Chapter 67 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   67 / 112

198K to 201K   out of 335.4K words

meyasa ita tay dakanta inba markici ba..simran ta fara burga irin tafi kowa sanin rayuwar san nan tana nuna musu anty suad cewa ai javeed ma baya memeta kaya kawai wahalar dakai ne yasaka nur ta wanke jinin waye waye...

hakanan suka dinga mata habaici a dakin tun abun bai dameta ba harya fara damunta koda taje alwalwa sai da tay kuka abun ya ragu mata snn ta dawo tay sallahn asr ta zauna shiru tana adduar Allah ya bashi lafiya, bayan isha kuma ta sake mai wankan snn ta cigaba da saukarta dan yau kwata kwata bataji dadi a zuciyarta yadda su anty suad da lady sid suka dinga gasa mata baqaqen magana acikin habaici ba.

farin cikinta guda daya shine numfashin daya fara wanda yasa vital dinsa yahaura with 4%
he is now at 34% which is still not soo encouraging to hope for life.


yaudin haka ya kare wani abu kwakwkara bai faru ba dake ana dai kan neman dr ruqayya da mother hauwa tunda da tafara karatun ta bayan isha matayen gidan suka watse tadan samu sarari

Hajy zubby ma lafya ta kwanta dan har dare ya rufa mr manny bai nemeta a waya kamr yadda yace ba.

9:30 pmm nur ta kammala hada suratul baqara ta fara karanta suratul ali imran takai kamar shafi biyu snn ta haqura ta hawo kan gadon tayi ma javeed aduaoin kariya masu yawa kai duk adduar da yazo bakinta inde na kariyane tamasa awann daren snn tadan kwanta agefensa da addua abakinta har bacci ya dauketa.

janet ne kawai dama ke watching dinsu ita bata samun bacci har sai nur ta farka yin sallahn dare sai ita takwanta tay baccinta zuwa safiya..

tunda nur ta kwanta agefensa tana bacci janet ta mike tanamai aikin duba security cameras recording tanamai lura da masu shige da fice musmn tasaka idonta akan dr simran da hajy zubby tanamai karantar yanayinsu tun ran da aka kawo javeed dakin zuwa nan..

downloading copy na video tay ta tura ma na'ima sabida tasan naima is witted nd very sharp minded hala zata tayata gane wasu abubuwn

har karfe 1;30 aikin datakeyi kenan tanayi tana duba nur da oganta for awhile ita dai taga nur na baccinta peacfully

can karfe uku na bugawa dede sai kuma taga nur din ta farka a mugun firgice tana salati da karfi ga wasu irin hawaye sharbe sharbe suna sauka a idanunta kamar wanda aka watsosu jikinta na rawa rawa ta sauka akan gadon ta tsaye asandare tanata kallon javeed da wani irin bugun zuciya

a hujajan janet tazo ta dan tabata sai taga ta tsorata taja da baya

hanklin janet atashe tace "ma'am lafya kuwa..ranki shi dade hajiya...kusan a rude nur ta fashe da kuka snn ta wuce wajen data ajiye maganinsam batare da ta kula janet ba tana daukar kwaryan kuwa taga ya cika da kumfa yay wani irin yauqi.

tsabar ta tsorata kiris ya rage ta sake kwaryan ya fadi akasa janet tay saurin karbewa taje ta zubar a sink snn ta dawo ta samu nur din a zaune tana kuka ahankli.

maganan duniya janet tay dan nur tagaya mata meya faru amma sai shiru sabida tasan babu kyau fadin mumman mafarki sai kuma tunda taga maganin ya lalace in reality ta gane cewa ba lallaine abunda ta gani ya zama mafarki ba..

sosai jikinta ya fara bata cewa koma miye aka cakke javeed dashi toh tabbas kmr blood oath ne akayi da jininsa da bakaken aljanu masu hatsari dan a mafarkinta gani tay tururuwa masu shegen yawa suna shigewa cikin ciwon bayansan sunata shan jininsa
da wani abu abakinsu kmar straw

janet harta gaji da lallashi da tambayr nur tay shiru dan dakyar nur ta dawo cikin hanklinta taje tay alwala tazo ta cigaba da sallahn darenta kamr yadda ta saba tanayi tana kuka dan a tsorace take sosai.

