Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
fararen labulayen windonsa
dan kawai yaji iskar sanyin safiya, karar ruwan teku da kuma kukan tsuntsaye.
Dakin nasa yafi karfin Ma ace dashi daki don yana da wani irin girmane its like an apartment on its own dauke da faluka manya aciki.
A tsakiyar dakin aka kafa masa Wani irin sharbaben oak wood with bronze colour king sized royal bed dataji lallausar katifa da aka lailaye da pure silk dark red cololur tsadadden zanin gado me bargo.
tun bayan daya dawo daga sallan asubh a masallacin gidansu bai motsa ba, zaune yay akan lafiyayyen kujerun dake dakin idanuwansa a lumshe dan kwata kwata baici komiba bayan cimen da yay a jirgi da yamma haryanzu bai saka komai a cikinshi ba, Ahalin yanzu ma bai jin sha'awar cin wani abinci.
Jiyay zuciyarshi tana yawan harbawa da wata boyayyar feeling na kamillen zakuwa da soyayyar nur firdaus me yawa dan kamar bazai kaiga karkare batun auren san nan yau ba haka yakeji..
bayan ya kammala latse latsensa a wata customised military system saida yadau lokaci yahuta sosai batare da andameshi ba Can Kafin nan ya tashi yafita wajen motsa jiki inda janet tasamu cikekken damar shigowa dakin domin ta hadamai ruwan wanka.
acikin zuciyarshi har Allah Allah yake ya gama kominsa ya fito dan yasan yaune kawai zai iya sanin next step dinsa sabida already wata mission me tsananin hatsari da kuma muhimmanci datake jiransa agaba kwata kwata baiso yaje mission din nan batare daya mallake nur firdaus a matsayin matarsa ba... .
yasan kuma inhar ya samu amincewar familynsa akanta ayau toh komi zaizo masa da sauki tunda dama ahalin nasu basa wani shirmen bidia a aure daga sunje sunyi yar introduction angana da iyaye an karbesu toh next time zasu zo daurin aure ne direct ayishi tareda daukar amaryansu a lkci guda sudama basu wani hidimar daurin auren ahalinsu abayyane.
As usual yana bada bayar kuwa cikin dan kankanin lokci janet ta shigo cikin dakin ta kimtsa, daga nan bayinshi ta nufa tay gaban Wata katoton mirror mai dauke da handler na kowani irin kalar kayan gyaran jiki mayuka da turaren wanka a wata show glass na jikin bango
Gefe dashi akwai scrolls na fari da milk da kuma dark blue colour soft cotton bathtrobes body towels dinsa kuma zallan fararene babu wani surkin launi ajiki wanda ajikin scrolls din drawers ne masu yawa na aje wasu kayayaykin gyarar fuska da tarkacen goge kai da hannu.
full size jaccuzi shine a tsakiya,da kuma site din transparent auto- rectangular glass wall shower stand dake wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba, Ko mai dai a bayin white nd golden colour ne hakama bayin ya kasance yana da fadi da girma sosai dan har flat screen tv da diner akwai agefe.
Nan danan tay setting masa ruwan wankan da luxurious bathrum themometer shi in warm nd relaxing tempureture snn tabi ta sassaka drops na almond essential oil da zai taya warware masa kasala da gajiya sai drops na rosemary oil danyay relaxing din muscles dinsa tareda sakamai nitsuwa.
Koda ya shigo farin towel mai kauri kawai yadora abisa kugunsa snn ya shiga wankan yadade yana nutse acikin ruwan wankan idonsa a lumshe yanamai jin balain dadin ruwan ajikin shi.
Bayan ya kammala komi ya fito Baidauke wani lokci ba yay yen shafe shafensa ya dada gyara kwanciyar lallausar suman kanshi da caved sajensa da gabaki daya suka dau sheki
snn yashafa kamshin original gallivant brooklyn musk a dukka fatar jikinshi kafin nan yabi da tsadadden turarensa na mufasa noir mai tsantsar kama jiki da wani irin sanyin kamshi mai dadi mai kuma ratsa zuciya da kwakwalwa.
coffe colour pantone shot da wani lallausa kuma hadadden coton v neck napoliana shirt mai nitsatsen blazer da limited edition smart watch na patek philip yasaka wanda gabakidaya komi ya dauke surar ginannen jikinsan casss casss provocking some deep sense of stability nd calmness.
daga nan wani simple coffe brown loafers ya saka a kafafunsa yay kyau bana kadan ba.
