Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
in samu in dinga biyan kuɗin makarantar. Mata da kike ganinsu a taron gidan biki ko suna, ko makaranta, ko ma'aikatu. Damuwowinsu na gidan aure wata da zata huda miki cikinta, kiji halin da take ciki tsakaninta da mai gidanta. wallahi sai kin ɗauka ba'a duniya kike ba, tsabar firgici. Maƙwociyarmu Maman Binta, bari kiji abunda ya faru da ita. Bazawarace Allah yayi ma mai gidanta na fari rasuwa. Suna zaune a wani ƙauye a nan Yola. Bayan rasuwar mijinta, ta shiga takaba, tana da yara uku da shi, biyu maza Babbar itace Binta mai shekara goma sha biyu. Data gama takaba, sai dangin mijinta mai rasuwa, su ka sa akai rabon gadon ƴar gonarshi da ya bari. Aka raba aka faɗi na kowa, harda nata tumunin takaba. Sisi basu ɗauka sun bata ba, sai suka ce da dukiyar, da yaran nasu ne, zasu haɗa su riƙe. Suka bata tuminin takabarta, ta kama hanya ta dawo Yola. Bata jima ba ta yi aure, aka kawota nan kusa da gidana, ana zumunci da'ita. Mijin data aure mai ƙaramin ƙarfine, kuma bama ita kaɗai bace matar tashi, mai gadine a wani asibiti, ganin haka sai maman Binta ta nemi aikin shara da wankin ban ɗaki a asibitin da mijinta ke aiki, cikin yardar Allah ta dace. Tare suke zuwa su dawo tare, a haka ta haifi yara biyu. Data je ƙauye ganin su Binta, sai ta nemi tawowa da Binta, dan ta ɗan sata a makaranta, ta kuma dinga kama mata aikin gida. Ta tawo da Binta, ana nan ana nan sai Binta ta shiga ciwo, tana ɗaukar Binta ta kaita asibiti, gwajin farko akace ciki take ɗauke dashi. Maman Binta ta shiga tashin hankali tare da tuhumar Binta wanda yai mata cikin. Hmm abun mamaki mijin Maman Binta ne ashe yake lalata da Binta, sau uku yanai mata ciki, suna zubarwa, a na huɗunne Allah ya tuni asirinsu duka, tunda ba tursasama Binta yayi ba, da son ranta komai ya dinga gudana. Kunji fa ƙarshen duniya, da ire_iren halin da wasu matan suke ciki a gidajen aurensu, wannan ba komai bane wallahilƙudrat akan halin da wasu ke ciki. A razane na dubi Hajja Fati nace.
Kuma ya makomar aurensu ta kasance Hajja Fati?" Murmushin takaici tayi mun tace.
"Kema kinsan makomar rabuwace kawai ai, amman ya cutar da'ita. Haka suka tattara suka koma gidan iyayenta. Yarinyar harta haihu ma, gashi maman itama tana da yara biyu dashi, amman dasu ta tafi, dan har kotu suka shiga. Hmmm Yahanasu nifa kaina a cikin matsaloli masu tarin yawa nake, daga wannan ya lafa sai wannan ya ɓullo, wallahi har ya zame mun jiki." A wannan daren kamar yadda suka ce, zamu raba dare suna bani magana. Hakan kuwa akayi, kuma na ƙaru gaya. Amman ni har su kai bacci idanuna biyu. Alwala na ɗauro na shinfiɗa ɗankwalina, na soma kai roƙona ga mahaliccina, buwayi gagara misali. Na yi sallah har ƙafafuna sai da suka kumbure. Kuka nayi shi a gaban mahaliccina, tare da roƙonshi ya bani juriya, da ƙarfin zuchiyar ɗaukar duk abinda zai tunkaroni a zaman aurena. Ya bani hanyar ɓullewa ba tare da naje gaban waninshi na durƙusa dan neman tallafi ba. Ya bani juriyar kawaici, da yakana kamar Ya Innana. Daga ƙarshe na tashi, na sha ruwa dan ɗaukar azumin nafila. Saini na tashi su Fanda dan su yi sallar asuba, idanuna sun kumbura da ganina, kasan nayi kuka har hawayena sun ƙafe. Ina jiyo muryar Bulama Babba yana magana da su Wakil. Sallar Asuba muka gabatar dukkanmu, ina zaune ina azkhar, na jiyo dawowar su Wakil.
