Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
in the moment suna mugun more rayuwarsu.
kusan sai bayan ishai can kafin nan suka tafi
bayan sun rakasu ta dawo room dinta ta danyi karatun qur'ani snn ta nemi waje ta kwanta tay shiru tanata tunanin kalar rayuwan kawayen razia dataji ya mugun bata shaawa dan tasha mamakin kalar nasu wayewar me aji so much energy, ga ilimin rayuwa, gashi sam basu shagala da duniya sun mance da tarbiyansu da addinin su ba,koda suke game din lkcin sallah na yi duk suka tashi suka gabatar ita iya wann shiyafi burgeta dasu sosai, ko frankie daya kasance shine ba musulmi ba kuma na miji acikinsu duk ma ya fisu kama kai da rike matsayinsa, he is kind of more calm and very classy, tunaninsu kawai tadinga ahaka har bacci me nauyi yay awon gaba da ita.
washe gari da Asuba ta farka tay sallah ta jima tana karanta qur'ani kamar yadda ta saba kullum bayan nan tahaura kan gado.
for like 20 mins tana Kwance a tsakiyar gadon nata tayi lub ayanayin ruf da ciki idanunwanta duka biyun a lumshe
Wani mayattacen qamshin turaren wuta ne yafaratada ta Jin sautin sallamar razia yasata mikewa zaune cikin sauri kunya yasa tahau mutsike idanun ta shyly...Tun kan tayi gaisuwa razia tarigata yin magana cikin sanyin murya tace my sis kin tashi lpya?har kasa nur tazamo daga kan gadon tana dan jajjan wuyar vest din dake jikinta cikin sanyin murya tace "lpya lau how abt you..'
Zama razia tay a bakin gadon daf da ita takara da cewa..i am good if u're..toh"yay jikin naki? akwai inda yake miki ciwo ne?
shiru tadanyi kafin ta girgixa kai alaman a'a tace Alhamdullhi..
razia tace Toh Yanzu za'a kawo miki sauran kayanki dana siya miki saikiyi sauri ki shirya ki same ni a kasa mu karya kinji? ba musu tace toh sannan razia tamiqe ta fice,ajiyar zuciya ta sauke tana bin rufaffen door din da kallo can ta juya karaf idanunta suka cikaro da madubi.
Wani irin kallo tayi makanta ganin yadda tadawo babu wani marabarta da Baba gwarangal tamkar ba itaba, takusa minti 10 atsaye tana kallon kanta kawai, ji tayi wai harta burme dan yatsun hannunta acikin kashin wuyarta dan batama san sanda tahau shafa jejjemewar da wuyarta yayin ba.
Hawaye ne taji suna shirin sauko mata amma data tuno da maganan su rico da molly sai tayi saurin shanye hawayen tay shiru.
ajiyan xuciya ta sauke har sau uku kamar yadda doctor taheer yake umartan tayi in tacikaro da wani abunda ya tokare mata kirji,cike da dauriya takau da idanunta daga madubin, sadaf sadaf tawuce bathrum ta tube kayanta ahnkli tana dada jin kalar ramewar datayi sei bata tsaya kula bugun xuciyarta dayake ta son zugata ta damu da yanayin zubewar jikinta ba kawai ta kunna shower ruwan dumi mai yawa ya soma sauka akanta shaaaaaaa wani nannauyar numfashi ta sauke me sauti
sosai takejin dadin saukar ruwan ajikin ta sabida hnklinta dayake dada kwnciya.
Sabulan wanka na kamfanin fenty masu dauke da hydrating shower gel ta gogga ajikinta dats so soft and silky tuni yadau qamshi da kuma qyalli
Fuskanta ma sosai ta wanke sa da scrub din neutrogena soft dake wajen tayi brush tayi marmaza ta kashe shower ta dora farin towel tadawo cikin dakin tahau shafa alovera lotion da wasu rejunevating creams dakema taga kamar yana farfado da yamishewar fata tayi sumul tayi laushi.
insecurities datakeji aranta ya saka ta dinga mulkawa sanda ko inan ajiknta yaji man sosai, ko wani powder bata shafa ba tahau saka dogon riga baka dataga razia ta ajiye mata awajen
Itade duk batasan yaushe aka siya mata kayan sawa ba amma kusan dukansu masu shegen kyaune na zamani dan kadan ne jallabiya na mata sai sabbin inner wears
dan haryau bata taba fita wani waje sama da falo ba, kuma basu taba barinta ta tsinana komi agidan ba toh ko hira ne saidai taga anzo an mata a daki sai dai in ita tagaji da zama ta dawo falo ta zauna.
