Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
gefen Bulama na rusina, kamar yadda na ganshi a rusine. Cike da fara'a na soma gaishesu muryata na rawa. Amman ɗaiɗaiku daga cikinsu ne ma suka amsa mun, ƙannenshi kuwa, ban kalli kowa ba, jira nake su gaisheni, amman naji shiru.
Kin sansu ai duka na sani, Hajja Fati da Yanunu ne kawai baki sani ba. Yanunu ƙanwar mahaifiyar su Yahanasu ne, Hajja Fati kuma ƙawar Ita Yahanasunce." Dariyar yaƙe nayi nace.
Ayya sannunku da zuwa, gaskiya kun shawo hanya, bari in shiga kitchen su Asiya su kama mun muyi abinci, in yaso Nafisa saita gyara musu BQ." Da sauri na fita a falon har ina tuntuɓe, tsabaragen ruɗewa, babu komai a idanun dangin Bulama sai tsagwaron tsanata. Wallahi nima na tsanesu sosai, kuma in dai ina numfashi Bulama ya rabu dasu kenan, dan bazai ƙare a kansu su kaɗai ba. Su Asiya na tarar a kitchen suna surutai.
"Cab Anty wannan baƙi haka cikin gida, sai kace wasu marasa hankali" Cewar Asiya kenan. Baki na taɓe nace
Kinsan ƴan ƙauye akwai rashin kan gado. Yanzu dai ku ɗaura farar taliya, ku zuba ma mayunwata a kula, ku fito da miyar kajinnan a firgi, ku tsuga ruwa dan tayi auki, da kun gama sai in kai musu."
Bulama:
"Waini Bulama Babba naga wasu mata masu ƙirar samudawa a gidan naka, harma sunfi hamshaƙiyar matar taka girma, su kuma daga ina? Da fara'a nace.
"Ya Bagulaji ƙannen Zubaina ne fa, ni nake riƙesu suna karatune, sabida ɗawaikiya tayi ma mahaifiyarsu yawa, Babansu shekara guda kenan da rasuwarshi, shine nace su matan bari in riƙe su, in basu ilimi, in sun samu mazajen aure sai in aurar dasu, su kuma mazan suna can gidansu Zubainar." Mama Gana tace.
"Ba shakka fa, wayyo shugaban ƴan jin ƙai na ƙasa da ƙasa sannu. Lallai Bulama Babba matarka kwai makira, ta rabaka da iyayenka da danginta. Amman ta saki jiki sai hidima kake da danginta ko? Sau nawa Ba Bakura yayi kiran wayarka baka ɗagawa, uwarka harta haƙura ta dena kiranka. Babu ruwanka da ƙannenka, Babaninka ma haka. Bikin ƙannenka da akayi, haka akaita sa idanu, amman Bulama Babba daga kai har matarka babu ku, babu wasiƙa, sabida iskanci da wulakanci. Kamar mu iyayenka, shine wai take cewa a share mana BQ sabida ƙasƙanci, duk faɗin falonnan baku da ɗakin saukar baƙi kenan?" A ɗarare nace
Mama Gana sabida tana tunanin zaku fi sakewa acanne sabida ku surukanta ne, shi yasa. Kuma anan ɗin babu ɗakin baƙi, ɗakuna ukune a falon. Nawa, saina ƙannenta, da nata shikenan"
"Uhm ba shakka. Ai tunda kai kana da naka, suma tsintattun magen suna da nasu, ta kwana gidan sauƙi."
MRS BUKHARI CE
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
[26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
5
SANARWA SANARWA SANARWA. ZAKU UMMU MAHEER MISS GREEN SHIRU BATA POSTING ƊIN LITTAFINNAN NATA MAI SUNA ZULFA, WANDA YAKE ƊAYA DAGA CIKIN TAWAGAR GAWURTATTU UKU. AYI MATA AFUWA, WAYARTA CE TA SAMU ƊAN MATSALA, DA ZARAN TA GYARA ZAKU JITA. MUN GODE DA ZAƁAR GAWURTATTU UKU.
