Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
haihu ba wani nawa a kusa Mama al'amarin gidannan tsoro yake bani wallahi" Tsaki Mama tayi tace.
"Ban kira ki dan ki faɗamun labarin gidanki ba. Zubaina ke kike sha'awar zama da Liti, babu wanda yai miki tilas, ke ba dai kince kin dena bin bokaye ba, kin ja hannu kin naɗe ko? Kuka yanzu kika soma. Mijin Asiya yayi mun burking jirgi, sati mai zuwa sai in tawo. Amman in kina jin halamun haihuwar a kusa ko jibi sai in kamo hanya ai. Asiya da Nafeesa dai sai ana gobe suna zasu tawo. Musa kuma ya samu matar Aure, har ma yaje ya samu kawunku da maganar, yau da daddare zasu je gidan su yarinyar. Sagiru kuwa ban faɗa miki bane sabida kar abun yayi miki yawa. Yau ɗinnan aka sakoshi daga fursuna watan shi hudu a gidan ɗan kande. Wata gagarumar sata suka tabka a wani kamfani, shine aka kamasu. Ai mun sha sintirin zuwa kotu. Musa kuwa hmmm wallahi yanzu haka ma dadironshi bata daɗe da barin gidannan ba, munfi wata biyu muna tare, tun ana boyewaa har aka dena. So suke su kasheni su huta, ga Asiya bata jin daɗi a kwance ma take." Kuka Mama ta fashe dashi mai ciwo. Shiru nayi ina sauraren amon kukanta. Bayan duk ita tai sanadiyyar ɓalɓalcewarmu, ita ta ɗauramu bisa mummunar turba. Ga tsinuwa bisa abunda bai taka kara ya karya ba. Yaya ba zamu gamu da iftila'i ba?"
Kiyi haƙuri Mama Allah ya shiryesu baki ɗaya. Asiya wanne irin ciwo ke damunta to?" Mama tace.
"To mijin dai yace kamar makarai take yi. Tunda ya kaita ƙauyansu ziyara suka dawo yarinyarnan a kwance take fa, ko bacci basa iyayi da daddare. Amman ana mata hayaƙi, da wankan magani. Ni dan ina fargabar yadda haihuwarki take ne ma, da bazan zo Ghana ba, itan zan sa ya kawo mun ita muyi jinyarta a gida. To kema ina duba yanayin da kike ciki. Rakiya kuma bata nan." Haka dai Mama ta kashe wayarta ta barni da jimami, kullum mu kai waya sai naji abu maras daɗi wanda bazai barni bacci ba. Bayan isha na kulle ɗakina na wuce turaka. Haka naita tura cikin zuwa kwana biyu. Mama tun asuba ta kirani tana Airport na Kano zuwa Lagos, sai da taje ta dubo jikin Asiya tukunna. Nima jikin nawa tun bayan hantsi nake jina sama_sama dai. Zuwa sha ɗayan rana ruwa ya soma bin ƙafata, sai uban wanke wanke muke yi ni da Zarah. Tun ranar da Alh Liti ya kayar da Zarah a tsakar gida, ta dena tsiwa, sai harara da tsaki da zaran kun haɗa idanu. Baya nane yayi wata iriyar ƙagewar da bansan sanda na ɗan saki salati da ƙara ba. Dafe ƙuguna nayi ina cije leɓena.
"Zubaina ko naƙudarce ta tashi? Nabeela goya ɗiyarki ke da Rashida ku kaita ɗaki. Tun jiya naga halamun naƙuda take yi a tsaitsaye." Rashida da Nabeela ne suka rirriƙeni, a daddafe muka isa ɗaki, a kan cinyayyar tabarmar ɗakin na durƙushe ina shan yaji ina cije bakina. Abu kamar wasa fa naƙuda ta rabkeni sai fama nake tata yi. Unguwar zoman dake karɓar haihuwar matan Alh Liti ce a kaina sai faman bubbugamun baya take yi tana faman yamutsamun cikina. Awa uku ina abu guda duk na galabaice, sai aikin sannu Hajiya Kubra da Nabeela suke jeromun. Ni kuwa bana ma iya amsawa sai cin kwakwa nake yi. Wani nishi ne naji yana tunkudo kanshi min indillah, ina yin wata ƴar ƙara sai ga kukan jariri ya faɗo a hannun unguwar zoma. Numfashi na shiga mayarwa ina ganin yanda yaron yake ta wiltsil_wintsil. Wani sabon naƙuda ne ya sake turniƙe ni, baifi na minti talatin ba na kuma haihuwa, ko wanne jariri da mahaifarshi, bansha wuya ba mabiya ta fito. Sai rawar sanyi dana soma yi.
