Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
sakacina ya jawo faruwar komi...i dont think zan taba iya yafema kaina da wani abu ya same general jiya..
cikin rage murya naima tace what happen taya hakan ya shafeki..altho i have my suspiscions too amma kuma likita yace....cikin katseta janet tace "mance da zancen likita naima, ni araina ina ganin kamr wancan matar has sumting to do with it
Na'ima tay wani irin muurmushin mugunta tace yess i knew it..amma ya akayi kika gane kema?
nan janet tafara bata labarin komi daya faru daga jiyan har izuwa abubuwan da suka faru da ita yau da safe wanda yasaka sosai jikin naiman yay sanyi musmn yadda taga janet tana blaming kanta sosaiii.
karfin gwiwa ta dinga bata amma inaaa janet saidada zurfafa takeyi tanajin kanta kamar ta tafka wauta jiyan sosai..
naima tama rasa me zatace mata tace toh muje ciki wajen hajiya i am sure zata fahimce ki sai mu roketa ita tay masa magana kinga hala ma saikici albarkacin ta cikin lallami tace but janet, no body is 100% ever careful a duniyan nan, manyan sarakuna da suka mulki duniyar ma da manyan sojoji da ke kwana cikin tsaro wallh poison da kuma
makircin mace yana iya kashesu. ke kuma tunda na sanki baki taba aikata kuskure da rayuwar general ba sai akan wnn matar but my dear this is just a proof that you are not a supernatural being ure simply a human being.
janet tace hmmmmm toh shikenan naji muje amma ke zaki fara magana nikuma sai na mata bayanin komi daya faru.
naima tace babu damuwa...
atare suka karasa cikin sashen nur da sallama abakinsu duka saidai jin sautin karatunta yasaka suka tsaya tun a falonta na biyu. bayan kamr minti goma sharp Nur ta kammala karatun ta ta fito falon ta samesu jikinta sanye da hijabi
duka suka rusuna suka gaisheta cikin ladabi sosai ta amsa su babu yabo babu fallasa.
kai tsaye cikin taushin murya naima tace Hajiya wata magana mukazo dashi muna neman alfarmanki ko zaki iya bamu dama??
Nur ta kallesu duka musmn janet dataga tamata daban jikinta duk yay sanyi cikin sauke karamar ajiyar zuciya tace toh bismillah, ku zauna dama ina da magana daku nima concerning abunda ya faru jiya
nur tana zama akan kujera suka koma kasa kai a tsunkuye na'ima tace ranki dade hajya maganan da mukazo dashi kenan saboda abubuwn da suka farun da akwai ayoyin tambaya aciki
nur tace inajinki go on..
nan naima ta fara fadin duk wani abunda ta sani da kuma wanda ta gani wanda ya dada razana janet ya karasakata cikin rudani dan duk bata lura da wnn ba.
Nur tasha mamaki jin wai harma simran ta taba smoothie din da bakinta
ta kalle janet da daurarren fuska tace and what do you have to say about this..
cikin gyaran murya janet ta fara nata bayanin idonta yay jaa kamar zatay kuka tafadi komi bata boye har zuwanta wajen simran da zuwan hjya zubaida ba.
Hankali tashe nur ta mike tsaye tana kallon su duka da wani irin yanayi a fuskarta wanda bazaka cemai bacin rai bazakace mai rudani ba.
da nai'ma ta fara saidai applauding dinta kawai tay na kkrin saka ido da ganowa
snn ta dawo kan janet da masifa, tace sam wann ganganci ne da rashin kula wanda dazai jawo mata rasa rayuwar mijinta dan haka ita babu ruwanta kawai taje ta gaya masa meyafaru aishi zai gano gaskiya kuma zai san kalar hukuncin da zai yanke
Janet batace komi ba face hakuri data dinga bawa nur bawai dan ayafeta saidan tasan tay ganganci da aikinta jiya
Tana mikewa zata fita naima ta juyo da fuskar tausayi tace Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki duba lamarin nan..janet is one of the best workers wllh bata tabayin kuskure akan aikinta ba hajiya pls have mercy on her
duk wacce za'a kawo banajin zata kai janet wajen kkrin kare mutunci da kuma ran general...