"Fandau ku yi maza, asubar fari muka so tafiya. Amman Ba Bakura yace muje gidan Amininshi Alh Munka'ilu tare dukka." Bulama ƙarami ke magana da Fandau, fita tayi taje ta same shi. Yarinyar Hajja Fati sai canyara kuka take yi, Hajja Fati ta shiga aikin jijjigata, da ƙyar ta koma bacci.
Wai ni Hajja Fati wannan maganin da naga kin sha jiya, na menene wai?" Dariya tayi mun.
"Maganin cire damuwa, da sanya nutsuwane, da in na sha, sai in kwan in wuni ina cikin bacci, amman yanzu ya riga ya bi jikina, in ba haɗe haɗe nayi masu yawa ba, baya sani bacci. Sai dai in na kwanta bacci ina samun yin lafiyayyen bacci, hakan yana taimakamun wajan sauke mun hawan jinina, kinsan masu hawan jini anason su dinga samun bacci lafiyayye, musamman na dare." Idanu na zare nace
Ke nan kwayar da masu shaye_shaye suke sha ne, kema kike sha Hajja Fati, har matsalar da kike ciki takai wannan ne?"
"Tafi yanda kike tunani, kina cikin halin rashin samun bacci mai kyau kema, tun sanda akai miki fyaɗe, zaki fahimci ciwon rashin bacci shi kaɗai masifa ce. Ga baƙin ciki da takaicin ɗa namiji. Da zaki sha guda ɗaya bacci zaki yi mai kyau, a ƙalla zaki rage wani zugi daga cikin zuchiyarki, kuma kanki zai rage nauyi, zan baki ki ajjiye ƙila yai miki amfani" Murmushi nayi.
Haba dai Hajja Fati, babu amfanin da zai yi mun. Duk da nasan rashin bacci, ciwone babba, ni bama shi kaɗai ke damuna ba, harda rashin son ganin kowa a kusa dani wallahi, yanzu haka jina nake yi kamar in kurma ihu fa. Sasaucin da nake samu shine karatun Qur'ani da nake yi, a duk sanda naji zuchiyata ta raya mun cewar, in kashe kaina zan huta. Amm...... Kukane yaci ƙarfina sosai, ga kaina kullum a cikin ciwo yake a ko da yaushe, sakamakon rashin samun lafiyayyen bacci. Rabon da inyi bacci mai tsayi, tun kafin wannan ƙaddarar ta dirarmun, tunda wannan abun ya faru dani, zuchiyata bata sake samun nutsuwa ba." Rarrashina Hajja Fati ta shiga yi, tana bani baki. Hawayena na share, muka fito falo. A nan muka samu su Wakil da Fandau suna tattaunawa. Duk idanu suka ƙura mun.
"Lafiya idanunki da fuskarki suka kumbura haka Yaha? Nifa ina tsoron damuwar da zaki shiga bayan tafiyarmu, ga rashin son shiga mutane da kike yi, in muka tafi kar ki je ki kashe kanki da tunani" Wakil ne yake yi mun Magana cikin nuna kulawa."
A'a bazan kashe raina da tunani ba. In kunji kabarin mutuwa ta, to daga rabbissamawati ne, kar ku damu ƴan uwana, na gode da kulawarku, zan iya kulawa da kaina ni fa ba yarinya bace" Bulama ƙarami yace.
"Kajita fa Wakil, wai ita ba yarinya bace, yaushe yaushe yarinyarnan, ita da su Ba'a Kaka muke zuwa ɗaukosu a makarantar firamare?" Wannan maganar da ya faɗa ita tasa duk muka kwashe da dariya, nan sukaita ɗan jana da raha, har sai da na saki jiki dan kaina. Ƙarfe shidda muka shiga ɓangaren su Bulama Babba. Mama Gana da Yanunu, da Bagulaji muka samu a falon, suna saman kujera Bulama Babba yana gurfane a gabansu kamar mai ɗaukar gafara, faɗa mama Gana take yi sosai, Bagulaji da Yanunu sai bata haƙuri su ke yi. Dubanmu tayi tace.
