Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
ajere sai da ta rubuta masa sako yafi guda takwas amma duka babu wanda yaje bare tay tsammanin samun amsarsa.
jingine kanta tay da jikin gado ta dinga kuka danji take kamar kirjinta yana tafasa zai faso waje yay bombinh ya tarwatse dan ko kadan batasan zafin soyayya ba sai akansa ji take kamar yanxu ne tasan me akeji in za'a rasa masoyi..
she tried her best to convince herself cewa komi karyane bazata kuma yanke wani hukunci ma javeed ba har sai shi javeed din ya gaya mata da bakinsa cewa razia yake so zai aura ba ita ba..
daga haka tamike da kyar ta sauka akan gadon jin koinanta ya kage da rauni sau kuma takoma kan kujera tazauna ta dan jingina kanta kadan sann ta lumshe ido tafara tunanin last words dinsa da sukayi waya ranar birthdayn munayayya.
wasu irin kalamai daya dinga gaya mata masu tsananin dadi da shiga rai da jin cewa ita kadaice mace a duniyarsa.....
[05/05, 19:38] BLUE💙: EPISODE 31🦋
Arewabooks @SURAYYAHMS
tunda ta lumshe ido cikin wann tunanin wani irin rauni ya kara lullumeta bata san sanda hawaye suka kara wanke mata fuska ba.
she is feeling like she cant even breath witout javeed harma yaushe za'ace mata duk wannan ruwan soyayyar dayake mata karyane? ji kawai tay bazata taba yarda ba
tana cikin wannann yanayin taji karar bude kofa, ahankli tabude lumsashun idanunta jin qamshin turaren razia ya mamaye dakin atake.
jikinta amugun mugun sanyaye tafara share hawayenta kallonta razia tadingayi da yanayin rauni har ta karaso gabanta sann ta tsuguna tareda riko hannunta da sanyin murya tace little sis ashe har kin tashi how are feeling ya kikejin jikin naki toh? are u feeling any pain,..in hada miki drugs dinki zaki sha?ko in kawo miki abinci ne pls me kike sha'awar ci i wll get it for you..
murmushin dole nur ta kakalo tanamai dada damke hannun raziar da wani irin karayar zuciya ahnkli tagirgiza mata kai da disasshen murya tace "i am okay an-razzy kawai kaina ne dama yakemin ciwo and its probably bcos i slept too much kuma dama period dina ya zo..
mikewa daga tsugunen razia tay ta dawo daf da ita tare da jawota jikinta ta rungumeta kadan cikin yanayin lallashi da mugun tausayi tana patting bayanta ahankli, sunfi minti biyar ahaka basuce ma junansu komi ba
addua kawai razia take aranta Allah yasa ace javeed zai samu sakonta duk dama ta turane kawai ta layin servant dinsa dake jikin code card na weding fittings din but she just dont care ta san koma yayane hala dai dole ne zai ji...
after like 5-7 mint of silence tadago nur din sukaje bathrum wani irin rawa rawa jikin nur din yake sabida zafin ciwon kai da zazzabi, haka ta tayata cire kaya tadora mata soft white towel snn ta hada mata ruwan wanka me dumi ta kyaleta tay wankan
ita kuma ta dawo cikin bed room din tadan gyarashi sama sama after some minutes tasake shigowa ciki tafito da ita tamata komi ta bata inner wears da pad da wani green colour satin plain gown marar nauyi tasaka ajikinta.
daga nan tea me kauri ta hada mata da kyar nur tay kurbi biyu suka zauna cikin sauke ajyan zuciya razia tace "Nur can we talk?
dagowa nur tay suka hade ido ta gyada mata kai ahankli..
