Chapter 85 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   85 / 112

252K to 255K   out of 335.4K words

yay sanyi sosai bacin kowa daya ke alhanin jin abunda akay ma yar yarinya suad ce take ganin kamar komi karya ne ai nur din ma bazata iya daukar kalar wann qaddarar ma yay mata nauyi.

hajy amira mufasa har hawaye taji yataru a idonta masu zafi musmn ma da javeed yakara da bayanin abunda su anty suad sukayi mata agidan nan. duk abunda ake ciki ya gayamasu snn ya gaya ma babansa cewa ba haka kawai ya aure nur ba, shidin ma yay bincike aknta kuma yana da file dinsa aknta kawai abune daya shafi personal trauma da baisaka kansa aciki ba wanda shima iya kuskuren daya san yay kenan.

javeed yana gama magana masu salati sukai jikin alhaj attah bai gama yin sanyi ba saida mother ta kara bawa sheik haidar ali daman yin magana a maimakonta.

dan tasan cewa in har wasu basu gama aminta da furucin javeed akan matarsa ba aidolene zasu aminta da ita nata shaidar..

nan haidar ali yace musu suma acan morocon sunyi nasu binciken wanda kusan duk abunda javeed yafada anan shine gaskiyan, da mamaki shina bai fayyace alaqar rashin jituwar nur da mrs haseena ko ya ambace sunan sadaat a matsayin mijin mrs haseenan ba.

cike da kare mutuncin nur firdaus yace musu case din was not even personal, harkace ta siyasa, daya jawo har akay victimizing nur firdaus da yar uwanta layla agidan iyayensu aka farmasu da fake Injections na HCG dat will mimick pregncy symptoms dan kawai a'bata ma mahaiyarsu suna da siyasarta.

har yadan kara musu ilimi akan dabi'un nur tare da nuna musu cewa asalin ba itace ma main target din farida bala ba, she was deeply cought into dis ne sabda kare ya uwarta dataje yi snn ya fayyace musu halayenta na kwarai har wanda basu san tana da shi ba, dan ya lura kowa agidan yana daukar kamar karatun qur'anin ne kawai madogaran ta face saida yagaya musu cewa record din nur a abuja ya nuna musu cewa ita din babban abar kwatance wajen manya da yara it was at end she got stained and traumatized with fake narratives.

daga ganin fuskansu zaka san cewa kowa yasha mamakin maganan amma dake shine babba namiji saida yay yar nasiha akan yanke ma mutum hukuncin gaggawa kafin nan ya zauna

mother tafara magana amma da alhaj attah tafara jan masa kunne akan yakara yin hankli da ire iren wnn half cooked labarukan daga nan sai bata wani ja maganan ba

saida ta dawo kan anty suad dake kuka kamar ranta zai fita duk ta kasa daga kai sabida borin kunya daya gama riketa ya hanata motsi gashi duk an bada shaidoji kwarara bata halin cewa komi snn ta tsaya tamata wani irin kallo snn ta amshi files din nur din duka biyu dana hannun javeed dana hannun sheik tasaka khaleefa mufasa yakawo katon burner tray aka kunna masa wuta snn ta jefa files din duka ciki suka kama konewa..

bedsheet din kawai ta dauka ta rike kafin nan ta mike tsaye tafara addresing dinsu da cewa yadda ta kona files din anan haka take so maganan nur firdaus yakare anan snn bata son tasake jin cewa wani yayi acting akan half truth harma yaci ma wani mutunci akai dan hakan ba adalci bane snn addinin musulci baice haka ba

darajar kamil yasaka bata ma suad tass tass agaban yaran ba musmn yadda take so taga tamata zagin da zai dameta har abada.

saidai duk da haka sanda ta dubeta ta gaya mata manyan maganganu masu ciwo akan hada kanta datay da su zubaida agidan har ana cin mutuncin javeed kai tsaye. maganganu ta gaya mata masu zafi da nauyi acikin ruwan sanyi agaban yaran snn ta nuna bacin ranta akan yadda tay watsi da girma da kuma darajar babban mace me hankali da suka bata aka damka mata amanar nur tare da bata daman zuwa gidan dantana kulawa da auren javeed din saigashi tazo ta maida abun kamar ego fight tana baza mulki da rashin adalci da rashin nitsuwa tanakuma zubar da mutuncinta agaban kowa.

