MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   29 / 67

84K to 87K   out of 198.3K words

kanshi mazauni a saman kujera sannan ya samu zarafin amsa gaisuwata.
"Mama Gana tace in gaisheki, zata zo ta duba ku, tana mana jaje. Kai nasha faɗa yau a wajan Mama Gana, sai da tai mun tas da kika sani" Dariya nayi mishi, daman nasan ba zasu wanye lafiya ba sam.
"Ina yaran ban gansu ba ko a cikin gidan?"
Au Fanna ta kwashesu ta tafi dasu gidanta, mancewa nayi ban sanar maka ba" Murmushin farin ciki yayi. Na kawo mishi abincinshi, yaci anan, sannan ya tashi
"Sai kin zo, ni zanje in dubo Ba Bakura da Hajja." Haka na wuce ɗakin Bulama Babba bayan na sake wanka, na bi jikina da turaruka masu jan hankali. Yauma a cikin jikinshi nayi bacci, sai dai cikin dare bansan yadda akayi ba, kowa ya saki ɗan uwanshi. Washe gari Bulama Babba yayi sallama da kowa ya tafi, akan zuwa ƙarshen wata zai dawo ya tafi damu. Sai naji ina kewarshi sosai, dan naji daɗin kwanaki biyun da mu ka yi tare matuƙa. Haka zamana a gida yaci gaba da gudana, yayin da shaye shayena yake ta gaba gaba, cikin sati guda na yi ɗan dumur dumur dani, hankalina a kwance yake sosai. Babbar matsalata guɗa ɗaya ne shine. In ban sha ƙwaya ba, sai inji kamar zan zautu, hakanne yake tursasamun wajan sha ala tilas, dan shine kaɗai kwanciyar hankalina. Ina zaune a ɗaki nayi zurfi a cikin tunanin yanda zan fitar da kaina daga cikin wannan rayuwar da damuwa, da kaɗaici ya sani a ciki, ina mai cike da nadamar jefa kaina halin shaye shaye da nayi. Ya Innana ta dafani.
"Meya faru kwana biyu sai inga kin zauna kinyi tagumi kina tunani, lafiya kuwa in akwai wata matsala ki sanar dani, duk duniya baki da kamata" Inama zan iya buɗe baki in faɗa ma Ya Innana matsalata. Amman kash ko kasheni zata yi bazan iya buɗar baki in sanar da'ita nasa ƙafa nayi fatali da tarbiyyar da suka ɗaurani akai ba, bazan iya sanar da'ita na tambaɗar da mutuncina bane. Ga sace _sace da nake yi mata, jiya a ajjihun rigar Ba Modu na zari kuɗi masu tsokar gaske. Na siyo ƙwaya nasha, na adana kuɗin dan gaba. Na zama ƴar ƙwaya ƙarfi da ya ji, dama ina jin labari cewar ɗan shaye_shaye ko kuɗin wa ya samu sacewa zaiyi ya sai kayan maye dasu, ashe da gaske ne.
"Wai ba dake nake yi ba kin barni ina magana, kan ki ɗaya kuwa? Baki na rawa nace mata.
Babu komai bana jin dai daɗin jikinane sam, zazzaɓi ke damuna." Amon sassauci naji a muryarta, sai dai hankalina ya matuƙar tashi da naji ta kira Wakil.
"Kana gida ne ko baka dawo ba?" Daga wayar Wakil yace.
"Ban dawo ba Ya Innana, wani abunne ya faru?"
"Babu komai, dama Yahanasu ce bata jin daɗi nake son ka kaita asibiti a duba lafiyarta kafin mijinta ya dawo"
"Ina hanyar dawowan ta shirya, dana zo ƙofar gida sai ta fito mu wuce kawai" Ni dai ina jinsu su kai sallama, cikin dariyar yaƙe nace.
Ya Innana da kin bari bafa wani ciwo bane sosai yake damu na ba" murmushi tayi
"Ai gara a duba ki a baki magani, yanda mijinki ya kawo ki lafiya, ina fatan ya dawo sati mai zuwa ya tadda ki lafiya. Daga nan sai ki yi ma su Hajja sallama Wakil zai saukeki a gidan Yanunu, za tai miki gyare gyare, in ana gobe Bulaman zai tawo, sai ki dawo gida." Jikina har wani rawa_ rawa yake yi, tsorona Allah, tsorona kar asirina ya tonu a asibiti likitoci su gano ina shaye_ shayen ƙwaya ne. Ina zaune Wakil ya kuma bugo waya ya iso ƙofar gida. A ɗarare na haɗa kayayyakin da Ya Innana ta bani nake sawa, na zuba a jaka na naɗa lafayata, a hankali na fito Ya Innana tana zaune inda na barta.