nur tay kamar bataji ba tama shareta har saida Janet din ta fita takama hanyar sashen javeed kafin nan tay wasu nazarin tace ma naima kije kice mata ta dawo nan.
da wani irin sauri naima ta mike tana godiya da gudu ta kira janet wanda har hawayen datake dannewa tun jiya ya sauko mata..
naima tace hajiya tace kizo yanzun nan
janet ta share tsillin hawayenta jikinta a sanyaye ta biyota suka taho.
har lokacin nur na tsaye tana tunanin nata rayuwar, yadda ta taso yarinya me ilimin addini, tarbiya na abun kwatance kamun kai ga shiru shiru bata san ma me ake kira da rashin kunya ba bare amsa magana wa babba amma with time duk saidata zubar ta aikata wasu abubuwan da ita kanta saida tay tuhume kanta da samun tabin hankali
in all of these ta gama lura cewa komin ilmi da kwarewa da kuma nitsuwarka akwai wani lokacin da zaka iya tafka wani rashin hankali da sokonci wanda ka cancanci ayi maka duk zagin duniyar nan sabida kayi abu marar kyau. amma fa game cikkaken hankali da nitsuwa yasan hakan bashine zai saka ayi amfani da moment na rayuwarka guda daya ayi measuring ko ayi condeming din efforts dinka na baya gabaki daya dashi ba dan hakan ya kaucewa Adalci ya kuma sabawa koyarwan Addini sabida shikan sa gyara da nasiha da jan hankali duk suna da cikakn ladubansu a musulunci, dan ba ayi da zuciya, ba ayi da zafin kai, da kuma kakkaursa lafazi, anayi ne da tunani me zurfi da horarsawa, da kuma tuna in irin abun kaima tazo ta sameka agaba ko wani naka toh yaya zakayi??
janet tana dawowa nur ta rufe idonta tay mata fada ta kuma gaya mata cewa tay wawanci da sakaci me girma akan aikinta amma tunda wnn ne na farko kuma ta gane ta amshi laifinta zata bata wani dama har ta jawo mata wani hadisi na manzon Allah dake cikin ibn majah hadith number 4251 dake koyarwa kowani cikakken musulumi da ya zama me nisan tunani da gabatar da sharhi cikin tattausar lafazi. idan kaga kuskure awajen wanda is sincerely remoseful ko is willing to repent toh amatsayinka ma musulmi anaso ne kayi understanding dinsa snn ka zamo very supportive domin wnn shine koyarwar manzon Allah S.A.W.
Har kasa janet ta tsuguna ta gode mata tareda dada jin tsarin musulunci ya kara burgeta, lafuzan nur yasaka sosai taji wani abu ya ragu mata aranta atleast her efforts where not compltely condemed just bcos of one single mistake wnn kmr wani babban dama ne agareta na kara jajircewa akan tsaro da saka ido da kuma daukar babban darasi akan mutane irinsu simran.
bayan an gama da wann
nan suka fara tattauna yadda zasu saka simran tay admiting na lefinta da bakinta sabida su samu shaida akan hajy zubaida nan gaba duk dama nur ita ba wanan take hanga ba tafison taga taci uban simran tay mata abunda kwakwalrta bazai dauka ba cos how dare her??ita ranta sosai ya bata cewa simran tay wasa da ran javeed ne dan kawai ta mata sharri tasaka a walakantata.
cikin kuskus suka gama shirya abunda zasuyi tace ma janet ta koma bakin aikinta snn ta nemo mata Air bag, ita kuma naima in lokacin daukr fansa yay tazo da scizzors.