kasa cewa komi anty suad tay tanata kuka har tanajan sheshhka ganin babu wanda ya kulata borin kunya kamar zai kasheta, wa ita mother ta bawa tokar files din nur din snn tace mata taje ta zubar awaje acikin ruwa me gudana.

ficewarta da tokar yasaka alhaj attah ya dawo gefen mother yanata bata haquri ayayinda duk sauran mazan suka dan shiga maganan musmn ma kamil mufasa sunata bada baki hajy amira ke zaune kusa da javeed kowa cikinsu dai yana magana.

anty suad tadawo daga zubar tokan kenan tazo ta samu javeed yanakan cewa inde zai zauna da matarsa anan gidan toh sai in har kowa ya tattare nashi ya koma inda ya fito sabida matarsa is enuf ta rike gidansu shi baiga dalilin da zaisaka mutane sutaru mata akai ba.. yanayi yana dan tausasa maganar amma kanaji kasan gaya mata kawai yake a kore su anty suad agidann ubansa dan bazai iya zama dasu ba matar sa nur da babansa sun ishe shi,

yana fadin hakan kuwa kusan kowa cikin mazan gidan suka hau goya masa baya...

hajiya amira kuwa ta dinga kawo korafi akan yawan zaman simran agidan da yadda ake bata wasu kananan dama da power da bai dace ba

shide alhaj attah baice komi ba anty suad kuwa kasa karasowa cikinsu tay tatsaya a kofa hawaye na zuba a idonta jin wai javeed yacema mother takore su akan nur firdaus itada gidan yayanta fa

a mugun zuciye ta aje tray din tokar ta juya zata bar falon mother ta kirawota ta dawo

hakanan ta sake nanata mata abunda javeed din ya furta agaban kowa snn tace mata ai tunda yanzu case yakare kuma kowa ya san asalin yarinya an gamsu dolene kawai ayi ma javeed da nur firdaus sabuwar bikin auren al'adarsu na karban amarya fully into the family sabida tana so ne marmaza aje can marocco dukkan atare da zubaida da kuma siddika da nur din tunda yanxu sune surkunayen gidan za'aje ayi initiation ceremony for the last time dan kowa ya san matsayinsa.

anty suad har taji wani sanyi aranta jin za'aje morocco tanata addua aranta Allah yasa ma jinin ahalin mufasa yaki karban jinin nur kamar yadda yay ma sauran matan

tanacikin raya haka kawai sai taji mother tadamka mata bed sheet din akan taje ta adanashi dan dashi za'a je moroco ayi bikin al'ada snn daga anyi bikin sushirya barin gidan nan
ita da saddika, shi kuma alhaj tace mai yasan yadda zaiy da kanwar matarsa dake jawo musu shaidan agidan.

yau da gobe kacal mother ta bayar domin afara shirin gawurtaccen bikin al'ada na auren javeed anan gidan kafin nan su wuce marocco for the family evening initials ceremony.

cikin ladabi kowa ya amsa mother kafin nan matayen suka watse jiki na rawa anty suad takira haj amira suka je sama domin fara shiri cos they know what it means by mother to say ayi gawurtaccen biki,gashi tace tunda javeed yariga ya taba nur sune kawai zasuyi mata komi da komi hatta kayan swan amarya dan haka babu bata lokaci anty suad tahau binne haukar baqin ciki dake damunta kodan ma ta wanke wann uban kunya da kuma zubar da girmanta da tay a idanun mother da kowa.

nan kuwa tafara tattaro duk wani ilimi da basirarta na haute fashion tahau zubashi wajen tsara irin kayan da nur zata saka na ranar event dinta.