"To Allah ya ƙara sauƙi, ki gaishe da Yanunu ko? " Kai kawai na ɗaga mata. Cikin gida na shiga nai musu sallama, matayen su Wakil sai zolayata suke yi. Ni kuwa da yaƙe kawai nake binsu. Da muka isa asibiti cikin sa'a ni kaɗai na shiga ɗakin ganin likita. Na faɗa mishi ciwon kaine ke damuna, ya rubuta mun magani, nayi mishi godiya. A gidan Yanunu wakil ya ajjiyeni, na shiga ciki. Ko da kayan maye na ya ƙare, sai naji kaina na birkicewa, har na soma sambatu ni kaɗai. Ba shiri na lallaɓa ɗakin Yanunu na dinga bincike, a cikin kwanon samira na samu kuɗi, dukka na kwashe na fice da sauri sai bayan kango dan siyan kayan harka."






KADUNA:
KOFUR ZUBAINA:
Dawowata daga wajan aiki kenan. Ina sanye da kayan ƴan sanda, riga da dogon siket, da ɗan ƙaramin hijabina. Yusuf kuma yana goye a bayan Zakiya, yarinyar maƙociyarmu dana ɗauketa take raka ni wajan aiki dan kula da Yusuf. Ina doso layinmu gabana ya faɗi ras. Matan layinmu sun fito ko wacce tana daga ƙofar gidanta a zaune suna hirar asara da suka saba. Suna hangoni suka soma zubar da habaici, wai har Raliya tana cewa ita tsoronta Allah, tsoronta kar a kaima matsiyacin mijinta farmaki. Mijin nata da ba miji ba, gadi yake yi a kamfanin giya can biriwuris na hanyar kakuri, Kai kawai na girgiza nayi wucewata, wasu munafukan sai son kulani suke yi, amman ganin babu fuska dole suka haƙura. Wata tiƙeƙiyar mota na gani a ƙofar gidanmu fara sol sai walƙiya take yi, Nafisa da wani ƙaton Alh mai ƙaton ciki na gani a jingine. Murmushi nayi, Yarinyarnan ko ina take samo zuƙa_ zuƙa kifi haka ohon mata. Su kuma mazan sun zama tamkar ƙudaje, dan kwaɗayi. Wucesu nayi banko kalli inda suke ba. Mama tana tsakar gida sai faman kaye kaye take yi. Asiya data dawo wankan jego kuma tana zaune a tabarma tana cin farfesun kifi, wayarta maƙale a kunnenta tana waya da mijinta.
Mama ina abincina yunwa nake ji, Zakiya shiga ki shinfiɗeshi uban ƴan rigima. Mama tace.
"Dama ke da Nafisa nake jiran ku dawo a samu a gagganɗa kuɗin cefane, tunda mijin Asiya dai ya jibge mana komai na abinci a wadace, to kuɗin cefanen kayan miya kuma ai sai ku ku bayar ko?" Kallon Mama nayi waini yau take faɗama haka, ta mance ni sanda nake siya musu komai hatta kayan miyan nike basu kuɗin saye. Ɗari biyar na zaro a jakata na miƙa mata.
Gashi nan, na yau dana gobe, kinsan wata ya raba bani da kuɗi, nayi ɗinkuna da kuɗina, dan bazan zauna babu kayan sawa ba ina zawarci ba. Mama ta karɓi kuɗin tace.
"Ba wancan baƙin yana turo miki da kuɗin abinci kullum ba?"
