Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
tun la'asar suke waje. Hawayenta na shiga share mata ,a hankali tace dani.
"Ka samu kayi wanka ka sake kayanka, lokacin sallah yayi. Ni kuma bari in je mu gaisa" Sake ni tayi, ta shiga kiciniyar sake kaya. Ni kuma na wuce toilet raina duk ya dagule ainun.
Yahanasu:
Ina zaune ina kallon tashar Sunna TV naji kamar ana sallama a ƙofar ɗakina. Da sauri na isa bakin kofar na buɗe. Su Ba Bakura na gani a tsaye, jikinsu a jiƙe sharab har ɗiga suke yi. Hajja gana kuma sai sharar ruwan hawaye take yi. Da sauri na rungumi Hajja Gana nima na saki kukan. Riƙeni gam tayi a jikinta sai ajjiyar zuchiya kawai take sukewa. Hannunta naja inai musu sannu da zuwa. Biyoni suka yi ciki jiki a mace. Ni kuwa da hanzari na shiga cikin ɗakin Bulama Babba na ɗebo kayanshi kabtan guda uku, na miƙa ma Dala.
Dala ku shiga ɗakin Bulama Babba ku sake kayan jikinku sanyi, gashi Ba Bakura baya son sanyi. Hajja mu shiga ki sake kaya. Ba wanda yace mun komai, a baya ta biyoni har cikin ɗakina. Doguwar riga ƴar itofiya na bata ja ta sake.
"Yahanasu rashin lafiya kike fama dashine ko me? Naga kinyi wata iriyar muguwar rama mai tsoratarwa." Murmushin ƙarfin hali da ƙarfafa ma kaina guiwa nayi nace.
Ciwo nayi Hajja, yaune ma naji dama_dama" kallona tayi da kyau taga yanda idanuna suka zurma, wuyana ya cika da ƙashi. Ni da nake da ƙiba Amman tashi guda na zube, duk da nayi rama tun a gida, lokacin da wannan abun ya faru dani. Amman sati biyu da suka wuce nayi biyun haka kumari.
"Ƙarya kike yi ƴannan kice dai bakya jin daɗin zaman aure kawai, dan nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi ko Hajiya Ramlatu ta tabbatarmun da walakin goro a miya tsakaninki da Bulama Babba" Shiru kawai nayi mata, dan kuka ke shirin fallasa asirin da nake ɓoyewa. Da ƙyar nace mata.
Babu komai Allah Hajja. Kawai dai kewar gida da abinda ya faru dani suke damuna." Murmushinsu na manya tayi kawai tasa kai ta fice, mara mata baya nima nayi. A falo muka tadda su Dala suna tsaye. Muna fitowa Ba Modu yace.
"Bari mu fita mu nemi masallaci muyi Sallah ko?"
A dawo lafiya Ba Modu" Kallona yayi idanunshi cike da rauni, kai kawai ya gyaɗa mun. Bayan sun dawo masallaci na gabatar musu da abinci. Amman sam sun kasa cin ko loma. Ana cikin haka Bulama Babba ya shigo da sallama shi da Zubaina. A yayyatsine Zubaina ta gaishesu irin gaisuwar reni da wulaƙanci. Hajja gana ce kaɗai ta kada baki ta amsa Bulama Babba ya gaishesu ɗaya bayan ɗaya, fuskarnan tashi babu annuri sam.
"Ki tashi kije, inason zanyi magana da ɗana" Ba Bakura ya dubi Zubaina ya faɗa mata haka. Harta yunƙura zata tashi, Bulama Babba yace.
"Zauna Zubaina" Zama ta gyara tana ɗan murmushin mugunta.
