Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
tamai qarfi tawani kalli kanta a madubin tareda jan tsaki snan ta koma ta zauna a kan gadonta tare da daukan wani roban magani nan tabude taciro wasu kananan kwayoyi aciki sun kai takwas zata afa abakinta sai kuma taji kwuiwar mikewa ta dauko gorar ruwa.
akan drawrta taga jakar data dawo daga kasar waje dashi jawosa tay ta bude ta dau wani karamin kwalban giya wanda tunda akace mata javeed yay aure shi take yawansha acan datake ciwon nan dan goyar yana rage mata tunani sosai
tana kkrin bude kwalban kenan yay dede da shigowar hajy zuby dake amsa waya
datse wayar tay cikin sauri tare da saurin buge hannun simran dake shirin kai wine din bakinta da drugs duka suka zube akasa
adan razane simran ta mike tsaye Oh my god ya zuby meye haka dan Allah, dan kadan fa zansha..
da bacin rai hajy zuby tace "Ke simran zanci ubanki..bana hanaki kusantar wani abu me kama da giya agidan nan ba, toh ranar da aka kamaki da giya agidan nan wllh u will be thrown out like a stray dog waimesa baki da hankline simran
...tafada tana bude mata ido kmr zata mareta.
Dada yamutsa fuska simran tay cikin kukkuni "just litle fa, ni yaushe nace miki ina shan giyar ma inba yau ba, bare ma magani fa kawai zan...
"ke dallah rufamin baki..Keep quiet karki sake magana anan
wai Inkuna cikin tashin hankli bazaku iya dannesa da karfn kwakwlwarku na dan adam ba saida giya? yar iska kawai kina neman ki jawomin abun magana agidan nan gacan hajy mamy da alhaji attah sunata ririta ilimin matar javeed ana cewa wai ita din mahadacciyr alqur'ani ne kekuma sai ace miki shugabr yan shaye shaye kenan ko
yaa zuby daga an fara magana saiki fara hadani da wancan kazamar yarinyar qur'ani fa ta haddace kawai nida nai karatun medicine fa..
hajy xuby tace dan Allah kimin shiru waye baisan cewa da taimakon baba kikayi karatun ba, you lazy brats who only know how to slag...
simran ta wara idanu tana nuna kanta yaa zuby are u saying im just useless kawai dan na dan sha giya dats not fair
tace no, Cewa nake bakisan meke miki ciwo ba, snn yarinyar dakike cewa kazama kingani ai ta iya rike zuciyar namiji kamr javeed,you, you..misss doctor medicine woman kefa?ko gama warwarewa jikin ki baiyi ba kinxo kinashan giya hm
"yaa zubby pls is enuf nowww haba, my hrtt is breaking amma lefin komi saikice nine awajenki, u dont even pity me, toh menene kuma banyi ba?ni wllh gaskiya nagaji ranar ma haka....
hajy zubyn bata bari ta karasa ba tace toh muje ki ma alhaj godiya yana falonsa kuma he is alone tun kafin wayancn matayen sufito susan ma ya baki wani abu.
dan rau da ido simran tay cikin dedeta nitsuwarta tareda sauke ajiyan zuciya tace wai nawane ma yabanin ne nifa banko bude nagani ba.
batare da hajya tace komi ba ta dau wata envelope ta mika mata tana cewa ohh dama sai kinsan nawa ya baki kafin nan kimasa godiya ko.
ko kulata simran batay ba jikinta na rawa rawa tsabar kwadayin duniya tawani yaga brown envelope din ta ciro wrapper of dollar guda biyar da ticket na 2 hours shoping free danshi aransa personally yay tunanin hala simran zataji babu dadi da zagin da aka mata awajen cin abinci ko hala tayi tunanin sauya dress code dinta and he hopely wish for that a irin anasa hikamar ta manya sai kawai ya bata har da free shoping spree to keep her motivated for 2hrs akoina ta siya kaya shizai biya mata kudin kayan dakansa.
