. Ban gushe ba na jawo Qur'ani na soma katanta baƙara. Ina cikin karatunne wayata ta soma ringing. Hannu nasa na jawo wayar. Dala ne yake kirana, cikin zumuɗi na ɗaga wayar tare da karawa a kunnuwana. Amon sautin tane ya cika mun kunnuwana.
"Yahanasu ina fatan dai kina lafiya kuma babu wata matsala ko? Dan Yanunu ta sanar dani irin tarbar da kuka samu a wajan Bulama Babba da matarshi. Ran Babanku Ba Bakura ya ɓaci sosai, dan bai daɗe da yin shiru ba, yau yayi faɗa sosai. Hajja gana tayi kuka kamar me" idanuna na lumshe, tausayin kaina da tausayin su Ba Bakura da su Ya Innana ya kama ni. Allah sarki uwa mai daɗi, jin muryarta ya sanyaya zuchiyata sosai, sai naji kewarta ta sake ɗaureni, cike da son kwantar musu da hankali nace mata.
"Ya Innana wallahi babu komai, ɗazu ma Bulama Babba yazo ɗakina ya kirani, muka je babban falon

12 / 67