tana gama saka kayan tabude kofarta ahankli sauko kirjinta nata bugawa ta lillibe kanta da mayafin rigar ta sauko wani slim Flat shoe ne mai kyau marar kara tasaka wanda a hnkli take taka matakalar dashi tana saukowa cikin saibin jiki da kasala dan tamkar wacce kwai ya fashe mata aciki haka take sauke kafafunta akan ko wani step tare da saukar numfashi jin jikinta yanayi mata wani irin dadin da bata sabajin irinsa ba,
wani wasai takeji acikin zuciyarta ga kaucewar jiri da yawan jin gajiya da dacan su suke bala'in addabarta sukesa ta jin tagaji da komi kamar rayuwan ne kwata kwata baiya mata dadi rabonta dataji an zageta ko wani sabon abun baqin ciki ya tunkarate tunda tabar Abuja.
jin yadda waje yy shiru yasata kara ware Fararen idanunta tana mai zubasu cikin falon ganin shiru yay yawa yasa ta kara kutsowa cikin falon jim kadan wata mai aiki ta bude kofar kitchen suna hade ido tace ma nur hajiya ina kwana? Nur tay karamin murmushi tace lafya..anty razia fa? mai aikin tace ohh tana jiranki a dinning
dan lumshe ido tay dan sai yanxu ta tuna ashe hakan sukayi.
tana zuwa dinning din kuwa tasame razia ta gama hada musu breakfast tana zaune cikin wani hamshakin classy dressing daya mata mugun kyau kai kaganta kamar wata sarauniya daular larabawa.
kusan freezing nur tay atsaye tana kallon kalar haduwar razia with all the big girl vibe dats radiating thru her veins sai ta karajin karayar zuciya gani take harta mutu bazata taba zamowa mace me aji kamar razia ba...DO NOT SHARE 08060712446
[23/04, 23:03] Anne-Aurora🦋: EPISODE3 wani irin nitsatsen kallo razia tawurga mata me tattate da kasaitaccen murmushi sanin meya dakatar da ita ahnkli tace little sis karaso mana why did u stand like a fucking statue.
cikin lumshe ido da budewa nur ta farfado daga tunanintan snn tafara tahowa ahankli kamr wacce take tsoron aje kafafunta kasa, daga gani kasan tagama rainawa kanta sai satar kallon razian take dan bakaramin aji razia take dashi ba komi taga da class takeyinshi and it was so flawless irin wanda abun yariga ya shige musu jiki sosai innan.
bama acikin hyyacinta ba ta matso daf zata ja kujerar dinning din dantazauna nan razia tamata wani irin kallon me kumshe da sigar dakatarwa..nur ta tsaya cak tanata kallonta nan taga raziar ta taso cikin sanyin taku ta matso kusa daf da ita ahnkli tadan dafa kafadunta tanamai dada gyara mata chin posture dinta da kuma yanayin tsayuwarta ayayin da nur din ta wani irin lumshe ido jikinta har nawani irin tsuma jin kalar qamshi mei shiga jiki dake tashi ajikin razia wanda is not loud kuma is not shouty just sneaky and wild, ahnkli taji razian nace mata lesson 1,.."you are not a horse, you are a lady kirika tsayawa with ur chin up not down like a horse, alwys look confident,mace me jini ajika ba gajiyayya ba. nan ta kare ma kayan data sa kallo cikin kyabe baki tace i wll forgive u for not dressing like me yet
.,dede nan danyi pause ta kalle fuskr nur din tana dan mata murmush playfully nd calm tadan lakata karar hancinta tace "amma kisani duk ranar da zaki zo wajen cin abinci make sure u dress nice, karkisa kayan da xai takuraki nd act like a queen that you are..walk..but don't be too quick dont be to slow. inde family dinning ne kar daga kin iso kawai ki ja kujera ki zauna kibari wani elder dake wajen ya furta muku hakan, stand behind ur chair, slightly hold ur chair with yr two hands and pave ur way in to the chair a nitse if ure ushered to sit. tana gama furta mata hakan ta hau gwada mata snn ta sakata tay itama, tace
karki zauna a takure kibar kafafunki yana taba kasa. idan akwai manya awajen koda mijinki ne karki xauna harse sun zauna, its seems like nur is such a fast leaner tana dan murmushi tana sata tana gwadawa dataga tanayin komi dede tace good,daga yau haka zaki na yi cos All great women must have good table manners.
ahnkli nur tace okay and then what???
idanu razia ta zuba mata snn tace" i want you to re-arrange this table a tsaye in gani.
nur tana shirin mikewa tayi saurin tsareta da ido nan ma takoya mata yadda ake mikewar nice and easy bada karfi katura kujerar baya kamar zaka je yaqi ba. bayan nan tashi nur tayi atsaye snn ta fara kallon kan table din sai kuma taji duk ta rude dan ba'a taba koya musu komi irin hakaba ita batama san ya ake wani arranging komi akan dinning table.
