Chapter 1 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 112

1 to 3K   out of 335.4K words

Ya Allah Bantaba rokonka ka hanani ba, ban taba cewa kamin ka ki ba saidai ma kamin wanda yafishi ya Allah DUK wacce ta min karanta nur firdaus ko ta SIYAR ABAYAN idona
Ya Allah kar kabarta ko shi sugama da duniya lafiya👏🤲🏻

LITTAFI NA KUDI NE WANDA YA BIYA SHINE YAKE DA HAQQIN MALLAKA DUK WACCE TA KARANTA BATARE DA BIYA BA I OWE HER 700 NAIRA IF NOT IN DIS DUNIYA ZAKU BIYA A LAHIRA TO PAY chat 080602446


_NUR FIRDAUS....._
#surayyahms.
*BOOK2*
Episode 1.
Dedicated to my beautiful kids.


ahnkli razia tafito daga dakin tana tafiya cikin ayyana wasu tunani aranta, wani karamin quiet palor ta nufa nan inda tasan babu wanda zai zo ya dameta ahnkli tabi talume cikin lallausar white rectangular cushion dake wajen wata nannauyar ajiyan zuciya nakufce mata ayayinda tabita dan lumshe idanuwanta masu sanyi cikin tunanin menene zata farayi na temako akan rayuwar yar uwartan aynxu. dan har cikin kokon ranta takejin cewa bazata iya kyale Nur firdaus acikin wann yanayin ba barin ma datasan batayi girman da zata dauki abubuwa masu ciwo da nauyi da suka faru da ita arayurwata ba kamar rape, teenage preganancy, abortion ga pain na loosing first love dinta to a blood sucking sister duk kuma a lokci guda wani irin tsakine ya kufce ma razia dan tunbata taba ganin layla ba amma sai taji ta tsaneta sosai.

tafi minti goma cikin jimami tare da alhini akan lamarin nur can sai kuma ta tuno da bukatun javeed A mufasa akanta which actually align with abunda take da niyyar yi da rayuwar nur din yanxu, dan karamin lazy smirk ne ya kufce mata cikin girgiza kai tace hmmm wann shi ake kira faduwa yaxo dede da zama but.."i got to think abt this first. sai kuma tabude lumsashn idanunta cikin sauri tadau wayarta tabude wasap tay scrolling chats dinta zuwa grop dinsun na shakikan kawayenta su biyar ta rubuta musu Heyyyyy guys,can we all meet tonite...batare da wani jimawa suka amsata da 'sure" sai kawai ta sauka ta aje wayar.

mikewa tsaye tay taje kitchen tahada ma kanta black coffe snn tadawo wajen zamanta tazauna acikin ranta tafara ayyana yadda wasu abubuwa zasu tafi musu daya bayan daya dan kowani kurba daya tay ma coffen wani bright idea ne ke faduwa cikin ranta. bayan ta gama shan coffe din tajawo wayarta ta bude personal phone book note tafara rubuta to do list dan tasan bata da wani lokcin batawa.


Week by week tay sorting komi tun daga Nurs inner healing da mindset reset, har izuwa kan personality polish kamar yadda javeed din yace, ga skin care nd sexual awareness,exprssion,social skills, exposure to luxury, indepence and influence. wanda tasan idan nur bata same wayann training din ba bazata taba iya rayuwa cikin jin dadi tare da ahalin javeed ba.

tana gama penning dinsu down tay dan murmushi dan tasan ma dolene wayann tsarin nata su canza rayuwar nur gabaki daya and she is 100% confident akan yanayn kwarewar kawayenta awann harkan tasan zasu saukaka mata wajen cimma burintan sosai.