fuska atamke simran ta jujjiya kudaden ahannunta cikin jan tsuka mai sauti snn ta sakesu a walaknce suka zuba suka fadi kasa..
baki bude hjya zuby tace bangane ba meye haka?.
cikin bude ido da lumshewa da bacin rai simran tace haba yaa zubby ynxu duk uban kudin mutumin nan da baisan ma iyakarsu ba d'an abunda zai ban kenan amtsayin farashin kudin son danayi ma dansa???mtsw shiyasa nake kaunar javeed wallh, ko mutum maqiyinsa ne bai isa yace masa marowaci ba, amma babansan nan kullum damuwarsa kenan agina free asibiti agina gidan marayu agina free schools akai kaya akai abinci wa mabukata yen yen yen shifa almajiraine ke cin kudinsa konima saina dawo almajirar ne inci ohooo...wallh ko, ina auren javeed shima hanashi wnn abun zanyi karyazo ya fara tsufa yadawo marowaci kamar babansa...
baki bude hajy zuby tace "ohh wai rainawa kikayi? toh ai da fitowa fili kika gaya musu cewa abaki kudin son dakikayi javeed abaya wallh tallah simran da zasu baki isasshen kudin da kaf zuriarki basu taba gani ba, amma ba amtsayin farashin
soyayya javeed ba saidan sunana miki kece makwadiciya
... hehe hmm yaufa karyanki ya kare...aidama nasan wallh tallah bason gaskiya bane aranki akan javeed kike wani min karya osheyyyy lashe money....abeggg stop pretending...why didn i even belive that ealier?
simran ta mugun bata ranta hartana huci yaa zuby yaa zuby gaskiya banason haka meya kawo wnn maganan kawai daga ance mijinki marowaci saiki zageni kema ai kin sani wallh inason javeed har raina kuma ai garani ban kashe kowa akan kudinsa ba.
wani irin make mata baki hajya zuby tay da wani irin tsawa tace ahirrrr dinki da furta wann maganan simran, the wall has ears karki sake kijawo kema din na kasheki yar iska kawai kema kinsan halina wallh baki fi karfin in murde wuyanki anan kimutu
hawaye cikin idon simran ta budi baki zatay magana cikin katseta hajy xubby tace is enuf pls lets go..
tsaki simran taja ta share hawayenta tafara binta abaya
tana kananan maganganu
tafiyar kurame suke kusan koina ajikinta na girgizuwa tsabar ta dame. karar tsinin takalminta ne ya cika gida tana wani irin yauqi har suka kai sashen alhaj attah dake kwance akan wata original sculpted black tuned sofa a wani purple tinted mini palour harya sauya Kayansa zuwa royal arabian jallabiya da wata doguwar carbi ahannunsa yana kan ambatar Allah ahnkli.
yana ganin shigowar su yamike zaune dan yakare idanunsa daga ganin abunda bai dace ba.
hajy zubynce agaba tay sallama ya amsa ta babu yabo babu fallasa lkcin kansa na dan kallon kasa..
da wani irin yauqi simran ta karaso ta gabansa wanda kafin ta tsuguna ma gabaki daya gugan manyan nonowarta sun wani hargitso ta gaban rigartan kamar wanda zasu fito waje..
cikin make murya kalar na tausayi tafara masa godiya kamar ba itace ba tay ta zaginsa a daki ba.
sam yaki ya furta mata abunda takeson ji din dan tasa rai kawai akan javeed ya bata kudin, sai yace kawai sabida ciwon datay ne ya bata wnn gift din taje tadan huta cos he knws shping make girls happy
suna cikin maganan kuwa saiga anty suad ta doso falon wani tsayuwar cak tay abakin kofar tanaji ana zancen shoping dake brain inta na aiki tuni ta gano salon yayantan..
da wani irin salon makirci ta shigo tun basu gama gaisheta ba hajya zuby tay ma simran ido akan su tashi su tafi amma zakewa da son neman gindin zama ya saka simran ta zauna tanama matar busy body.
nan danan kuwa anty suad tafara murmushi tana cakka mata baqar magana cewar anbata kudin canza sutura.
