Chapter 80 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   80 / 112

237K to 240K   out of 335.4K words

suka fara bayani saidai bata kan nur din suka sauka ba

hjy zubyn was mockingly making fun of shirun javeed in dis situation dan badama nur firdahs ta kai abinci bakinta sai suta jefa masa baqar magana direct musm lady sid, simran da hjy zuby and even worst da hajya suad tafara cewa kamata yay ma nur tay dutynta kawai amma tadena zaman cin abinci dasu tunda kowa yasan in 3 days time ita ba komi bace a gidan nan.

yadda take maganan bluntly kuma directly insultive a fuskar nur yasaka javeed yaji ya mugun hatsala da bacin rai ayanayinsa ya daka ma anty suad din tsawar da saida abincin dake gabanta ya zuba mata ajiki

mamaki ne ya rufesu duka yadda yay mata tsawan kamar bai taba saninta ba

da wani irin rashin kunya directly yace mata ta iye bakinta dan nur firdaus din is still his wife bazai lamunta ba kuma bazai kyale kowa yaci mutuncinta agabansa ba he wont stand to be disrespected.

jikinta har na bari ta buga table din da karfi ta mike tsaye amugun zafafe tace mishi not anymore, ive called nd reported the crime to the Ancestral mother duk wani karyanka akan matarka ya kare javeed tunda mother tace she is coming. and this crime must be purnished Wallh wallaj wnn kwailar yarinyar sai ta bar gidan nan kuma babu abunda ka isa kayi mana, yatsarta har na bari take nunashi da shi tana dada cewa gaskiyane baka son ji amma kasani your darling wife whom uve planed to stain our familys reputation with will be casted out in front of every oda family member gara ma kasan cewa na kira kowani member na family bamai rufa mata asiri..yadda aka shigo da ita bada son ranmu ba haka zata fita out of our lives and neva to return.

javeed yadan runtse idonsa yadda yay crushing din glass din dake gabansa into pieces da hannu sosai yakara basu tsoro baice komi ba ya ja kujerarsa da bacin rai yabar musu wajen.


ahujajan alhaj attah ya biyo bayansa nanma sukaje suka kara samun wata sabanin saboda ihun da yay ma anty suad agaban kowa baban nasa cewa yake dolene yana bin doka, nd now tunda ma suad ta kawo solution kawai ya shirya akan batun maida auren sa da simran din sabida asamu family stability karya zamo akwai wnn rainin atsakanin su.

jin hakan ya dada sakawa javeed ya harxuka ya masa rashin kunya sosai snn yace bazai aure simran din ba kuma ya wuce dakinsa abunsa yabarsa a tsaye.



bayan faruwar hakan wani rashin mutunci suka tsira ma nur firdaus, kayanta da duk wani abu nata suka fara batun cewa zasu saka naima tafara tattarawa,

simran harda sawa akwace keys a mika mata, ahaka ta saka aka kirawo nur ta kawo keys din komi dake wajenta snn ta mikawa hajy zubby agabansu duk abunda suke mata bata taba kuka agabansu ko tay wani magana ba sai dai shiruntan yay ta basu haushi da takaici.

suna cikin kwana na biyun sakon mutuwar saratu ya kara zuwa kunnen hajy zubaida

ranar shagali akan shagali sukayi jin cewa tun ranar da simran takai maganin mutuwa wa javeed wani mutum me kan zaki ya fito a madubin tsafin saratu ya shake wuyar saratun harta mutu snn baban saratun ma yana chan yana kwance a cikin ICU a america yana kwance kamr wanda baya numfashi.

ranar har rawa sukayi da simran a daki dan tsabar murna dama sukadai ne suka san sirrikansu a duniya.

hajy zubaida ta riga da tasan tsarin dake jikin javeed din shine yakashe saratu murus.

simran bataso da akace aurenta da javeed zaizo mata ahaka agaggauce ba but she dont care tunda tasan babban burinta ne zai cika a goben.

batare da ta sanar da hajy zubaida plan dinta ba tabi zugin babban kawarta dr na U.K data kawo mata wann cigaban
dan yanxu kud da kud suke da juna.

marmaza tasa simran ta kwashe sauran 4 million us dollars dake asusun ahalinta kaf ta hau saye sayen wasu ridiculosly expensive weding dressws da jeweries da famlily gifts komi tay odernsu sai datay fata fata da duka kudin kamfanin gidansu ya zamo baifi 800 thousan dollars bane a acct din ahalinta gabaki daya

aganinta inhar ta auri javeed gobe ko irin zoben nan daya bawa nur firdaus kyauta ya bata zata iya maida kudin kamfaninsu harma da kari dan haka bata damu ba.


tun bayan abunda ya faru a dinning javeed yay fushi sosai ya share uban kowa

shide yana ta kkrin ganin an samu masa komi dayake son ji kafin gobe dan haryau mr aqeel bai gama aikin da ya aikesa a abujan ya dawo ba.