Yana turowa, ɗari biyar ce yake turomun, amman yanzu ma so nake in huta in naci abinci zan kirashi in faɗa mishi Yusuf ba lafiya ko zan samu wasu kuɗaɗe masu kauri. Ina kaiwa nan na miƙe na shige ɗaki bayan na banka ma Asiya uwar harara ji nake yi na mugun tsananta. Tuɓewa nayi, na ɗan watsa ruwan ɗumi. Nafi minti goma ina kwalliya, na fito ɗas dani gwanin ban sha'awa, doguwar rigar bubu na saka ƴar kanti wacce take zuwa da babban mayafinta, nayi kyau sosai. Fitowa nayi tsakar gidan, na tarar Asiya ta gama wayar da take yi, ta miƙe tsaye tana wani ihu. Da harara na bita, danni yanzu kowa haushi yake bani, musamman ma masu Aure, kai zawarci fa babu daɗi sha'awa tai ta damunka, sai dai ka shiga bayan gida da ɗan kendir ɗinka, ko ka biya ma kanka buƙata da hannu. In bakai ɗayan biyunnan ba, to tabbas sai dai in maza zaka nema.
"Mama albishinki" Da gudu Mama ta ƙaraso har tana murjemun yatsuna, da sauri na janyesu.
"Goro fari gangariya, menene Asiya?"
"Alh yace ya biya mana Umara dani dake dashi, da zaran nayi arba'in zamu wuce." Ihu suka shiga yi ita da Mama dole nima na shiga taya su murna cikin dariyar yaƙe. Haka fa al'amura sukaita garawa, kullum a cikin gantalin bin gidan ƙawayena nake, dan zaman gidan baya mun daɗi sam. Sai tatsar kuɗi a hannun Bulama nake yi, dan kullum Yusuf a cikin ciwo yake a wajena, dan kawai in dinga samun kuɗi, yana iya bakin ƙoƙarinshi har mamaki ma nake yi."






Bulama Babba.
Motarmu ce ta fice daga tasha ta ɗauki titi zuwa Damaturu. Ahmad ya dubeni yace.
"Yau ka kira kaji ya jikin Yusuf kuwa? Kuma ya kamata in muka dawo, mu je Kadunan mu dubo shi ai" Idanu na lumshe a hankali.
Nima nayi tunanin zuwan, amman ganin Zubaina bana son yi. Ɗazu na kirata a waya, tana asibitin ma a lokacin dana kiratan." Ɗan hira muka taɓa ba mai yawa ba, naja bakina nayi shiru. Inata tunanin yanda zamu yi rayuwa a ɗaki ɗaya jol gamu da yara . Ni nafi jin Yahanasu ma, naso ace yanzu ne nake da kuɗin da zan iya kulawa da'ita. Gashi kullum ita ke warwaremun gajiyar aiki, da kalamanta sauƙaƙa, masu sauƙaƙa mun zuchiyata in na kirata ta wayar Ya Innana. A cikin wannan wata gudan da nayi ba tare da Yahanasu ba, sai nake jina wani iri. Amman wannan ɗan tsukukun shi ya bani damar wanke kaina a wajanta. Ta hanyar bata lokacina, kulawa da'ita, yawan kiran waya dan jin lafiyarta. Sai mu kai sabon shaƙuwa, bacin wancan da muke dashi. Kullum kuma ina sanar da'ita ta shirya tarbata, dan a ranar dana iso bazan iya raga mata ba, dole ta mallakamun kanta. Dana faɗa mata haka sai tace.
A shirye nake in faranta maka ranka a cikin ko wanne yanayi. Ai ni gonarka ce." Da ƙishin ruwan abunda nake tafe kenan, da so samu ne ma dashi zan so in soma arba. Haka mota tai ta lulawa damu a titi, yayin da zuchiyata tayi zurfi a cikin tunanin Yahanasuna. Zuchiyata sai zabarin son ganinta a kusa da masoyiyarta take yi. Allah ya sani ban iya soyayya ba, domun in inason abu sonshi nake yi da dukkan rayuwata, in ƙin mutum nake yi shima haka hakanne yasa Zubaina cutar dani, dan taga na jarabtu da sonta. A yanzu ina jin motsin son Yahanasu fiye da na Zubaina a da. Duk da Zubaina itace irin samfurin macen da nake da burin ƙare rayuwata da'ita. Ni ba kyakkyawa bane, za'a iya kirana mummuna kai tsaye kuwa, dan bani da wani abu dake sawa ayi kyau. Kuma ni baƙine wulik irin baƙaƙen kanuri ɗinnan. amman ina son mace mai kyau, kuma fara, hakan ne yaja ra'ayina akan Zubaina, dan tana da kyau dai dai irin kyawu na hausa fulani, kuma fara ce ɗas, ga gayu ga diri, tafi Yahanasu takota ina, gata da zati. Amman ina mamakin yanda lokaci guda na jarabtu da son macen da ban taɓa kawowa zan iya auren wacce ma ta ɗarata a kyau ba. Gashi banason mace mai ƙiba, Yahanasu kuma mai ƙiba ce, yanzu ne tayi rama a sakamakon halin dana sakata a ciki. Amman motsin sonta da sha'awarta ba ƙaramin taɓani suke yi ba. Lallai cikakken so na tsakani da Allah mara algus, ba ruwanshi da muni, ko kyawu, kuma babu ruwanshi da launin fatar mutum, balle jinsi, ƙabila. Haka naita lulawa duniyar tunani, har muka iso wani ɗan ƙauye. Anan mu ka yi sallah sannan muka sake nausar hanya, yunwa da ƙishirwa duk sun dame mu, mu ba wani wadataccen kuɗi ba, balle mu sai abinci kamar yanda ƴan cikin motar suka siya."