tun simran tana playing dump har abun ya fara mata zafi musmmn ma da anty suad ta ciro paper ta rubuta mata kudi ta kara mata tace mata ta siya harda hijabai tace mata ai jikintan na tsufane kuma na masu saka hijabi ne bana masu gaye ba.
it was a very classic insult data musu shi in a joking way..
hajy zubaida haushi ya cikata tama kasa boyewa a fuskarta kawai tay excusing dinsu ta fita kafin can simran dinma ta mike ta biyota abaya.
suna zuwa daki ta dinga ma hajy xubyn complain akan zagin da anty suad ta mata hajy zuby ta shareta musmn jin rantsuwr da simran takeyi na cewa baa isa adawo da ita kamar nur firdaus agidan nan ba ita ba yar sekandarin kauye bane da zata saka wani hijabi ko ta daura dan kwali a wann centuryn kuma acikin gida.
ko kulata hajy zubaida batay ba, wajajen four na yamma simran tafarka daga bacci ta shirya tsaf ta wuce shoping dan tana bukatar wasu abubuwa dan haka acikin lagos din kawai ta yi siyayyarta..
shopping bags sunkai 150 wanda ta dawo dasu dan acikin two hours din nan sai data siya banza wofi da abubuwan da batama bukatarsu da tunanin ai kudin banza takeci..
koda ta dawo gidan ko nur firdaus datake can estate dinta saida taji gurmin labarin dawowar dr simran daga shopping dan masu aikine ta tara sunkai talatin suna debo kayan anakai mata ciki.
gata da gadara, iko, da tsawa, kai zaka dauka itace asalin jinin mufasar ma.
ran anty suad ya sosu da irin bankamar da simran takeyi bana kadan ba, musmn ma yadda taga lady sidd tafara yagalgala simran din tana biye mata.
wai har cewa take yakamata abawa simran private maid
sabida arage mata stress na aikin gida.
Dakyar lady suad ta amince badon komi sai dan wani hijabi guda daya da simran tay wayo ta siyo na eye service data nuna mata ita kuma dama tafi kaunar ace ta zagi mutum snn taga yana mata biyayya tana kuma controlling dinsa tunda simran tanuna mata hijabin sai kuma ta amince da komi.
bakaramin dadin hakan hajy zuby taji ba lokcin masu aiki na shirya ma simran kaya da yamma lis ta sake wanka ta sako wasu matsatsun kayan kuma nan suka fito maid estate ita da hajya zuby da lady sidd akacewa simran ta zaba
straight ta zabi wata elderly servant me suna liyatu wanda akalla takai ma 45yrs bakace kibabbiya katuwa an dan basu hutun aiki suna lura da masu ta sowa amma hakanan simran ta nace tace sam ita takeso.
badon anso ba aka dawo da liyatu cikin main building da zama akan zata fara aiki ma simran a matsayin private maid yau sosai duniya tay ma simran dadi bana kadan ba.
a fannin nur kuwa duk kananan surutun da yake tashi tsakanin servant din dake wulgawa tanaji dake a garden dinta yau suka wuni time to time haka faiza zata kawo musu abun tabawa daga kitchen ko naima taje ta dauko..
ahaka har sukaji labarin duk abunda ke faruwa agidan dan simran haka kawai takanyi wayar karya agaban maids dan kawai ta baza zancen cewa ai javeed mufasa ne ya bata uban kudin shopping na danna kirji sabida ya mata kishiya..
dake ba a rasa masu zazzagen baki da son yada gurmi da gulma acikin ma'aikatan kuwa hakanan aka ta yayata maganan akasa kasa...
