Chapter 19 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 112

54K to 57K   out of 335.4K words

shan ciki da tsokanar muna amma haka tay ta bari dan gabaki dayane Hanklin nur baya jikin ta dan tun daga aiport din har ta iso gida text-chating sukeyi dashi dan bazata iya cewa taji wasu abubuwan da muna ta dinga mata hira akai ahanya ba.

Koda tadawo gida already yamma yayi sosai samu tay duka matayen kawuntan har sun dawo gida.

hakanan tabisu one after the other da tsarabar data siyo musu ta gaggaishesu har cikin sashensu kowana murnan ganin ta duba da yadda ta karayin wani fresh sai tambayar labarin trip ake itade sama sama take amsasu hira kadan sukayi kafin ta koma room dinta

saidai tunda ta koma bata iyayin komi ba sai kwanciya da kuma tunani masu aiki ne suka kimtsa mata jakarta, nan ma taga ashe javeed ya riga ya zuba mata tumin kudade aciki batare da saninta ba duk sai tarasa mema zata nay dasu wani drawer na musammn ta bude ta hade duka cash din awajen takulle snn ta cigaba da tunanin sa.



ata dayan fannin kuwa rayuwar gidan adnan shehuri da matarsa layla bakaramin kara tabarbarewa ya ke karayi ba.

musmn ma da yanxu duka yafara zame ma layla tamkar ruwan sha dan wani bin in zai jibgeta haka zai jawota har palo daga ita sai pant ya wurgan da ita kai duk yadda taso taga ta zauna da shi lafya baya yuwa

atunaninta kome zai zo yawuce musu amma gani take kamar tsanar da adnan shehuri yake mata gaba gaba yakeyi akowani rana.


daga auren su izuwa yau sau biyu kenan yana kwabar mata ciki da duka, akaro na biyun ne Mrs haseena tagane cewa dukar yarta adnan yakeyi wanda ya jawo musu mummunan musayar yawu har yakaiga ya sallame laylan gida tunma bata warke ba

wani abun mamakin shine wai koda mrs Haseena takai korafin sa awajen hajya mairam shehuri atake atake matar tahade rai tabi bayan danta tace ai inma dukan laylan yakeyi duk ita ta jawo...mamaki duk sai yacika mrs haseena.

hjy mairam na kallon tsakar idon haseena tace mata yarta laylan ce bata da tarbiya kazama ce snn tazo tasauya mata danta tamaidashi marar kunya madukin mata.

gabaki daya tama hana mrs haseena cewa wani abu tahau bori tafita daukar zafi tadauki lefin adnan duka ta maida shi akan layla, tace sam ba haka danta yake ba komi dayake faruwa dasu lefin laylah ne


wann lamarin ba karamin ciwo yay ma mrs Haseena ba, dan koda tadawo da layla gidanta suna jinyar jikinta ko bacci bata samun yinshi tsabar damuwa, gashi jikin laylan yabi ya lalace da bruises, da wasu irin kalar tabon duka, wanda badon tana samun lafiyayyen abinci ba da halama bazata ganu ba.

izuwa yanxu babu irin neman taimakon malamai da bata shigayi ba amma duk dai babu wani canji kamar ana zubawa rariya ruwane kasa kuma na shanyewa.

yanxu haka duk duniya babu wanda mr hasina takejin ta tsaneshi kamar adnan
shikuwa ko ajikinsa tun da ma nur firdaus tay blocking lambarsa ya kasa samun nitswa last week ya sashi jiki yaje kadunan ma ya nemi gidan kawunta amma hakanan akace mai bata qasar ba'a kuma san yaushe zata dawo ba.

shide gabki daya ya kasa iya cireta aransa wanda hakan ya dada zurfafashi ya fada harkan neman matan sosai.