***
Bayan nan kowa ya koma bakin aikinsa normal janet tana jin abun aranta amma dai batace ma javeed komi ba sabida nur tace mata karta fada komi tukuna sai tay tunani.
wajajen 9:00am na safen lokcin nur ta gama shirinta tsaf ta saka wani plain saki material custard yellow aka mata dry natural make up irin marar lip gloss din nan tay kyau kamar amarya, tasaka wani golden cover heel na valentino garavani snn ta yafa wani karamin golden veil shima irin kalar talkaminfa veil din kamr chantilly yake amma kuma material na turkey ne me mugun tsada.
tana zauna agaban madubin kenan naima tana gyara mata zaman abun wuyan gwal dake wuyarta sai ga aika daga javeed cewa ta fito nan da 20 min zai kasance a waje yana jiranta domin suje karyawa.
Duk da wani irin dadin dataji ya lullume but cewa dayay wai zai tsaya awajen ya dada karya mata zuciya watoh dai shi sarkin pride da ego irin tunda takoreshi a dakin shi bazai sake shigowa ba hmmm..
tunda taji zaizo saida ta kara tabbatawa cewa fuskarta yay masifar kyau agabn madubin.
Ata dayan fannin kusan kowa ya shirya amma dake 9am sai ba afara fitowa ba
simran ce cikin wata shiga ta girgio armani suit wandon ya wani irin dameta ta saka wig dogo kai babu marabarta da arna ta dauko wani labcoat fari ta rike waita shirya zuwa aiki dan tasan tsoron janet ma kawai bazai kyaketa ta iya zama agidan yau ba
tagama shirin kenan ta debo kafafunta tazo dakin hjy zubaida tafara tambayarta abunda ake ciki nan hajy zubaida ta labarta mata cewa ai taje ma ta same janet din tay gaslighting inta ta komar da lefin dukan kanta bata tsammanin zata kara dago maganan sabida tamata barazana sosai
wani irin tsallen murna simran tay ta rungumeta yaa zuby ohh my goshhhh thank you ure best sister in the world and i promise u bazan sake miki irin haka ba
da wani irin harara hajya zuby tace ke dalla matsa can Dakikiya kawai..ki rasa ma wanda zaki yi dashi sai janet? ke wai baki da brain din yin tunani ne ai dama ita amaryan javeed din kika tunkara da wnn makircin kai tsaye amma dan hauka kika kama janet dake ke bakisan cewa duk wanda suke zageye da javeed makisa bane. u have no idea mata wawaye irinki nawa janet ta binnesu da ransu tsabar karfi da mugun zuciyarta yasaka aka dakatar da ita daga base na sojojin boader snn aka kaita Rehab, daga nan aka kawota aikin kare rayuwar javeed mufasa bawai dan kin ganta anan abanza tana binsa tana masa aikin gyaran daki tana masa girki ba ki dauka itadin jakace kamarki wanda batasan metake yi toh nikaina na mata barazanar ne amma idona nakanta dannasan wllh janet
bazata kyaleki ba.
Wani irin tsorataccen hadiyar yawu simran tay sai batace komi ba dan dama jikinta ya jima yana bata cewa mr aqeel, na'ima da kuma janet duk cikin ma'aikata sune kawai suke mata abu kai tsaye kamar basujin tsoronta tunda yau tasan janet soja ce tasan hala wata rana zaa ce mata naima special agent ne it feel like they is too much undergrond secrets in this mufasa mansion.
duk a tsorace take amma tacije ta kaucar da abun akan fuskrta batace komi ba ta jira hajy zubby ta gama cakkara daurinta data saka na wani mayen code lace na soltis of london baki da ash sai walwal kake gani wasu manyan gwalgwalai na gwal na haskawa a wuya da hannunta taci wani uban kwalliya.