Nur taji komi sarai amma ta kafa kanta akan karatun takeyi tayi kamar bataji ba saidai daga ganinta kasan ranta a hargitse yake da bacin rai da tsananin rudani tare da uban zafin kishi
ita kuma naima tana dar dar ne wajen yima nur hirar wani agidan duk dama tasan tanada abubuwan fada ma nur dayawa wanda zai taimaketa amma sai tay shiru tana lura da ita kawai duba da suna mugun tsoron bacin ran javeed akansu.
kishi sosai yafara controlling din mood din nur suna kaiwa magrib awaje tace ma naima suje cikin daki snn batason abar kowa yashigo koda mijinta ne sabida tanajin bacci kuma kanta yana mata ciwo sosai.
nai'ma ta amsata cikin ladabi nan da nan kuwa ta kulle kofar sashen nur din gabaki daya da strick biometric security duk dama tariga tasan meye ya hatsalata sosai...
javeed anashi fannin, baimasan meyake faruwa agidan ba dake tun safe yana can sama home office yana kan aiki akan secret files na gold mine dinsu sabida sunaso ne su shigo da harkan monopoly ciki su zama sune kadai suke controlling wajen ba mabiyansu daga kasar france ko south africa ba.
Aikin daya daukesa awanni bai gama ba dan daga sallah sai yawan dauko ruwan sha ke tadashi dan ko mr aqeel dayafi kusan ci dashi bai barsa yashigo inda yake ba
iyakacine kawai yay magana da yan uwansa wato mufasa cousins, awaya ko ata video call musmn ma Amira, khaleefa da ali haidar dan haryau wani boyayyar kishin nur yanaso ya dan fara shiga tsakaninsa da kamil mufasa dan tunda yama nur dinsa kallon iskanci dana sha'awa sai yafara baya baya dashi sosai batare da yasan ma yanayi ba
shi kwata kwata baisan meyake faruwa agidan ba amma he was able to finish his work bayan ishai yana saukowa wanka kawai yay baiko je ya duba mahaifinsa ya taho estate din nur yana haba haba yaji dumin nur din ajikinshi suyi magana na fahimta snn ya fayyace mata komi.
isarsa keda wuya ya samu koina a kulle bai saka komi aransa ba ya fidda master door card dinsa zai bude kenan sai ga na'ima ta fito ata bayansa kanta na kasa da sanyin murya ta rusuna tafara gaishesa..
dan tsayawa yay ya amsa snn ya tuhumeta akan meyasa wajen yake kulle da biometrics ita kuwa bata boye masa komi ba daga abunda nur tace mata ba...
Da can tsaki yay zai bude ya shiga ya dubata sai kuma wani abu yace masa he shud respect her wish maybe kawai hutun take so ta samu yau..
[20/05, 20:01] BLUE💙: EPISODE 54
Arewabooks@surayyahms.
Da wann tunanin ya maida master card dinsa aljihunsa cikin sauke boyayyar ajiyan zuciya ya kalle naima yace mata tay make sure bata bar site din ba snn tana kulawa da lafyar nur sosai in wani abu ya taso ta kira mr aqeel awaya zai gaya masa komin dare zaizo.
cikin ladabi ta gyada masa kai..
bbu bata lkci ya koma dakinsa saidai dakyar yay bacci da tunanin yaci kwana daya yau saura masa Kwana hudu yaje mission dinsa wanda baisan ko inyaje zai rayu ko zai mutu acan ba..
sassafe bayan sallahn asuba yakoma sashen dan ya fara matsuwa da tunanin gaya ma nur komi daya faru abaya kafin aurensu dan yana son yaga sun shirya kansu tay haquri ta yafe masa kafin ya tafi.
ana idar da sallan fajr ya taho sede yana isa sashen still naima ce ta tsaresa daga kofa tace mai ai nur tana lafya, amma tace bata son ganin kowa ynxu..
nan ma yay hakuri da niyyar zai dawo kawai sai yawuce training abunsa dan yasan baida wani lokacin batawa sosai.
awani katon fili dake can baya bayan gida yakeyin irin vigouous training dinsu na sojoji masu jan hula din nan daga shi sai wani dogon wandon khaki da olive colour men vest datake dan matsesa kadan akirji.