kwana hudu kawai aka dauka ana case din amma atake rayuwar nur agidan yabi ya dawo wani iri

ya zamo bata kukan saidai ta zauna shiru cikin kunci kowani lkci kawai addua takeyi bata ita cin abinci sai dai madarar da su cocunut drink ko kunu ko in naima ta takura mata tasha fruits ko syrup dins da suke bata wanda suma dakyar take karba tasha gashi tsabar damuwa period dinta har yau daya cika 3 days zuba yakeyi each time anxiety da intense depression yay hitting inta.



ata fannin razia kuwa duk uban jiran nan da tasha a dubai bata wani samu ganin balarabiyar nan ba sai only son dinta sheik Ashraf abdallah daya ke mugun ji dakansa yama ki ya kula batun raziar yanata ja mata aji dalilin haka kawai sai taji haushi ta dawo UK cikin daren bata ko jira ba


da baqin cikin ashraf din tadawo gidan tun wajajen 4am na safiya dakyar tasaka kanta bacci still kuma ta farka 6am tay sallahn fajr sai nan ta ke lura da wasikar da molly ta aje mata akan coffe table da fake loan documents na bank na cewa taci bashi ne tay freeing inta daga debts da fine inta snn ta koma nigeria amma zata dawo.

haka razia ta dinga tsallen murna ita daya duk a tunaninta cewa taimakonta molly tayi
saidai tay tay ta sameta awaya taji how come ta samu bashi me shegen yawa haka amma inaa sai bata sameta ba.

she was soo happy, har ta koma bacci jikinta ya dan warware, sai kuma ta fara tunanin hanyar da zata biya bashin dan so take koma yayane ta aje batun fashion da film ta koma gaban iyayenta kawai.

can da yamma tana zaune email ya kara shigowa daga dubai cewa ana nemanta

..da kamar bazataje bama sabida kalar walakncin da ashraf dinnan na ya mata jiya bayan uban jiran mahaifyarsa datayi, saidai babu yadda ta iya tana so tafara tara kudin da zata biya bashin da molly taci mata ta rufa mata asiri.

hakanan ta dauki jakarta da dan sauran canjin da mollyn ta bar mata ta kama hanya ta koma dubai takama hotel dan ta zauna acan taga me Allah zaiyi.


within these few days
wahala kawai ta dinga sha awajen Ashraf din sabida koda kowa zai mata tambaya wajen interview me sauki sai ga shi ashrf kuma yana tsawwala sabida sosai yakeda labarin career flobs na razia da yadda taki sam ta zubar da mutuncin kanta dana addininta dan ta yi achieving dreams dinta

ashraf kyakkawan balarabe ne saidai mahaifinsa was a native of ethiopia wanda yasaka tsabar kyansan yay na daban acikin larabawan ma.

mahaifyarsa sayyida hanifa ta mallakke multi million naira abaya and muslim dress codes top fashion brand a dubai da saudi arabia.

saidai dake basuda wata kwarayryar top international muslim model da zata zame musu kamar show stopper yasa kasuwa yake baya baya dake dama arab fashion world is sumhow limited to muslims or only arab elites and royalties of middle east and other muslim countries.

abaya da gowns da matan musulmai ke sawan ba abu bane da duk duniya suke da intrest akai sosai

tun razia bata san da ashraf abdallab ba shi ba yasan da ita, shine dakansa ya kuma kawo tallarta wa mahaifyarsa har saida ta amince masa ya saka aka kirata tazo duk dama bata san shine yay duk wann ba dan baima mata kama da me saukin kai ba.

tun haduwarsu bai taba mata dariya ko murmushi ba sai zafi da yake hada mata takota ina...

razia duk ta dauka waidan sabida kyansa da gatarsa da kuma kalar kudinsa yake wakalantata bata san bakaramin sonta yakeji aransa ba

kwananta biyu a dubai tana zuwa auditioning a karkashin ashraf a rana na ukun ne ya dauketa aiki batare da yabata abunda take so ba ya bata role din stylist, ita zata dinga zabar kalar make up din da za'a na yiwa model dinsu da kuma styling din, da kuma yadda xasuna fitowa dashi..

bata wani damu ba bcos the pay is very good saidai koda ta rokesa zataje dauko kayanta a UK sam ya hanata yace bazata je koina ba... later later in d day kuma taga ya aiko da wani assistant dinsa hotel din datake zama da bank golden card dinsa aka kaita shoping ta saya duk kayakkin datake so.

ita duk ta dauka duk wai formalities na aikin kamfanin ne batasan da kudinsa ake mata komi ba.