YAHANASU:
Tun sha biyu rana nake tsaye a kitchen ɗin Anty Aisa matar Wakil, ina girke_girke. Dan can na gudo sabida kunyar da nake ji. Gashi so nake in gwangwaje Bulama na da girke girke masu gamsarwa. Burabusko nayi mishi da miyar gyaɗa wacce taji naman kan saniya. Sai kuma nayi mishi kunun gyaɗa, da funkasau, sai jus ɗin tsamiya wanda yaji kayan ƙamshi. Dukkan abincin da nayi ma Bulama na, nasan sune abincin da baida tamkarsu. Ina cikin gyara kitchen sai na jiyo sallamar Fanna. Murmushi nayi kawai, uwar gulma nasan tazo ne dan taga wacce tarba zanyi ma Bulamana, ranar dana kwana a gidanta, kusan raba dare mu kayi muna waya da wayarta, tana jin yanda muke ma juna musayar kalaman ƙauna, da yanda Bulamana yake fasalta irin kewata data yara da duk ta addabeshi. Ina cikin tunaninnan naji Maryam ta riƙeni ta baya tana gwalan gwalan. Dariya nayi mata, nasa hannu na ɗauketa, itama sai dariya take yi mun. Tayi kyau sosai, Hajja ce tayi mata kwalliya da sababbin kayan da Ba Bakura ya sai musu ita da Bawa. Tasha jan ƙunshi da kitso, kamar yadda nima jiya muka raba dare ana mun lallen salatab da kitso ƴan yis yis irin na Kanuri. Ƙamshin da jikina yake yi a wannan lokacin sai wanda yaji.
Kinyi kyau maryama na, ina Bawa yake?" Sai nuna mun hanyar fita take yi tana gwarancenta. A haka Fanna ta shigo ta same ni, ina sauraron shirmen Maryama.
"Uhm su Yaya Yahanasu sai shirye_shiryen taran Bulama Babba akeyi, anata zumuɗin zuwan mai gida, an sha kewa." Hararar wasa nayi mata, nayi ƙasa da muryata nace mata.
Kar kiga laifina, yayan naku ne ya iya soyayya da shagaltar da mace." Baki ta kama.
"Au Yayanmu mu kaɗai kenan ke kin fita sahu? Hahaha lallai Bulama Babba ya samu gurbi mai kyau" Dariya nayi mata, na sauke Maryama.
Ungo kulolinnan fitar mun dasu ki jera mun a daining ɗin Anty Aisa, ki dawo ki kai mun waɗannan kwanukan." Dariya take ta faman yi mun, ni kuwa banza nayi da'ita naci gaba da gyaran kitchen, tare da wanke duk abinda na ɓata. Ana kiran sallar la'asar na shiga wanka a ɗakin baƙi dake cikin falon Anty Aisa. Na jima ina kuɗe jikina da sabulun gyaran jiki da Yanunu ta haɗa mun. Ina fitowa na shiga aikin shafa turarene, kulaccar jiki data gashi ne, turarukan mai ne, na shafa turare kala biyar a jikina, kaina kuma kala biyu na shafa,. Na saka turaren turara gashi a cikin gaushin dake cikin kasko, wanda nasa Fanna ta ɗebo mun tun kafin in shiga wanka. Na turare gashina da turarennan, na yi turaren jiki, dana tsugunno, kusan minti arba'in na ɗauka ina gyare_gyare. Na zura rigar material a jikina kenan Fanna ta bango ƙofa da sauri gulma na cinta.