Na'ima kuwa duk sanda ta kawo ma nur sakonshi sai ta furta matashi acikin hikima dan tariga da tasan gurmin da gulma da wasu kananan maganganun da akay ta yadawa jiya akansa da simran ne ya bata ma nur ranta da mood dinta gabaki daya.
furucin na'ima mai cike da hikima kuma sai yana neman ya carke mata tunani kawai tafarajin gara kawai ta danne kishin tay confronting dinsa da komi.
sosai tasaka rai akan zataje har dakin javeed din yau suyi magana kawai ya fito fili yagaya mata asalin gaskiyar abunda yake tsakaninsa da simran saidai koda ta saka hijabinta ta fita taje sai tasamu babu kowa a estate dinsan.
Dawowa tay dakinta Wajajen karfe takwas naima ta fara matsa mata akan sufara shirin yin wanka da shiryawa sabida family breakfast is by 9;30am kuma kusan dolene kowa yaje...
batay musu ba tay wankan suka shirya tsaf tasaka wani hadadden saudi fishtail abaya fitted at the top kasar kuma adan baje kadan tay rolling din veil dinsa as usual kominta a killace.
Dake grey colour ne sai tadanyi natural make up look daya mugum fidda natural beautynta baqin kwallin idonta ne kawai yake haskawa sosai..
ta jira javeed ko zaizo su sauka kasa tare amma bata gansa ba har lokacin breakfast din ya fara kurewa kawai sai ta ce ma naima ta rakata hanya in ta shiga main palon sai ita dawo ta kimtsa waje.
hanklinta baya jikinta sosai har suka isa kasa suka kai kofar main palon naima ta tsaya anan har saida nur ta shiga ciki snn ta koma kan aikinta...
wani nannuayr ajiyan zuciya tareda kuma bugawarsa taji sun kufce mata atare da taga kowa ya hallara awajen amma bataga javeed ba.
tana zuwa ta rusuna ta gaggaishesu babu yabo ba fallasa suka amsata ta zauna aka yi breakfast.
itade sama sama takeci sabida tasha mamakin dataga babu wanda ya tambayeta inda javeed yake duk dama ita ma batasan ina yake ba.
yadda akaga suna soyayya duk an dauka tafi kowa sanin cewa yana wajen training dinsa a wajen wanda alhaj attah ne ya gaya musu tun kafin ta fito shiyasa ita batasan da hakan ba..
yau table din ba ayi wani hira akai ba ita ma kuma bata wani ci abincin sosai ba..
duk tana lura da yadda matayen suka saka mata ido suna kus kus da juna amma bata damu ba after like 40 minutes aka gama breakfst din alhaj attah ne yafara tashi ya basu waje da waya a kunnensa.
simran data saka wani tsinannen dogon riga ta dubi agogon hannunta taga time tasani sarai dolene javeed zai shigoshi gidan bada jimawa ba
wani buuut ta mike ta bar wajen ta haura sashenta tay maza ta saka wani wando me kama da leggings ya kamata damass snn tacire brazzierta ta dauko crop top ta zura yadda nononta zai na daka tsalle dakansa snn ta barbaja wig dinta ta saka wani mayyar heel ta fito cikin sauri da sanda tay hanyar sashen javeed danta tarbesa da ruwansha dan bakaramin son tay magana dashi takeji ba..
daga falon kuwa bayan tashuwarta a dinning table din bada jima nur itama ta mike zata nufi estate dinsa tasake dubashi kawai sai lady siddika da hajy zuby suka kirata
suka fara mata wasu bayanai akan kulawa da harkokin gidan dan tasan responsiblities din abubuwan da zata dauka daga next week, ahakan ma anayi anty suad tana lekowa tana cakko mata baqar magana aciki tana nuna mata kamar irin auren ma dai bajimawa zaiyi ba hala ma kafin nan da one year din ya kare
still kuma lady sidd suna mata gorin cewa tunda batay karatu me nisa ba aidama yakamata ace ta fara tunanin riqe wasu respnsblitys na gidan mijinta tunda itace bata da aikin yi agidan
itadai nur batace musu komi ba tay musu shiru har suka gama lady sid da hajy zubbyn ne suka hau kaita sashe sashe na gidan danta zama familiar