Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
lafiyar ƙwaƙwalwata na gane kaina, har nazo a fahimci a inda nake. Na koyi darasi masu yawan gaske, na haɗu da mutane mabanbantan ra'ayi. Da a ɗakinmu mu goma ne, amman yanzu mu huɗu muka rage, da sannu sannu anata samun lafiya. Na koyi sana'ar ɗinki. Kuma ni malamace ina koyar dasu ilimin Hadith, sai matan ɗakinmu da nake yi musu ƙarin Qur'ani. Bani da wani buri daya wuce inga na bar cikin gidannan na koma ɗakin mijina, na shinfiɗa kyakkyawar rayuwa mara algus. Ina tausayin Bulamana fiye da yanda nake tausayin kaina. Ina jin tsantsar kunyar haɗa idanu da Ba Modu, da Ba Bakura, da Ya Innana sosai. Ina fargabar yanda zan fita in shiga cikin al'umma da irin tarbar da zan samu. Idanuna na buɗe na dubi ƙawayena ƴan ɗakinmu ko wacce na kalla sai inga tana zubar da hawaye irin na nadamar masifun da muka jefa kawunanmu. Murmurshi nayi na ƙarasa garesu na zauna ina fuskantar su.
Mrs Bukhari ce
[16/08, 9:21 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
47
Ga wani hadisi zan karantar daku ko hakan zai kawo sanyi da haske a cikin ƙirazanmu.
( An karɓo daga Abu Malik, Harith bin Asmin Al_Ash'ariy yace, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace. "Tsarki rabin imani ne, faɗin Alhamdu lillaah tana cika mizani, faɗin Subuhanallaah wal hamdulillah, su biyun suna cika, ( ko kuma kowacce ɗaya daga cikindu tana cika) abin da yake tsakanin sama da ƙasa, kuma sallah haske ce, sadaka kuma hujja ce, haƙuri kuma haske ne, AlQur'ani kuma hujja ne gare ka, ko a kanka, dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa ya sayar da kansa, ko dai ya ƴantar da kansa, ko kuma ya halakar da kansa" Muslum ( #223) ya yawaito. Idanu na zuba musu hankulansu da nutsuwarsu duk sun miƙa mun. Sai naci gaba da bayani na.
Da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, tsarki rabin imani ne, magana mafi inganci dangane da tsarki, shi ne abin da hankula yake zuwa gareshi da zarar an ambaci kalmar tsarki, kamar alwala, da wanka, da taimama. Waɗannan su ne ake kira da suna tsarki, cewar tsarki rabin imani ne, akwai maganganu da yawa a kan hakan. Ko dai mu fassara imani mu ce shi ne sallah, sai ya zamanto tsarki ne rabin sallah. Masu wannan magana suka ce, saboda sallah an sa mata suna imani a cikin AlQur'ani. ( ... Da ɗai Allah ba ya nufin ya tozarta imaninku ( Sallarku).... Suuratul Baƙara: 143) Imani a cikin wannan aya ana nufin sallah. Don haka Bukhari ya kawo wannan hadisin a cikin babin da yake nuna cewa sallah tana daga cikin imani. Sai suka ce tsarki, wanda tsarkin nan wanda ya danganci wanka ne, alwala ne, duka biyun ne, taimama ne, sai dai da tsarki ake yin sallah, sai fa in wani uzuri ya hana ka dukkan waɗannan. Waɗansu kuma suka ce a'a, al_imaan yana nan a bisa ga yadda muka san imani. Tsarki shi ne rabin imani, imani kuma shi ne wanda ta'arifinsa ya riga ya gabata, tun can a baya. Suka ce abin da ya sa muka ce haka, saboda imani shi ne ƙudiri kyakkyawa a cikin zuchiya dangane da kaɗaitakar Allah da manzanni da sauran duk abin da ake faɗa. To ɗan Adam , wato ɓangare biyu gare shi, ɓangaren jiki da ɓangaren zuchiya. Imani zai tsarkake ɗaya ɓangaren na ɗan Adam, wato zuchiya, shi kuma tsarki wanda ya danganci alwala ko wanka zai tsarkake ɗaya ɓangaren na ɗan Adam, wato gangar jiki. Sai ya zamanto da imani da tsarki kowanne ya ɗauki rabi kenan!