javeed da yan uwansa kuma suka dan fita a falon shida brothers dinsa maza suna dan maganarsu ta normal business stuffs hade da abunda zasuy akan hidimar atacan waje kowa da yar drink dinsa ahannunsa


akabar daga mother sai alhaj attah a babban falo inda ta hau tsillashi da tuhuma tareda nuna bacin ranta na biye ma wann shirmen da yabar suad sukayi ma yar yarinya karama

shiko bai boye mata komi daga abunda yake damunsa ba yagaya mata yadda yar uwansa suad din ta nuna masa boro boro na cewa idonta na kan dukiya tana kuma sone a dora danta kamil dan kawai suyi wasarsu da ma'adanan gwal da na diamonds na ahali

duk wani furucin da suad din tay saida ya memeta ma mother yace yagama lura ana zugata sosai dolensa ne yabi bayan su sabida ya saukaka ma ahalinsu illar abun da zaije ya dawo baison yar uwarsa na jini da suka hada uba ta dawo musu fitina azo ace itace babban enemy dinsu na ahali bayan tagama sanin sirrinsu da duk wani weakness dinsu

dolene kawai ya runtse idonsa ya nuna ma javeed baiy daidai a idon kowa ba dan ya cire ma suad wann misconception din aranta najin cewa shima bazai iya yanke hukunci wa javeed sabida ceto darajar ahalinsu ba dan shidai babban damuwarsa hadin kai da kuma kimar ahalin nasu ne.

dakyar dai mother ta gamsu da bayanansa sann tace masa itama tay bincike da jimawa kuma tasan nur matar javeed ce ta qaddara shiyasa ma ta amince da auren tun farko dan haka babu wani abunda zai faru da izinin Allah kawai su karawa suad wasu ayyukan akanta da zai rabata da lady siddika
in aiki yay mata yawa bazata tsaya jin zugi ba.

su javeed suna daga waje securty ya kawo aika cewa wai ganan kawunan hjy zubaida sunzo daurin auren simran da javeed mufasa suna main gate amma ba abarsu sun shigo ba saboda basu da invitation permit.

jin hakan yasaka khaleefa da kamil kwashewa da dariya

javeed ya hade rai kai tsaye sheik haidar shima ya hade ransa yace ace musu subar wajen kawai tin kan ya fito, sai kuma kamil din yace barsu kawai zu shigo kawai dan bakaramin so yake yaga anyi mummunan embrssing din simran din akan javeed ba dake ya jima da mata tayin kudade akan ta dawo mistress dinsa amma sai taki sam

shoda yanason ma ta bashi jikin ta ne yay disvirgining inta suna yin sex basai sunyi aure ba amma zai na bata yan kudaden kashewa, kawai shide da virgin yakeso ya fara sanin mace arayuwrsa basaida aure ba ita kuma idonta akan javeed yake haka taki tayin kamil din sam da boyayyqr mugunta aran kamil yace kawai abarsu su shigo

ana barinsu kuwa sheik haidar ya sanar ma su alhaj attah cewa ga nan fa magabatan simran sunzo neman auren javeed har gida, haba mana khaleefa ko da an furta haka sai kaji ya tuntsire da dariyar mugunta dan bai taba ganin inda iyayen mace sukazo neman auren namiji har gidan ubansa ba sai akan javeed mufasa

haka dukansu suka watse suka koma main falo dan ayi show din agabansu nan suka bar javeed dayace musu shi bazai tsoma kansa acikin wnn shirmen ba


sashensa ya wuce direct koma dan ya duba lafiyar nur dinsa daya bari tana waya da Dr surayya.

wanda tunda tagama bawa Dr surayya labarin abubuwanda ya faffaru da ita a abuja ahannun mrs haseena kusan atare sukay kukansu suka share hawayensu dan ta tausaya ma nur din sosai bana kadan ba

duk dama dakyar take magana bata boye ma nur din komi ba sosai ta fayyace mata cewa ai ba raping inta akayi ba Allura kawai aka mata meisaka symptms din ciki kuma wann duka da mrs haseena tay mata bashine sanadiyar zuban jinin datay ranar ba anxiety da depression ne ya hadu da high hormonal imbalance data samu daga side effect na alluran shiyasa taga kamar cikin ne ya zuba...