"Ba Bakura ni ina ganin duk abinda zaka faɗa mun zaka iya faɗa mun ba sai Zubaina ta tafi ba. Tunda naga ga Yahanasu a wajan, dukkansu iyalainane, Zubaina itace uwar ƴaƴana, yin hakan dai dai yake da cin fuska ko san kai" mamaki sai da ya kama kowa a falon, hatta ita kanta Zubainar sai da ta kalli Bulama Babba da mamaki.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
Muje zuwa
[26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
12
*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
Yahanasu:
"Baka da hankali Bulama har lalacewar tamu ta kai kayi mana rashin kunya gaba da gaba, akan wannan matar taka marar ɗa'a da ladabi? Lallai kayi nisa baka jin kira" Da yare Ba Modu yayi ma Bulama Babba magana a zafafe, har yana kumfar baki, ni dai sai hawaye kawai nake ɗigarwa. Ba Bakura ya zuba mun idanu yana kallona cike da tausayina. Bulama Babba yace.
"Gaskiya ai na faɗa Ba Modu a duba wannan lamarin dai, Zubaina fa banga abunda tayi muku kuka tsaneta ba." Zubaina cikin kisisina ta miƙe tsaye tana murmushi tace.
"Duka kuyi haƙuri dan Allah, bari in baku waje dama gaisuwa nazo yi" Tana kaiwa nan ta fice abunta. Ba Bakura ya dubi Bulama Babba yace.
"Sanar damu dalilin da yasa ka hana Yahanasu fita aiki alhalin kasan yin aiki yana cikin tsarin gidanku, uwarka gata bata daɗe da yin ritaya ba, da aikinta kayi wayo ka ganta, kuma da kuɗin albashinta wanne irin hidimace bata yi maka ba, Akan me zaka tauyema ita Yahanasu ƴancinta, alhalin ga matarka ita tana zuwa aikin, aikin ma na cuɗanya da maza, da ɓarayi, da ƴan iska iri_iri, aikin da har tone ɗin night ake yi. Bulama Babba yace.
"Sabida ban yarda ita tayi aikin ba, in dai har ni nake amsa sunan mijinta. Sannan Ba Bakura ina neman alfarmarku dan Allah ku dena zuwan mana haka bagatatan ba tare da kun sanar ba. Ni ina roƙonku ku dena zuwa ni zan dinga zuwa duk shekara" Kuka na fashe dashi mai ƙarfin sauti ina ambaton.
Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun A fili har sau uku. Ba Bakura kuwa tari ya soma yi, yana dafe ƙirjinshi dan ya shiga ruɗu ainun, yawun bakinshi ne ya ƙwarar dashi. Hajja kuwa hawaye kawai take ta zubarwa tun sanda Bulama ya soma magana. Dala yayi maza ya sauke kanshi ƙasa, Ba Modu sai ajjiyar zuchiya kawai yake saukewa yana ambaton.
"Lahaula wala ƙuuwati illabillah, ya Allah" shine kalmar dake fita a bakin Ba Modu.
"Bulama ni kake ma iyaka da gidanka da iyalinka, ka mance nine mahaifinka ni nan na ɗauki nauyin ci, sha, suturarka, maganinka, kuɗin makarantar ka, dama tarbiyyarka? Wannan mahaifiyarka ce fa wacce ta ɗanɗani zafi da azabar naƙudarka, ta raineka, kashi, fitsarinka duk ta cinye, In baka da lafiya aikinta shine kuka da tagumi, amman itace yau kake saka mata wata doka taka? Wannan fa Modu ne, wanda ya ɗauke dukkan ɗawainiyar karatunka da kula da tarbiyyarka, ya fifita sonka sama da yaran daya haifa. Lallai Bulama ashe abun naka yayi nisa sosai, kayi sake da adda'a wannan ba yinka bane tarkon shaiɗaniyar mace ka faɗa, amman. Amman ka sani kuma ka rubuta ka ajiye ni Bakura babu ni babu kai, babu zuriyarka baki ɗaya, wallahilƙudrat inka tako ƙafarka ka zo inda nake bazan taɓa yafe maka ba. Dala ka shaidama ƴan uwanka maza da mata, duk wanda ya sake tako ƙafarshi yazo gidannan ban yafe mishi ba, kai ko kiran wayar Bulama kuka yi, Allah ya'isa tsakanina daku. Ka sakarmun ƴa mu wuce kaje ka rayu da matarka, iyayenta su zamema uwa da uba, dama dangi. Ba da dukiya kake taƙama ba? Gaka nan ga dukiyar Bulama nace gaka ga dukiyar ga macen kuma, ga ka ga MAI IDO A TSAKAR KA DUNIYA, wacce tafi bagaruwa jima Ni bazanyi maka baki ba, amman babu ni babu kai." Hawaye ya soma fitarwa yana tari kamar zai mutu. Ba Modu yace.