9;28am dot javeed ya karaso sanye da wata neat dark blue kaftan ajikinshi datasaka ya zama soo calm and irresistbly handsome
shigar datay na kamala har da lullumi sosai yay dede nashi shigar na jumfa ta samesa a waje yana kan jiranta da sabon salon girmamawa ta gaisheshi ya amsa yana mamakinta duk dai ta kasa dauke ido akansa shima kuma taga satar kallonta kawai yakeyi amma yake basarwa kadan kadan.
hannunta cikin nashi suka shigo falon lkcin su anty suad duk sun fito ita da lady sidd da alhaj attah, suna yin sallama ko numfashi matayen basu barsa yaja mekyauba suka rufeshi da ya jiki? ya jiki, da mamaki nur taji basu gaya mata wani baqar magana ba infact basu sake sun dago zancen jiyan akanta ba.
tana gaishesu taga bason kulata sukeyi ba sai kawai ta koma gefen alhaj attah ta tsuguna takara bashi hakuri akan abunda ya faru jiyan shikuwa sai albarka yake saka mata yana dada kwantar mata da hankali.
sosai anty suad ta kulu ganin nur batazo gabanta itama ta bata hakurin ba duk ransu sai ya dawo kan hakan kuma suka fara bambami ciki ciki. har aka kai kan dinning table da aka cikesa da abinci kala kala dat are soo sumptious and well seasoned with clinical precision ba tarin junks ba.
ana zama sai gasu simran yaune karo na farko da suka yi latti lady sid tanata tambayarsu hajy zuby tace ai simran dinne bata jin dadi shiyasa ma jiya bata fito ba kwata kwata.
da wani irin kinibibi ta gaida kowa sai kuma tabi tahau yima javeed jaje tana cewa ya jikinsa bayan kowa yasan bata wajen jiya da abun ya faru..
anty suad dake da shegen kwakwala aikuwa ta kasa hqura ta tambayeta ya akayi ta sani
caraf hajy zuby ta amshe maganan tana washe baki tace ai da safen nan ne ta gaya mata komi.
da uhmmm kawai anty suad ta kashe maganan aka fara cin abinci javeed na kusa da babansa nur tana kusa da javeed dinta
Dan kadan kadan yake taunawa kamar me koyon cin abincin dayaga kuma nur ta dan bata rai tana satar kallonsa sai ya faraci da dan yawa ana hira kadan kadan atable din shidai baice komi ba har gara nur in alhaj attah yayi da ita tana amsawa.
abazata wani abu ya shake masa wuya tari yadan kufce masa marmaza simran ta dau glass din ruwa tahau zubawa zata miko mai saidai kafin tagama nur ta dauki nata na gabanta ta mika masa tana dan cemai sorry kai tsaye yace mata tabashi ruwan abaki tukuna
hannunta tasaka abayansa tana patting kadan snn ta fara bashi ruwan abaki yana karba
simran ta tsaya cak da nata ruwan a tsakiyar jamaa tana kallonsu ayayinda suke tamfasa rashin ta ido, ga tulin abun kunyar datayi dayabi ya isheta har bata iya motsi ba saida hajya zuby ta mutsineta da karfi snn tabi tazauna da ruwan ahannu ahnkli cikin sadda kai kasa.
sanyin muryan nur ne ya ratsa table din tana kallonsa kamr ranta tace mishi "are you okay?cikin lumshe ido da budewa yace "i am okay baby, thanks.
da wani irin mugun uncontroble borin kishi me tafasa zuciya simran ta tashi very coldy tabar kan table din wanda atake wani irin silly coments ya fara tasowa awajen kadan kadan
simran bata tsaya ba taje dakinta fuuuu ta dau gucci bag dinta da labcoat tabar gidan ta kofat baya ma ta fita zuwa garage din hjy zubbyn ta dauki wata babban jeep tana tuki tana kuka har ta isa asibitin
Basu gama breakfst din ba wayar javeed yay kara ya dauka for 2 mints baice komi ba sai daf zai katse snn yace give me 5mints
yana katsewa nur ya fara kallo muryansa kasa yace "ina da muhimmin bako zanje nagansa i wll be back by noon.. kinji ko?
innocently ta gyada mai kai da sanyin murya tace okay, take care of urself..
murmushi kawai ya mata snn ya tashi sukayi magana da babansa kasa kasa
kafin nan yama su anty suad sallama ya fita...