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, yawan maimaita lafazin Alhamdulillah yana cika mizanin awon ayyukan mutum a ranar tashin ƙiyama. Wannan misali ne Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yake bugawa. Ma'ana da a ce waɗannan kalmomi za a yi halitta da su, da wannan za ta iya cika mizani in an zo auna ta a kan mizani a ranar tashin ƙiyama. Ko kuma ka ce lada da mutum zai samu sakamakon faɗin Alhamdulillah yana cika mizani.
Sai kuma manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, faɗin ....subhanallaah wal hamdu lillaah, su biyun suna cika, ( ko kuma kowacce ɗaya daga cikinsu tana cika) abin da yake tsakanin sama da ƙasa..... Wato ladansu kenan. Wannan mai wannan riwayar hadisin ne ya yi shakka, imma dai Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ce su biyun ko kuma ya ce kowanne ɗaya daga cikinsu.
Sai kuma manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce .....sallah haske ce, sadaka kuma hujja ce... A nan ana nufin sadaka ta wajibi, wato zakka. Ma'ana hujja ce bisa ga cewa mutum yana da imani, hujja ce bisa ga cewar mutum ya amsa umarnin Allah , hujja ce bisa ga cewar yayi yaƙi da zuchiyarshi. Sai kuma ya ce, ........ Haƙuri....." Ma'ana yayin da duk ka tashi kafa hujja a musulunci, to ya zamanto ka kafa hujja da AlQu'ani ko hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, in ba haka ba kuwa ba kabi Allah da ma'aikinsa ba, AlQur'ani ya zama hujja a kanka. Sai kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ce ......dukkan mutane suna jijjifi da safe..." Suna wayar gari da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa ya sayar da kansa, ma'ana ya wayi gari wajen mummunan aiki kenan, akwai kuma wanda zai ƴantar da kansa. Mutane kala biyu ne, wanda zai wayi gari cikin aikin ɓarna, to shine mai sayar da kansa, ko wanda zai wayi gari cikin aikin alheri, to wannan shi ne mai ƴantar da kansa) Yawu na haɗiya ina mai sauke numfashi zai zafin dake tokare mun munfashina tamkar mai ciwon asma. Ƴan uwan zamana na kalla, ko wacce cikinsu ajjiyar zuchiya kawai take saukewa. Amina tace.
"Madallah dake Yahanasu. A zamanmu dake mun ƙaru sosai. Dariyar ƙarfin hali nayi nace.
"Ai gidannan makarantar rayuwace mai ɗauke da ajujuwa zamani_zamani. Zaman gidannan ya ƙara wangalemun idanuna na gane ainihin menene haƙiƙanin rayuwa. Na koyi darasi mai ɗunbun tarin yawan da bazan iya mancewa ba har ƙarshen rayuwata. Ni daku inason mu zamewa kanmu ƴan uwa majiɓantan lamuran juna." Maman Amira tace.
"Da yardar Allah ai mun riga da mun zama dangin juna. Zan baku labarin abunda ya jefa ni cikin duniyar masu shaye_shaye yanzu." Zaman mu muka gyara cike da zabarin son jin labaran juna.
