Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
kauyanci tana kalle kalle dan wajen ya mata kamar suna cikin wani serene environmnt a America. dan banda first class decoration da akayi tun daga gate din shigowa wajen is huge and eco friendly koina yay green gwanin ban sha'awa.
cikin wani babban dakin baki na alfarma aka basu masauki ita da jadidah aka aje musu servant guda biyu yan mata sanye da ceremonial uniforms suna musu duk wani abun da suke bukata
karamin nitsuwa wann layla takasa samunsa ta kalle nan ta kalle chan dan duk uban jiji dakai da mulki datazo dashi saida kashi ashirin aciki yaxube kasa warwas musmn ganin quest room din da aka basunma fa bata taba ganin irinsa ko da a mafarki ba.
jadidah kam relaxing kanta tayi akan lumsatsen kujera tanata ciye ciyen su meat balls sushi shawarma da wasu hadaddun mocktails da aka kawata gabansu da shi.
ata dayan shashen quest falo na manyan kuma hajya mammy ne ababban kujera ta zauna cikin hadadden wankarta na lafaya data sabayi yau ta saka golden and red colour me kauri irin indian murlberry silk din nan tay kyau sosai kamar wata prime minister.
itama sosai tazo da tarkacen kyautukan na al'ada dan iyaka wann al'adar ce kawai ta aminta dashi,saboda tafi kowa sanin kalar yawan arxikin da danta attah yake dashi, tunda har akace za'ayi ma nur firdaus wnn hidimar tarban tasann rabonta nayin arxiki ne a duniyan nan kawai yarantse wanda hakan yay mata dadi aranta bana kadan ba.
gefe da ita dakin su hajya sa'a da hajy bilqisu ne wanda sune kadai ake bawa darajar uwayen amarya, kusan anko sukayi na leshuna suma pure gold da wani irin Maroon head and shoes sun sako limiited desing na jaweries dan kawai sudaga ma yarsu nur darajarta sosai.
ata fannin amarya kuwa saida su anty suad da su hajiya amira suka tsaya kyam akanta har aka gama shiryata snn aka bata french salad aka sakata taci ta koshi sosai akay sallahn axhr.
karfe daya da rabi na wucewa da kadan zallan matayen gidan mufasa aka fito in grand style duk sun saka ankonsu ta dark army green material daga original kamfanin kaya na swavroski,sunyi pairing dinsa da pepper red shoes and custome heads kowacce wuyarta da hannunta da clutch dinta da white or red diamonds ajiki.
iya arzikinka iya kalar haduwarka saidai dukkan sun nan bazaka iya cewa waye yafi wani haduwa ba.
motocinsu na alfarma mercedez benz sunkai goma sha biyar suka hallara dasu wajen biki
suna sauka a motocin aka mika nur a hannun lady sid da hajya zubaida akan sukaita inda su hajiya mammy suke domin tay gaisuwa snn afara gabatar da wasu formaliies na al'ada dan zuwa 2pm za'a fara hidima kuma za'a kareshi ne before 5:30pm sabida yau da dare zasu wuce morocco for the main mufasa initation culture.
matar sultan mimie ce ta rike ma nur jelar kayanta har suka shigo sashen suka rusuna kasa suka gaida hajy mammy
snn suka shiga can ciki suka damkata a hannun su hjya sa'adatu Kirjin nur lokcin kamar xai balle da murna data ga kanta agaban su hjy sa'adatu
wanda suka damkatan suna ficewa nur ta yaye mayafin da tsalle ta rungumesu duk suka taru suna kuka kagansu zaka dauka shekara hamsin sukayi basuga junansu ba
babu kalar tambaya da tarairaya da basu mata ba ganin zumudin murnan nasu baxai kare ba ya saka suka nitsu suka kara gyara mata jiki suka rufeta fess hajy bilqi dama da shirinta na turare tazo
haka ta kunna turare na alfarma tabi jikin nur din snn suka fito da nur suka damkata hannun hjya mammy kamar yadda aka musu bayani angama mika nur kenan sai gasu layla da jadida sun shigo
duk layla tabi ta rude sai kalle kalle takeyi kamar batacciya
sun shigo dede hajy mammyn tana yi ma nur adduoi kenan su hjy sa'a sun kewayeta suna amsawa da ameen
hakan yasaka su layla basu samu damar zuwa kusa da nur ba gashi bawai sanin fuskokin matayen kawuntan tay ba,tazo da jiji da ka da giggiwa amma koda taxo taga yanayin kowa sai atake taji ta dawo insecure ganin kamar kowa yay wanka ne daya kere mata tunani danko bikin gaggan yan siyasa da suke xuwa bata taba ganin irin wann shigar ba.