kai tsaye razia tace nur dan Allah ki gaya min meye ya faru..pls ask me anything abt him wallh zan gaya miki, i know ure hurt bcos of what i said at the balcony kuma har yasa kikaje zaki kashe kanki i feel really realy guilty, pls talk to me sis, bana son hakan ya kuma faruwa dake har na bar duniyar nan
dan shiru nur tay dan atake idanunta yakara cikowa da wasu sabbin ruwan hawaye jitayi brain inta da zcyarta sun hadu sun mata caaaaa sai zzxfr muhawara da juna sukeyi duk ta rasa wanne ne zataji guda daya..
is like some part of her is breaking into pieces with pain and anger, wani bangaren kuma is tryin hard to deny everything nd stay very calm sabida wann mugun kaunar javeed datakeji acikin ranta.
itakanta bata son ta amince da javeed zai iya aikata mata haka, kuma kai tsaye takejin bazata iyama zargin sa akan cin amanarta ba sabida bakaramin makahon son shi takeyi ba...
toh ince dai duk rintsi duk wuya duk kuma rashin samunsa a waya nan da kwana kadan dai zai bayyana kansa agidansu tunda dai shima zaizo ayi daurin aurensa inma shine angon...
ji tay gara ta cigaba da kasancewa acikin pain of denial harse ranan daurin auren yay yazo gidansun snn ta gansa ido da ido inyaso duk wani borin da zatay masa ta masa agaban sa amma ynxu kam batama san mezata kama a matsayin hujja tarike ba he dint call her or text her kuma bata san ko shi javeed dintan bane ko ba shine ba koma yaya ne kawai de she just dont want to belive it.
jikinta kara mutuwa yakeyi inta tuna yadda razia take balain sonta takuma damu da ita she knw razia bazata hurting inta da gangan ba. to kenan bei kamata itama tay mata wani hukunci akan abinda ya shafe tsakaninta da javeed mufasa ba.
kanta na kallon kasa hawayenta nata zuba tahau saka wayann tunanin a kwakwarlta
harsaida tagama gamsar da kanta da kuma zuciyatta kafin nan tashare hawayen ta tadago muryanta a sanyaye sosai tace "anty razia dan Allah kiy hakuri..i think, i just over reacted abt wat you said to me at the balcony jiya...
cikin wani irin lumshe ido da budewa razia tace nur karki sake kimin wani karya.. pls let discus dis, did u knw javeed mufasa that much da dakike cewa hakan? ko ke aranki kina tunanin..
cikin wani irin datsar numfashinta da ggwa nur tace anty razia wallhi bana tunanin komi akansa i really trust him and know der must be some sort of a mistake toh wayasan ma ba nawa javeed din bane..i am sure ma ba shi bane toh in ma shine mubar wann maganan lets pretend like it neva happen har sai na tabbatar, dan Allah anty razia dont say no to me..aciki muryan kukan ta karasa.
razia tay shiru batace komi ba can dai ta dago takalle nur din ganin har yanxu kukan take cikin sauke ajiyan zuciya tace nur bazan iya ba, i cant watch u cry like dis nide kinga gaskiya zanjeni falo na gayawa baba sede dik abunda zai faru ya faru...
da sauri nur tahau share hawayenta dake zubowa cikin magiya me ban tausayi sosai tace haba anty razy toh na dena kukan kuma zan ci abinci zan warke.. nayi miki alkwari i wll be with u akowani step na shirin aurenki
..but you have to promise me zamubar wann maganan harse bayan na hadu dashi munyi magana duk abunda yayanke mana tsakanina ni dashi sai muyi amfa i dashi wajen deciding din gayawa baba abuda muke ciki daga baya.
anty razzy pleasee dan Allah Dan Allah
banason kowa yaji wann maganan what if i am wrong abt it..
kituna fa kece kika koyamin cewa na iya riqe emotions dina, ki tuna alkcin danazo gidan nan banda kowa banda komi i was rlly feeling traumatized but u stood by me and help me with ur own time and money...
kece kikayi sanadiyar da nazama mace na kuma san kaina, bai kamata na yanke miki ko shi wani hukunci batare danasan meke faruwa ba...