Cikakkiyar nitsuwa da dedetuwar hankli duk natare dashi ayayin da yasa harman fitowa..
ahankli ya bude kofar dakinshi Har Lokcin mr aqeel ne kawai a tsaye yanamai jiran fitowar san..
wnn azabbaben sanyin qamshin turarensa mai rikitarwa dake bibiyarshi a duk inda yaratsa ya fara sanar da kowa fitowarshi.
Ratsa dogon hallway din sashen nasa yay Cikin sanyin taku mai tafeda sassanyar kasaita batare daya kalle kowaba ya nufo kofar da zatakaishi ainihin falonsa takasa kai tsaye yaratsa ciki mr aqeel din na mara masa baya. hadaddun manyan faloka masu amsa sunansu faloka sunkai uku suka ratsa kafin suka bar sashen nasa.
Direct suka nufi hanyar bangaren mahaifinshi wanda ke gefen dama da nashi bangaren.
wani irin shiru gidan yadauka kamar babu wasu halittu acikinsa dake duk inda javeed zairatsa babu wani servant ko maid daya isa yahada hanya dashi.
gidan nasu is not a Luxury home da aka saba gani,infact its a typical mafian fortress basu wani saka masa kyale kyalen kayan duniya Da wasu tarkace ba
furniture da komina gidan is in simple cozy dark colour irin strong vintage moud woods din nan wanda zasu iya yin shekaru aru aru batare da sun girgiza ba, they are mostly historic sculptures dat have strange traditional meanings and secret symbols. saidai ko wani sashe anayinsa ne da wani irin girma da yelwatan fili tun daga kan extra large halls, family rooms,art galleries, drawing rooms,great rooms da wasu irin secret doors daba mai shigansa saisu, ga wasu irin sharbeben home offices, da libray me science laboratory aciki wanda shima ba maishiga ciki saida card na cikakken izini..
vintage dark golden colours are the most powerful colour for wealth nd power dan haka yasa design din yazama soo lush nd cozy kominsu is soo lucrative and calm ba irin flashy luxurious din nan ba.
javeed Yana tahowa sashen wani autom. security robots masu tsaron kofar sukay marmaza suka bude mashi kofa yana shiga mr aqeel yaja ya tsaya daga waje.
A nitse Ya kare ma ko ina kallo dan Wani falon ne na alfarma da babu motsin komai aciki saina karar ac dake tashi a hankali
Azaune ya hango mahaifin nasa cikin shiga ta Alfarma da kasaita, kyakkwan Dattijone sosai da Hutu da tsantsar power yagaji da ratsasa manyan kaya yaska wacce suka zauna daram ajiknsa
Kallo daya yayi ma dan nasa da ruwan idanuwansa masu tsananin kwarjini da darsa tsoro dataso rudewa da tsantsar farinciki yayi saurin daidaita kansa acikin wata takaitacciyar murmushi mai balain sanyi da ratsa zuciya.
da sallama abakinsa ya shigo ciki tareda dan rusunawa akan dadduma dede inda aka aje wani tray dake cike da y'ay'an zaitun.
Kamar yadda suka saba cikin girmama wa da kaunar juna suka gaisa snn yaji lpyarshi.
cikin nitsuwa suka soma tattaunawa akan meeting dinsa najiya daya tsareshi dan dama kwata kwata javeed bai sanar da mahaifinsan komi gameda sabuwar mission dinsa dayake shirin zaije ba.
badon komi ba saidan
yasani cewa mahaifin sa baida wani babban maqiyi dasuka mugun tsanarsa aduniya sama da wanda zaije aikin akansu wanda ake cemusu, "THE NAGAZA BROTHER HOOD. mafian counter part on drugs and ammunitions they run control of slave girls da kowani irin manyan gidan karuwai all over the world.