"Bulama Babba ya'iso yana cikin gida" Ajjiyar zuchiya na sauke, gabana ya shiga harbawa, duk sai kuma naji na dibibice ma. Gyara zaman rigata nayi, na ɗaura ɗan kwali, na feshe kayan da turare mai taushin ƙamshi. Na dawo falon Anti Aisa nayi zamana, amman zuchiyata tana can wajan Bulamana. Anti Aisa sai dariya take yi muni, tana zaune tana ba jaririyarta nono, ni dai sai Murmushi kawai nake yi. Wakil ne yayo sallama ya shigo, dawowarshi daga wajan aiki kenan.
"Au wai dama kinanan, Bulama Babba naga ya tura a kirawoki a ɗakin matar Ahmada." Wasa nake da zoben hannuna, wata kunyace take ta fisgata. Anti Aisa tace.
"Yana ina ne Bulama Babban Abban Yahanasu?"
"Yana ɗakin Bulama ƙarami na samartaka, sai nemanta akeyi fa ashe nan tazo ta ɓuya"
"Ai itama sai jiranshi take yi, kaga abincinshi ta jera mishi a daining, anan ɗin taso tarbarshi. Amman Yahanasu kije ki haɗa mishi ruwan wanka, in yayi wanka ya huta sai ki kawoshi yaci abincin. Zan bar miki falon a buɗe, ni zamu fita da Abban Yahanasu." Miƙewa nayi na fice, ajjiyar zuchiya na sauke. Cikin bin bango nake tafiya, banason in haɗu da kowa, ai kuwa cikin sa'a babu da wanda na haɗu, da sauri na shige ɗakin tare da mayar da ƙofar na rufe.
Yana tsaye a filin tsakar ɗakin. Sanye yake da wata shadda kalan sararin samaniya, mai sauƙin kuɗi, ɗinkin jikinta ma mai sauƙin kuɗi, kanshi saye da hula zanna wacce ta dace da shaddar jikin nashi, yanata ƙamshin turarenshi na farar humra. Ɗago da kaina nayi muka zuba ma juna idanu cikin kallon kuɗa, soyayyarshi sai wani fisgata take yi, yayin da naga halama jazbiyyata tana janyoshi tamkar yanda mayen ƙarfe ke jan ƙarfe.( Daku nake maman Yasser da ummu nabeeha, da Fatima Zara, da A.A 🤣) Hannayenshi ya ware mun tare da gyaɗa mun kanshi halamar in tawo. Cikin sassarfa na isa gareshi, a maimakon in afka ƙirjinshi sai naja tunga, wata kunya ce ta durarmun. Jawoni yayi da ƙarfi na faɗa jikinshi, kewayeni yayi da hannayenshi, nayi lub a ƙirjinshi, sai ajjiyar zuchiya yake ta faman saukewa, yayinda hanayenshi suke shafar jikina a hankali. Tsaiwa ce ta soma gagararmu, babu shiri muka afka kan katifar dake ƙasa a ɗakin. Ɗago mun da kaina yayi, nayi saurin runtse idanuna, kunya na shirin hallakani, ban aune ba naji tuɗun manyan leɓɓanshi a saman nawa, cikin ƙwarewa yaima bakina riƙon alewar yara. Wata sabuwar babbar duniyar ma'aurata muka lula, bana iya gane komai. Gabaki ɗaya Bulamana ya canja mun, ya dawo tamkar mayunwacin zaki. Da ƙyar na ƙwaci kaina a hannunshi, ban bari ya cinma burinshi ba.
Ka bari kayi wanka kaci abinci tukunna." Hannayena ya riƙo dukka biyun yana ɗan murzasu a hankali.
"Da kin bari na gama da wannan tukunna, Yahanasuna nayi kewarki sosai."
Nima nayi kewarka, gabaki ɗaya zaman gidan sai naji ya hau kaina." Ranar ni naga fitina, Bulamana ya hanani saƙat. Da ƙyar na lallaɓashi yayi wanka, muka je yaci abinci, sai uban santi yake ta yi mun na kirawo mishi su Bawa. Bayan ya shiga cikin gida ne wajan Hajja, ni kuma na samu na gudu. Amman abunda nake gudu sai da ya faru da daren ranar da yazo ɗin. Munji ɗumin juna a wannan daren, a ranar Bulamana ya mayar dani cikakkiyar matar

29 / 67