Duk da prolong magiyan da nur ta dingayi ma razia dakyar raziar ta bar maganan nan ya wuce
dan bakaramin kashe mata jiki nur takeyi ba da tausayi itade duk tagama lura da cewa gabaki daya nur is not herself again she just want to live in denial dan batason ta jin wann zafi da radadin.
wani tunani tay aranta tace toh tunda abunda nur din take so kenan gara kawai ta kyaleta kodan ma tasamu lfya snn tasamu daman tursasata tanacin abinci dan karta rame ko wani ciwo yaje ya shigeta.
sun jima a dakin suna magana amma haka nur taki sam har razia ta gaji tay shiru dan ta lura hala inba shi javeed din dakansa yazo ya furta mata komi dabakinsa ba bazata wani amince ba..
well, is a matter of four days now. duk yadda takejin ciwo da kuma nauyin ganin yar uwarta nur acikin wnn yanayin hakanan ta daure tabiye mata suka yanke hukuncin binne duk wata magana data shafi javeed mufasa a tsakaninsu da zimn harse javeed din yazo
kafin susan me zasu dora agaba.
bayan komi ya lafa suka fito waje iyayen bakaramin dadi sukaji da sukaga nur ta dan sake jikinta ba sede yanayinta na rauni yasaka suke tunanin kodan hala batagama warwarewa bane daga
incident din ruwa data samu yasaka ta zama bata da karfin jiiki sosai.
wann daman razia take amfani dashi wajen tursasa mata cin abinci hakanan zata daure agabansu ta tuttura amma tana komawa dakinta zata amayo su waje tasss.
dagata dayan bangaren kuwa sosai maganganun mrs hasina yay mugun tasiri a wajen laylah badon komi ba saidan dataji ance mata nur firdaus ta zama wata abar kwatance har tana da ma'aikata.
hakanan itama ta fara kukkusawa tana shiga sharaf babu shanu musmn yanxu dataga adnan baiya shiga tsabgarta itama tuni tafara warewa tana bin taron siyasa na surkuwanta koda kuwa za'ayi mocking inta a zageta hakanan take daurewa kawai dan asan da ita koda ma itama zata zama abar kwatance kamar nur firdaus
a sannu sannu cikin satin nan kuwa har tay sabbin abokai wanda suke tsammanin ai tunda ita surkuwan hajy mairam ce toh zasu iya bin kafarta su samo wani alfarman
itama ahaka ta bude wani sabuwar dabara
da cuccusa kai tare da kuma taimakon mrs haseena takan rubuta letter office din hajy mairam abata financial grant da zatay mobilizing wani organisation na mata.
tafara aikin kenan bata jima ba rayuwa yafara mata sauki
dan har kudi tana samu awajen wanda suke neman gindin zama daga waje.
wann yanayin ya bata daman rage zama a gida,itama tana dan fita ana damawa da ita gashi yanxu mrs haseena ta saka mata ido sosai akan batun gyaran jiki da shan maganin gyaran jiki dana kiba sabida kawai ace aure ya karbi yarta tay dumul dumul acikin arziki.
washe gari a kaduna nur tana zaune akan dadduma dan ko bacci bata samu tay jiya ba zallahn tunanin javeed dinta kawai ta dingaji komi ya zame mata kamar sabo dan duk ta rasa toh mesa bataji wann kalar ciwo da wahalar akan adnan ba.
yauma hakanan tun da ta idar da sallah dinga neman layinsa
tana turamai sako amma duk basa shiga
kuma duk sanda tay hakan sai kaga ta raunata tanata kuka
amma dake tasan razia zata iya shigowa any moment sai yau batay kukan me yawa ba wanka tafada ta shirya cikin wata simple fitted gown
na sky blue atampa
tagama shirin kenan saiga razia suka gaisa
ta tambayeta lfyarta snn sukaje kasa sukayi breakfast.
still ana gamawa ta taso tazo ta dinga kwaza amai dan kwata kwata batajin sha'awar komi in ba javeed dinta ba.