babban maqiyan ahalin nagaza a duniya basufi ahalin MUFASA sede tunda mahaifiyr javeed tazo rasu mysteriously they have been keeping their distance batare da ansan dalili ba waau suna harsashen basu son ajona musu lefin mutuwartan ne.
dan kowa yasani cewa babban burin nagaza brothers a duniya shine sukashe ahalin mufasa daya bayan daya tunda mahaifyar javeed ta rasu idonsu ya dawo kan matar da javeed din zai aura, shikuma javeed jiyake idan bai shafe tarihinsu a duniyaba hala bazai taba hutawa ba dan yasan his future wife's life is already in a mortal danger itace ynxu first predicted target dinsu.
ahalin mufasa suna da maqiya masu yawa aduniya amma tsanar dake tsananinsu da nagaza brotherhood is very personal beyond business dan cewa suke mahaifin javeed da kakan javeed din wai sune suka kashe musu iyayensun and they vent on taking close family membr lives as their own revenge shiyasa mutuwar mahafyr javeed bakaramin dadi yamusu ba duk dama basu suka kasheta ba.
duk iya tambaya da mahaifinsa yamasa bai sake yabashi wata clue nacewa ya amshi wann mission dinba
dakema zancen auren sa kawai yafi zakuwa dashi yanxu.
suna tsaka da wnn tattaunar saiga kirar Anty suad ta video call da babban pc screen din dake falon
aka jonata dukansu suna kallonta zaune a offishinta na gida as usual ta sha wani irin cooperate wear da fararen sunglasses.
yayantan kawai tafara gaisarwa ya amsa ta da fara'a.
snn javeed yagaisheta ta amsashi ciki ciki dan haryanxu bata gama saukowa ba sabida jiyane suka jirashi da maganan auren amma yakama yaje meeting dinsa, ita kuma dama abun haushi sam baya mata kadan bare ma da jiya taso ace lallai ayi maganan auren agaban amintaciyar surkuwar gidan wato lady saddika saddik dan tare suka gama kulla duk wani salon makircin dazasu shimfida
already ta riga ta tay list na family datake so javeed ya zabe matar aure aciki amma jincewa wai har yakawo zancen wata na daban yasaka tace ma yayantan lallai itama zata shiga cikin maganan auren
domin kuwa aranta tanaso ace koma wacece javeed din zai aura tazama tana a karkashin ikon ta da mulkinta, ko kuma ta zame musu kamar wainar da zasu iya juyawa duk yadda sukaso tunda javeed dinne yake iya saka hannu akan komi na gidan gashi bawai basu hadin kai yakeyi ba.
suna gama gaisuwar kai tsaye mahaifin javeed yafara bata damar gabatar ma javeed nata zabukan..
wani dogon list ne agabanta na manyan mafia families sunkai goma sha biyar aciki
kowa ta karanta sunan familynsa sai tafadi irin tarin power da yawan dukiyrsu da kuma ta inda ahalin mufasa zai amfana in aka hada auran.
javeed da tuntuni ya nitsu yagama karanto manufarta aransa sai ya zamo kowanne sunar family ko yarinya takira kai tsaye baya cewa bai masa ba amma kuma zaifito da wani boyayye ko mummunan tarihin su ko wani bad busines reputation nasu ya fedesu karara snn yay disqulifyin dinsu dasu...
kai karshe dai harta gama kirar list din ba asamu ahali daya zuwa biyu da basuda wani boyayye kuma mummunn matsala ba, dan daga masu money loundryn ne, saimasu illegal money looting, drug cartels, secret sex tracking, sai kuma manyan matsafa da barayi sai masu tarin boyayyun basukan banki akansu which are all not good for thier familys reputation.