time nayi hajy mammy takara rufe fuskar nur da veil snn ta jawo hannunta suna tafiya ahankli iyayen nabin su abaya za'aje hall din hidima jadida tabisu abaya
layla ta kasa motsi ta zuba ma nur firdaus idanu kamar bata taba ganinta ba dan azahirin gaskiya ankere fuskanta ne da wani irin nude spiking make up daya gama daukar kalar fatar ta ya fallasa sirrin kyaun ta fiye da na kullum.
Flowing hauticultural gold and caramel hand stiched wedding dresss din ta daya zube kasa yana binta An tattare sumanta an karkare shi da diamond Corchet pin, trnsprnt long and flowing head wrap din ta dogo ne kuma sharara sosai yana sharar kasa.
Ga wani tsadadden rock stud pump akafar ta dayaji jan lalle wanda da ace za'ayi auction dinsa ba karamin kudi za'a kwasa ba.
haute weding attires ba na kananan masu kudi bane dan shikansa ma wani asset ne.
layla dake tsaye kamar burar giwa ji tayi kamar wuta na bin gangan jikinta da wuyarta dan wani zafi kirjin ta ya shigayi kamar ana tsikarar ta da wuta. ganin ta tsaya adaskare kamar kungi yasaka jadida ta dawo ta fixgo hannunta sukabi bayansu hajy mammyn
laylah Bata tashi sumewa da kishi ba sanda aka shigo dasu babban hall din da za'ayi hidimar dan wani dogon rail ne me zig zig shape an cikeshi da snow white flowers da pure blood red roses here and der
dake asaka ma nur professional shapers ya kara fidda shape din ta uwa zana ta akayi da hannu.
Wani salon kyau da haduwan da tayi sosai ya girgiza ma kowa kwalwawa
layla Bata san ta ina nishi mai zafi yake kufce mata ba duhu gabaki daya yana neman ya rufe mata ido.
ahalin mufasa da bakinsu sune akasa cikin hall din all dressed in the most expensive and luxurious wears kowa ya juya yana kallon shigowar nur...
all the other mufasa brothers are wearing dark grey kowa da kalar nashi adon sai na sultan light bai shiga kalar nasu ba da few quest da sukaxo musu code din bikin is eida gold, army green or black.
javeed yana tsaye wajen babansa da wasu amintattun abokan baban nasa da suka sakoshi a tsakiya kayansa is lure black made frm all this persian theme haute knee drop royal court, typical dress na olden days persians simply very dramatic, elegant and regal wanda kagansa zaka dauka angon wani arab kingdom ne his face is glowin and shining yana ji kamar yaune xaiy aure
yan uwa da abokan arxiki babu wanda baixo da xumudi da kuma shirin bikin ba.
wasu suna tsaka da hira aka sanar da fitowar amarya duk na xaune anata karkata kai ana dan leko breath taking flowery and slow bridal enterance na tawagar amarya..