"Kai masha Allah, Allah ya kawo mana ƴan biyu kyautar Allah cikin zuriya. Duk aure aure da Alh yaita zabgawa babu wacce ta taɓa haifar biyu sai ke Zubaina. Ni dai sai yaran kawai nake kallo ina tausayama rayuwar da zasu taso su ga kansu. Wani irin ƙauna ta mahaifiya da ƴaƴa ta shiga hudani. Zani Nabeela ta miƙo mun na ɗaura, na zame wanda ke jikina, gado na hau na lulluɓa na shiga rawar sanyi. Kafin kace me sai zazzaɓi ya rabkeni. Ana cikin yi ma jariran wanka sai ga Rashida da akwatin Mama da jakarta. Tare suka shigo.
"Au ta sauka ashe? Wooo ƴan biyu muka samu? Allah ya raya mana ku yara" Cewar Rashida. Mama kuwa babu wani fara'a a ranta sam. Tsallakewa tayi ta same ni a kan gadon. Jira _ jiran kuma an saka musu kayan gwanjo, wanda sai da na siyar da ɗankakkun kayana kala biyu na je kasuwa na ɗan tsinto kwashe.
"Zubaina lafiya lau kike dai ko?" Magana wannan na kasa. Mama duk tabi ta ɗaga hankalinta. Babu shiri ta tattagemu daga ni har jariran sai asibiti. Gado aka bani, kafin mu je asibitin ma duhu ya mamaye mun idanuna.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
[17/08, 12:06 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. 50
Asibiti:
Mama:
Tana zaune a ɗakin ganin likita yanai mata bayanin halin da kofur Zubaina take ciki.
"Mama hawan jini ne ya rafketa mai ƙarfi. A binciken da muka gudanar Zubaina tana cikin matsananciyar damuwar da in ba kwantar mata da hankali akeyi ba. Komai ka iya faruwa da'ita. Kinga hawan jini babban ciwone wanda a shekarunta bai kamata ma a sameta da wannan ciwon ba. Ga ciwon damuwa da a yanzu yake jefa mata a cikin fitintinu iri daban _ daban. Ya kamata a ririta mata lafiyarta ne. Gashi ta galabaita sosai a haihuwarta, basu samu wata kulawar daya dace ba." Kuka Mama ta fashe dashi tace.
"Mugun kafiya ne da Zubaina, ita ta jefa rayuwarta cikin rayuwar da take a yanzu. Allah na gode maka dame mutum zaiji ma to wai? Ta dubi likitan tace.
"To yanzu likita menene abunyi? Ka ganni babu wani ishasshen kuɗi a hannuna, zamanmu a asibitinnan ba yiwuwa zai yi ba. Likita ya dubi Mama yace.
"Zan iya sallamarku in ta farka daga baccin da take yi zuwa gobe. Amman kar a barta ta zauna ita kaɗai tana da buƙatar masu ɗebe mata kewa. Sannan a guji abunda zai jawo mata ɗacin zuchiya, Allah ya sauwaƙe" Mama tayi jin kafin tayi ma likitan godiya ta fita a ofishin. Jiki a mace ta koma ɗakin da aka kwantar da Zubaina, Rashida ce zaune a gefen gadon. Jariran dake bayan Rashida a jere duk su biyun Mama ta ƙura ma idanu. Ƙaddarar ƴaƴannan ce ta kawo Zubaina Ghana aure. Amman tana tunanin ƙaddarar ita ce dai zata sa ta rabu da Alh Liti ta bar mishi yaranshi, ta bi Mama su koma gida najeriya.
Washe gari
Zubaina:
A hankali na buɗe idanuna ina ƙarema Mama kallo wacce take zaune a kujera tana ba jariran ruwa a karamin kofin filas na yara.
Mama maza ne ko mata? Na tambayeta cike da son na son me na samu." Idanu Mama ta kafa mun tace.