haryau mrs haseena jira take taga yazo bikon layla koma ya kirasu awaya yaji ya jikinta amma sai shiru ga laylah kuwa tasha baqar azaban wahala dan har wanke mata ciki akayi...yau take cika sati biyu da wasu yan kwanaki agida, tana jin tafara warkewa nan da nan kuwa tasoma tunanin komawa gidan mijinta saidai tsoron gayama mrs haseena takeyi ganin yadda suka rabu baramm barammm da adnan da kuma irin mugun cin fuska da maganan banza da uwarsa ta gaya mata.


layla kuwa tun da taji tafara samun saukin nan sai taji kamar duk wann be darata ba da wann tunanin aranta tafara shirya kayanta ahankli tana boyewa

kullum a lissafe take tanata jira ace yau mrs haseena taje wani social campaing ta gama yankewa aranta cewa ranar zata gudu ta koma dakin mijinta dakanta dan bazata iya jiransa ko uwarsa su gane gaskiya suzo bikonta ba she just want to stay married to adnan, koba dan komiba saidan bataso tabar cikin familyn shehuri musmn yadda ake riritasu a bakin manya,tauraronsu na siyasa na baalain haskawa,suna kuma cin ganiyarsu da kuma yadda take tunanin kar yaa nur da duniya gabaki daya su mata dariya inta fito waje a matsayin bazaura.


a fannin nur kuwa tun Washe gari Da safe da suka dawo tunda tayi sallahn asubahi ta kasa mikewa daga kan gadon tsaban yadda takejin kanta not in the mood of everything yasa bata ma sauka kasa tay breakfast ba.

tunda sukadan yi good morning call da masoyinta javeed take kwance da wayarta a hannu tana murmushi wasu mayun romantic texts kawai suketa exchanging atsakanin su har wajejen karfe sha dayan rana bata tashi ba kawai dadin soyayyar javeed din ne yake cizonta ta kota ina.

rungume da pilow tayi lumui Tana juyi from end to end na gadon harsanda tagaji da hira da shi snn ta sauko tay wanka, Wani kwalliya tazauna ta tsala ma fuskanta kafin tashirya cikin wata pink dry lace ta sauka kasa duba su hajia.m


tana zuwa sashen hajya sa'a ta samesu a falo zaune tareda hajya bilkin suna ta famar tattaunawa akan razia sedai bataji me suke magana akai takamame ba dake suna jin sallamartan sukayi shiru suka dan wanye.

rusunawa tay cikin ladabi ta gaishe su kamar kullum de haka suka sakata taci abinci isasshe snn suka korata daki dan ta huta da tunanin ko gajiya ne yahanata saukowa tundazu shiyasa ma basu dameta ba.


haka yanayinsu ya kasance agidan, tun noor tana dauke kai akan strange meeting dinsun har ta fara lura cewa da akwai wata matsala da basu son su sakata aciki wanda gani take kamar ya shafi razia sosai.


tun daren ranan abun yafara damunta ta fara neman raziar a waya don sugaisa saita tambayeta sai kawai taji wayarta a akashe abun de ya bata mugun mamaki saboda tasan razia bata kashe wayarta duk rintsi amma sai bata sakakomi aranta
ba.

washe gari ma haka ta sake kira shiru still kuma tazo dinning da safe ta same su hajya suna familycoference call da kawunta, taji kamar ma hayaniya sukeyi da kawun tan
sunajin motsinta kuma sai suka zanca hirar gabaki daya.

itadai batace komi ba dake ko kadan basu basu sauya mata fuska saidai ko daga yanayin hjy saa zaka gane da akwai babban matsala dake cinsu akasa kasa agida

haka abun yayi ta damun nur aranta amma sai tay kamar bata san me yake faruwa ba,yanxu duk rashin samun razia a waya shiyafi komi daga mata hankli.

dan kowani rana sai taga sabuwar tashin hankli a fuskar hajy sa'a...

yau jumu'a bayan sun kammala breakfast dinsu lafya lfya marmaza nur ta mike tabarsu anan takoma dakinta taje tafara kirar molly awaya, sosai gaban ta ya fadi jin lambar mollyn ma akashe, ta kira frankie shikuma yace mata yana aiki basu ma samu dama sunyi wata magana ba,
toh koda ta kira muna itace take gaya mata ai tun kwana biyar da ya wuce razia suka gama rubuta final exams dinsu toh hala basu son su dawo gida ne yasaka suka kashe wayoyinsu.