Da zucyarta daya tagama tsara komi dan tasan inhar ta taimake nur kamr ta taimake yar uwarta ne kuma at same time tay aikin da javeed mufasa ya sakata so its a win win, she wll have her dreams in return of all these.


tana gamawa da haka ta rufe notebook din tamike tsaye ta shiga sashin mum dinta nan suka tattauna aka hau ware ma nur nata personal room din wanda baida nisa sosai dana razia..

babu abunda babu acikin dakin amma haka raxia ta sake yin sabon list na kayan zamani na gyaran daki aka bawa servants na gidan sukaje manyan stores aka sissiyo nan ma wasu professionl room decorators suka hau aikinsu na shirya ma nur personal room dinta into a perfect disney princess theme bedroom komi aciki is lush pink with touch of red here and dere kai tunba agama ba gyara dakin yy wani irin kyau bana wasa ba.



after few hours lkcin har an gama komi ganin har yanzu Nur firdaus bacci take kanyi yasaka razia ta sauke ajiyan zuciya

adaddafe ta shigo dakin ta dan tallabota jikinta tana dan shafa fuskarta ahnkli harta dan farka tabude idonta ahankli dan jikinta ko kadan babu karfi.

kallo daya zaka mata kasan ba a cikin hayyacinta take sosai ba saboda mugun ciwon ciki da zazzabin fitar effects na ruwan alluran ajininta dayake son ya rufeta.

cikin yanayin jiri ta sauko kasa Razia ta tarbota ajikinta da kyau suka wuce can sabon dakintan tare.

Bata ajeta a koina ba sai akan gado lkcin banda kalle kalle babu abunda Nur takeyi a cikin nitsuwa razia ta shimfideta akan wani makeken italian bed wanda yagaji da haduwa ankawata shi da kwalliyar jan zanin gado me tsantsi,zama tayi abakin gadon tana kallon fuskarta da yay fayau, a hnkli tafurta mata kalman sannu sai sannan hawayen nur suka dan kara gangaro ta gyada ma razian kai tana ta mamakin sabon kirkinta aranta.

ita kuwa razia tausayi nur take bata shiyasa batajin aranta yadace ta takura mata tun aynzu da wani persnl tambaya akan abunda ya faru dan gani take kamar itama zata iya barkewa da kukan tausayi agaban yarinyar alhalin alkwari sukayi da iyayenta nacewa bazasu bari Nur taji aranta ita abar tausayi bace awajensu.

yau wajen breakfast suka yanke wannan hukuncin tsakaninsu shida matansa dukan su biyu, acewar Alhaj abubakar tunda ynxu nur ta dawo hannunsu kamata yay sumata duk wani abunda ya dace dan ta dawo cikin hayyacinta sosai

matayen ne suka kara masa karfin gwiwa dan ganinsu babu wanda zaice ya san asalin me Nur take ji a zuciyarta na damuwa.

Razia ce ta fara kawo shawarar afara hada Nur da kwararren likitarsu na therapy dan aduba lafyar mental health inta sunanshi doctor Taheer maijama'a wanda shidin Special physchologist ne dayayi karatunsa a kasar india ya balain kwarewa a fannin harkan psychology da social human neuro therapy,...he can deal with trauma and stress at all levels akanyi aiki dashi har a asibitan mahaukata infact akan yi aiki dashi in ana neman wani taimko akan gane yanayin mutum musammn inshi murdadde ne ko physcopth ko chronic narcisist.

nan da nan alhaj ya amince da shawararta yasaka uwargidansa hajiya sa'a ta kira likitan suka tattauna akan zaina zuwa yana duba musu yanayin Nur firdausn agida.


koda razia ta kawota new room dinta batay wata wata ba, wanka da ruwan dumi kawai ta taimaka mata tay snn ta saka mata pad a sabon panties dinta snn ta tursasa mata shan shayi me kauri da small chops snn ta koma bacci. daga nan basu sake zagowa ba seda Dr taheer din ya zo gidan da yamma ya gwadata harya mata wasu allurai masu zafi guda biyu wanda atake atake suka kashe mata jiki tahau wani sabon bacci nan ma ya aje musu sunan wasu magunguna snn yamusu sallama da cewa sai jibi zai kara dawowa ya dubata