A karon farko da wajen ya dauki shiru na musamman kenan anty suad dama ta gayyato wata shaharriyar mawakiya daga can middle east wacce tayi tsaye akan red capert har saida aka fara sauko da amarya snn ta bayyana da mic a hannunta Kerarriyar Muryanta daya ratsa ma kowa tsikar jiki tana sharo wani wakar soyayya da harshen larabci musmn da aka fara saukowa kasa da amarya izuwa fili..
hajiya mammy ne agaba tana janta ahnkli iyeyenta kuma na gefen ta jadida na tayata rike jelar gown din..
matar sai wani irin kirarin soyayyah take cikin sautin waka mai tafiyar da yanayi
...,kowa sanda yaji ya mike yayi tubarkallh dan kuwa kayan da nur tasaka da irin kwalliyar da akayi matan ba karamin abun kallo bane..
anty suad tafara jin kamar kanta zai fashe musmn dataga bakin su sun shagala suna yaba kayan amarya wanda ita ta shiryashi.
kafafun Layla sai harhadewa yake abayan jadida tana jin jiri jiri kamar zata fadi kasa daga sun hada ido jadida zata watsa mata muguwar harara tsanan me tattare da murmushin mugunta
ana sauko da nur kasa gaban su mother za'a mika musu ita wato mawakiya tayi wani zazzafar stanza awakar da sunan Nur firdaus tana maimetabcewa auren soyayya da babu mai rabawa tana yi tana cewa aure yana da dadi ne in mutum ya so mai sonsa...
laylah da bawani sosai take iya tuna larabci ba amma taji wannan stanzan kuma jitayi kamar da ita kawai akeyi
haka kawai tabi ta hade rai idonta ya ciko da hawaye saidai ba wanda ma ya ke kallon ta bcos she look local ko jadida ma tafi tahawa kaya me tsada ..
cikin girmamawa da gaisuwan ban girma hajy mamy da su hjy sa'a suka mika nur wa mother hauwa ayayinda duka matayen dake wajen suka gewayesu
wani irin muguwar guda me kara wata mata acikin quest dinsu takeyi daya mugun girgiza zuciyar mahassada kamr layla da kuma hajy xubaida subiyu ne awajen gabaki daya kamar basa cikin hayyacinsu.
alhaj abbkar zai murmushi yake yana hawaye aransa yana jin inama mahaifin nur din yana raye yaga yarsa dan duk wani karammawr uba mashi kawai ake bayarwa.
har saida aka mika nur wa ahalin mufasa sann iyaye maza suka taho da ango dayake jin kamar baxai iya jira ba suna isowa yataro matarsa dakan shi in a very special way.
Dawani irin salon nuna kauna mecike da karramawa yanemi izinin karasawa da ita wajen zamanta Kowa awajen yasha mamakin yadda duk girma da kama ajinsan ya ke rawan jiki akan matarsa.
layla tunda taga javeed ta kuma tabbata wai shine mijin nur din hawayen datake dannewa zirrrr yafara bin kuncinta she look lost and alone gashi ko kulata matayen kawuntan basuyi ba sabida ko a fuska ma basu santa ba ita ma bawai saninsu tay a fuska ba.
ahnkli javeed ya xaunar da nur akan farin kujerar su na pure crown anty suad da hajya amira suka xo da wani katon hand woven morocon red and golden royal carpet madaidaici aka shimfida agaban nur firdaus.
daga nan mother ta dauko leg anklet din da ake sawa na bridal acceptance azuriar sun ta bawa javeed ya tsuguna kasa ya dora kafarta akan cinyarsa snn ya daura mata anklet din a ankle din ta.
bayan nan daga jadidah sai mimie kawai aka bari suka xauna agefenta javeed ya tsaya tare da sultan da sauran brothers dinsa
sai asann alhj abbkar ya lura da layla dake tsaye ita daya yay ido ma hjy sa'a akan taje ta kirata suna xuwa yace musu ai layla kenan, sunata mamaki, ita kuwa laylan tsabar ba acikin hayyacinta take ba sama sama tamusu gaisuwa hjy bilqi kam taki sam ta saki jiki da ita hjy saadatun ne dai babu yadda ta iya suka ajeta agefensu.
ana samun zama aka dan zantar da jawabi game da al'adar mother da hajy mmy sit dinsu iri daya ne amma ita hajy mammy a wajen dangin amarya ta xauna sai matayen familyn mufasa agefen mother hauwa.