BULAMA BABBA
Yahanasu, da Fanda, da Hajja Fati. Sai ka nuna musu ɗakin naka su kwana a ciki. Mu kuma iyaye, sai a kaimu ɗakin tsintattun mage mu kwana acan. Su Bulama ƙarami sai ka kaisu BQ ɗin su kwana acan. Tunda kai baka lissafi darajarmu ma baka sani ba."
Jikina a mace yake da maganganun Mama Gana, nasan dole ta kasance cikin fishi, kuma dama itan mai zafi ce. Iso nayi ma Su Mama Gana ɗakin su Asiya. Su kuma su Yahanasu na kaisu ɗakina, na fito naja su Wakil zuwa BQ.
Wai wannan kayan da na gani a mota fa Bulama ƙarami na wanene, daga ma ina kuke naga kamar biki zaku je ko?" Bulama ƙarami nake tambaya. Yace dani.
" Ba biki zamu je ba, daga Damaturu kai tsaye nan muka tawo, mu kam gobe da asussuba zamu koma, Mama Gana da Yanunu kaɗai zamu bari anan. Su Baguji sunce a gaisheka. In an kira wayarka Bulama Babba baka ɗagawa sam, haka watan can daya wuce Ba Bakura yaita kiranka baka ɗaga ba, baka kirashi ba kuma. Wai akwai wani laifin da mu kayi maka ne daya sa ka guje mu? Bamu saba da kai a haka ba, tun muna yara kake kula damu, kai ke nan kullum a cikin goyanmu" Hawayene ya gangaro a kumatun Bulama ƙarami, Wakil kuwa idanunshi sun kaɗa sun zama jawur dasu, kamar zasu zubo da ruwa. Kasancewarshi mai taurin zuchiyane yasa kukan bai zubo mishi ba. Jikina yayi sanyi sosai, bani da amsar tambayar ƴan uwana, kuma wallahi ina tunowa dasu duk kwanan duniya, aikine da hidimar Zubaina da ƙannenta yake sha mun kaina.
Kuyi haƙuri dan Allah Bulama ƙarami, da wakil, in sha Allah zan dinga kiranku, kuma ku ba su Ba Bakura haƙuri, suci gaba da yi mun adda'a. Dana samu hutu zan zo in sha Allah. Ya su Ba Modu, da Ba Baana, ina Ya Hajja Gana, yaya su yagaji suke, su Fanna? Haka naita jero tambayar ƴan uwana ina tuno da fuskokinsu. Hawaye ya cika idanuna tab.
Wakil bari in barku kuyi wanka, sai muje masallaci, magriba ta kawo kai, kafinnan an gama abinci." Da murna na baro ɓangaren saukar baƙi zuwa cikin gidan. Asiya na tarar a falon tana kunna turaren tsinke, Zubaina kuma, fitowarta daga kitchen kenan hannunta ɗauke da ƙaton farantin silver cike da kayan abinci. Da sauri na ƙarɓeta na ajjiye farantin silvern a ƙasan kafet.
"Am Dan Allah Bulama taya ni kawo musu ruwa, so nake gudu_gudu inje in yo wanka, in anyi sallah sai in kirasu suci abincin. Suna BQ ɗin dukkansu ko? Asiya ta share duka ɗakuna biyun dake ciki." Murmushi nayi mata.
Sannu da aiki Maman Maryam, Allah ya baki lada, kin shiga aikin baƙi ba shiri." Dariya kawai tayi mun, amman da dukkan alamu akwai wani abun da akayi mata wanda ya ɓata mata rai. Ban dai ce komai ba akan wannan.
Ai Mama Gana taƙi fur su je BQ, Su Wakil ne kawai suke BQ. Mama Gana suna ɗakin su Asiya. Su kuma yaran matan suna ɗakina. Kiyi haƙuri da sha'anin ƴan uwana, fitina garesu, musamman Mama Gana fitinanniyace ta gaske." Wucewa nayi ɗakinta dan gabatar da alwala, naji ana kiraye kirayen sallar Magriba, a tsaye na bar Zubaina bakinta a wangale."