nur duk ta rude sai taji kamar gundumamen dutsi kawai aka daga mata daga kirji sai kuka kawai take tana godewa Allah da ya wanketa daga wann mumumn qaddara tun anan gidan duniya

dakyar dr surayya take fidda magana amma bai hanata dagewa wajen tausasa nur da kalamai masu sanyi ba..

ita tasaka nur ta sake samun sukuni da wani irin sanyi aranta musmn akan boye ma javeed gaskiyar labarin trauma dinta datay wanda tajima tana daukar hakan a matsayin wani babban shirme da kuskure data tafka wanda ya jawo mata fadawa cikin walakcin data sha agidan kwana biyun nan.

Dr surayya tace mata Allah shine kawai yake da ikon rufawa bawarsa asiri, bawai mutum ne yake da ikon rufawa kansa asiri ba, nan ta jawo mata wasu yan ingantattun fatawowi da hadisai dakenuni ma musulmi namiji kona mace muhimmimcin rike sirrin kansa dana iyayensa agaban miji ko matar aure inkika karanta min book batare da kinbiya ina binki 500 chat 08060712446 to pay ko mu hade acahn
[02/07, 16:14] Ladysu: Dr.tace ma nur babban kuskure ne mace ta bayyanawa mijinta wani mummunan tarihi ko sirri daya shafi zubar da kima da mutunci ko darajar iyayenta kona ahalinta wanda komin so da yardan dake tsakanin ku, komin girmansa, iliminsa, nitsuwarsa da komin wayonsa bazai hana hakan haifar da illa me girma wa auren naku ba.

dalilnta na an halicce mace da rauni wanda ya saka ma'aunin tunani da judgemnts inta kashi 99.% is base on emotional and not logical reasoning, shikuma namiji ma'aunin tunaninsa babu wani rauni sosai aciki side of judment insa is very logical not emotional shiyasa muke da bambamci sosai wajen yin uzuri saurin nuna tausayi da juriya su kuma suke da kaifin basirar warware matsalar rayuwar aure

yau dadin soyayya da amincewa kacal zai iya debar mace tace ma mijinta ai mamana tay min kaza, baba na manemin mata ne, mamana tana da zafin kishi harma tana xuwa wajen malamai bata zama da kishiya, ko bata kulawa da mu,na taso bamu jituwa sabida tana da hali kaza,ai tana warayya, ko mama tafi son mijinta akanmu, ko bata da addini ba, ko ta tsaneni, ko tana zargina akan mijinta ko akan zina..
...negative dalilai suna da mugun yawa wanda mace me ragwon azanci zata iya kawowa da zcyrta daya danfassara iyaye da shi wa mijin data aura.saidai abunda ba a alakari dashi shine, wani namijin zaijiki yay shiru, wani zai tayaki daukar mataki, wani zaiji tausayinki, wani zai nuna hakan aiba komi bane,
wani atake zai maidashi weapon nacin fuska, gori ko tozarci akanki, kusan dai kowane namiji da yadda zaiyi amfani dashi.

saidai general illan da bude sirrin iyaye da naki nakanki yakeyi aure shine ginawa da kuma haifar da sabon rashin kima, daraja, da yadda mai tsawo cikin aurenki, kai koyaya mijin kin yake inde har kin fassara mahaifinyrki ko mahaifinki tawani siga a idanunsa, its doesnt matter if he understand you or not already kina furtawa kwakwarlsa zai adana wann information snn yay processing dinsa koda bada son ransa ba sai can can wata rana, ko halama kin manta, koda kuwa kun tsufa tare akwai ranar da zaki gane cewa tuntuni fa yana auna tunaninki, darjarki da tarbiyanki, harma da wanda kike bawa yaransa da iyayensa da wayann nazari dayayi akan sirrinkan iyayenki dakika gaya masa ya rike a mind insa.