mikewa tsaye razia tay"tafara odering inta dauki wann aje acan, saka wann agefe, dont touch the tip, ta nuna mata wanne position spoon zai zauna ina kuma fork yakamata ya zauna and all other table ettiqutte. Dinner plates sune a tsakiya, fork din salad a hagu, na cin abinci kuma daf da plate. knives and spoons sune a dama amma knive yafi kusa da plate din cin abinci, bread and butter knife da napkin dats neatly folded suma duk ata hannun hagu. sai glasswares agaban knives amma glass cup na shan ruwa shine yake zuwa farko kafin na wine ko juice, ba arike jikin glass sai stem dinsa.
tace zaki saka napkin akan cinyarki ne only when ure seated
sann ba agoge baki da food napkin da karfi sharewa kawai akeyi ahankli. snn karkina cin abincin da sauri sauri, just small bites and pace urself. in bawai kin koshi bane zaki dan huta kadan tozaki aje cutlry dinki in V shape, inkin gama kuma zaki ajeshi a shape din kamar yadda agogo yake nuna karfe hudu dede.
sann alwys say please and thank you in kina son a mika miki abu ko inhar anmika miki, snn karki sake ki mika hannunki across table kidauki abu kice ma wanda yake kusa da abun ya mika miki
..no gossips, babu jan dogon magana wajen cin abinci. snn in zaki tashi please excuse them.
nur taji tab ashe dai rayuwar masu kudin nan ma akwai shegen wuya komi sai anbishi a qa'ida, razia tay dariya tace table manners ba zallan na masu kudi bane na mutane masu daraja kansu ne
..haka nan dai suka dingayi razia bata kyaleta sun zauna sunci abincin ba har saida ta koya mata yadda ake setting table kamar sau uku sann suka zauna suka karya acikin nitsuwa.
sosai ta koya ma nur yadda ake cin abincin yan gayu.
har saida suka kusa kammalawa nur ta kalleta tace An..razzy please can i ask you a question? Razia ta aje spoon nur na kallon yadda ta ajen calmy snn tace am all ears.
cikn sauke ajiyan zuciya tace but why all this..ni amfanin me zaiyi min. Yar dariya razia tay tace.."Nur u'r just a child amma kisani no knwldege is a waste, infact knowlegde is power
..ko baki da arziki wata rana kika zamo me ilimin rayuwa zakayi kima da daraja a idon mutane sosai duk inda kikaje bamai iya raina miki wayo ko da yafiki arxiki da wayewa, barema ke bakisan ina rayuwa xai kaiki nan gaba ba
toh wayasani saiki auri wani hamshakin me kudi and this is exctly how he was raise with class and manners, kina nufin saikin je gidansa ne kafin nan zaki fara koyar duka wann abubuwan?huhh, toh ai kansa ma raina ajin ki zaiyi bare ajega danginsa..oh lets not say aure, ajega public event, ace kin yi karatu har kin dawo wata public figure. ppl are going to look at you as a role model,young girls will admire yadda kile daukar kanki. kuma kinsan abu na farko dake sanyawa mutum kima a idanun jama'a shine yanayin yadda yake daukar kansa, like the manner he walks, talks, sit, eat, nd even sleep. idan har kina son ki zama kina da value u must be a lady with excellent ladylike manners..ur manners build ur standards,and ur standards are ur values,ur value is ur integral cost. nur kimance cewa kina da kyau sosai, kisan cewa mazan zamani da suka san kansu snn suka amsa sunayensu na maza they alwys go for women with brain value not just beauty
..let ur beauty be a surplus not the only thing u possess kinsan kuwa yanxu kyaunma baida daraja a idon maza dan ynxu akan iya a siyenshi inkana da kudin yin plastic and cosmetic surgeries, likitocin nan zasu iya dawo dake duk yadda kikeso, amma kinga ilimi, nitsuwarki da kamun kanki...wnn ajikinki yake nd its ur greatest asset my sis.
cikim sauke ajiyan zuciya nur tace hmmmm okay fine...i got it..but we shud do it again ina dai zaki cigaba da koya min?tafada hakan da shagwabe dan sosai maganan razian ya fara tabata.
