Chapter 50 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   50 / 112

147K to 150K   out of 335.4K words

dan yasan tsakanin mata da miji akwai sirri amma kodaga yanayinta yasan tay nadama kuma a tsorace take da hukuncin da javeed din zai yanke mata

jimm yay har saida tay shiru ta rage kukan kafin nan yafara rarrashinta da kalamai masu taushi da sanyaya zuciya.......

ya dinga lallabata yace mata karta damu
javeed zai dawo mata bazai kwana awani waje ba kartaji tsoro ai shi mijinta ne dama kuma sabanin fahmta irin haka na shigowa cikin lamarin zaman aure.

shiru tay tanajin lallashinsa me tahowa da nasiha ita duk abu daya ke mata yawo aranta tunda yace wai javeed yana alfahari da halinta shide kawai baison mace me disrespct ne.

ton memakon taji dama dama sai ta karajin ta damu soai sabida tasan inde raini ne to ai jyau tay masa kololowarta da safen nan tunda ta ambace mahaifyarsa.


hakanan yasakata taci abincin agabansa na dole har ta dan sake jikinta ta dena kukan
suna hira kadan har saida aka kira magrib snn suka bar wajen ta koma dakinta domin yin sallah.


bangaren javeed kuwa duk dama yay niyyar kwana ne a Abujan amma koda suka fice shan iska da sultan a undeground club dinsa sai nemi waje yabata shiru akan kujera yana lissafin yadda zai gyara ma nur dinsa zama dan ta nitsu dan harga Allah shide bazai taba iya dora hannunsa akanta ba yasan wnn kam.


yafi awa biyu baice uffan ba yana shiru bayan yagama ayyana abunda zai matan aransa ne ya dingaji kawai gara ya dawo
lagos din komin dare.


baiko tashi dawowar ba sai da karfe goma na dare ya cika snn sukayi sallama da sultan ya tattari guns din daya saya ya kama hanyarsa ya fito within few minutes helicptersa ya dawo dashi lagos cikin dare.


koda ya dawon bai bare kowa daga gidan ya sani ba banda su mr qeel da janet dake taredashi a kowani lokci, dakinsa kawai yanufa yay wanka snn ya hada ruwan alluran bacci yay makansa snn ya kwanta danya samu isashenn baccin da zai saka jikinshi ya warware.


Da kyar ya farka yajeshi sallahn asubh
yasamua har an idar
suna hade ido da alhaj attah yace masa idan yagama sallan yazo ya sameshi a dakinsa yanxu

hakanan yay sallah da tunanin ko yaji labarin mission dinsane but he plan to deny it sabida baison rauni ko tsoron mutuwa ya kwace masa wann babban damar da ya samu na kawar da nagaza brotherhood

wanda sukadai ne in suna raye yasan cewa bai isa yayi sake wani a family musmn ma matarsa tay normal rayuwarta da freedom ba, bai damu da rashin goyon bayan da bai samu daga can sama ba sabida yasan harkace ta gwamnati da kuma siyasa wann shikuma awajen sa shafe tarihin rayuwar nagaza kamar shafe daya daga cikin manyan matsalolin ahalinsa ne shiyasa har ransa yakejin babu abunda zai hanasa zuwa wnn mission din face mutuwarsa.


nur tana idar da sallah ko addua batay ba ta taho sashensan ta samu dede lkcin janet zata shiga ta gyara dakin kenan suna hade ido ta rusuna ta gaisheta kirjin nur na bugawa ahankli tace mata ina javeed yake

janet tace mata ai ya wuce masallaci kuma daganan yace musu training zaije hala sai wajajen karfe goma da rabi kenan ya dawo cikin gida..

wani abu nur taji ya tsaya mata a wuya sai kawai gyada kai ahankli ta koma estate dinta wanda kafin ta isa hawayenta masu sanyi har sun fara zuba wato ma babu ita acikin plans dinsa hmmm...


kan gadonta ta haye tana kukan ahankli cikin saka wasu abubuwa aranta har bacci me nauyi ya kara daukarta.