"Bakura kayi haƙuri, in hankali ya gushe hankali ake aikawa ya nemo shi. Kar akan sharrin mace kaima ɗanka baki ya ɓalɓance. Maganar ya saki Yahanasu bata tasoba, na riga dana bashi Yahanasu duniya da lahira, kuma in batai mishi biyayya ba bazan iya yafe mata ba, ko gutsurarta zasu dinga yi ƙarshe azaba, ta ci gaba da zama a ɗakinta. Bulama bai isa ya ɓata mana zumunci da dangantaka ba. Duniya ce mai ido a tsakar ka, kayi a hankali. Da mace da dukiya haɗarine dasu. Sannan ka sasssauta maganarka kan cewar baka yafe ma duk wanda ya kawo ma su Bulama ziyara ba. Karka zama silar kawo rushewar zumunci a tsakanin wannan ahali, idan basu zo gidannan dan Bulama da Zubaina ba, ƴar ka Yahanasu da take cikin gidan fa. Ku taso mu tafi kawai. Allah yayi muku albarka duka." Duka wannan maganar da Ba Modu yayi, yayine a cikin raunin zuchiya da sanyin jiki. Haƙiƙa ni kaina na tsorata da kalmomin Ba Bakura akan Bulama Babba, sai dai abunda suka kasa ganewa shine, ƙarfin sihiri ke aiki a jikin Bulama Babba ba haka aka barshi ba. Inda a hayyacinshi yake ko ni bazai iya yima wulaƙanci ba balle su Ba Bakura. Kukane ya kece mun jin kalmar in banma Bulama Babba biyayya ba ba'a yafe mun ba. Na rasa gane shin iyayena ƙyamata suke yi dan ƙaddarar data same ni, ko kuwa ƙaunata suka dena yi? Sallallamin da Hajja Gana take yi shi ya dawo dani hayyacina.
"Nace ki taso mu tafi ko Hajja Gana. Ki share hawayenki ki dena kuka akan yaron da baison darajar hawayenki ba, ki fito mu tafi"Fita suka yi a cikin ɗakin, Ba Modu yana riƙe da Ba Bakura gam, Dala na biye dasu a baya. Ni kuma sai hawaye nake zubarwa. Kallona Ba Bakura yayi bayan ya zauna a mota idanunshi jawur, cike tab da ruwan hawaye yace.
"Allah ya sanya ma rayuwarki albarka da abinda zaki haifa. Yahanasu Allah yana gani ban haɗaki da Bulama dan mu cutar da rayuwarki ko mu hofantar dake ba. Munyi ne dan ƙarfafa zumunta, da rufin asirinki dana ɗan uwana rabin jikina. Kiyi haƙuri da duk abinda zaiyi miki tsanani. Albarkar iyaye tana biye dake a duk inda kike, Allah yayi miki albarka, Dala ja mota mu kama hanyar Damaturu a yanzu" a tsaye a wajan suka barni ina tsiyayar da ruwan hawaye, na jima a wajan sosai kafin na koma ɗakina. A takure waje guda na samu Bulama Babba yana zubar da hawaye, a karon farko dana soma ganin hawayenshi kenan, idanunshi sunyi jawur abun tsoro, duk wata jijiya dake goshinshi tayi raɗa_raɗa. Wuceshi nayi na ƙule ɗakina, duk da na tausaya mishi sosai akan irin fishin da mahaifanshi suka tafi suna yi akanshi. Yau na kuma gasgata Asiri Zubaina tayi ma Bulama Babba ba haka ta barshi ba. Tsari na nema a wajan Allah. Akan Allah yayi gaggawar ɗaukar raina a ranar da zuchiyata kawai zata aiyana mun inje wajan boka zai biya mun buƙatuna. Sallar Isha na tayar dan tun ɗazu aketa kiraye_kirayen Sallah. Bayan na idar na ɗaga hannuna ina kuka a gaban mai duka akan Allah ya huci zuchiyar su Ba Bakura akan zafin da suka ɗauka akan Bulama Babba, Allah kuma ya kuɓuto dashi daga mugun asirin da Zubaina ta dabaibayeshi dashi. Sannan na nemi tsari da sharrinta, na sake roƙon juriya da jumurin shanye duk abinda zai tunkaroni."