Dariya me aji razia tay tace sure sis. nan ta kamo hannun nur din gently tace "i want you to be better than me
..shiyasa na tsara miki wasu abubuwa da zakinayi a wann yan kwanakin kafinsu mama suce zasu dawo nigeria sufara cikaki da rayuwarsu ta gargajiya, nur tay yar dariya me sauti tace toh menene plan din..
razia ta danyi shiru snn tace inaso daga yanxu ki dinga fita kina spending time dinki alone tare da duka kawayena. i mean u wll spend time with each of them alone haka.
nur na shirin budar baki zatay magana cikin katseta da lallami razia tace nasan baki saba dasu ba but trust me you cant do it alone wasu abun dolene fa saida taimakonsu..nima dakike ganina ahaka awajen wasu nakoyo abubuwa masu shegn muhimci wa rayuwana harna cimma wani matsayi ayanxu. u have to learn to take advantage of oprtnity kinsan ance it comes only once. wann fa babbam damarki ce cmn dont be shy or afraid sis, nasan fa zaki iya.. ta dada riko hannunta da lallaami
tace Nur kowa dakike gani a duniyan nan yana da kashi a tsuliyarsa kuma kisani bawai zancaki zasu yi ba, jst let them show u who you are, dan ke kadaice kike da ikon canza rayuwarki yadda kike so...
cikin sauke ajiyan zuciya me nauyi nur tace ohk fine,..naji. amma zakina zuwa wajen ko..razia tace yeah not alwys, amma dai zanzo na dubaku
...nur batace komi ba ta gyada kai daga nan suka tashi suka bar wajen suka koma ta daki razia tanata koya mata abubuwa daya shafi yadda ake yin magana with refine speech," simple and clear, not emotional, or overly expressive and bluff. da yadda ake kame kai da kuma jan aji a cikin mutane both mata da maza.
wasu abubuwan da razia take mata su practically sosai suke burge kwakwalr nur cos der is a whole new world da tafara kallo agabanta...
wajajen karfe 10am da rabi molly ce tafara zuwa gidan da motar ta cos she the spirit of the crew dan haka dolene afara cire nur a duk wata damuwa kafinma su jawota cikin komi, yau din ita dauke nur firdaus din a motarta suka fita for her first session with her agidanta..
daga cikin motar molly nur ce Sanye da wata white shirt me dagon hannu da high waist skit baki snn tay rolling kanta fully da wani black veil tay kyau fuskarta yay haske duk dama fuskrtata babu wani kwalliya. wani soft afro soul beat ne ke tashi acikin motar time to time haka molly take jawota cikin hirar rayuwa har suka isa wani hadadden gida inda mollyn take zama, the house was lit with fairy light, sai manyan
pillows thrown arnd like confetti...
molly tana murmushi ta nuna ma nur kujera ta zauna sann taje ta sauya kayanta izuwa simple crop top da baggy jean suman kanta ta daureshi in a messy bun snn ta dawo palon da two mocktails ta bawa nur suka xauna tare
nan suka fara hira kadan duk dama ta lura da nur kamar bata sake jikinta sosai ba..
nan molly ta fara bata labarin rayuwar mum dinta, who is being killed by her own blood sister akan babansu.
jikin nur yay mugun sanyi dan yadda tay describing mamanta da kanwartan sai taji kamar ita da layla ma haka suke..
molly tana murmushi tana hawaye tace ma nur kuma haryau kanwar mum dinta data kashe mata maman itace ta aure babansu, suna zaune da ita, just bcos they is no enuf prove cewa itace tay kisan. tace ma nur tana zamane da bqin ciki aranta kowani rana, tana kallon antynta wacce takashe mata uwa a matsayin matar baban su, molly tahau gayawa nur yadda take kallon tsantsan butulci da mugunta da son kai irinna na yan uwan jini, ita kuma nur laylanta take tunawa tana mamaki dama wai ashe ba ita kadai bane hakan ya faru da ita? dagaske ne dan uwanka na jini daka sha wahala dashi zai iya kwace abunda kake so harma ya kashe ka akan namiji,
shiru tay cikin tuno da bakaken kalaman da layla tayita furta mata akan adnan saikamar zata sauke hawaye wanda yasa molly tarike mata hannu gently cikin girgiza mata kai tace its okay dear, karki tuna komi wai dan kinga nima ina hawaye, kawai de in nuna miki cewa alot of us are breaking in silence but we choose ourself..we choose to live, we choose to be happy not to wallow in self pity..duk wani abunda ya faru dake munji labarinshi amma kisani wann duk qaddara ce daya zama past dinki, how u want to see ur future is totally ur choice, eida happy or sad kece zaki iya yanke wann hukuncin nur.
ahkli molly ta share hawayenta tafara murmushi snn ta miqa mata glass tace if u choose happiness frm now on get up lets cheer to unlearning sorrow.
jiki a sanyaye nur ta dinga kallonta dan bakaramin tausayi mollyn tabata ba
taga ashe gara ita ta iya rabuwa da mutanen da suka cutar da ita amma molly is still living with that same kanwar mamanta data kashe mata mama danta aure musu baba. this is another level of torture musmn da bata da wani shaida akanta duk dama ta san itace.
ahnkli tamike tsaye tay clinging na toss in tace to 'happiness' molly tay dariya me sanyi tace and fun.!
daga haka suka fara sabawa da junansu sosai tun aranan farko sabida molly tana da abubuwan