6:30 am na safiyar na bugawa javeed ya gama shafe adduar sa dayay bayan azhkar sann ya mike ya taho cikin gidan agaggauce


sashen mahaifinsa ya nufa direct ya samesa
yana shan hot coffe a tea mug ya tsuguna da ladabi suka gaisa
babu yabo babu fallasa suka dan fara hira sama sama shide yasha mamaki dan babansa bai taba tuhumarsa inda yaje ba sai yau kawai sai ya fara shigomai da wa'azin cewa aiyanxu yay aure baidace yana barin matarsa acikin damuwa shikuma yana jimawa a wani waje ba.

Da kyar javeed ya fara dago kan maganan
musmn daga yadda babansa yake ta fada wai jiya nur taki cin abinci tanata kuka sabida shi sai ce masa yake ai rainonta zakayi bakomi ne zata fada maka ka na daukawa da zafi ba yarinya ne fa dole ne kabita ahankli


shide shiru yay yana jinsa baice komi ba harya gama sai ya nuna masa kawai shirmen nur ne amma shi ba fushi yakey da ita maybe dan ya tafi bai gaya mata bane.

dahaka ya shashnatar da maganan duk dama yaji mamaki da kuma dadin data gane cewa tay masa lefin tun ajiyan.

koda ya fice a sashen wani bangaren na ransa ce masa yake yaje wajenta kawai su shirya wani bangaren kuma yana tursashi da tunanin nan gaba sabida maganan nata yay masa tsauri sosai duba da mahaifyrsa ta kawo aciki ba wata na daban ba, kai dolene ma kawai ya dauki matakin dayafi haka

da wann tunanin ya fasa zuwa wajenta ya canza kaya ya wuce wajen training dinsan.


har wajajen karfe takwas saura nur tana kan sharar bacci..

naima ce ta shigo silently ta bude dakin da key card sanye da gogaggen uniform din aikita ajikinta ta daure kanta da dankwali

saida tay sallama kamar sau biyu kafin nan ta karaso ciki jikin window straight ta nufa ta bude labulen


nur tay juy akan gadon da gigin bacci jin fresh air da qamshin flower tareda hasken safiyar rana na shigowa

tun bata gama bude ido ba tafara jin wani irin qamshin lemon water da mint aciki

da murmushi me taushi naima ta karaso ta gefen gadon ta dau ruwan mint da lemon din ta mika mata sann tace fatan kin tashi lafiya hajiya? nur bata amsa ba saida ta shanye ruwan which is so refreshing snn ta kalle na'ima tace lfya alhamdullhi naima..

naima ta karbi cup din tana murmushi ta sake mika mata almond guda uku da akayi soaking inshi da kuma dabino guda biyi shima ta karba taci dan tunda suka fara aikin ya zame kowani safe ne ake bata lemon nd mint water da wnn soaked almond and dates din duk dama batasan amfanin me zasu mata ajikinta ba

nur was feeling a bit btter tunda dai ta gane cewa javeed ya dawo gidan kawai de magana ne hala bazai mata ba dan yana fushi daga nan suka fara normal routine tay wanka tazo ta saka kaya me kyau baby pink lace me daukar ido,gown ce da aka masa wani irin high ends celeopatra style akabi jikinsa da wani shimmery silver stones masu aji wanda yay kamar ajikin lace din ya fito

duk wann aikin razia ce, dan ita kanta nur wani bin takan rasa a inane anty raziarta take samun talented designers haka a nigeria da suke musu dinkin zamani me mugun dauke dauke ido shiyasa ko ita duk kayanta da suka dinka babu na yarwa aciki duk high ends decent celeberity styles ne.