"Ba shakka Zubaina, wato da zancan daya dace ki tareni kenan a naki rashin hankalin ko? To mata kika samu duka, bayan wannan sai me zaki tambaya kuma uwata?" Idanu na lumshe ƙwallar data taru a guraben idanuna suka gangaro. Lokaci ɗaya Mama ta sakko ta shiga rarrashina.
"Ki dena kukan haka Zubaina ya'isa haka nan. Kinga yaranki farare sol kamar ubansu." Matso mun dasu tayi na kallesu da kyau har ina ɗan murmushi.
Alh Liti yazo kuwa Mama, ke kaɗai ce a nan ɗin?"
"Ki ture waɗannan tambayoyin ba lafiya bace dake, yanzu dai ki tashi ki sha tea, kafin in siyo miki abinci. In kika gama ci mayi magana. Sai da Mama ta haɗa mun tea kakkaura sannan a ajjiye yaran a gefena ta fita siyo mun abinci. Soyayyar taliya da soyayyan kifi ta siyo mun. Zagewa nayi na cinye take away biyun data dure mun, nayi gyatsa an daɗe ba'a haɗu ba.
"To likita ya bamu sallama da safennan. Dama ke kawai nake jira ki farka sai kuma mu kama hanyar komawa firsina ko? Taso bari in taimaka miki." Sai da mama ta goya ƴan biyu a bayanta ɗaya ta gaba ɗaya ta baya, sannan ta taimaka mun na miƙe, kaina kamar zai fice ga ruwan jiri yana dibata. A haka muka shiga ofishin Likita. Shawarwari masu yawa ya bani. Mu kai mai godiya muka fita a asibitin. Lori Mama ta tarar mana zuwa gida. Ni dai ina zaune ne a motar, amman tunanin dana saba shi nake yi dai. Ina tunanin yadda zanci gaba da zaman uƙubar gidan Alh Liti. Da kuma tunanin yanda zan bar yarana a tsakar gida in yau Alh Liti yaga wata macen yazo ya tafa mun takaddata a hannuna. Oh ya Allah kaimun mafita, Allah na tuba kaine majiɓancin lamurana. Juyowa nayi na kalli Mama nace.
Mama kuna zuwa dubo su Maryam a Kano kuwa, ko Asiya ta taɓa zuwa?" Harara Mama ta zabga mun.
"Babu wanda ya taɓa zuwa, banjin akwai kuwa wanda zaije. Ke dai tunda yaranki ne in kika samu damar zuwa Najeriya kinga sai ki je ki dubosu. Bulama sai yaga lalacewar da kika yi, kinga sai yayi miki dariya. Yahanasu tayi miki Allah shi ƙara. Zubaina wallahi ba dan likita yace a lallaɓaki kin kamu da hawan jini ba, kuma ciwon damuwa zai iya kamaki a ko da yaushe ba. Wallahi da kinci ubanki da duk maganganunnan. Ke nifa wallahi ko mutuwa zaki yi in baki bini mun tafi najeriya kin rabu da ƙaddararren mutuninnan ba, to Zubaina sai dai fa in kika mutu a burne gawarki a Ghana, ƙila ƙasarki ce take nan. Ke kinga yadda kika koma kuwa kamar wata dodanniya? Ko sha'awar rayuwa bakya yi, da ƙuruciyarki da kyanki, da kuma lokaci, amman sakarcii kina son ki bari ya dakusar miki da hasken tauraruwarki. Alh Litin da daya sake ki, kina haɗe idda ƙila wani hamshaƙin ɗan kasuwan yazo yayi wuf dake, muma mu dangwali arziki daga gareki." Murmushin takaici kawai nayi. Waɗannan tunane_tunanen na Mama shi ya jamu zuwa ga wannan rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Allah ya kiyasheni taɓewa. Bance mata komai ba, har muka shiga cikin gida Mama tana sababi. Dan ko da Nabeela tazo da saurinta zata karɓi kayayyakin hannun Mama cewa tayi.
"Ƴarnan basshi kinji, da lafiyata ras bana buƙatar taimakon kowa a cikin wannan jarabben gidan mai cike da jarabawar rayuwa." Ta ja hannuna muka ƙule ɗaki. Kwanciya nayi ina lumshe idanu. Mama kuma ta kunce goyon tagwaye a bayanta, zata fita kenan Hajiya Kubra ta shigo da sallamata. Ni na amsa mata, Mama kamewa tayi a jikin bango tana jiran ƙiris.