ta fito daga bayin kenan agajiye zata dan kwanta saiga hajy bilqis ta shigo tare da razia....
tashi tay zaune dan bata son su gane me take ciki hajy bilqi tace"Allah sarki auta nuriii sannu wallh sai naga kamar haryau baki gama dawowa hayyacinki ba, toh gashi yau za'a fara bridal fittings din razia gobe za:a yi wankan amarya, jibi lalle, sai kuma daurin auren already kunga mun bata lokaci yakamata ace tunjiya akaje akayi fittings din nan dan kunsan dinka kayan amarya ba abu kadan bane toh kode akira su molly ne su rakata inyaso ke ki xauna kihuta tunda jikinki babu karfi
nur na shirin amsawa da ehh, caraf razia tace "a'a mummy gaskiya nafison komi zanyi inyishi da yar uwata nur, zan kirasu mollyn amma sai munje can nur ko bazaki rakani ba?
murmushin dole nur ta kalalo tace zanje anty razzy nima nafison nabiki
hajya bilqi tana dariya tace toh masha Allah ai haka mukeso dan banajin dadin ganinki haka nur pls ki sake jikinki kinji?
ahnkli tace toh mummy...anty razy muje dakinkin to mu shirya saiki kira su mollyn..
daga haka suka mike suka fita atare razy ta turawa molly text amma sai tace mata tazo tare da su frankie kawai, amma karda ta sake tagaya musu komi game da auren..
molly bataso hakan ba amma sanin halin razia yasaka hakan kuwa akayi nan ta kira frankie da muna tace musu kawai zasuje wani wajene, nan da nan kuwa suka hadu rico ne kawai bata gari dake ranar taje lagos ita da mum dinta.
tunda suka shiga dakin razia ta xaunar da nur agaban mirror
ta cancara mata wani irin mayyar cool make up a fuskarta tay kyau hatta goshinta na kyalli irinna na amare kai kamr gasar kyau zataje..
wani bakin straight skirt da burgendry v neck top na burbery nur din tasaka ta dora long chester coat akai shima na burbery din snn tay rolling kanta da bakin veil tasaka bakin cat eyed sun glasses waidan ma kar ana saurin gane halin datake ciki
kwalliyar da razzy ta mata tay tsaf tay wani irin kyau kamar babu komi aranta haka ta fito tana qamshi sosai
side bag dinta da booth dinta iri dayane bakake na balenciaga
she look chic and calm ita kadai tasan meke tafe acikin ranta
sede mamaki ta dinga sha dataga razia bata wani cancanre kwllya tay kyau kamar yadda ta saba ganinta ba
daf an kirasu cewa motocin sunzo zasu fito taga razzy ta dau wani drugs ta sha hae suka fita tambayarta take ko bata da lfya haka razzy tace mata ai tunjiya take zazzabi ko bacci batay bama
nur ta dinga jera mata sannu sukaje sashen iyayen suka musu sallama aka saka musu albarka.
koda suka fito harabar gaban nur ya kuma faduwa musmn data ga tabbas su janet ne sukazo wani irin rawa rawa jikinta ya farayi abainar jamaa dan dolenta taja gefe ta dinga ambatar sunan Allah har saida abun yay mata sauki snn ta dawo.
motoci uku akazo da shi,direct janet tazo ta fara gaishe da nur din
nur ta amsa ta bayabo babu fallasa taga dai kamar wa ita suke komi aranta tace kode
basu san ba itace bace amaryan oho.
hakan nan taki shiga motarsu tace lallai nata motar kawai zata shiga dan dolensu su ka haqura suka kyaleta hakanan motocinsun suka sakota atsakiya tana tuki amma hawaye na sauka mata duk dama tasako karatun qur'ani a motar dan ya dauke mata hankli amma ganinsu janet sosai ya dada rushe mata dan dauriyar data fito dashi.