[23/05, 21:35] BLUE💙: EPISODE 62
Bayan nur ta gama karasa cin abincinta snn ta tashi zata wuce sama da mamaki taji alhaj attah ya kirata har cikin dakin baccin sa sukaje atare.
wanda koda ta shiga for a minute daukawa tay ta shigo cikin wani duniyarne na daban dan bata taba ganin wajen da is soo dark and cozy kmar nan ba like komi na dakin abun kallone duk dama babu wani abun kyale kyale..
akan wani katon dark British cottage oak wood chair dinsa mai crown din kan zaki ya zauna ita kuma ta zauna akasa akan lallausar daddumar dake gabansa kanta na kallon kasa kirjinta na bugawa sosai duk ta dauka zai mata fada ne akan yadda javeed yake sakawa suyi wasu abubuwn kunya akan table din duba da yadda simran take reacting dan ita kanta d'aurewa kawai takeyi da irin mugun evil eyes dake yawo akansu kowani lkci.
shiru tay tanajinsa har yafara mata jan hankali akan wasu abubuwa da ya dan danganci zama da mutane musmn ma wajen kimantawa da darajawa da kuma hakuri snn yace mata duk yadda za'ayi karta bari wani dan adam yamata shaida da rashin gaskiya sabida shi me gaskiya baya taba fadi kasa..
saida ya babbata hakuri akan wasu dabiun yan uwansan snn yakuma umarceta akan ta zama me jarumta, ta kula da kanta da mijinta, ta bude idonta sosai, snn ta tsaya makanta ta kwace yancinta kar tajira kowa yaxo ya ceceta idan kuma ba haka bazata iya rike gidan anan gaba ba.
Nur tay shiru harsaida ya gama mata nasiha snn ta masa godiya sosai, dan inbanda kawunta da kuma shi ita batasan menene dadin uba awnn stage din ba. but alhamdullh babanta ya rasun, but atleast she is still finding fatherly comforts nd advices awajen mutane biyun nan da suke kkri wajen fahintarta da kuma nitsar da ita.
koda ta fice a dakin tunanin abubuwan daya gaya matan takeyi tana isa falo ta samu anty suad da lady suna hirarsu da baya karewa.
da mamakinsu suka ga wai Nur takara gaishesu fuskarta babu yabo babu fallasa ta sako maganan abunda yafaru jiyan snn tabasu hakuri cikin basu cikakken girma tace musu in sha Allahu zata gyara duk wani kuskurenta akan abincin..
kamar an zuba ruwa a wutar dake cin kirjin anty suad hakanan tasauke wata ajiyan zuciya dan dacan tagama dora nur a matsayin marar kunyar yarinya da bata girmama na gaba dan bata taba basu hakuri akan komi ba tunda suke samun sabani da ita agidan saiyau.
lady sidd kuma abun bai mata dadi ba sam tasone nur ta cigaba da taurin kai sai ta samu abubuwa da yawa da zasu kai gaban mother hauwa in lkci yay.
duk zafin kan anty suad dataga nur ta saukar musu dakai yau sai itama ta dawo kasa kasa tafara mata fada amma bada tsawa ba.
nur tagama jinta amma uffan batace ba sai dai tabata haquri
hajya zuby ko uffan batace ma dan bakaramin ji take kamar ta kama nur din da dukan mutuwa awajen ba.
ita da lady sidd gabaki daya sun aje hakan a makirci ne kawai ita kuma nur gani tayi yakamata wata rana kai karami ka saukar da kanka ma babban dan azauna lafiya dan bakowani yakine ake ci da karfi ba wani yakin da dabara ake cinsa kawai.
hakanan anty suad ta gama surutunta nur ta musu sallama ta bar wajen abunta daga nan bata sake sanin abunda ya wakana agidan ba.
tana komawa sashenta tarage kayan jikinta ta danyi bacci bayan tafarka tay alwala tayi sallah