Anty suad kawai ta nade hannu ta tsaya tanata kallonsa dan bata san ta inda zata faramasa tsiwa da masifa ba dakema baibiyo da maganan tahanyar nuna musu zakewarsa akan nashi zabin ba..
atake babansan kuwa ya hau goya masa baya akan duk wani shaidojin daya gabatar musu akan duk wanda ta kira...
shikasan Mahaifin nasa yariga yagane cewa yar uwarsa suad din tanada wani boyyn manufa, she is just after more power and control, so kawai take tamaida auren javeed din yazame musu kamar wani alakar business deal inda zata zama itace da full underground control, tasani in har ta samu daman juya matar da javeed zai aura toh babu shakka duk wasu abubuwa masu muhimmci na ahalin dayawa zasu dawo hannunta da kuma danta kamil mufasa kamar yadda takeso..
tunda aka kore nata list din, maganan ya kare awajen sai bata sake cewa komi ba ta zuba musu ido har saida mahaifin javeed yagama musu bayani akan duk wani nauin bincikensa da yay akan ahalin Alkhadi muhammad ciroma.
dake yana balain son
cikama dansa burinsa shi binciknsa sama sama kawai yay baiko duba halayyar yaran ba shide akan iyayen nasu kawai yay nisan bincike.
haka javeed ya dingaji kamar zai nitse kasa dan farinciki jin yadda mahaifinsa ke fadin kyawawan tarihi da halin girma dake cikin wann ahali ryt frm their great grand father mutanen kirki ne masana addini da suka shayin shugaban ci na adalci,snn ahalinsun ba masu kashin tsiya bane
...alhaj attah yace da acema basu tsaya akan imani da gaskiya a lamuran rayuwarsu ba dayanxu suna daya daga cikin manyn masu arzikin kasa da akeji dasu,
yay magana akan hali na gari da irin yawan shaidar gaskiy da rikon amana da akai ma mahaifin nur firdaus in paticular, in such a way da yasaka anty suad din jan wata hatsallen tsaki batare da ta san tay ba cos all she can hear are names of ppl dat are powerless nd poor dats all
ranta a harde tace yaa Attah toh anji mutane kirki ne dat aside, toh ya maganan yarinyar can Doctor kannuwar matrka zubaida dan naji kishin kishin zancen cewa suna nema da javeed.
alhaj attah yace "toh gashi nan dai saidai ki kara tambayarsa kiji nide yace min shi baisan da wann maganan ba.
wani irin harde rai tay tace"kenan ita doctor din ne take son shi, shikenan kuma shi baya kaunarta?but waht is wrong with her,wallh saddika tanuna min hotonta awaya last week aikuwa tamafi min zubaidan ai tsari ..isnt she a better choice? ni kwata kwata bangane me javeed yake nufi da jawo mana wasu bare acikin ahalinmu ba...ga gida bai koshi ba sai akaiwa dawa..
javeed ya dauke kai yay kamar bayajinta
dan daga inda yake tsugune reflection din tray din seeds din zaitun dake gabansa na hasko masa kalar mayafin hajy zubaida data mannu da kofa ta musu labe.
yasan hala ko sunbi kafar hajy siddikan ne yasa ake son cuso maganan simran aciki yi yay kamr baiji me take cewa ba ya kyabe baki.
nan ta dada hatsala tafara masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, yaa attah magana fa nakeyi da javeed amma kaga yana daukemin kai koni sa'ar shi ne toh wallh ka gaya masa ko marigayiya uwarsa bata raina ni ba bare shi..this is some serious talk..
dede nan javeed din ya dago kai kai tsaye yace.."Aunt, ive made my own choice wacce kike magana akanta itama ai bare ce, ina ganin tunda har baki da matsala da ita bai kamata ace kina da matsala da wata baren ba ko dama mun hada family da simran ne bansani ba.
a masife tace hey young man, karka gaya min maganan banza anan..snn kasani mahaifnka bashine kadai zai yanke duk wata hukunci akan aurenka ba gara ma ka bini ahankli. i am trying to make a good choice for you here.
yay shiru baice mata komi ba tagama bambaminta, toh ai shikenan tunda ya nace akan nashi zabin ni zanje moroco zanyi magana da ancestral mother koma yay muka kare zakuji.
amma ina so javeed ya tabbatar mana dacewa bai dau wannan shawarar aransa dan saboda tausayi ko son rai ba,sabida aurensa wani abune da zai iya shafaar mutuncin ahalin mu duka, kaima kasan dokokin ahalin mu na Mufasa Ko maida zamuyi sai munbi mun tabbatar da kawo cigaba da kariya wa mutuncin ahlinmu...