"Mama ayi haƙuri bamu samu zuwa dubiyar Zubaina ba. Wallahi mai gidanne ya hana mu zuwa. Dan yace ba'a nemi izininshi ba aka fita da Zubaina ba. Amman munso zuwa, yanzu dama Rashida take shirin kai muku abinci. Umman ƴan biyu ya ƙarfin jikin?"
Da sauƙi Hajiya nagode." Nabeela ce ta shigo da kwanon abinci da kofin ruwa ta ajjiye a gefen gado.
"Umman ƴan biyu yaya ƙarfin jikin? Kinga bamu samu zuwa ba ko? Hmmm buyagin da Alh yayi a tsakar gidannan ranar da kuka tafi ai bata wasa bace. Shi ya hana mu zuwa ma. Mama ayi haƙuri" Ni dai a ido_ido nake kallon Mama tsoro na Allah, tsorona karta tsinka ni a gaban kishiyoyi. Sai cewa tayi.
"Hmmm Allah ya kyauta. Ai kuwa ina ji ina gani bazan bar ƴata a cikin haɗari ba, da har saina tsaya wani neman izininshi ni da ɗiyata. Am bayin Allah, zata samu ruwan wankanta dana yaran ne, ko shima ruwan ya hana?" Banji daɗin kalaman Mama ba, amman su kansu sun fahimci a halin da Mama take na fishi. Hajiya Kubra tace.
"Zata samu, akwai ƙatuwar tukunya a wuta, Zubaina ki shirya za'a kai miki ruwa. Nabeela zata kawo ruwan wankan yan biyu." Fita su ka yi tare.
Haba Mama, dan Allah......
"Kinci ubanki, Zubaina in baki bini a sannu ba, sai in ɗaga miki nono kinga sai ki ƙara miƙe ƙafarki a duniya. Ni zaki ma ƙorafi dan na caccaki kishiyoyinki. Au yanzu ke nan har kishiyoyi kin ɗaukesu ababen shawara ko kuma ababen yarda kenan? Tana cikin sababi Nabeela ta shigo da ƙaramin bokitin ƙarfe, da ruwan zafi rabi. Harda sabulun salonta da take ma jaririnta wanka dashi.
"Kawo ɗaya in soma yi mata" Cewar Nabeela. Mama tayi carab tace.
"Mun gode, jeki abunki" Nabeela bata tanka ba ta fita abunta.
"Haka kawai a je a kashesu a banza, kishiyoyi da muguntar tsiya, yau ni naga tsiya da wasali ƙasa, a bokitin zanyi wa yaran wanka Zubaina?"" Ni dai tsabar haushi banko kalleta ba na yafa fallen zani na fita a ɗakin ina bin bango, da zagi ta bini. Sai da na sake surka ruwan wankan, dan likita yayi mun gargaɗi kan ruwan zafi. Naji dama dama sosai dana yi wankan. Ƙunzugu nayi da ɗan kwalin atamfata na yafa zani na fito. Na shiga ɗakin na tarar Mama na gasa ma ƴan biyu cibi, har ta kunna turaren wuta a ɗakin. Ina zama wayata ta shiga ruri. Mama ta jawo wayar tace.
"Rakiya ce ko lafiya?" Wayar ta ɗaga ta sa a handsfree taci gaba da gashin cibi.
"Rakiya kin dawo ne daga tafiyar?" Mama Rakiya tace.
"Na dawo babu shiri Musa ne ya kira ni jiya wai mijin Asiya ya dawo da'ita gida. Jikin nata ya tsananta ainun. To shine na dawo ba shiri Yaya. Jikin babu daɗi, gashi wuyanta yayi wani irin mugun kumburi. Nifa ina ganin ko garin biye biyen ƙauyukan bin bokayene tayi gamo da jinnu. Dan ciwon yafi kama da hakan. Sambatu iri_iri. Yaya ba ma wannan ba, mijin yarinyarnan fa tunda ya zo ya ajjiyeta wallahi bai sake kiran waya ba. Daga cikin danginshi babu wanda ya kira mu, kuma bai ba da ko sisi ba. Akwai matsala." Daga ni har Mama dukkanmu mun shiga cikin damuwa ainun, hankalina ba karamin mugun tashi yayi ba. Mama tace.