this makes alot of sense to her tuna cewa taji raziar ranar awaya tana cewa bazata dawo nigeria akan lokaci ba amma kuma still saita gargadeta kar ta gayawa kowa kode wann shine matsalar da hajya saa take damuwa akai??.


sosai kanta ya daure tarasa asali menene yake faruwa, cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya ta mike kenan zata fita tajeta wajen hajiya sai wayarta yay karar shigowar sako..

tana dagawa taga notification da heart emoji cikin nitsuwa ta koma tazauna tana dan murmushi ta bude
taga ya rubuta" baby gal i am picking u up tmrw for golf and formalities a karshen text din taga dress code da kuma time.
[30/04, 21:18] BLUE💙: EPISODE...22🦋
Ajiyar zuciya ta sauke dacan kamar zatay replying dinsa atake sai tafasa dan duk dadin soyayyar dake janta she knws men dont value women dat are too available for them, hakan yasa takan dan matse son dominta kama ajinta

bata amsa ba kawai ta aje wayar gallantly akan gado tafita cikin nitsuwa tayo hanyar dakin hajiya sa'a.

Da sanyin sallama a bakinta takaraso cikin sashen saiji take hajya na daga murya sama sama har kamar ma kuka takeyi tanata cewa alhaji kawai kasan yanda zakayi yata ta dawo gida she cant be gone missing, kafasan razia da taurinkai abu dan kadan ne yake bata mata rai kuma duk kai ka jawomin alhaj lefinka ne. memekon ace kamata zancen celebrating na gama schl dinta firstly kawai saika kawo mata zancen shirin aure? haba alaji saurin me kakeyi haka kode sun biyaka kudine akanta kake saurin ka rabu da ita,u dont even care abt how i feel, kafi kowa sani fa mutanen nan suna auren razia ba lallaine mu sake ganin ta ba, she is my only child ahaka kakeso ka rabani da ita. gaskiya nikam bakamin adalci ba nide koma miyene kawai kasan yadda za'ayi yata ta dawo gida inma kun hade bakine da su suka dauketa kawai su dawo min da ita, tunda kai kanace auren dole zaka mata fine..you dont have to piss her off about it yaufa sati guda kenn wayarta ba akunne ba
shinsu ahlin mufa..s..

bata karasa furtan mufasan ba idonta ya sauka akan nur dake tsaye daga bakin door tadan sukuyar da kanta can kasa dan sosai jikinta yay sanyi ganin yadda hajy sa'adatun take diri tana maganan tana kuka da tashin hankli


ganin nur din yasaka tay saurin saka hannu tanamai share hawayenta cikin sauke murya kasa kasa tace "we ll talk later..ga auta tazo.

kawai saita katse wayar tanamai kalalo murmushi ahnkli tace Nur karaso mana kyakkwata meye kika tsaya daga can kamar ruwa ya kwaso ki.

jiki a sanyaye nur ta dago kai da faint smile a fuskarta ta karaso cikin rusunawa tace "gud morning mumy kin tashi lafya?

ajiyan zuciya me nauyi ne yakufce ma hjya saa tace lafya kalau
auta whats wrong ya naganki haka.,

girgiza kai kawai nur tay sai can kuma ta dago takalle hajya da sanyin murya tace mumy dama inata kirar anty razia ne amma bana samunta awaya shine nace zan tambayeki inji ko ke kina samun ta???

dan shiruuu hajy tay tana kallon nur tasan yarinyar da kawaici aduk dama taji wasu tattaunarsun awaya ba lallaine ta iya dago mata da maganar ba.

wani sautin humm ne yakufce mata muryan ta asanyaye sosai tace "nur,.. ure like a doter to me kuma nasan razia tana kaunarki sosai dolene kema zaki damu da ita karkiga kmr wasu abubuwa na faruwa kawai de banason na sakaki cikin maganan ne sabida youre too young for all this drama...