Zubaina:
Kusun uwa, kai ya sa ƙannen miji akan gadon mijina, kuma dan kuturun wulaƙanci shi hakan bai dameshi ba? Tabb lallai Bulama yana wasa da ni wallahilƙudrat ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, nasan da wanne kalar ƙulunboton suka zo mun ma
Ga uban kaya da suka shigo dashi cikin mota, kona uban meye oho, fuuuu na bi bayan Bulama."
Yahanasu:
Jikina a mace murus yake, tsoro da fargabar da nake ciki a bayyane yake. Ɗakin Bulama Babba na bi da kallo, lallai wato Bulama Babba haka ya yi kuɗi mu bamu da masaniyar hakan. Tabbb abun mamaki baya ƙarewa a duniya, a rayuwa da mun ɗauka Bulama Babba shi zai maye gurbin iyayen mu bayan ƙasa ta rufe idanuwansu. Sai gashi tun ƙasar bata rufe idanun nasu ba, yasa ƙafa yayi fatali da ƴan uwanshi. Ga matarshi da gani yana tsantsar sonta, dan sai haba_ haba yake yi da'ita. Zubaina kyakykyawar macece, mai duri sosai, farace fes wanke hannu ka taɓa, gata da hanci, gata da idanu masu kyau, ta kere mun gudu sosai ta ko wanne fanni babu wani abu dazan nuna mata, gata da kyan jiki, ba kya ce ita ta haifi yaranta ba. Hmmm na sauke ajjiyar zuchiya, tare da kallon ƙofar ban ɗakin da Hajja Fati ta fito, alwala ta ɗauro.
"Yahanasu wai har yanzu uban tunanin kike yi ne? Karfa kije ki jefa rayuwarki a matsala. Haba Fanda ya kamata ki dinga bata baki ai ko?" Fanda ta dubi Hajja Fati tace
"Kinsan Allah jikina yafi na Yahanasu macewa, dauriya kawai nake yi. Ke da ganin Bulama Babba da matarshi, kinsan da wuya matarshi ta bari ayi zaman lafiya. Ke kinga yanda zuwanmu ya ruɗa ta kuwa, jikinta da muryarta fa har rawa yake yi, sanda take gaisawa dasu Ya Bagulaji. Kina ganin data miƙe bin bayanta yayi da kallo bai dawo da hankakinshi kanmu ba har sai da ta ƙule. Yahanasu ni abunda zan faɗa miki shine ki yi haƙuri ki karɓi zaren ƙaddara ki saƙa a duk yanda kalar zaren yazo miki, me haƙuri shi ke dafa dutse har yasha romonshi. Ki riƙe adda'a, ki kuma riƙe azumin monday da alhamis kamar yadda kika taso kika samu Ya Innana tana yi. Sauran shawarwarin zamu baki, ki bari muci abinci, muyi wanka yau zamu raba dare ni da Hajja Fati muna miki darasi akan aure, dan kisan asalin girman zamantakewar aure, labari kawai kikeji, ƴan mata basa fahimta, da dama hangen dala ƴan mata suke ma rayuwar aure, musamman ma waɗanda suka auri masu mata, ki tashi kiyo alwala " Miƙewa nayi, bance komai ba, na shiga bayan gidan na ɗauro alwala na fito, Fanda ta shiga. Hajja Fati tana zaune a ƙasan kafet tana waya, da dukkan halamu da mijinta take waya. Tsuru nayi mata da idanu, ina kallon yanda take sharar ƙwalla.