washe gari still ta tashi da azumi tun kafin kowa yazo taje ta sake nika ganyen guda bakwai tay repeating same process ta kara wankeshi dashi..

haka kuwa tay shiru bata gayawa kowa meyafaru jiyan ba janet ne tadan sulale waje ta samu ta gaya ma alhaj attah duk abunda yafaru wanda koda suka shigo sai baice ma nur din komi ba dake dasu anty suad suna dakin har saida ya fita ya kira hajya mammy yagaya mata
komi da nur ta gani

itace ta warware masa cewa bakaken aljanu ne suke bata ruwan wanka dan haka duk suyi hankli amma kar adena kulawa da wanka da kuma karatun qur'ani a dakin.

daga nan babu wani abu dayafaru javeed was stable, mr manny haryau bai kira hjy xubby ba sai cin karen su ba babbaka suke agaban su anty musmn da sukaga yau nur ta zama very quiet and alone tana yawan ware kanta da su duk damuwar datake dannewa sai ya fara nunawa ayanayinta sosai.


shide alhaj attah bai fasa neman mafita ba yayi nan yakira nan saidai komi na musu wahala ne sabida spritual prblems na famliynsu is compltely secretive koda ya samu masu taimakon ma bazai iya bude musu sirrin gidansu ba gashi mother hauwa datake daukar wann ragamar haryau bata fito ba komi ya taru ya masa yawa aransa ya tura sultan neman dr ruqayya but he is still feelling bad da yake ganin kamar nur tay karamar da zai sake mata komi duba da su anty suad yanzu sun fara muzguna mata awajen.

wajajen 3:30pm yay wanka kenan zai shiga sallahn asr sultan ya kirasa yace mai yana hanyar zuwa gidan nan da minti 20 haka zai iso ce mai yay ya samesa a masjid kawai snn ya shirya ya fita.

daga sashen da javeed yake kuwa ana shiga sallahn asr suka watse a dakin nur taji wani irin sanyi aranta dan dama sun isheta a dakin

marmaza taje tay alwala tazo ta hada ruwan maganin akan intay sallahn asr kawai wankeshi zatay tay sauka sabida kar su anty suad su sake dawowa.

tana hadawa tace ma janet tana duba mata ruwan nan ajeshi akan table ta fara sallahn har tay sujada na biyu kenan taji janet ta saka ihu tana cewa blood of jesuss blood of jesus

mummunn faduwa gaban nur yay amma haka ta daure ta cigaba da sallahn ganin likitan ya shigo da gudu shima jin ihun janet yajawo hanklin kowa har da su mr aqeel dake waje.

nur tana sallahn amma jikinta rawa yake jin yadda janet ta hau nuna musu yadda kwaryan ya cika da ruwan kumfa har yana zubowa kasa tsoro duk ya cikke idanunsu

mr aqeel ne yay ta maza yaje ya dauke kwaryan dan yaga da alaman ruwan zai iya zuba akan gadon da javeed yake kwance da gudu janet taje takira su anty suad kafin kace wani abu dakin yacika kowa yana kallon ikon Allah

nur tana yin sallama agurguje ta taho tawajen to make sure javeed is okay snn ta amshi kwaryan a hannun mr aqeel taje sink ta tsiyaye shi ta wanke kwaryan tazo ta kifasa da bisimillla duk panics da surutunsu anty batace musu komi ba tafita da taurin zuciy taje ta sake debar magaryan guda bakwai ta sake nikawa tazo da shi

tana shigowa ta samu alhj attah da sultan sun shigo shiya musu bayanin cewa ai wukar da aka cakka ma javeed blood oath ne da baqaqen aljanu har sai an rabashi da su kafin asamu sauki

nan yace musu akan azauna duka afara karatun qur'ani adakin kafin nan nur ta sake hada ruwan....
[01/06, 20:31] BLUE💙: BONUS.
nan kuwa anty suad ta jerasu akan dadduma harda likita da su mr aqeel kowa aka zauna aka debo qur'anai aka raba qur'ani za 'a fara karanta suratul yaseen hmmmm zokaga idonsu simran da hajya zubby duk yay tsuru tsuru dan saida janet ta kawo ma simran scarf ta rufe jikinta dashi snn aka bata qur'ani ta zauna kusa da hajy zubby amma badon rai yaso ba.