alhaj attah yace “To, in hakane zamu bukaci haduwa dasu akan lkci,mother bazata hana auren javeed ba tunda har nay bincike kuma tunda Ba auren mutum daya muke yi ba idan muka aure diyarsu mun Aure ahalinsune gabaki daya sai mu tabbatar cewa an azurtasu ta inda zasu iya daukar nauyin sunan Mufasa azuriarsu kafin mu kulla alaqa.
cikin lumshe ido da budewa yadda zaka san maganan ya mugun kona mata rai muryanta ciki ciki tace
"'..another charity case?..dede nan javeed ya dago kai ya mata irin mugun kallo
....cikin rolling eyes tace toh toh toh naga danka yafara harara na nikaina ma na ciwo, tunda dama kunce gaskiya yariga yakashe sauran ahalin kenan da wanda yaran suke zaune a hannun sa kawai zamuji
..nan take ta zaro wani chechqe book ta yagi paper daya cikin kyabe baki tace since i am incharge of our finances here..lets see wat we can do..,
kai tsaye tahau rubuta cheque din sann ta kallesu tace this is 20 billion naira..
takalle javeed da kasar idonta snn tace "non negotiable price, aiya ishesu sutada kashin arzikinsun da akace suna dashi dn gaskiya iya abunda ahalin mufasa zasu iya rubuta musu kenan.
javeed baiko dago kansa sama ba yay shiru yanajin mahaifin sa yana yar dariyarsu ta manya...yace haba suad 20billion naira ma ahalin da zasu bamu mata?...ohhh pls u can do better. let make it 50-80.
dawani irin jiji dakai da giggiwa tace i am sorry but no, yaa wann din kawai ya ishesu, ahaka fa bawai baza mukai musu kudin sadaki dawasu abubuwan bane..
nan tafara kukkuni tabi taharde ranta muryanta kasa kasa tanamai cewa hmm aisune zasu moremu bamune zamu moresu ba kawaide dama yaaya kaine ka saba da bin bayan danka toh Allah yasaka dai kar ayo mana zaben tumun dare dan naji kace yan mata biyu a gidan.
alhaj attah baiwani kula shirmen kananan maganan tan ba yace kedai kawai Ki shirya sheik haidar da kuma khaleefa ko kamil maza susaka ranar ganawa da ahalin yaran nan a kaduna dan a tsaida maganan
abamu ranar daurin auren kawai.
snn ya kalle javeed yace kaikuma ka tabbata wannan ba soyayyar zuciyarka kadai bace Ka dauki girman sunanmu da mutuncin wannan ahalin.
ahankli javeed yace
“Insha Allah, Zan tabbatar da hakan.”
daga haka suka karkare maganan auren, hajy zuby dake musu labe tanajin motsin fitowarsu tay marmaza tabar wajen takoma sashenta taje takira yar uwarta Dr simran awaya tahau gaggaya mata abun da aka tattauna.
sede abun yau bae wani darasu sosai ba dake ma tun last week suka fara ganin haske, dan kamar yadda saratu volkner tafada musu hakanan kuwa ya faru, dan lady saddika sadik ce ta fara kirar hajy zubyn kwasam akan batun zancen dr simran, har yakaiga tahadasu da simran din awaya suna dan gaisawa kullum.
satikan da suka wuce sosai suke cikin farin ciki da annashuwar ganin sunsame kan lady saddika wacce ita tadingakai zancn simran din kunnnen anty suad mufasa
haka hjya zuby ta dinga kwantar ma Dr simran hankali da cewa aiyanxu kam ta zuba ido kawai ta gani
nasara kam kamar yazo hannunsu,tunda manyan matan ahalin mufasa sun dawo gefensu snn ma ai ahalin da javeed din zaiyi aure aciki ance talakawa ne basuda wani arzikin azo agani
wann bayanin sosai yadan faranta ma Dr simran rai yakuma cire mata tsoron razia dan atunaninta samun kan javeed ymxu zaizo musu dasauki sosai muddin sunada support din lady saddika da kuma anty suad mufasa...
[02/05, 21:37] BLUE💙: EPISODE 27🦋
Ata dayan bangaren kuwa gabaki dayane mrs haseena shariff