Around 8pm nur ta farka daga baccin data dingayi yau Zama tai ta dan dukunkune kanta cikin cinyoyinta kafafunta na rawa rawa ga wani irin zufa dake keto mata ta koina sabida azaban ciwon cikin dake murdata, tun tana zaune har saida takai kwance awajen tana juye juye, tsahon lokacin data dauka ahaka yasa ta jin kamar anyashe mata hanjin cikinta ne,tuni ta soma harsahen hala ba ciwon bane kadai harda yunwa dan rabonta da taci abincin kirki me kuma nauyi tun jiya da daddare, tashi tayi zaune a hankli tana waige waige ganin babu motsin kowa anan ,gashi bata son shiru yayi yawa a waje yakan tuna mata wasu mugayen abubuwan data riga ta binne akasar zuciyarta game da abubuwnda suka faru da ita.

A hnkli takoma ta kwanta tadan rufe idanunta gam gam zuciyarta na kkrin karanto Addua, cikin ikon Allah kuwa saiga wani baccin mai mugun dadi ya kwasheta da alaman hakan nada nasaba ne da wahalar datake sha na rashin samun cikakken nitsuwa ta zuciya..



Da Dare wajajen 8:30pm Razia ta dau driver suka fita can wani gidan hutawarsu da suka saba haduwa da kawayenta domin tattaunawa tasan in ba a wann lkcin ba da wuyane tasamu cikakken nitsuwarsu akanta gashi tana so me su dauki lamarin nur din da matukar muhimmanci....


tana isa kuwa ta samu kusan dukansu sun hallaro kowanne na zaune wasu idonsu nakan tv na wasu na kan wayoyinsu, they are all Her ride and die friends wanda tun primary suke yawo tare, grp dinsu is like that of a soul sisters
yan mata hudu ne sai namiji irin mata maza din nan guda daya.
sede kuma sun balain Aminta da junansu bana kadan ba kujerar farko Rico ce azaune also knwn as Rakiya Ahmed, wato in ana neman best sensual sex educator to itace dan har karatu akan hakan takeyi a United state. daga gefenta akwai molly (mariya suleman), she is a law student cikinsu duk tafi shakuwa da razia Abu sabida course din su daya a schl, tana da saukin kai sosai bata da saurin fushi so she is the fun queen and flirt master of the grp, dan duk wani abu daya shafi iya magana with deep expression, magana a public with confidence da kuma iya seducing din maza molly ta shanyeshi, agefe kuma sai muna wato munayya Ali Hakeem itace slay queen mrs indepedence, irin babe din nan ne yan gata da suke mugun ji da kansu cos she is the luxury viber na grp din saboda mahaifinta yafi nasu kudi snn ita half cast ce babanta balarabe mum dinta ne yar nigeria duk abunda yashafi rayuwar masu kudi da exposure takure kowa anan, and the last person dake danna remote din tv was frankie, namiji guda daya acikin mata,he is a fashion freak, infact wani bin shine yake driving in interest in razia akan ambition dinta na harkan film da fashion sabida shi frankie kusan ma ince kwararre ne awajen harkan kwalliya da fashion sosai.

suna samun zama razia ta hau gaggaya musu duk wani abu daga cikin bukatunta akan yar uwarta nur firdaus batare da ta boye musu asalin labarin dayafaru da ita
ba,duk dama bata iya budewa sosai ba amma 70% of it is out, sabida so take lallai su taru su taimaka ma yar uwarta da zuciya daya tanaso taga sun sauya mata rayuwa da kuma babban burinta nason ta iya kwace freedom inta wajen javeed mufasa.

tana gama basu labarin nur masu tausayin cikinsu jikinsu yay sanyi dan sosai suka jinjina ma kokarinta amma kuma alkwari sukayi cewa bazasu nuna ma nur din ita abar tausayi bane dan karsu kashe mata karfin gwiwa wajen jin zata iya tada rayuwatta..anan suka tsara komi da cewa har sai bayan nur ta warke daga zazzabin datakeyi na mental break down snn zasu fara nasu sessions din da ita.