babban dalilinsa shine ai jinin iyayen naki ne ajikinki, kuma nonon wnn uwar taki da kika tonawa asiri ke yawo ajikinki kema dan haka bazai kalleki a matsayin wacce Allah ya bambamta muku hali ba, kai tsaye brain dinsa zai na dubawa dan yaga wani abu na kuskure ko rauni da zakiyi wanda zai kawosa ga ranar da zaice miki ai wann mummunar dabiar ajininku yake kuma haka zai cigaba da rikewa aransa komin kokarin da kikeyi akan aurenki bazaina gani sosai ba. shoyasa daga zarar ka budewa iyaye ko dangi asiri a idon miji bawasu kayima illa ba, makanka kawai kayi illa me zurfi, dan duk rauninka da sonka da fadin gaskiya sai wani negative impression marar kyau ya ginu aran mijinka wanda zai canza pattern din yadda zaina kallonki dashi koda bai taba fitowa fili ya furta miki ba.

its natural mace taji wann intense guilt, tsoro, tashin hankli, rikicewar tunani ,da rashin nitsuwa dake tattare da sirrikanta datake boyewa wanda azahiri fadinsu yakan zama halal ne muddin zai kawo cutarwa wa mijin kamar a misali ace da aka yima nur fyaden sai aka samu ciwo ko mahaifarta ya lalace bazata iya haihuwa ko daukar ciki ba, ko kuma takamu da wani ciwo me hadari kamar hiv tou a wann fagen ne ya zama dole ta fadawa mijinta wann sirrin.

amma muddin babu irin wann condition din, rufawa kai asiri da rufawa iyayenta asiri da kare darajarsu da kimarsu a idon miji ya zama babban dutyn akan kowace mace datake matsayin mutum me ilimin addini da kuma nisan tunani.

sosai Dr surayya ta ganar da nur cewa ba kuskure tay wajen kin bayyana ma javeed gaskiyarta ba hakan ne ma daidai tunda har tamika wa Allah komi kuma tay addua takuma yi hakuri da hukuncin da Allah ya yanke mata duk dama tay kuka taji babu dadi, an mata mummunan fahimta amma gashi nan dai Allah dakansa ya warware mata matsalarta cikin ruwan sanyi, kuma tun ba akaiga ita dakanta toni asirinta dakanta ba, wnn ya ishi mutum yasan cewa ba ayima Allah gaggawa inda kana da gaskiya toh Allah zai wanke ka dakansa.

snn tace mata karta damu da halin su anty suad akanta, dan bazaka taba cikka mutum ba saikana da tarin maqiya, saikana da wanda ka tsole musu ido komin kirkin ka, bare ma zaman aure ai bakowa bane zakace wai dolene saiya soka a dangin mijinka dolene sai kayi haquri da rayuwa.

sosai nur taji dadin wayann maganganun dan kuwa tabbas ko bakomi tasan javeed yay kkr wajen fahimtarta batare daya damu da yaji labarin ba kuma gashi komi ma ashe sharri ne ba gaskiya ba yanxu fa da ta 'bata sunan mahaifyrta a idanunsa kenan.


bayan sun kammala wayar ne ta kwanta ahnkli bisa kan gadon a rigingine idanunta dake lumshe na fidda hawayen matsanancin farin ciki da murnan datake ciki na sanin cewa duk abunda ya faru da ita abaya ya warware ya fito fili and dis explain why she is a virgin last nyt sosai yanxu kam ta fahimce hakan..

inda ta aje kantan gabaki daya haka ya jike jagwab da ruwan hawayentan bakinta sai godiya wa Allah yake furtawa tun daga kasar zuciyarta takejin wani dan uban sanyi da dadi na mamayeta kalar wanda bata tabaji ba.


tana cikin wann yanayin javeed ya bude kofar dakin ahnkli ya tsaya daga kofa yanata kallonta jin sonta na karuwa sosai acikin ransa batare da yasan dalili ba, acikin nitsuwa ya karaso wanda saida ya iso daf snn yay mata sallama wanda

85 / 112