hakama yasaka aka bata daya daga cikin gidajensa fully serene and furnished komi ma raguwa ya zamo mata kamar sabo

kowa awajen aikin na sonta sabida ilimi da wayewata amma ko kadan ashraf baya sake mata fuska haka dai ta fara sabon rayuwarta anan



**** yau ya kasance rana na karshe da aka bawa javeed domin tattaro na shi shaidun dan gobe da sassafe mother hauwa daknta tace musu zatazo dan javeed ya gabatar da shaidar agabanta sai kuma su masa aure da simran in komi ya tabbata.

basu san hakan ko gaskiya bane amma labarin da su anty suad suke yayatawa kenan dan alhaj attah shi ko kirar mother hauwan ma baiyi ba dan baison yadda suad take zarginsa akan cewa shine ya lalata tarbiyan javeed da yake yawan sakaltashi ana masa alfarma fiyeda kowa


yau dake rana na karshe ne shirin biki da simran takey har ya wuce misali inda hankali zai dauka

tsabar zumudi sai duk tahau rabe rabe da kyauta da kayanta da su jewries dinta tafara zagawa tana tsorata wokers din gidan tana cemusu daga gobe kowa zaigane kurensa a hannunta musmmn ma naima da janet datafi tsana


javeed baya gidan tun safe nur kuma tay wankan sallah dake tunda ta samu bacci jiya tafarka taga jini ya dauke mata kawai sai tay wanka ta debi damuwar komi ta aje agefe dan har ta gaji da tunani.

koda na'ima ta kawo mata batun su anty suad akan tattara mata kaya tace mata tabari kawai ita bata bukatar kayansu nata kawai zata maida mata su ajakarta guda daya datazo da shi.


kansu naiman a kulle yake dake basu san asalin kan batun dake faruwa ba, amma daga yanayin da suke ganin javeed da nur sunsan wani babban matsala ne kawai akasamu tsakaninsu

dacan kamar zata tattara kayan sai kuma ta barsu ta fita taje ta samu chef faiza ta karbo ma nur wani irin tsumi me masifar kyau da akay da saiwar itacuwa, kayan qamshi, ruwan rake, goron tula da zuma, mazarkwaila.


hakanan nur ta wuni tana shansa dan chef faiza tace mata ai zai wanke mata mararta tunda ma jiya ta gama fidda dattin period wann ruwan tsumin nur ta wuni tana sha sabida yana da masifar dadi yadda sukayishi da original herbs kuma basu cika mai zaki sosai ba

sai can da yamma data gama naima ta kawo mata hadin fresh water melon fruits da apple da glass in madarar da sukayi masa hadi sosai shima ta sha har ta samu isassehn bacci da tunanin gobe zata rabu da javeed dinta na har abada kodama zai huta da fitinar data jawo masa kwana biyun nan.


yau kowa yana sashensa anata budurin nur zata bar musu gidan mufasa washe gari da sassafe


lady sid da hajy xubaida atake suka dawo kamar kawaye dan damuwar hjy xubaida baifi ta cuccusa maganan auren simran a bakin su dan taji nawane zasu bada sadaki da sauran yan formalities na kudi da mufasa sukeyii dan yanxu haka ita kudin ne babban damuwarta so take sai komi ya lafa bayan auren ta tada makirci ayi ma simran babban hidimar aure dan tasan ahalin mufasas suna iya azurtaka da billions of naira a rana daya.

hajy zubaida tana harkan hasashen kudi while simran din tana can dakinta tanata rabe rabe kayanta masu tsada tanata shirin tarban kayan aurenta da super expensive express designers sukace mata zai iso yau da yamma liss wajajen bayan isha'i.

zumudi akan zumudi duk ta kasa nitsuwa nan tahau tura ma javeed text yafi dau goma tana cemai ai destinynsu na kasancewa ma aurata dayake gujewa ne yaje ya auro nur firdaus shine ya dawo kuma in sha Allah itace matarsa snn babu mai rabasu har abada.
[11/06, 16:39] BLUE💙: Arewabook@surayyahms

javeed bai taba kula sakontan ba amma duk yana karantawa yay tsaki, sai can da yamma ana daf za'a kira sallahn magrib lokacin duk matayen gidan sun sha wanka an fito falo suna dan raha akan maganar sabida kowa yasan gobe warhaka nur firdaus din da suka tsana zata walakanta agaban kowa snn zaa koreta korar kare.

ana hirar sai washe baki simran takeyi dan sosai tatara dumbin walakanci da bakaken maganganun da zata gaya ma nur din gobe da safe in komi na auren su ya kammalu dan kusan bata san meya ma tafi zumudin gani ba, aurenta da javeed din ne koko kalar walakancin da ta shiryasu zata ma nur firdaus gashi agaban kowa komi zai faru wani dan uban farin ciki takeji aranta bana kadan ba


ata fannin nur kuwa bata wani jima da fitowa waje dan shan iska ba aka aiko wai anty suad din tana kirarta a falon, dama can wani riga da skirt tasaka na atamfarta golden colour ta yafa mayafi madaidaci nan ta fito zuciyarta na bugawa dan duk sanda taji kirar anty suad tasan baqaqen maganane da walaknci zai biyo baya..