wani private waje suka shiga acikin wani estate a GRA barnawa
securityn mufasa was all over, is like siyan wajen gabaki daya akayi na musmn dan kawai ayi bridal fitting
da sauran shirye shiryen amarya...
tsabar kyaun wajen zaka dauka wani five star hotel ne ga komi na duniya ga su blue swimming pools,ice cream spots da coffe da kuma sauran kayan cime cime ga uwa uba suya spots agefe ana gasa kaji da balangu wajen ya gama cikewa da qamshi me dadi.
suna shiga aka kulle gate din nur na kkrin kimtsa kanta sai taga su janet sun sauko sunzo gaban motatta cikin ladabi tabude mata motar snn ta karba mata jaka
zata amshi wayatta tace mata a'a dan haushi ma suka fara bata ganin sunbar razia acan ita sunzo suna wani damunta da formalities sun wani mamayeta kamar itace amaryan
ba razia ba.
kusan ince ranta a mugun raunace ta shiga wajen kowa na haba haba dasu all the way from london aka kawo agent na designer na Ellie saab da kuma zuhair murad dan su zauna suyi aikin jera diamond crystals ajikin kayan amarya
Nur ta kasa gane komi ga abubuwan sun fara bata mata rai sosai ganin yadda kowa awajen yake mata bare bare kamar wata sarauniya kome za'ayi sai antambyeta
kuma daga ta fara korafi sai razia tace mata kawai tay haquri ai sister amarya ma amarya ce...
haka razia ta nemi waje ta kwanta tace kanta da cikinta na ciwo dan haka nur ce zatana reprsnting inta akomi, nur ta dingaji kamar purnishing inta kawai razzy takeyi amma kuma dake taji jikin razzyn ya dau zafi sai batace komi ba
za'a fara kenan sai gasu molly da frankie da muna sunzo wajen
take wajen ya zama so lively frankie kamar zai suma tsabar dadi dan haduwa dayayi da two fashion icons and designer da baitaba mafarkin zai gansu ba
acikin raha da wasa da dariya aka dan gaggaisa nan da nan molly taje wajen razzy tazauna ta fara cika ta da tambayar ko lfya taga tazo gefe guda ta kwanta da zaazbi ajiki bayan kuma ita akazo gwadawa.
cikin sauke murya kasa kasa razy tace ma molly karda ta sake kowa acikin frnds dinsu yaji wnn maganan sabida tasani sarai ai ba aurenta bane auren nur ne so deirs no need to play games.
hmmm kawai molly tace..taja bakinta tay shiru dan haushi razia ta fara bata sosai.
can saiga su nur din sunzo tawajensu, dake ma ganinsu frankie da muna ya saka wani haushin datakeji aranta ya ragu mata sosai yasa ta dawo tana yar fara'a.
jikin frankie na rawa yace ma razzy ta basu kanun labari fitting din waye haka aka musu suprise...?
kafin molly ta bude baki razy tay saurin cewa ai bridal fitting na nur ne...
nur ta kara jin wani irin haushi tagwalo ido waje kenan zatay magana, muna tasa wani irin ihuuuun murna ta rungume nur tahanata maganan ma gabaki daya..
duk rantsuwar duniyan nan nur tamusu cewa ba aurenta bane na razzy ne amma sukaki jinta a tunaninsu kunya takeji dan zatay aure at young age.
musm ma frankie sai tsokanarta yake razzy kuwa tanuna musu dagaske take sai cewa take ai dama in zatay aure kamar nur ce zatay so its al the same vice versa kawai nur tanajin kunya ne.
razy tamaida abun kamar wasa amma har ga Allah dagske take tace musu sam sam komi anan wajen na nur ne har abin dai ya dawo abun wasa.
molly kam tayi shiru dan bakaramin takaici hakan ya bata ba
musmn da muna da frankie suka dau abun da zafi, suka janye nur zuwa wajen designers da dress decorators din akaje aka fara juya nur kamar waina ana gwadata tsala tsala
tun agida razy tay mata wann wayo bata gane