tun anan suka hau tsara komi har da irin yawam kudaden da zasu kashe wajen cimma hakan, smm kowa ya dauke fannin da yafi kwarewa akai, razia kuwa dama itace chief co-dinator tasan dole itace kawai zata iya koya wa nur wasu mafian etiquette da composure na yadda zata na daukar kanta like a lady of elegance
with refine speech,

dan tasam ba asan hadadiyar mace me aji da yawan surutu ko kuma furta maganan da baida wni amfani ba,first class table manners,harda ma posture na yadda zata zauna ko ta tsaya duk dai body language na manyan mata. cikin shirunsu ko kawo wani batun kantantar shekarunta basuyi ba, kawai de sunsan dolene su hadu su sauya mata rayuwarta tsarinsa me gabaki daya akan lkci.

wajajen karfe goma suka gama hada komi they seem all excited about it sabida hutu sukeyi dama basu da wani kwakwaran aikin yi banda yawon jin dadin rayuwarsu da sukeyi a kasashen waje kullum.



washe gari da safe Bayan likita yazo ya duba jikin nur ya sake mata Allurai tay bacci sai can kafin ta farka
Kanta ta sauke kasa tana boye sautin ajiyar zuciyar daya kufce mata abazata..

nan sai taji motsim sallama ata kofar tay sauri ta jawo dan kwalinta ta dan rufe kanta dashi.

ahnkli aka bude kofar suna hade ido da kawunta yawani sauke boyayyr ajiyar numfashi baice mata uffan ba har sanda yanemi waje a babban kujerar dake gefen gadon ya zauna sann suka fara gaisawa yana mata ya jiki tare da dada tabbatr mata cewa likitansu yace babu cikin sadaat ajikinta yanxu.

duk da mugun nauyinsa datakeji batayi nauyin baki ba tazauna adan rakube akan gadon snn tay masa godiya sosai tanata kuka me sanyi ganin shima hawayen yakeyi yana tuna yadda babanta zaiji mugun zafi aransa inda ace yana raye ne aka mata wann abun.

daga nan shirun minti biyune ya dan gifta a tsakaninsu alokacin ya dena hawayen yay gyaran murya ya juyo yasoma mata magana cikin tausshiyar muryansa wanda yy kama dana lallami da kuma neman yafiya.

kaifin nasihar sa tuni yahau shigar zuciyarta ta yanai mata debi da soyayya irin na uba zuwaga yarsa dayake matukar kauna da kuma jin tausayi, Maganganun sa sosai yasata ta dinga tunowa da nata mahaifin.

hawayene suka sake kwace mata da qarfin gaske daga cikin idanunta sukahau zubowa ta tuna tunda tazo duniya tsakanin ta da mrs haseene dai bata taba nuna mata yanayin tausayi ko soyayyar uwa a agareta ba, saurin share hawayen da sukekin dena zubowa tayi dan ta saurari kalaman kawunta dakyau yadda yake bata assurance na cewa daga yanxu ta zama nasu.

A hankli harta dan samu nitsuwa dan Maganganun dayake mata a fayyace suke babu boye boye da irin feeling din nan na inferiority ko wani superiority irin kace bazaka gayawa mutum gaskiya ba sabida aganinka bai girma ba ko baikai yaji hakan ba ko saboda karkai girman ka ya fado kasa agabnsa

Tabbas Da a akwai babbanci sosai wajen yin magana a tsakanin iyaye da y'ay'an su
musaman ma inya shafi abu na qaddara irin haka.

Shi malam bahaushe yanada wannan dabiar alkunya da kamewa sabida ansan shi da alkunya amma kuma ko da maganan tayi masa nauyi zai fadeta ne a dunkule.

Hakan yasa in alhaj abubkar yay mata waazi sai yace toh ga abunda ya dace dake ga abunda bai dace ba And above all ya cusa mata jin cewa duknsu agidan zasu tayata wajen yaki da duka damuwowin rayuwarta amma badonsu tallafa mata kadai ba,hakan zaisa ta dena kallon kanta a matsayin weak and unintrested with life.

da haka ya rinka karfafa mata jin cewa zataa iya yin sabon rayuwa mai dadi fiye da wanda tayi adacan
tare dasu,he stressed dat she must try and put her fears behind kuma a shirye suke da su tayata mancewa da komi..