ta wulga kasan main falon kenan javeed ya hangota, ido kawai yay ma janet ta shigar masa da wasu manya mayan romantic gift bags da yaxo dasu, ya tsaya yanata kallon nur din tana tafiya kanta kasa duk sai yaji tausayinta ya kamasa sosai. dan wani bin yana ganin kamar harda lefinsa dabai tsaya yadda ya kamata ya ga menene ke kumshe acikin rayuwarta na abujan so deeply ba bayan sultan yasha bashi shawarar yayi hakan amma yaki sam ya duba toh gashi nur dinshi is now facing the consequences of his error.

dacan kamar zai wuce ciki dan agajiye yake dake tun safe ne baya gidan sabida yagaji da jin hayaniya gashi yanata tsammanin feed backs tako ta'ina amma ko daya bai shigo hannunsa ba tukuna tsayawa yay yanata kallonta tana tafiya ahankli har ta sauka kasa bada son ransa ba amma sanin cewa bazai wuce anty suad ke nementa ya saka shima ya yanke hukuncin biyota abaya


nur tay sallama a falon duk suka tsura mata ido basu amsa ta ba kusan tsakiyarsu suka sakota anty suad tazage tafara gaggasa mata bakaken maganganu masu zafi a tunaninta gobe bata da lkcin zaginta haka nan agaban mother hauwa dan tasan mother hauwa tana da dattako da kamiya bazata amince ayi hayaniya ko wani abun zubda kima irin haka agabanta ba


javeed na saman stair daf abayansu yana ji yadda suka zazzage matarsa tare da gaya mata cewa gobe gobe idan suka gama tona mata asiri agaban kowa zasu replacing inta arayuwar javeed da simran bazama sujira ba snn koda an wanketa da batun rape it wll mean nothing dan ahalinsu basu hada aure da wacce wani namiiji ya shigeta bada aure ba kuma harma tay cikin shege ta xubar

duk kalolin cin fuska da zagin da ake mata bata taba jin wanda ya mata ciwo kamar wann ba, wanda bata san ko batun auren sa da simran din bane ko tsananin kishi ya saka ta fara kuka agabansu batare da ta shirya ba

tana juyawa zata bar wajen taga javeed na tsaye yana kallonsu yadda taga suka hade ido dashi tasan yaji komi amma tunda har bai karbi bakinta ba kenan tabbas hala gaskiya su anty suad suke fada

kuka ta kara fashewa da shi ta haura sama idanunta a rufe da tsananin kishi tabi bayansa hankli tashe childisly kishi yabi ya rufe mata ido tahau tambayarsa ko wai dagaske ne zai aure simran din a gobe

dacan baiy niyyar kulata ba saida ya kai bakin kofar dakinsa snn ya juyo ya kalleta

their had a slight finch of hot argument akan simran din yace mata ai itace ta jawo komi he dint plan dis,itace ta jawo masa wann matsalar dats going to cost him to loose her goben..

kawai yana mata masifar ne dan ya kara motsa borin kishinta akansa amma bawai har ransa ba..

dan har numfashinta shakewa yake intana masa bori sosai akan simran din he actually enjoy watching her get soo mad and jealous akansa dan kwata kwata bata sanin ababen shirman da take furtawa.

hakanan yaki yabarta tay wani magana me yawa akan lamarin sun har ya rabu da ita ya shiga dakinsa ya rufe kofar yabarta awajen a tsaye tanata kuka tana masa bori..

and since then she was dead worried akan maganan wai zai aure simran gobe duk ta kasa nitsuwa haka harta dawo sashenta dakyar tay sallahn magrib da isha tun da tagama sallahn kuka kawai takeyi kanta a kife akan sallaya dan batasan wani irin ciwo takeji aranta na batun auren nan ba.


wayancan kuma sosai duniya yay musu dadi, ganin javeed baice komiba da suka zage nur agabansa suka ce mata gobe akwai daurin aurensa da simran they a tot that ai dan ya aminta da hakan ne yasaka yay shiru.

bayan sallah isha'i aka kawo duk wasu kayan da simran tay odersu na aurenta gobe da safe da duka arxikin ubanta kaya guda aka kawo a boxes da komi da komi batama bari sungani ba tasaka aka kai mata daki bayan duk anje sallah isha'i dan tasan da wuya ne kowa ya sauko tunda anata zumudin korar nur agidan gobe da safe.


tunda taje dakinta banda gwaje gwaje da murna babu abunda takeyi duk ta dagawa hajiya zubby hankali akan ace

80 / 112