"Ku shigo ku zauna. Kai kuma ka biyo mu ɗaki dan akwai muhimmiyar magana da zamu tattauna da kai. Tunda dukkan ku fita aiki zaku yi ku barmu jiran gidan, tunda baka san mutunci ba, wallahi ka bini a hankali daga kai har matarka da ƙannenta na faɗa maka kenan. In banda iskanci har mu kake faɗama akwai muhimmin aikin da zata je ta gabatar, da uwarta ce tazo gidan ai bazata hofantar da'ita haka ba. Kuma wa zai bamu abincin da zamu karya kumallo dashi tukunna?" Ya Bagulaji tace.
"Mama Gana ki bar yaronnan ya huta haka na roƙe ki, sannan ke kika ce bazaki kuma cin abincin matarshi ba, muma wallahi bama so akai kasuwa. Kai kuma Bulama kaci gaba da bin maras kunyar matarka Allah ya bamu lafiya. Kuma tunda baka ƙaunar zaman mu, zamu tattara mu bar maka gidanka yau ba sai gobe ba, ni dai bazan sake tako ƙafata in zo ai mun rashin daraja ba. Mama Gana mu shiga daga ciki mu sanar mishi abinda ya kawo mu, dan karma yayi tunanin dan kuɗin daya tara muka zo mishi gida" Da kuka ta ƙarashe maganarta, tare da shigewa ciki, suma baya suka mara mata. Shi kuwa Bulama Babba ba guiwa haka ya bi bayansu, idanunshi sun kuma rinewa, hawaye tab gurbin idanuwanshi. Ni kuwa tuni hawaye ya gama wanke mun fuskata, da sauri na fice a falon, na koma B Q ina kukan fitar hayyaci"
Bulama:
Gabaki ɗaya zuwan su Mama Gana ya zame mun matsala, tun sassafe an tusani gaba da tijara, sai kace wani ƙaramin yaro, ko iyayena naga ai sun shafa mun lafiya. Ɗan guntun tsaki naja a fili, bayansu nabi zuwa ciki. Sharar ƙwallar dana shigo na tadda suna yi, sai ya karya mun guiwa. Gurfana nayi a gabansu, ni dai bance komai ba, akwati na gani sabo fil a gabansu, a buɗe akwatin yake kayan maza na hango a cikin akwatin, harda su huluna zanna. Ya Bagulaji tace.
"Wannan zuwan da kaga munyi, umarnine daga wajan Bakura, da Hajja Gana ba wai yin kanmu bane, kai baka bimu ba amatsayinmu na iyayenka, ai kuwa baka isa mu mu biyoka ba,. Wannan akwatin daga gani a gabanka, kayane wanda al'adar Kanuri ta tanadarwa ango, wanda yake fitowa daga dangin Amarya . A cikin akwatin akwai shaddajo, akwai yadika, wasu kayanma anyi musu ɗinki irin na sarakai, akwai takalma, turare, agogo, huluna, sallaya da Qur'ani. Dukka naka ne Bulama Babba. Ga Yahanasu nan Ba Bakura ya aura maka ita, ma'ana matarka ce ita a halin yanzu. Yayi hakanne dan sanin cewar ya isa da kai, kuma shi ya haifeka, ya ɗau jirimin tarbiyantar dakai, da baka ilimi. An haɗa aurenne a sakamakon ƙaddarar data gibta cikin rayuwar Yahanasu, aka samu wani azzalumi ya keta mata haddinta, yai mata fyaɗe. Anyi taro sosai kafin a haɗa aurenka da'ita. Kai dai jininta ne, muna da tabbacin in dai kana cikin hayyaci, da nutsuwa, baza ka bari wani ma ya cutar da Yahanasu ba, ballentana kai a kan kin kan ka ace ka cutar da'ita. Ya rage naka in ka hofantar da ƴar uwarka ka rungumi bare. A wajanka ne kaɗai zata samu nutsuwa, ba tare da ta fuskanci ƙalubale dangane da ƙaddarar data faɗo mata ba" Tunda ta soma magana jikina da hantata suke rawa, kalmar Aure data faɗa ya firgita tsigar jikina, ya jijjiga duk wata tsokar dake jikina. Maganar fyaɗe yasa na ɗimauta, harma na rasa wanne tunani zanyi, damuwata shine taya zan tunkari Zubaina da wannan zancan, sannan a matsayina na wan Yahanasu ya zamu yi mu gudanar da rayuwar aure, a rasa da wanda za'a haɗata saini, saida akai mata fyaɗe bata da wata daraja sannan za'a liƙa mun ita, mummuna da'ita ƴar lukuta wannan ai abun kunya ne ma a gareni ace Yahanasu ƴar lukuta matata ce, anya kuwa Ba Bakura suna ƙaunata kuwa? Ciwon kan da nake fama dashine ya kuma tsananta, sai tsalle zuchiyata take ta faman yi, in haɗiye yawu ma in samu salama abu ya gagara, sai dambe nake da yawun bakina. Ina cikin wannan saƙe saƙen na kuma jiyo muryar Mama Gana tana cewa.