kwalliyarta me kyau tay da tunanin javeed zaizo amma sai shiru
hakanan ta danne zuciyarta taje dinning nan ma bata gansa ba

bata kuma ji anyi maganansa awajen ba

sabida alhaj attah kawai ta daure tana cin abincin amma bakaramin tafasa takey aciki yadda simran din yau ta fito da wani irin gigin iskanci da fade fade

sai nunawa take kamar itace take controlling komi na gidan su lady sidd kuma sai zugata suke

wani hirar ma da gayya suke suna nuna ma nur kamar bata san responsiblty din gidan miji ba ko tay karama ne ohooo

sudai so suke lallai ta gane cewa simran is a doctor at same time a responsible lady dake kulawa da harkokin gidan including the cooks and food stores management.

sun furta maganganu dayawa da ya kuntata ma nur amma tay burus kamar bada ita akeyi ba har mamaki take bawa alhaj attah yadda tay mastering dauke kanta akan irin baqar magana da sukar da suke jefa mata acikin hirar tasu

Shiru kawai tay amma dukansu basusan meye acikin ranta ba

ana gama breakfast nur ta dauki sabon plates ta debi abincin da komi da komi ta shirya neatly akan wani mini tray ta haura dashi sama sashen javeed abinta

nan ma ta samu har yanxu bai dawo ba shiga dakin tay ta aje masa abincin akan center table snn ta fice ta koma sashen ta da niyyar anjima sai ta sake dawowa.


Ganin hakan da nur tay yasaka hanklin simran yafi na kowa tashi acikinsu duba da javeed ya hanata sake taka estate dinsa

tunda nur ta debi abincin matayen gidan ke kananan maganganu sabida tsarguwa da jin ko dan sunazaginta cewa she is not a responsibl
yasaka ta shaka irin bari ta gwada musu ita ta isa shine ta kwashi abincin takai masa sama..

anty suad tace nur tana da raini sosai..

lady tay rantsuwa tace
wallh mocking dinsu kawai tayi irin simran din da suke gwadawar itace shawuya ita kam saidai taci ta koshi snn ta deba takaiwa mijinta

nabu kalar zagin nur da basuyi ba duk dama suna mata cin fuskan dayafi haka akan table din amma debar abincin kawai datay yasaka duk ransu yay baqi ya kone kurmus da zafi


nur ta zauna agaban mirronta tanata kallon kanta duk ta kasa samun sukuni aranta tanaso taga ko javeed zaici abincin sai ta samu daman zuwa ta bashi hakuri..


time to time haka zaka ga taje sashen sa ta leka still taga be dawo ba taje yakai sau hudu ana biyar din ne ta haqura ta dan kara masa kamar 40 minutes tana fitowa kuwa tazo taga wayam saima janet datagani tana fitowa da abincin baiko taba ba.

wani abu me nauyi ta karaji ya tsaya mata akirji tanajin kamar tay kuka gashi duk wai tay kwalliyar dan shine amma kuma sai ji take janet na ce mata ai yace bazai ci ba kuma yanzun nan yashiga gari a boat shida wani mutum sai anjima da yamma yace zai dawo.


Da tsananin damuwa aranta ta cije ta dawo dakinta ranta a mugun dagule tana zama tace ma naima taje waje, naima na fita kawai ta fashe da kuka marar sauti me tattare da wani irin matsanincin karayar zuciya da jin fargaban rasa kulawar mijinta dan izuwa yanxun bakaramin nadamar rashin kunyar data masa da fargaban hukuncin da zai dauka akanta takeji ba.

jiya abun ya faru amma dake tun jiya da safe ne bata sake sakashi a idonta ba sai taji kamar duniyar ne ya rushe akanta gabaki daya


tana cikin wann yanayin jimamin sai ga sallamar na'ima

dacan har zata dismissing inta sai kuma taji tana ce mata ai sako janet tazo ta bata.