akan daddumar dakin akay zama aka fara rero karatun hajy zuby ta sadda kai kasa kamar zata kife fuskarta cikin qur'anin dan tasan ko cin bakin bazata iya ba iyaka sabbi karatun ta ya tsaya...simran kuwa sai bis bis bis bis min min lun lunn take da baki in akazo karashen aya taji tadan capke wani abu sai kaji tayishi da karfin tsiya da wani irin kalkalar karya wai dan ace tanada qira'a irinna nur ana gabar tana yamma duk takaici yabi cikawa anty suad ciki kamar tamata ihu ta koreta haka ta dingaji.

janet na tsaye agafen nur harta gama hada ruwan magannin alhaj alhaj da sultan suka taso suka dan tsaya agefenta yana kallo tay bismillah ta fara tsoma clean towel a ruwan magaryan tana shafawa ajikin javeed

ta shafamai sau uku zata tsoma na hudun kenan tana dagowa taga towel din yana janta tsabar yauqi ita kanta bata san sanda ta jefar akasa ba

ihun blood of jesuss da janet tay yasaka kowa ya razana ya mike tsaye sultan ne ya fara ganin jinin javeed da ya barke yahau tsikalowa daga bayansa kamar ruwa yana tsilalawo kasa gashi yay baqi kirin kamar an damashi da kwalta

mummunan faduwa gaban nur yay da wani irin karfin hali hanmunta na rawa rawa ta bawa mr aqeel ruwan dake kwaryan tacemai ya zuba acikin sink ya dawo mata dashi zata sake hada wani

yana shiga bayin kuwa kofar ya rufu dashi anyi anyi abude sai shiru alhaj atttah dayagene ba normal bane sai yacemai karya dena addua kawai

nur tay sauri ta dora hannunta akan goshin javeed tafara masa asalin ruqiyya jininsa dake zuba sai wani irin zanen abin tsoro yake a dakin akasa

atake waje ya kara rikicewa da tsoro simran data wani capko jikin hajiya zubby nan jikinta yafara rawa kar kar tana neman ta falla da gudu

hankli tashe anty suad ta daka ihu tace musu bamai fita kowa kawai ya zauna adawo kan karatu they cant back down now

jikinsu na wani irin rawa aka zazzauna bakin simran har cijewa yake tsabar tsoro dan firgita takeyi intaji muryan mr aqeel daya makale abayann gida yanata addua shidaya

Nur tana zafafa karatun jikin javeed yay wani irin zafi kafin ka hankara glasses din frame sun fara faffashewa fass fasss fassss fasss straight wani ya cakka sultan a hannu kowa ya fara yin kasa dakansa simran ce tafara wafcewa zata gudu ana kkrin rikota ta rikota akan anty suad ta turmusheta kasa nan waje ya kacame anty suad dataji wani mugun haushi wani irin tureta akasa tay tacigaba da karatun ta ita da lady sid

nan kowa ya fara neman kaucewa dan duk glass dake dakin fashewa suke kamar ana tarwatsu da bindiga kuma duk wanda suka sameshi cakkensa suke.

hannun nur da gefen wuyarta duk glass din ya cakketa amma bata dena ruqiyyar ba dan ita kanta bata san daga ina karfin halin yake zuwa mata ba.

alhaj attah ne kawai a tsaye yana rike da gadon da karfi ganin yadda yake kaduwa can yafara ihun cewa a rufe babban madubi

sultan marmaza ya cire jacket din rigarsa zaije ya rufe kenan sukaga wani sudden guguwar iska ya fettosa kasa da wani irin karfi yabugu da jikin gado duk karfin san nan saida yakasa mikewa tsaye.