Bulama Babba:
Ji nayi kaina yayi wani irin gingiringin, kamar zan tashi sama, tsabaragen firgita da ɗimuwar dana shiga. Haƙiƙa nasan iyayena sun ɗau fishi dani sosai. Banyi tunanin furucinsu a gareni zai girgizani ba. Jikina a mace na bar ɗakin yahanasu na nufi masallaci. Ban fito a masallacinnan ba sai wajan goman dare, ina zaune shiru kaina ya kaure da tunani. Zazzaɓi mai zafin gaske ya ɗumama jikina, da ƙyar naja ƙafa na koma cikin gida. Amman bayan kwana biyu na mance da babin su Ba Bakura, naci gaba da gudanar da harkokina. Ahmad ma ya kirani yana mun faɗa, tsaki kawai naja na datse wayata. Haka lamura suka ci gaba da tafiya lami lafiya. Bikin Asiya ya matso sosai harma Zubaina ta tattare kayanta ta koma gidansu, bayan na cika mata zabirarta da kuɗi masu kauri, itama Mama na bata kuɗaɗe masu kaurin gaske. Banda fenti da naima gidan ciki da waje. Kayan ɗakin dana sake ma Zubaina, saita kwaso nata na da ta jere a ɗakin Mama gidan ya fito shar. Dani akaita kai kawon bikin Asiya, tare dani aka ɗaura Auren a cikin maza a waje. Ina daga cikin mutanen da suka shiga jerin gwanon ƴan kai Amare Kano. Lallai Asiya ta auri hamshaƙin tajiri sosai, dan gidanta ya kai a kalla a kuma. Washe gari da safe muka dawo, sai lokacin na samu nutsuwa, na koma bakin aikina.
Yahanasu:
Haka rayuwa taita garawa dani, cikin ƙunci da damuwa. Ƙwayoyin maye kuwa sun zame mun tamkar ruwan sha, dan babu ranar da bana sha. Jiya jiya ya ƙare, sai maganin tari na siyo na kwankwaɗi rabi, rabin kuma ina jiran wani daren in sha.
Ta ɓangaren su Ba Bakura kuwa. Bayan fitarsu daga gidan Bulama Babba masallaci suka nema su kayi sallah, sannan suka ɗauki hanyar Damaturu, dan Ba Bakura yayi rantsuwar bazai kwana a garin Kaduna ba. Basu suka isa Damaturu ba, sai da Asuba. Jama'ar gida sunyi matuƙar mamakin wannan dawowa ta su Ba Bakura. Ga jikinshi ya rincaɓe da ciwo, babu shiri aka wuce dashi asibiti dan jikin yayi tsanani. Bayan abubbuwa sun ɗan lafa ne Ba Modu yaja Innana gefe guda suka soma tattaunawa , nan ya sanar da'ita abinda ya faru wanda shine sanadiyyar tayar ma Ba Bakura hawan jininshi, har takai baya gani sosai. Ta shiga damuwa sosai, duk da dama tunda Yahanasu ta tafi, take cikin damuwa. Sai dai kullum a cikin yi mata adda'a take. Yakanarta da biyayyarta yasa ta kasa furta abinda ke zuchiyarta, illa iyaka tace.