"Asilin iyayena fulanine gaba da baya mazauna jihar Gombe. Kiwo ne ya dawo da mahaifana garin katsina cikin anguwar masanawa. Ƙannena biyar dukka maza nice ɗiyar farko a wajan iyayena. Munyi aure da Baban Amira yardar juna soyayyar gaskiya. Sani talakane sosai, ya gama karatun digri ɗinshi aiki bai samu ba. A haka muka ganganɗa mu kayi aurenmu, daga bisani yaci gaba da yawon neman aiki, shine kullum a tafe. Ɗaki ciki da falo Sani ya kama mun can gangarar layin gidan iyayenshi. Kullum in nayi girki ina zubama mahaifiyar Sani a bisa kyautatawa, dan bai sani ba. Wata ran inje in kai mata da kaina, wataran kuma ƙanwarshi Adawiyya ce take zuwa ɗaukar musu. Duk bayan sati na kanje in yi ma mahaifiyata wanki, inna dawo sai in tsaya a gidansu Sani in ma Goggonshi nata wanki, da share_share, duk da yaranta matane, inayi mata ne dan in ƙara siye zuchiyar Sani. Na samu fada sosai a wajan mahaifiyarshi da ƙannenshi, harma da yayyenshi. A lokacin da garata ta ƙare ne muka soma shiga taskun rayuwa, gani da cikin Amira ƙarami a lokacin. Haka Sani yai ta faman faɗi tashin ganin ya rufa mana asiri. A wannan halin na haifi Amira a cikin gida. Ba mu yi taron suna ba, Sani bai samu kuɗin yanka mata haƙiƙa ba. Ni kuma duk ban ɗauki wata damuwa na ɗaura ma kaina ba. Tunda dai baya barinmu da yunwa yana ƴan bige_bigenshi. Amira na da shekara ɗaya na samu cikin Mujibul Rahman. Cikin yazo mun da laulayi ainun, dan har sai da na tafi gida jinya na tsawon wata biyu. A dawowar da nayi ne gidana gabaki ɗaya ya sauya. Domun Sani kullum a cikin ƙunci da tsaki yake in dai ya ganni. Na yi mishi tambayar duniya ya faɗa mun laifina, amman Sani yaƙi ya faɗamun inda matsalar take. Ga sabon wulaƙanci daya samo, in yasa ƙafa ya fita tun safe, sai isha yake sake waiwayena. A lokacin ne zai shigo da cefanen abincin dare ya miƙa mun. Shi kuma yayi wanka ya fice, bashi zai dawo ba sai wajajen ɗayan dare ko fin hakan. A cikin wannan halin na haifi Mujib. Bayan suna kamar da sati biyu na kwashi ƙafata naje na samu Goggo nake faɗa mata halin da Sani ya tsiro dashi. Tai ta rarrashina, tana bani magana masu daɗi. Nasan Sani yana matuƙar son mahaifiyarshi. A cikin kwana biyu Sani ya dena mun duk wannan sabon halin. Ya sake muka ci gaba da rainon yaranmu. Anyi haka da sati biyu wata ranar talata da daddare, ina zaune muna hira da mata a tsakar gida, sai ga Sani ya shigo jikinshi a mace mus. Tsallakeni yayi ya shige ɗaki. Ba shiri na bishi. A falo na tarar dashi ya kai mari ya kai gwauro, idanuwanshi sunyi jawur.
"Sani lafiya kuwa, me ya faru naganka ka dawo a haka? Na dai ga babu leda a hannunka, bazai wuce dan baka samo kuɗin da zaka yo mana cefane bane yasa ka shiga wannan halin ko?" Kallona yayi tare da yin jim, sai ya fesar da iska daga bakinshi kana yace.
"Naja'atu wani taimako nake so kiyi mun. Ki taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeki uwar ƴaƴana." Da kyau na kalleshi, bance komai ba na kama hannunshi muka zauna a kujera.
Yi mun bayani Sani. Ai ko raina kace in zare in damƙama da akwai halin yin hakan kasan ni mai yi maka ce." Jin na faɗi haka yasa Sani washe bakinshi yace.