nur ta dago kai tace wani drama kuma mummy??? tun hjya bata amsa ba da mugun tsoro a muryanta tace anty raziar ta bata ne???

idon hajya sa'a atake yaciko da ruwan hawaye tace a'a, nasan razia bata bata ba, is just one of her ways of purnishing us dama kuma ta saba mana haka idan aka takura mata amma karki damu zata dawo gida...

nur harta budi baki zatay magana cikin katseta haj sa'a tace calm down auta karki damu duk shirme ne aike kanki kinsan yadda razia take son babanta she is just pissed cewa bai mata congratulation na gama schl ba kawai he went strght ahead yafara mata maganan shirin aure kuma ya san batason auren nan, wallh dakyar ma tay accepting sabida farin cikinsa aida sai mubarta koda dan wata biyu tazo tay mana agida kafin afara wani kawo mata zancen aure...

jikin nur a sanyaye sosai tace mummy toh dan Allah kiyi hakuri, pls calm down kema kidena damuwa she will come back in sha Allah natura mata sakonni dayawa i am sure she wll be back inta huce,kuma baba bazai takura mata ba she knws how much he love her.

cikin sauke ajiyan zuciya hajya tace hakane abun ne sai addua kawai amma banason auren nan Allah ma ya sani..yanxu kinga mubar wann maganan tashi muje muci abinci kinje kin duba hjy bilki kuwa


kusan atare suka mike tsaye nur tace a'a yanxune zanje na duba ta itama ai bata fito ba. cikin kakalo
murmushi hajya tace toh kije ki fito mana da ita kafin na gama shiri na fito nan nur ta gyada kai cikin ladabi snn ta fice a dakin tay wucewarta izuwa dakin hajya bilqi..


bada jimawa ba suka hallara duka akan dinning kamar kullum sukayi breakfast kowa dai nanuna damwarsa akan rashin dawowar razia gida, bayan sun kammala suka shirya kowa taci adonta da native dress suka dan fita gari ziyara wa few distant relatives dinsu dake yau jumua ne
akan danyi zumunci da yan uwa dan a gaggaisa, basu dawo gidan ba sai can da yamma tun awajen dinner nur take gaya musu cewa zataje shoping gobe, nan hajya bilki tace mata ai suma zasuje taron Addni na matayen kungiyar NASFAT da FOMWAN kawai inta dawo dawuri saita samesu acan..


washe gari da asuba nur ta farka da adduar tashi a bacci a bakinta ahankli ta yaye bargon daga jikinta snn ta mike zaune cikin sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tuna jiya basuko yi waya da javeed ba yasa ta jawo wayar ta duba sama sama taga tun sar text din data tura masa ne babu wani sako. ajiye wayar tay a kasale snn ta saukar da heathy fresh long legs dinta kasa cikin sanyin taku ta wuce bathrum ta cire silk nityn dake jikinta iya cinya dama kuma shikadaine tana ajeshi a loundryn tashiga gidan shower ta kunna ruwan dumi akanta yafara zubowa shaaa tanamai sauke ajiyan zuciya me nauyi

har cikin ranta take son taga razia tay haqri ta dawo gida koda hanklin iyayen su zai kwanta saidai tunanin yadda zatay tafara neman taimakon javeed akan hakan shiyafi damun ta dan bata fiye son involving saurayi akan personal problem na gidansu ba lissafi ta dingayi a brain inta ganin babu wata mafita sai kawai tabarshi.

tana kammala wankan tay brush agaban sink sann tay steaming sumanta da kuma fuskarta da antioxidant herbs.

tay alwala snn ta fito
sama sama ta shafa lotion a hannu da kafa kai tsaye ta sanya wata doguwar jilbab ta tada sallah bayan ta idar ta zauna wajen tay karatu tare sa azhkar around six am ta mike takoma gaban madubi sann tadau handrier bushar da dogon sumanta ta shafa masa leave in moisturiser tabi da cap snn ta koma gado takwanta.