"Sannan Bakura yace mu sanar maka, in har ka kasa riƙe Yahanasu tsakani da Allah, to bazai yafe maka ba, ya kuma da cewa in kayi sanadiyyar wargajewar zumuncinmu, bazai yafe maka kan wannan ba. Da munso mu ni da Yanunu muyi ma Yahanasu zaman bakwai. Amman a halin yanzu mun canja ra'ayi, tafiyar da su Wakil zasu yi yau, na dakatar da'ita. Su bari zuwa gobe in muka gama yi ma yarinya jere, sai mu ɗunguma mu tafi baki ɗaya, sannan inaso ƙannen baƙar tijararriyar matarka su bar gidannan kafin mu tafi, domun hakan zaifi muku alkhairi baki ɗayanku. Ni dai na kasa cewa komai, sai ta'ajibi nake yi a zuchiyata, da ƙyar na ka da baki nace.
Amman to a ina zata zauna ita Yahanasun, gidana na zaman mutum ɗaya ne, sai masaukin baƙi da nake dashi, kuma ƙannen Zubaina suna zuwa suyi mana hutun makaranta, acan suke sauka. Sannan Mama Gana kiyi haƙuri kar kice na yi miki rashin kunya. Amman su Asiya anan zasu ci gaba da zama tare damu, domun ni nake kula da su, kuma nauyin karatunsu akaina ya rataya"
"Rufe ma mutane baki gafara, rashin kunya kuma na nawa, ai baka cika ɗan iska ba tunda baka haɗesu ka auresu dukka ba ƙarshen zama kenan. ƙannen Zubainar banza da wofi. A can BQ ɗin zamu jera kayan ita Yahanasun, sai ta zauna a can, ita kuma mai sarautar birnin zuchiyarka saita ci gaba da zama a nan, tunda dama nata ne, kar a takura mata, su sakata su wala da ƙannenta. In ƙannen nata maza sun zo hutun sai ka basu naka ɗakin su kwana, akwai wani gyara ko fenti da BQ ɗin yake buƙata ne?"
A'a baya buƙatar gyaran komai, baifi wata ɗaya ba dana sabunta fenti, sai dai babu kitchen a ciki, bansan yaya zata yi ba" Ya Bagulaji tace.
"Zamu ga dabarar da zamu yi mata dangane da wannan, maganar abincin kari fa Yaya zaka yi damu?"
Me gadi zai kawo muku waina, tun ɗazu ya tafi siyowa, ni zan tafi office sai na dawo" Ficewa nayi a ɗakin, ina jin kaina kamar zai buga, ji nake yi kamar a mafarki, wai ni aka aurama Yarinyar da akaima fyaɗe, hmmm gaskiya iyayena ba ƙaunata suke yi ba. Ba wanda na kalla a falon, ɗakina na wuce kai tsaye, dan shirin fita office. Zubaina na samu a ɗakin tanai ma Maryam wanka, Bawa kuwa har ma ya sa kayan makaranta. Kallon Zubaina nayi, idanuwana sai wani zugi suke yi mun.
"Meke faruwa Bulama, naga fuskarka ta sauya, duk da dai ina jiyo yanda ƴan uwanka suka dura a kan ka. Ka yi haƙuri kasan fa sai haƙuri da ƴan uwa, amman bana jin daɗin yanda suka tsangwameka, kuma duk dan sabida nine"
No ba sabida ke bane Zubaina, ba sona suke yi ba. Tunda suka zo basu barmu mun huta ba. Ni wallahi bana farin ciki da zuwan nasu, shi yasa ma bana son zuwa inda suke. Mtwss. Naja dogon tsaki mai sauti. Kaya na sake, ko karyawa bana ƙaunar yi, Zubaina tayi tayi dani in karya, amman naƙi, jikina wani irin ɓari yake yi. Tsoron Zubaina na barazanar kekketa mun zuchiyata.