"Shikenan Baban Nasiba, tunda dai haka kace, kuma baka son in fadi gaskiya shikenan. Ni bani da kuɗin motar dawowane, shi yasa ma kaga ban dawo ba. Kuma nayi maka magana kace, in iyayena sun gaji da zamana su biya mun in koma ɗakina. Kasan Mama fama suke suma da kansu, nera biyar bana magani. Amman inna koma Damaturun zan nemi kuɗin mota in dawo" Galala ta sauke wayar a kunnenta. Kuka mai sauti ta fashe dashi. Cike da tausayinta nace
Kiyi haƙuri Hajja Fati, ai da kin faɗa mun baki da kuɗin mota, dana baki, bai kamata ki dinga sa damuwa a ranki ba haka"
"Hmm Yahanasu bazaki gane bane, kar Allah yasa rayuwarki ta ɗanɗani azabar ɗa namiji, ke maza da yawansu ko azzalumai ne. Mugun miji Allah ya haɗa ni dashi, mara tausayi, da tunani. Amman ba komai, bazan bari ciwon zuchiya, da hawan jini su kasheni a banza ba." Tana kaiwa nan, sai naga ta miƙe da sauri ta ɗauki jakar hannunta, ta ɗebo wasu magunguna, fin guda goma ta zuba a bakinta, tabi da ruwa. Tambayarta nake shirin yi, sai Fanda ta fito daga banɗaki.
"Kukan wa nake ji ina bayan gida?" Ta tambayemu tana tsatsaremu da idanu.
Kukan Hajja Fati ne, ita da Baban Nasiba ne fa" Kai ta kaɗa tace.
"Allah ya kyauta, maza duk yanda ka kai da kyautata musu, sai sun gano inda ka gaza, Allah dai ya bama mata haƙuri da juriyar shanye ƙunci da hawan jinin namiji. Mu yi Sallah muje mu samu su Mama Gana, ni yunwa ma duk ta bi ta isheni." Hijabai ko waccenmu ta zura, muka soma sauke farali.
Kofur Zubaina:
Cikin ɓacin rai da huci na sameshi a cikin ɗaki, fitowarshi daga bayan gida kenan.
"Wai Abban Maryam da gaske kake yi, ƙannenka sabida raini a ɗakinka zasu kwana? Bari kaji wallahi baza su kwana a ɗakinka ba, bazai ma yiwu bane. In ba dai da wata manufar suka zo ba, me yasa zasu kwanta a ɗakinka. Kenan ni bani da wani mutunci da ƙima a idanka ma kenan ko, to su Asiya ina zasu kwanta su?" Kukan munafurci na fashe dashi, duk da inajin mugun ɗaci a zuchiyata. Naso danne baƙin cikina na ganin danginshi, amman sai da suka turani har zuwa bango hankalinsu ya kwanta. Tsattsareni da idanu Bulama yayi, yana nazartata. Cikin kissa na isa gareshi na faɗa ƙirjinshi, ina shessheƙa.
Sabida Allah fa Bulama, ina laifi dan sun sauka a masaukin baƙi su ƴan matan, ɗaki biyu ne da falo fa acan. Ai bai kyautu ace a ɗakinka zasu kwanta ba. A gadon fa muke kwanciyar aure, kuma kawai sai ƙannenka su kwana a kan gadon? Haba Bulama na. Sannan ni abinda ban gane ba, na gansu da sababbin kayan ɗaki cikin mota, wai daga ina suke, kayan kuma na waye?" Duk wannan maganar da nake yi, cikin karya harshe nake yinta, ko da asiri sai an haɗa da kissa, duk da ina da tabbacin Bulama bazai taɓa ganin aibuna ba, domun a hannu yake ram, bashi da tsumi bashi da dabara sai abunda nace mishi shi yake aikatawa. Hannuna kuwa yaja zuwa bakin gadonmu. A cinyarshi yaimun masauki. Dubana yayi da kyau, harda murmusawa yace.