tun tana jiran ganin kirar javeed harta haqura ta kira layinsa tanaji akashe ta jefar da wayan gefe ta kwanta cikin yanayin sanyin fushi bata wani jima ba saiga kirarsan ya tasheta

acikin gigin bacin ta daga ta masa sallama da wata kasalalliyar muryan data sending masa chill duk a ilahirin jikinshi..

shagwabar duniyan babu kalar da bata mai ba yace mata meeting ya shiga jiya shiyasa bai kirata ba sai yanxu,..they talk abt few things snn yace mata wajajen 1;30pm haka ta zama ta shirya za'azo a dauketa....

bayan sun kammala wayar ta koma bacci ba ita da farkwa ba sai can karfe 10 da rabi saura, kimtsa kanta tay ta fito ta zo tasamu su hjya har sun gama shirinsu ma fita, suna gaisawa ta rakasu har kofa snn ta dawo tay breakfast dinta ta shirya ta fice saloon itama daga nan tayi pedicure nd manicures 12:30 ya mata agida...

ganin babu sauran lkcin batawa kawai tafara shiri duk dama dakyar ta iya zabar makanta kayan sawa dan bata san ma meyake nufi da formalities ba kawai de tasan dole ne ta saka kayan da zai fito da kasaitarta sosai. walk in closet din ta ta nufa ta fara duba peferct covered traditional dress that has the touch of class and sophiscation.

koda ta ciro cape gowns dinta sai taga kamar cape din sunyi guntu, tunda ba abaya zata saka ba she still need sumting da zai rufe duk wani sirrin dirin jikinta entirely something like a cloak

nazarto hakan yasaka tay cikin wani sashe ta bude long standing wardrop inda ta zaro wasu hadaddun kayan tabi sashen jaka da takalmi ta dauki wata classy Chanel hand bag da rock stud shoe dinta shima bamai tsini sosai ba.

akan gado ta ajiyesu snn ta zauna agaban mirror ta tattala kan fuskarta da wata fine powder yay neat and smooth sama sama kawai tay brushing eye lashes da brows dinta bata zanashi ba kawai ta gyarashi tabi layin shape din fuskar ta da dark coutours snn ta shafawa idonta bakin kajol, bakinta ta sakamai wata cream nude lips stick mai sheqi da maiko data zagayeshi da brown pencil,tagama setting da spray, nan da nan tafito so natural and fiercely pretty, babu wani tarkacen eye shadows da sauran tarkacen kwalliya dan yau ko su foudation bata saka ma fuskrtan ba baki sidik din suman kanta da already ta gyarasa a saloon ribbon kawai ta sakama dognut din kai snn tabi baki bakin sa da curly gel sukayi wani irin waves harta wajen sajenta snn ta saka wani hadadden gold colour earings da tsiririn abun wuyansa

kayan data ciron ta dauko ta fara sawa ajikinta wanda duka collection ne daga kamfanin fashion na _zalando_ dats far far exclusive and too rare kagani ajikin kowa.

simple off shoulder plain dusty gown me guntun hannu tafara sawa aciki sann tay pairing dinsa da full floor length charcoal black cloak dayayi wani irin saukowa daga kafadunta ya zube daga bayanta har izuwa kasa kamr alkyabbar sarauta

babu wani design na embroidery ajiki bare kuma tarkacen stones she just look calm and very wealthy like a royal qatari diplomat lady musmn ma data saka karamin dusty color plain mini hijabi kalar rigar data saka aciki,along with her mini chanel bag and classy stud shoes ita kanta sosai ta gamsu da wann shigar nata yo koma wani irin formalities ne tasan zata iya fuskartasa a haka batare da taji dar dar ba...

tana cikin shafa turaruka sama sama ajikinta aka aiko daga waje ana nemanta...

saida tagama kominta anitse snn ta kalle time agogonta taga harma lokacin tafiyar yay, fitowa tay kamr sarauniya ta samu mr aqeel da janet da wasu body qurds a tsaye agaban motocin

19 / 112