"Rakiya ni nama rasa me zance, na shiga ukuna asirina yana dab da tunuwa, ko aikin da muka yi akan Alh ya samu tangarɗane. Ƴata kuwa wallahi duk wanda ya taɓa mun ita da asiri ya tono tsuliyar dodo. Gobe zan kamo hanya, yanzu ku kuna ina?
"Yaya muna gidanki. Ina wani tunani ko dai abokiyar zamanta ce tayo mata wani agumun? Ke kinga yanda Asiya ta canja lokaci guda kuwa, sai dai kin zo Yaya. Zubaina me ta samu?" Sai da Mama ta taɓe baki tace.
" Ƴan biyu mata, yanzu muka dawo asibiti ma, hawan jini ne ya kamata, sakamakon uƙubar azabar da take ciki. Rakiya komai ya kwaɓe mana. Ita fa kanta Nafeesa a cikin ƴan matsaloli take, yarinyarnan ko bacci bata iya yi. Rakiya sai dai na dawo kawai." Ƙit Mama ta kashe wayarta, ta rushe da wani kukan baƙin ciki. Nima kukan nake yi. Dama nasan tunda dai su Mama suka ƙi tuba, ƙarshen ba kyau zaiyi ba. Ai duk bawan da yayi fito na fito da ƙudurar Ubangiji, to ƙarshenshi taɓewace, tare da shiga fitintinu iri_iri. Ina nema ma dangina sassauci. Muna cikin wannan halin Alh Liti ya shigo cikin ɗakin ranshi a taurare. Gabana ya yanke ya zube, Mama ya tsallake ya matso bakin gadon ya ƙura ma yaran idanu, nima ya dubeni da kyau yace.
"Yanzu ba anjima ba ki same ni a sama, ki kwaso yaran naki kizo dasu" A ɗarare nace mai.
Ina jin jiri da yawa, banjin zan iya hawa sama. Ga Mama Alh ku gaisa" Sai cewa yayi.
"Oh wai Jummai?, dole ne sai na gaisa da uwarki dan tazo wajanki? Wancan zuwan nayi mata gargaɗi akan yi mun kutse cikin lamarina bata ji ba." Ni da Mama baki muka sake muna kallonshi. Tsallake Mama yayi, har yana take mata yatsun ƙafa.
"Jummai daga yau sai yau karki kuma zuwar mun gida, ƴarki nake aure, baku kuke aurena kamar yadda kuka saba ba, ko Alh da kuka tabkeshi da asiri yanzu kanshi ya fito a tukunya, in kin koma najeriya kya ji mummunan labari. Ita kanta ƴarki alhakin mijinta na baya da iyayenshi ke bibiyarta, a hakan ma nata yayi kyau, bari mu jira naki, ƙila kafin ki mutu haushin kare zaki soma"
Alh Liti...... Karka kuma kallon mahaifiyata ka dinga faɗa mata kaifafan maganganu irin wannan....." Bansan sanda na miƙe tsaye ba, cikin ɗaga murya da dakiya nake magana dashi. Mari ya gaura mun, ya kai hannu zai ƙara mun Mama ta shiga tsakani, marin a kan kumatunta ya sauka tau, Alh Liti ya ɗaga ƙafa ya tunkudo mama ta faɗo jikina duk muka zube a ƙasa muna kukan baƙin ciki."
"Yan iska, wallahi ni ba ƙaramin aikina bane in muku fitsari a ka ba. Ni babu wata tsohuwar ƴar iskar data isa juyani. Na fiku bin bokaye, mahaifina tsohon ɗan tsubbune. Kuma wallahi gobe_gobe ki tattara ki bar mun gidana kar ki kuma zuwar mun. Ke bake ma kaɗai ba har waɗannan karuwan ƙannen nata karsu sake su tako inda muke. Ke kuma ki taso dan ubanki ki kawo mun yara in yi musu huɗuba"
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE[18/08, 9:16 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 51
Wani gigitaccen kuka na kuma saki mai ƙarfin sauti, nayi imani duk wanda ke tsakar gida ka iya jiyo kukana. Wani irin duhu ne yake mamaye mun idanuna, kaina ya sake tsananta ciwo ainun. Adda'a dukkan wacce