wani irin ihu hjya zubaida da simran sukayi suka tashi tsaye simran ta riiike rigar lady sid tana wani irin tsorataccen tsalle kamar zata dauke nunfashinta

alhaj attah ya sake gadon yayi kan sultan da gudu zai dagasa amma yaji yakasa da wani irin karfi windon ya budu sai iska frm no where ya fara shiga dakin wanda atake komi yafara kadawa banda alhaj attah dake addua akan sultan da anty suad likita da lady sid, hajy zubby da simran da janet kam babu kanta dan banda razana da ihu babu abunda su sukeyi.

iskan sosai yaso yarike ma nur hannu dan ji take kamarma ana kkrin finciketa ne daga jikin javeed din amma hakan ta cije da iya karfinta takara danna hannunta a kanshi tana kan rero karatun ta wanda takeyinshi da rawan murya da dunbin tsoro babu kakkautawa after like 2 scdns taji kamar iskan yabar jikinta da wani irin speed ya koma kan windown

bata san inda hanklinta yay ba kawai muryan Alhaj attah taji yana ce mata karta juyo ta kalli madubin aikuwa dan firgitan datayn nan taji an shakure mata wuya kamar za'a kasheta

nan kowa ya mike a mugun tsorace simran tafara fitsari ajikinta zirrrrr ganin iskan dake fita a madubin ne fa boro boro yake jaaann wuyar nur da wani irin karfi duk wanda yazo kusa dan ya ceceta hakan iskan zai fettashi waje..

tun da aka fetta anty suad har kofa tabuga kwankwasonta bata sake iya tashi ba likita ne yaje ya dauketa ya fita da ita kofa a mugun tsorace lady sidd da hajy xubby data jawo simran dake bari kamar mazari fitsari na bin jikinta tana tafiya kamar antsoma kaza aranda tay waje itama...

suna fita kofar ya rufu kiriff shima anyi anyi yaki buduwa karshe ata jikin windon wajen suka taru suka tsaya suna leken abubuwan al ajabi da ke faruwa aciki...

banda alhaj attah da sultan daya mike da kyar suketa kkrin su kwaco wuyar nur da aka shake babu kowa sai janet data saka karfinta duka ta rike gadon javeed dake shaking kamar ana kadashi da karfin gaske

mazan suna krin jan nur anma ji suke kamar they are competing againts the army of 1000 na zaratan maza wanda suka shakureta atare

basuda wata mafita suna ta addua itama nur din da aka riga aka shakure adduar kawai takey tana fitarwa daga bakinta da kyar kafin can ayatul qursiyyu ya ceceta dan sai da sukajata tun daga gado har kasa da wuya snn suka saketa da kyar

janet tun da ta rike gadon a kangare awajen bata ko motsi dan asalin sumewar tsaye tay dan tsoro bata taba ganin wnn bala'in ba

aljanun sun sake ma nur wuya kenan ta fado kasa a rakwabe tafara wani irin tarin jini alhaj da sultan ne sukazo da gudu zasu dagata akasa sai sukaji rigib akasa janet ta fadi kasa kamar an tureta

kamar an tsakura nur ta mike tsaye ta kalli mirror sai taga wani irin fuska me mugun abun tsoro da igiyar canular da aka sakama javeed a hannun dodon yana mata dariya kusan ihu tay tajuya kan javeed din tana isa tahaura kan gadon sai taga igiyar canular kuma awuyansa an shakuresa da shi sosai

wani irin tsorataccen kuka take duk batasan ina karfin hali ke zuwa mata ba, a gurguje ta saka hannunta tafara kokawa da canular tana karanta ayatul qursiyyu da karfi muryanta na rawa cikin kuka she is nearly traumatized dan ita daya take gani sauran nasa gani

amma dataga su sultan da alhaj sun tsaya agefenta suna tayata karatowa sai taji ta samu kwarin gwiwa saida tay ayatul qur'siyun kamar guda bakwai snn taji ta capko canular da karfin tsiya ta cireshi a wuyar javeed taga wai harya masa shati da sauri ta jefar akasa ahankli ta rungumeshi tana tsorataccen kuka..