"So nake yi ki siyar da komai na dakinki ki bani kuɗin a hannuna, zan buɗe shagon provision ne, sannan zan sai P O S in dinga harkar. Ana samun kuɗi sosai. Zan mayar miki da kuɗinki wallahi." Jim nayi ina tunanin wannan maganar ta Sani. Amman sai da Sani yasan kalmomin daya dinga yi mun a wannan dare, har sai da na amince mishi. Washe gari kuwa mota tazo ta kwashe kayana tas aka fice dashi. Labule da katifa sai sutura da kayan kicin kawai na tsira. Cikin sati guda provition ya haɗu tsab aka saka kaya ga P O S duka dai. Rayuwa ta warware mana. Sai dai sai Sani ya kai Sha biyun dare bai shigo ba, da nayi ƙorafi sai yace ciniki yake yi a shago ai bazai bar ciniki ya tawo gidaba. Duk fa wannan labarin mahaifana basu sani ba, sai ranar da Mamana tazo duba Mujib ba lafiya. Sai taga ɗakun wayam, haɓa ta kama tace.
"Me zan gani Naja, kayan ɗaki Sanin sai sauya miki ko yaya?" Cikin sosa kai nace.
A'a Mama siyarwa nayi na ba Sani kuɗin. Ya buɗe shago yana kasuwanci, amman zai mayar mun da kayan, harma ya shiga adashe hannu biyu, duk dan ya dawo da kayan ɗakin.
"Ba shakka" Shine kaɗai abunda umma tace, tayi dubiyarta ta tafi. Haka al'amura su kai ta juyawa, har shekara guda ta sake zagayowa. Sani ya karya jarin shago tas, gashi bai mayar mun da kayana ba. Naci kuka na gode Allah, rayuwa ta sake tamke mu. Sai ƙannena maza ke taimakanmu da abinci. Wannan yai mun_wannan yai mun. Kullum a cikin babu nake, suturar arziki ta fita kunya bani dashi. Wata ranar juma'ar da bazan mance da'ita ba Sani ya zo mun da wani babban al'amarin daya jijjigani.
"Naja, kinsan kuwa ashe matar Umar Saudiyya ta tafi ashe tana aikatau? Ke kinga tamfatsetsen gidan data gina ma Umar kuwa? Ga kayan alatu ta zuba musu, ta sai ma Umar mota yana kabu_ kabu. Bata dawo ba tukunna tace sai ta kuma gina musu wani gidan tukunna. Baki na riƙe nace.
Shi Umar ɗin ya bar matarshi ta tafi aikatau har ƙasa mai tsarki, to yaran fa Yaya su ka yi dasu?" Sani yace.
"Yara suna wajan Umar ɗin. Mai aiki na kulawa dasu, amman da kafin Umar ya gama ginin gidan, yaran na wajan mahaifiyarshi. To yanzu da ginin ya kammala ne suka koma gidan. Makatanta mai tsada maman ta sa su." Mamaki na dinga yi. Mu kai ta hirarmu da lokacin kwanciya yayi muka yi baccinmu. Ashe tsugunne bata ƙareba. Da rana fatse_fatse ina kwance ina ƙailula sai ga sallamat Sani.
"Naja tashi abun arziki ya same mu. A gigice na tashi ina mistsike idanuna.
Sani lafiya kuwa na ganka duk a rikice?" Zama yayi kusa dani.
"Uhm gidan Umar na koma Naja. Harma ya ban matarshi a waya mu ka yi magana ta fahimtar juna. Babban abunda yafi ƙayatar dani shine yanda ta sa Umar ya bani number Hajiya Kati, wacce take tura mata Saudiyya aikatau, in kayi aiki ka biyata kuɗinta. Gobe zamu je wajanta muma." Cike da mamaki na dubeshi da kyau nace.
Kana nufin nima saudiyyan zaka turani aikatau dan in gina mana gida?"