cikin sauri ta share hawayenta tazo sai janet din ke ce mata ai ba sako bane kawai de tazo ta sanar mata cewa ai javeed ya kira mr aqeel yace nan da awa daya zai dawo...

dan shiru tay dan daga ganin yanayin su tasan kawai sun damu da itane ita har kunya takeji yadda taga suna
lura da abubuwan dake faruwa da itan sosai.

godiya ta ma janet din snn ta koma dakin ta dada gyara fuskrta yay fresh ta kara seta make up inta after like 30 mins tazo ta samu
naima na goge mata frames din falonta

naima tay saurin rusunawa gani nur ta fito, fuska ba yabo ba fallasa tace "lets go to the kitchen i want to make sumting for my husband by myself..

naima tay karamin murmushi tace toh hajiya..i am after you.


hanyar hadadden private kitchen din tan suka nufa direct wanda yake cikin madaidacin building me ji dakansa dake tsakanin nata sashen da na javeed its a very secured place anyishi anan ne sabida nur da javeed sukadai for ther lunch and dinner

kusan kowani babban sashe akwai private kitchen amma a main kitchen kawai ake hada dinning wanda shi main building yake


na nur ne kawai akayishi acikin cozy environment ginin sa daban, kai kace ba a nigeria kake ba dan ko taps da worktops da dinning tables dake cikin kitchen din nata ma abun kallo ne bare ajega frames da fresh flowers da wasu irin kayan kitchen auto mated na zamani da show glasses masu daukar ido.


suna shiga kitchen din suka samu chef faiza tana kan aikinta akan worktop wani irin qamshin nikakken ridi ya karade koina ga nikakken cardamon da honey da alama tanakan shiryawa nur
wani hadadden hadin kayan mata ne wanda zai jimar da niima da gardi ajikinta musmn in ana yawan matasu amma kuma sukan sakayane suce mata abincin warware jini ne ita kuma ako ajikn ta bata damu ba dake ma chef faizar ma Allah yay mata baiwar iya sarrafa abincin

duk dama ta dan manyanta amma bashine ya hana ta rusunawa ta gaida nur ba.

da sakin fuska nur ta amsata wata junior staff agefe dake tayata yanka fruits kuwa jikinta sai rawa rawa hake dan tagama daukawa nur ma kamar simran take

dakyar ta iya gaishe da nur jikinta na rawa rawa sai taga nur bata ma kula ta sosai ba


naima ce ta gayama faiza bukatun nur duk dama chef faiza taso taki sam da tunanin nur batama iya girki ba hala, saidai babu yadda ta iya haka nan ta kyaleta duk suka ja gefe suka tsaya suna mata hira kadan kadan komi take bukata zakaga an bata da rawar jiki


wani irin hadadden nikakken meat sauce tay me masifar qamshin dadi snn tay patotoe bags bayan
irim wanda ta tafasa dankalin turawa sama sama tasaka wuka me kaifi ta fafe cikinsa suka bada shape kamar bags ta soyasu suka soyu ta tsame tay sturfing din meat sauce din aciki


dake abincin bawani mai daukar time bane within 15 minutes she is almost done hakan nan ta tursasa ma su naima cin abincinta kowa na satin suna mamakinta sosai

iya yanxun ne kawai zaka iya cewa nur ta dan samu tsukuni aranta harkaga tana murmushi

dede tana kan hada water melon juice dinta kenan sukaji wani irin rundanan mutane na shigowa da kaya kitchn din


liyatu ne ta fara shigowa da store keys da kuma masu stufing kayan abinci wanda
marmarza faiza da junior staff suka fara tayasu suna jerawa


naima na tsaye kusa da nur dake kan hada juice wanda tun nur in bata daga kai ba su kaji saurin kwas kwas ana taku kamar an sako kofoton aljanu...


naima ne ta dora idanunta akan kofar tana jiran ganin wazai bullo ciki nur kuwa ko daga kanta batay ba sabida honestly an riga an dameta da yawan gaisuwa gashi taga har wani irin tsoronta maaikatan sukeji batare da tasan dalili ba abun har yana daure mata kai.