Godiya ta rinka masa har tana dan sake kyawawan murmushi cikin hawayen da suke kan sauko mata da alaman ta jijji dadin abunda yagama shawartarta akai kuma zuciyarta a shirye yake daya bita wannan salon don itakanta ta gaji da rayuwar kunci aranta

harso take taga ta dawo kamar da yadda take da kuzarinta da buriirkan ta na rayuwa da komi. Adan lokaci kalililan taji xuciyarta yawani cikke da sbon shaukin dawowa da kanta kamar da can koma fiye amma kuma in wani abun ya fado mata arai sai taji kamar yaune aka fara zubomata zafin sa a zciyarta.


Suna cikin wann yar tattaunawar razia ta shigo dakin tay inviting dinsu wajen cin abinci acan dinning area na falo inda aka riga aka shirya musu komi

Bawani sha'awar cin abincin nur takeji ba dakema bata wani jin dadin bakinta amma haka razia ta tuttula mata acikin plates din tasaka mata ido akan sai ta cinye. tafara ci slowly sai kuma taji yana dan shiga ahnkli hade da maganin cin abinci da aka fara dorata akai da yanayin sakewarsu da ita yasa tadan daure ta ci abincin fiye da na kullum.

Sai tsokanarta matan sukey suna sakata murmushin dole ita kuma harga Allah wnn hadin kai da soyayyarsun mai mugun sanyi da take gani a yanayin iyayen yamugun bata sha'awa da mamaki dan harga Allah bata san ma ana irin wannan rayuwa me dadi a family ba duba da yadda suka taso da mrs haseena who is alwys unavailable, passive agressive, harsh and a chronic emotionally dismissive mother.

bayan sun kammala cin abincin Alhaj abubakar yay hamdala yace Alhamdullhi ya kamata Nur wata rana tasoma shiga kitchen din nan itama takoyi Abinci da kyau, it wll be better for her now to get busy, sabida girma takeyi wata rana sai kiji ance zan mata aure

dukansu suka fara dariya hajy bilki tace

"yes ooo good idea my darling, ai nur bazata xauna hakann ba..Ko yaya kikagani nur?

kanta ta dan sunkuyar kasa ta gyada kanta a hankli tana kakalo murmushi.

hajy saadat ta riko hannun mijinta tace "katashi muje karkayi latti, leave evrything to us honey, beside i knw she can cook saidai akoya mata na turawa irin wanda yarka take ci.

yadda razia tayi giggles yasa dukan su sukahau dariya .

Suna mugun jin dadi aransu sukaga Nur tana kkrin yin dariyar itama duk dama da alamar dariyar kawai zaka gani ayanayinta bawai takan sake tayishi bane har can can ranta..

Tsaye ya mike ya doddora wa yarsa Razia kiss asaman goshi ita kuma nur ya rikota jikinsa ya mata addua yana lallabarta data sake jikinta sosai

da haka matan suka rakasa waje dan sunsashi da yawan tafiye tafiye ba lallai ne sugansa anjima ba,

suna dawowa suka samu har razia ta dauketa sun koma can sama dakinta, anan suma sukaje suka samesu a dakin nur din sun zauna kenan abakin gadonta har zasu fara magana ganinsu yasa sukayi shiru, Da dan gyaran murya haj bilki ta karaso itade mamaki takesha yadda taga nur din ta rame skin dinta har yay fayau ya yafara yamushewa kamar ba ita ba..

nan Dukansu suka zauna suna masu jan Nur da hirarrakin rayuwa har tadan sake jikinta da haka suka soma fahimtar me ta iyada dame bata iya ba afannin abincin ma Babu laifi ta dan iya dayawa wasu abun musaman wanda suke ci agidan su ita da layla wasu kuma ta iya amma bata taba gwadawa ba.

Bayan sun kammala Hirar suka fito cikin gidan nan ma hajya bilki ta hau gwada mata yadda ake yin in za'a tsaftace manyan faloka da kayan sawa da sauran wajaje da turarensu na can meduguri har suyi kyalli suna qamshi

1 / 112