"Allah ya bata ikon yi mana biyayya, ya albarkaci rayuwarsu baki ɗaya. Shi kuma Bulama yayi kuskure mai girma. Kaje ka kula da ɗan uwanka, yana buƙatar kulawarku" kwanan Ba Bakura goma a asibiti yana jinya, kab ƴaƴan gidan maza da mata da surukan gidan, sun sha sunturi. Bayan an sallami Ba Bakura daga asibiti ne, ya haɗa taron yaranshi maza da mata. Ya kafa musu umarnin da su ka ji yai musu mugun tsauri sosai. Sai dai basu da ikon cewa komai, kuma sunji zafin abinda Bulama Babba ya aikata musu sosai, harda masu hawaye.
"Daga yau na yanke dukkan halaƙarku da Bulama Babba. Ban yarda ku ɗaga waya ku jirashi ba, ko kuma shi ya ɗaga ya kiraku. Haka kuma ban yarda ku taka ƙafafunku kuje inda yake ba. Alfarmar da zanyi guda ɗaya ne shima sabida Yahanasu ne. Na yarjema matan in dai Yahanasu ta haihu suje ayi suna dasu, Baya ga hakan ban yarda aje inda Bulama yake ba, duk wanda ya take umarninnan ban yafe mishi ba" Rarrashinshi sukaita faman yi, ba rarrashin yayi haƙuri ya janye furucinshi ba sam. Haƙurin irin rashin ɗa'ar da Bulama Babba yayi musu suke bashi. Haka suka watse jikunansu a mace mus, Bulama dai ɗan uwansu ne, kuma akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninshi da kab yaran gidan. Yahanasu kuwa, kullum sai ta kira taji yaya jikin Ba Bakura. Iyalan cikin gidannan sun shiga damuwa, musamman ƴan ɗakin su Yahanasu da ƴan ɗakin su Bulama. Mahaifiyar Bulama kuwa tun da wannan lamarin ya faru bata sake samun lafiyar jikinta ba. Duk sanda ta samu damar keɓewa saita zubar da hawaye, dan tana matuƙar kewar ɗanta, kuma tana buƙatarshi a tare da'ita. Sai dai takan shanye damuwarta in tana wajan mai gidanta dan gudun yin abinda zai ƙona mishi zuchiya. Haka al'amura suka shuɗe tsawon wata biyu.
Zubaina:
Ina zaune a falo ina kallon TV. Naci kwalliya da kaya masu tsadar gaske. Bulama yayo sallama ya shigo. Da murna naje na taryoshi. Sai na lura yana cikin damuwa sosai, idanunshi sun kuma runewa.
"Lafiya Abban Maryam meke faruwa? Ni da nake cike da albishir mai daɗi kuma. Sai gashi kashigo cikin damuwa." Baice dani komai ba. Hannuna yaja zuwa ciki a ƙasan kafet ya zauna ya tusani a gaba.
Kai mun magana dan Allah meke faruwa, mutuwa akayi ko me?"
"Babu wanda ya mutu. An sallameni a aiki ne Zubaina. Har sun bani takaddar sallama." Da sauri na miƙe tsaye inajin ruwan zufa na tsatstsafomun. Hankalina ya tashi fiye da yanda hankalin Bulama ya tashi, ban sani ba ko dan shi namijine shi yasa ya fini dauriya oho.
An sallameka fa kace, akan me, me kuma kayi haka?"
Bashin banki dana ci ba tare da bin ƙa'idar cin bashin ba, kuma kuɗaɗene da suka kai million goma, da million bakwai ne, to sabida hidimar bikin asiya sai na sake karɓar million uku. Sun bani wa'adin sati biyu in biya su kuɗaɗensu, ko kuma suyi gwanjon dukkan kadarorina su fidda kuɗaɗensu. A hakan ma sun raga mun ne, da sai sun miƙani firzin ma, amman duba da irin daɗewar da nayi ina aiki dasu, da irin jajircewata ne yasa su ka barni salin