lokacin Kishi kamar xai kashe hajy zubaida ganin kamr nur ta ta maye gurbin ta a xuciyar surkuwanta wato hajy mammy
lady sid kam shiru tay kamar bata wajen dan tasan abunda zai faru anan bazai mata dadi ba. nur will be super wealthy today and dats just a great heartache mata babu karya.
tasan mufasas sunayin wnn al'adan ne kawai dan su bawa newly weded bride dinsu kayan duniya iya kayan duniya ta inda arxikin zai isheta taji koda maqiyinsu yanu na mata awani kudi awaje bazata saida sirrikan ahalinta ba, komi da suke zantarwa a ahalinsu yana da boyayyar manufa da ma'ana
lokaci yayi na bude fuskan amarya za ayi al'adan nasu da initially wa yarinya budurwa akey dan its believe dat sai anyi wann bikin kafin ango zai yi saduwar aure da amaryansa toh tun a farko hajy mammy ne tace musu hakan bazaiyu ba, anty suad kuma sunyi zaton nur din ma bazata kai wnn matsayin a gidan mufasa ba sai gashi komi ya canxa salo
Duka Sun sha mamaki da javeed ya bita da kiss agefe da gefen kuncin ta batare da yaji nauyin kowa ba
dan hakan yana da meaning a al'adan su nufin matar sa is no longer a virgin shida ita sunriga sun dawo daya wanda hakan ya fara bude fili ma abunda ya tara su.
main event na bikin shine kowa daga cikin ahalin mufasa xaixo ya siya jinin da nur ta xubar na budurci da wani abu me daraja
amma banda kudi, it maybe stones, jeweries,compnies, shares. da sauransu banda dai kudi dan sukan dora darajar mace ne sama da kowani irin kudi.
Laylah tanajin yadda hjy mammy take ta bayanin hakan masu hajy sa'adatu kowa cikinsu yana masha Allah tubarkallah.
layla sai taji takara rudewa wai mafarki take ko gaskiya? wata nur din ce virgin? bayan tasan har cikin shege tay, jikinta sai rawa rawa yake ta rasa ma uban waye zatay ma wann gulman a tunaninta ko hala ma basu san labarin rayuwar nur bane
tana cikin tunanin wanda zata iya samu anan ta toni asirin nur
koda ma bikin nan zai tarwatse caraf sai taji hajy mammy tana cewa wai Ai bame zama akan wancan kujerar da nur din ta zauna sai budurwa
sukansu hajy sa'a sau sukaji kansu ya kulle sosai gashi suna jin nauyi suyi tambaya..
laylah kuwa kamar wacce aka tsikareta tamike taje ta wajensu jadidahn
sai yanxu nur ta ganta ido da ido bakaramin mamaki tasha dataga laylan ba saikuma ta tuna cewa jiya mrs haseena tace xata mata suprise ko hala laylan ne suprise din oho.
dacan har security zasuy awon gaba da ita nur tace musu ai kanwartace sai kawai aka barta tazo ta xauna tare dasu asama kusa da jadida Allah Allah take wani yaxo ta tada tarxoma ta tonawa nur asiri dan sosai wann uban kudi da hidimar yake neman ya haukatata
idonta sosai ya rufe da baqar hassada da tsinannen kishi data kasa dannewa..
Suna dan hade ido da nur nur din tay mata murmushi me sanyi saidai tun bata mayar mata ba kawai sai ga mother ta iso wajen sheik haidar mufasa yana rike da ita
ana binsu da wani katon silver tray wanda aka shimfida kyallen bedsheet na jinin budurcin nur
firdaus da mother ta saka aka nannade mata shi da kyau aka boye wajen jinin
akai mother ta xuba
Wasu duwatsun heart of eternity diamond, extemely rare ko kera wani abun wuya dashi ba ayi ba gungun dutsen ta dora akai a matsayin tukucinta
dama can bisa al'ada sai wakiliyar ahalin ta dora kyautan farko atafin hannun nur tayi jawabin darajarsa sn ajeshi akan dadduman da ke gabanta daga nan kuma kowa acikin ahali zai kawo nasa ajere.