"Iya rigima, yanzu akan wannan matsalar shine harda kuka? To a mayar da wuƙar, ni kaina sanda Mama Gana tace wai su Yahanasu su kwanta ɗakina, naji irin abun bai dace ba. Amman dai na barsu sun shigane a lokacin sabida in kauce faɗan Mama Gana, wallahi duk ta bi ta fitineni. Zasu koma BQ su ɗin, amman Mama Gana in ba so kike ta tara mana jama'a ba, a barsu a ɗakin su Asiyan shikenan kukan ya ƙare? Su Asiya sai su kwanta a nan ɗakin, ke kuma sai ki kwanta a ɗakina" Ɓoyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, nayi Murmushi mai cike da kissa tare da shafo gemunshi nace.
Shikenan kuwa, ai kasan ina kishin shimfiɗar mijinane, sirrinmu ne fa, ko kusa bai dace ƙannenka su hau kan gadonmu na sunna ba. Sai maganar kayan da suka tawo dashi a mota fa?" Na ƙagauta inji na meye kayan.
Su kam bansan na meye ba gaskiya, dana tambaya ma sai Mama Gana tace wai sai da safe naji. Uhm bari muje masallaci da su Bulama ƙarami saina dawo" Miƙewa yayi ya fice. Ƙugu na riƙe tare da bin bayanshi da uban harara.
Hmmmmm Bulama kenan. Karen haukane ya cije ni da zan bar ƙannenka su kwana a cikin ɗakinka? Kalan suje su yi mun birne _birne, ko su tono mun nawa binne_binnen da nayi. Tabb lallai ma waɗannan to wai me suke nufi da nine wai?" Tsaki naja mai ƙarfi, na shige bayi, wanka nayo tare da ɗauro alwala na fito. Asiya da Nafisa ne suka shigo rai a dagule. Da kallo nake binsu, ina son jin meke faruwa.
"Wallahi Anty kiyi ma dangin mijinki magana fa, ni wallahi zan ci uwar tsohowane babu abunda ya dame ni. Dan na fita zafin kai fa. Sun zo sun cika ma mutane gida da ƙauyanci, sai yare suke ta mana munafukai" da sauri nace.
Wai meya haɗaku da su ne Asiya?"
"Daga shiga ɗakinmu fa. Muka same su sai faman zaginki suke yi. Shine fa wata shegiyar tsohuwa mai bakin aku ta daka mana tsawa, wai mu fita mu basu waje, an turomu jin gulma. Ke ki ji fa, naji tana cewa wai Abban Maryam ɗin zai shigo ya sameta ne" Kai kawai na shiga jijjigawa, ina ta'ajibi. Baƙin ciki tare da neman tudun dafawane ya hanani magana sam. Zama nayi a bakin gado hannuna riƙe da haɓata.
Wato ma zagina da suke yi a Damaturu bai ishesu ba, har sai sun zo gidana sun zageni, sun hanani rawar gaban hantsi ko? Da kyau, zanyi maganinsune ki barni dasu kawai dani suke zancan. Ku zauna bari in yi Sallah. Maganganu cunkushe a zuchiyata nayi Sallah, na sake kayan jikina daga atampa, zuwa doguwar rigar lace, hoda fara kawai na murza a fuskata. Ina zaune a gaban mirror Bulama Babba ya shigo
"Kune anan Asiya, yau su Maryam sunyi muku tawaye ko, sun shiga dangi? Dubanshi nake yi, ina karantar yanayinshi, sai wani murna yake yi da ganin ƴan ƙauyen danginshi, cike da kissa nace.
Dan Allah ka ɗan shiga ɗakin su Asiya, ka fito musu da akwatinsu zasu je gida?" Da sauri yace.
"Sabida me zasu je gida, ba nace su su kwanta anan ba?"
E kace. To kayansu suka je ɗauka a ɗakinsu. Shine su Mama Gana sukaita zaginsu, wai ka tara karuwai a gidanka, sun rasa gane wacece ma mai gidan a ciki. Babban abinda banji daɗinshi ba ma shine, Baba da sukaita ƙundumama ashar yana kabarinshi." Na ƙarashe maganar ina hawayen kissa. Shi