nan sultan yay saurin kunna radion karatun qur'ani wajen yay wani irin shiru iskar sai ya bace baaat nan kofar bayi yafara buduwa mr aqeel ya fito agaggauce da kwaryan a hannunsa kafin nan windown daya budun yakullu dakansa, kofar waje ma ya bude su anty suad suka shigo kowa cikinsu ya firgita yana salati mr aqeel ya daga janet akasa ta mike tanata addua simran da hajy zubby sam sukaki shigowa suka tsaye a kofa jikinsu na rawa rawa...

alhaj attah ne ya rike kirjinsa jin yarasa meke masa dadi
sultan ne ya matso ya dan jawo sa sukafita waje dan ya samu ya dawo hayyacinshi

aman jini duk ya batawa nur jikinta tanata kuka wamda Akaro na farko da anty suad taji mugun tausayinta tazo ta dagata takaita bayi tafara zuba mata ruwa tana wanke bakinta dashi...
[01/06, 21:32] BLUE💙: EPISODE 76
AREWABOOKS@SURAYYAHMS.



sun jima a bathrum din kafin anty suad din ta kyaleta tay alwala tafito ta samu har an watse janet tanata goge baqin jinin javeed dana nur din dake yawo akasa wanda tay amansa sai few domestic wokers da suke share broken glasses da cire expensive frame din da suka faffashe.

nur tana fitowa ta samu they are almost done with the cleaning bata daddara ba ta dau kwaryan ta wanke ta sake zuba clean magarya water babu dandanin tsoro aranta sabida ta mugun yadda da Allah, nan tayi karatun ayoyin duka tazo ta wanke jikin javeed dashi har ta gama ruwan bai lalace ba.

bayan nan tace ma janet tace ma na'ima ta kawo mata sabbin kayan sawa.

nan da nan janet ta fita after a while suka dawo da na'iman ta kawo mata har da ababen shan ruwa dan already har an kira sallah magrib

nur tana canza kaya madara me dumin kawai tasha snn tay sallahn magrib na'ima ta matsa mata saida taci abincin kadan bayan tagama tayi zaman diris tacigaba da karatun qur'aninta
dan gabaki daya gidan jimamin abunda ya farun kawai akeyi akasa, wani dan uban borin kunyar fitsari a tsaye ya hana su simran lekowa cikin falon alhaj attah inda ake tattaunawa ynxu haka sune kawai suke dakinsu haryanxu basu fito ba

acan sama kuma nur ce kawai da likita da kuma janet sai nai'ma data kawo mata kaya da abincin wanda bata jima ba ita ma tafice ta koma bakin aikinta.


daga falon kasa daga sultan sai alhaj attah sai su anty suad da lady sid anata magana akan abunda ya farun wanda ya girgiza kowa takwas na bugawa sai ga sallamar Dr ruqayya

ta shigo da kayan aikin ta cikin sauri alhaj attah ya mike tsaye suna kallon juna da mamaki dan daga irin kallon data masa yagane ba lafya ba.

anty suad ce ta wani harxuka har zata fara tada sabon hatsaniya dr ruqayya ta tsaresu da sabon labari dayaso ya sake rudasu inda itama abubuwan al'ajabi suka dinga samunta

dan duk motar data shiga sai ya baci ko ya kama da wuta kuma duk wanda yay yunkurin bata abunda taje nema sai wuta ya kama shagonsa frm no where wutar yake zuwa, tace dakyar saida tanemi taimakon mlmi snn akace mata baqaqen aljanu ne suke attacking inta tace musu hakanan tay ta biyar asarar da ta mawa masu shagona tanamai cigaba da neman abunda taje nema da kyar ta samu shine ta taho

jikin kowa ya dada sanyi dadin

67 / 112