mother na isowa wajen hajy mammy ma taxo da nata 3 hefty boxes of rare jeweries da wasu gift wanda sanadiyar jawabin farko na mika kyautar daraja dake bisa bedsheet din da mother tayi ne layla ta kara jin matsanancin rudewa jin yadda ake cewa wai tukuicin jinin daren farkonta kenan
kuma yadda tabasu jininta haka zasu bata dukiyarsu da darajarwarsu.
bayan ta bata stone ta hade mata wasu kyautaka na sarkoki da abun hannu da shares na business na man fetur anan nigeria, kafin hajy mammy itama tabata komi da aka kawo sai anbudeshi akan wann carpet din kowa yana kallo..
cike da nuna so da kauna hjy mammy ta hademata da gidajen gona snn tasaka mata albarka aciki.
daga nan alhaj attah ya kawo nasa gift din set of triangular mousseife red diomnds da blue fancy vivid diamonds stones da share na computer technology firms guda biyu a singapore snm yasaka mata albarka.
anty suad tazo ta saka original wittels bach diamond jeweries da wasu mayun gwalagwali na fashion da akayi su da pure gold tabata pent house a hawaii snn ta saka mata albarka ta wuce
snn aka dawo kan sheik haidar shima jeweries na duka na 5 precious stone din nan ya bata, medauke da ruby, topaz, emirald
, gold, and diamond all in thier boxes da wani crypto wallet, khaleefa ya bata wani katon box na customed collection of rare gold watches d katon fili a ikeja lagos. kamil ya bata varieties of bracelet, anklets, da abun wuya yan tsirara na casual dressings da sukaji white diamonds ajiki snn ya bata 2 customixed G wagons.
hjya amira ma ta kawo mata set of jeweries da stock share na new food industries a mexico
wanda kafin kabude ido dadduman da aka shimfida agaban nur yacike da kyautuka da box box na stones da varieties of jeweries da gifts
javeed yana saka nashi kalar kyautar aka rafka guda iya guda albarka da adduoi samun zaman lafya babu wanda ba ayi ba.
lokacin layla hawaye kawai take xubarwa kamar ruwa tana numfashi kamar me ciwon iska dan tun hannunta na rawa rawa tana daukar kan dadduman da video kai har takasa iya daurewa abun yabi ya dame mimie dan kukan baqin ciki da layla takeyi yay yawa
ta dan tambaya jadida ko lafyar laylan jadida ta kalle laylan ta fashe da muguwar dariya me ban haushi tace ma mimie ai haka nan layla take idan taga yar uwanta na cikin damshin daukaka ita kuma kukan murna kawai take iyayi.
mimie kuwa har wani tausayi taji laylan ta bata she genuinely tot kukan murna kawai layla takeyi ma nur, lokcin hankalin nur baikansu sabida rububin masu bata kyauta.
har saida aka gama sann hjy mammy ta jagorance su alhaj abbakar da matayensa suka dauki nur din daga wajen zamanta suna zagawa da ita sashen wajen zaman ahali domin nuna godiyarsu bisa al'adar hidima.
saidai dan xuwa da sukayi da nasu kalar tukuicin yasaka bakaramin dagawa nur din kima da daraja ya karayi a idanun duk wanda suke wajen ba
Jadida tay tay da layla akan ta tashi taje tabi tawagar familyn su layla taki sam sai rabxa kuka takeyi tanajin kamar da ruwan barkwanon duka duniyarn nan ne gabako daya ake tafasa mata gangan jikinta dashi.
cewa ma jadida takeyi wai inta tashi tsaye jiri zai kayar da ita beside aima kawunsu abbakr nur firdaus din kawai suka sani itace yarsu ita uban miye zataje ta musu acan.
mamakin layla ya gama cika zucyar miemie jin sunata musu da jadida har ta tsoma musu baki sublty take bawa laylahn shawara akan tamike kawai taje ta samesu ayi komi da ita dan for