"Ƙwarai kuwa harma da mota, in kika ji gida ɗaya kenan gidaje zaki gina mana ai" miƙewa nayi fuu na barshi a nan yana ƙwalamun kira. A fusace ya biyo ni. Mun sha rikici da Sani sosai. Baiyi zaton zan yi mai kafiya ba. Tun yana ruwan masifa, har ya sakko ya shiga lallaɓani. Amman ya kasa gane kaina sam. Kullum a cikin rikici muke ni dashi. Tunda yasan babban abunda yake jagulani shine kaiwa dare a waje. Sani in ya fita wataran a waje yake kwana, wataran kuma ya dawo gida ukun dare ko biyun dare. Na yi zaryar kai ƙarar Sani gidansu amman bata sauya zane ba. Na kai ƙararshi gidanmu. Hmm abun mamaki mamanmu ta lulluɓeni da faɗa, wai matan aure nawa ne suke saudiyya dan rufa ma kansu asiri? Nima inje tunda mijinane ya yarje mun. Ƙannena maza suka nuna su atafau basu yarda ba, Mama tayi ruwa tayi tsaki akan ita ba ruwanta kar inje in kaso aurena in ɗaura mata jakar tsaba a wajan dangin Babanmu. Haka dole na yarjema Sani zani saudiyyan. Jiki na rawa ya kaini gidan Hajiya Kati. Cikin wata ɗaya da zuwanmu jirginmu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki, ina kukan rabuwa da yarana da nayi. Sani kuwa bakinshi tamkar gonar audiga. Bari in taƙaice muku shekarata biyar a Saudiyya ina bautama Sani. Sabida tsabar sha'awa data dame ni a matsayina na mace mai lafiya, na faɗa harkar shaye_shaye kamar da wasa har ya zame mun jinin jikina. Kullum in na ce ma Sani ni zan dawo sai yace mun a'a in ƙara lokaci. A lokacin gidaje biyu Sani ya gina, kuma ya sai mota, Mama ma na sai musu gida, na buɗe ma ƙanina Anas shagon sai da takalma da jakunkunan mata. Ranar dana gaji kuwa na hau shirin dawowa gida Najeriya. Ina dira kai tsaye na wuce gidan da Sani ya gina mana ni da yarana, dama ya sanar dani layin. Har hoton gidan akwai a wayata da number gidan. Hmmm abin mamaki da shigata."
Kuka ne yaci ƙarfinta, mu kuwa munyi jigum muna jin labari mai taɓa zuchiya.
MRS BUKHARI CE[17/08, 12:05 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
48
Ci gaban labarin Maman Amira:
Sai da Maman Amira tayi kukanta mai isarta sannan ta share hawayenta, ta ɗan yi murmushin da yafi kukan data gama ciwo ta ɗaura da cewa.
Wata mata na gani fara sol tana zaune a falo tana shan jus ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya. Ga A c na hurata, tashar Arewa 24na aiki a ƙaton talabijin ɗin dake manne a ɗakin. Tana ganina ta miƙe tace.
"Baiwar Allah ke kuma daga ina zaki shigo ma mutane kai tsaye cikin falo ba sallama?" Sai da ta yi magana na tuno da banyi sallama ba ashe. Zuchiyata ta kwaɗaitune da son ganin Sani da yarana.
Yi haƙuri baiwar Allah, na sha'afane shi yasa banyi sallama ba. Assalamu alaikum" A taurare ta amsa mun, tare da watso mun tambayar.
"Daga ina na ganki da akwati?" Zama nayi ina kallon wannan yarinya dake gabana, ni dai ban santa a dangin Sani ba. Ba tai kama da ƙyar aiki ba, to wacece ita?. Bani da amsa, ɗago da kaina nayi muka haɗa idanu da'ita. Na kalli bango na hango hotonta da Sani a jikin wani ƙaton agogon bango, da rubutu kamar haka a jiki ( happy married life) da date da komai. Anan naga sunanta harma da inkiyarta. Wani ruwane ya shiga kai kawo tsakankanin jijiyoyin idanuna da jijiyoyin kaina, zuchiyata ta shiga tsalle a ƙirjina. Yarinyarnan mai suna Husna tana tsaye a kaina ƙerere sai magana take yi. Kukan dake tunkudo kanshi na haɗiye nace.
Wajan mai gidan nazo, in yana ciki aimun magana dashi, in baya nan kuma zan iya jiranshi dan Allah?" Baki ta taɓe tace.
"Honey baya nan, amman ba jimawa zaiyi ba. Zaki iya jiranshi." Tana faɗar haka ta fita ta barni a falon. Kwayoyi na afa