wani irin shigowa kitchen din simran tay dayaso yaja hankalin kowa awajen

kayan jikinta as usual is so gorgeous irin kure adakan adakan nan she was branded in Arriva saphiere tigh gown me tsagu agefe da gefe ayayinda Duk wani plastic surgery dake sassan jikin ta ya fito zak zak ya bata hadadden shape ya dada sata dawo abun kallo gashi ta wani kara baza kwalliya kamar zataje gasa.


ko daga kai nur batay ta kalleta ba har ta gama kinibinta masu faiza dan bakaramin dadin samun nur a kitchen din tayi ba

zagewa tay da iko da gadara tana zagin faiza tare da gaya mata cewa she is the boss of this kitchen kai kowani kitchen agidan nan ma yana karkashin oder inta ne
snm intaga dama zata saka a basu long term suspension in basuyi mata biyayya ba

wani irin bragging takeyi cewa ai keys din komi na food stores a hannunta yake dan haka daga yau faiza sai tazo ta nemi izini awajenta kafin nan tana taba wasu abubuwa


duk da naima bata ko motsa daga jikin nur din ba amma sosai furucin simran ya bata haushi bana kadan ba


nur datay kokarin danne fushinta tay focusing wajen fara shirya abincinta akan tray tanakan jerawa carefully sai kawai ga simran dim tazo ta tsaya mata akai tanata kallonta banda wani irin annoying taunar chewing gum datake mata a kunne tana hurawa.

sai data gama karewa abunda nur din takeyi kallo kafin nan taja wani numfashi ta ciki me tattare da uban mamakin daya kusa shakure mata wuya tana mamaki wai har wnn yarinyar ta iya abinci..

nur tadaga kai ta kalli chef faiza tace faiza ki kiramin janet pls..

tun faiza bata wuce ba wani caraf simran tace "she is not going any where, nine nake bada oder anan, u get it.

nur ta dada hade rai cikin shareta muryan taciki ciki tace faiza be fast bana son mijina ya dawo snn ya jira abinci.

faiza tay sauri zata wu e simran ta daka mata tsawa i said come back here u filth

nur ta kalle faizar dake bari, a nitse tace haa yau zan gani aikan matan gida zaki je kona karuwar gida

a rikice simran tace whaaaaaat!????what did u just say


nan nur ta kalleta da wani irin ruwan masifa a kwayar idonta tace aikinji ni sarai..

faiza dont waste my time. da sauri faiza ta fice...

azafafe simran tace
u did not just call me karuwar gida agaban yaran nan? ke ni saar..

cikin datsar numfashinta nur tace ohh please to meye aciki, jibeki fa? aibaki da wani maraba da su masu aikin gidan waima ba abincin kika kawo ba tunda kin gama aikinki you can
now leave. .and hey dont u ever come to this kitchen and talk to my maids like this..

da wani irin diri simran tace oh haka ko? toh bakomi zan kuwa koya miki hankali zaki asalin sanin matsayi na agidan nan


nur tay banza da ita looking composed ta fara zuba hadadden water melon juice dinta a hadadden glass jug snn ta zuba like 4 cups more ta ta bar sauran a cikin container din

Simran sai masifa take tana cewa zata nuna ma nur iyakarta agidan nan saiga nam janet takaraso itama ta dauke kai tay kamr bataga simran ba tazo
gaban nur da ladabi tace i am here maam.

calmy nur tace mata ta dau tray din takai ma javeed daki she wll be der shortly

babu musu janet ta dau tray ta fita..

sauran daya rage ta rabawa naima faiza tabawa junior staff din da liyatu data karba da kyar ta rike sabida tsoron idanun simran dake huci kamar zaki..


in sha Allah yau ya zame miki last day

50 / 112