"Maganar kayan da suka zo dasu cikin mota fa sun sanar da kai na menene, tunda sunce sai da safe? Ni har mafarkin kayan sai da nayi" Gabana ya yanke ya faɗi, amman bana iya ɓoyema Zubaina komai, kuma ko na ɓoye zata sani dan bama abun ɓoyewa bane.
Bawa kuje ku samu su Asiya a ɗakin Momy ko maza yanzu zan zo sai mu tafi" Zubaina tace da Bawa.
"Kace su baku tea ku sha, maza kuje" Nutsuwarta ta dawo dashi gareni tace.
"Ina sauraranka, baka da lokaci, dan ka kusan yin latti" Jim nayi, bansan ta inda zan soma ba.
Ba Bakura ne ya ɗaura mun aure wai da Yahanasu, shine suka kawota, kayanta ne a motar" Ajjiyar zuchiya na sauke, na dafe kaina tare da runtse idanuna, ina jin wani ciwo a zuchiyata, tare da jiran abunda Zubaina zata ce." Murmusawa naji Zubaina tayi, abun mamaki, dan ba abunda na zata daga gareta ba kenan, wallahi na ɗauka ƙaramar hauka zata yi mun. Hannuna ta zame mun zuwa ƙasa, tana hawaye, ga murmushi a fuskarta. Gabaki ɗaya ta rikirkitani.
Ki dena asarar hawayenki, babu wata mace da zata samu irin kwatan so da kulawar da nake baki, Bulama naki ne Zubaina. Akan waccan kucakar yarinyar kike kuka, ta isa ta haɗa kanta da ke ne?" Murmushi tayi, ta sa hannu ta share hawayenta tace.
Bulama wannan hawayen daka ga ina zubarwa bana komai bane, face tausayinka. Yau na kuma tabbatarwa lallai iyayenka da ƴan uwanka ba sonka suke yi ba, kuma suna adawa da aurenmu ne sabida ni ba Kanuri bace. Amman kayi haƙuri ka rungumi ƙaddarar data tunkaroka. Ta ɓangarena baka da wata matsala, Allah ya bamu zaman lafiya, kuma kar wannan yasa ka damu kan ka ma sam. Damuwar shine, a ina to zata zauna tunda dai ni na cinye nan?" Ajjiyar zuchiya na sauke, dan dama babban damuwata shine, bansan da wacce siga Zubaina zata fassara lamarin ba. Amman naga bata ɗauka da zafi ba. Lallai Zubaina ta cika matar rufin asiri, mace ta gari, mai son farin cikin mijinta da ƴaƴanta.
A BQ Mama Gana tace zasu yi mata jeren. Zubaina me kike so inyi miki dan in faranta miki rai a matsayin dannar ƙirji? Ki sanar dani duk abinda kike so, ni kuma zan mallaka miki" Dariya tayi tace.
"Wannan ka bari sai ka dawo sai mu tattauna. Ka ɗauki yarannan ku tafi, ni kuma zanje ƙauye bincike dangane da case ɗinnan, bansan ƙarfe nawa zan dawo ba, gashi inason zuwa in ga Mama." Key ɗin babbar motata na miƙa mata, ta harareni cikin soyayya tace
"Wannan na meye to kake bani?" Rungumeta nayi tsam a jikina ina sauke ajjiyar zuchiya. Cikin raɗa nace mata.
Na baki motar kyauta, ni zan riƙe taki. Zubaina duk abunda na mallaka naki ne, ke da su Mama, abinda kike son ayi a gidannan shi za'ayi Zubaina. ki ɗebi kayan abinci a store ki tafinma da su Mama dashi" Sakinta nayi, na ajjiye mata key ɗin motata na ɗauki tata, na fice a ɗakin, ina share zubar data tsattsafomun. A dai dai wannan lokacin da za'a auna ni, haƙiƙa jinina ya hau, tsabaragen rudanin