Author : SURAYYAHMS Category : Romantic Hausa Novels
masa na'ima, da mr aqeel dukansu su ukun su samesa a daki yanxun nan..
jikinta na rawa ta amsa snn ta mike taje tasame na'ima azaune agefen nur dake kan bacci tagaya mata general na neman su hakanan suka fito atare suka kira mr aqeel sukaje dakin suka sameshi yana zaune yanata latsa wayarsa gabaki dayan su basu gane kansa ba.
yana gama latsa wayar ya dan kallesu su ukun sai ya mike tsaye ya dauki wata abu acikin envelope ya mikawa Mr aqeel yace masa yahau jirgi ynxu yaje Abuja idan ya isa zai gaya masa mezai masa acan.
witout any question mr aqeel ya karbi aikan ya fice a dakin agaggauce.
nan ya kalle su janet fuskarsa ba asake ba yace mata karta sake barin nur tazo sashen bare ta tsaya a kofar dakinsa har sai ya bata izini.
ita kuma naima ce mata yay ta tabbata ta kulamishi da ita, ta bata magani, tasaka ta taci abinci da duk sauran kulawa kar ta sake yaji labarin cewa nur tana ciwo ko wani abu na lahani ya sameta.
daga haka yay dismissing insu
janet tafita tahau saka wasu extra security restriction asashen ta inda nur bazatana samun damar shigowa cikin wajen batare da izininta ba
na'ima ma hakan ta koma kan bakin aikinta thinking of ways da zata saka nur ta samu notsuwa tana cin abinci da sauran su kamar yadda ya bata oder.
yau ko breakfast ba ayi a gidan ba tsabar yadda anty suad take exxergerting komi ga nan su simran agefe da sukejin mugun matsuwa akan komi
dan sunso ace yau yau din nan ayima nur firdaus korar kare agidan kowama ya huta dan hatsaniyar da suka tayar agidan jiyan bakaramin dadi ya musu ba..
hakanan maganan yaki karewa saima dada zafafashi sukeyi ta kasa kasa sabida zuga lady sid da hjy zubaida da simran sukey a boye dan sunsan itace kawai zatana karawa anty suad din wuta.
hakanan suka taru a falon Alhaj attah tun safe anata jiran javeed da nur su fito
javeed bai samu wani notsuwar fitowa ba har saida ya gama magana da mr aqeel da already ya turasa neman masa sultan a Abuja dan shima so yake ya gudanar da nashi tsattsauran binciken akan rayuwar nur firdaus musnmn wnda tay a abuja da bai bada hanklinsa sosai akai ba.
he kept hoping dat ba saurayintan can bane yay ma nur dinshi fyade har da ciki ba
yana idar da sallahn azhr ya shirya kansa tsaf snn ya taho sashen mahaifinsa kai tsaye dan ya nemi wata alfarma.
fuskarsa a matukar daure ya shigo sashen yanayin sallama wani wufff anty suad ta mike tsaye tanafa kallonsa da wani irin fushi da takaici dan ko kadan bataga dalilin da har yanxu ake maganan nur ba
kawai tunda gaskiya ya bayyana so take ataru a zage nur din sann a kulleta ko ma akama familynta duka snn a saketa saki uku atake snn a muzantasu.
javeed baiko gaishe ta ba jin yadda ta fara tuhumarsa tana cewa ina munafukar take and why is she still under our roof bafa zaiyu ta zauna mana a gida ba.
shareta yay saidai duk dama gaban mahaifin sa ya dosa dan ya gaishesa yanayin yadda anty suad din take diri take zafafa lamarin al'adarsu da dokokin aure ahalinsu yaso ya jawo wani hayaniyar na daban.
javeed yay shiru yana jin yadda kowani kare da doki acikin duka matayen gida suke magana akan nur firdaus kowa na fadin albarkacin bakinsa ko wani dar dar basuji acikin ransu
musmn ma hajy zubaida datake kan claiming cewa ai wann abun ba abun rufa asiri bane tunda dai mutuncin gidan gabaki daya za'a zubar.
sanin cewa javeed bacewa komi xaiyi agabansu ba yasaka alhaj attah ya dakatar da hayaniyar tareda sallamarsu harda ma lady sid ya zamo daga shi sai anty suad da javeed din dake tsaye.
kai tsaye baban nasa yahau tambayarsa dan yaji ko nur ta gaya masa wani abu game da abunda suke hayaniya akai dan shi abun ya ishesa.
javeed yay shiru for a while kafin can ya kalle mahaifinsa yace
masa a'a basuyi maganan ba tukuna, amma zai kyautu a masa adalci abashi kwana uku dan yay nashi binciken tunda dai matarsa ce
tun kafin nan alhaj attah ya amsa anty suad ta tuma tace sam bata amince ba kawai javeed yana neman wata hanya ne da zai rufawa matarsa asiri sabida baison ace yay kuskuren auren watstsiya kuma karuwa arayuwarsa
nan tafara aibanta dabiun javeed din, kamar dama wann damar take jira all her life dan tagaya masa kalar haushin dayake bata acikin kokon ranta..
she called him names like egoistic,selfish, spoilt brat who is non chalant akan dokokin su na ahali dan yaga kawai an dorashi akan dukiyarsu da komi komi nasu kuma mother hauwa tana karramasa fiyeda kowa an dauki son duniya anzuba akansa shikadai...
wasu irin manyan maganganu take furtawa tana impliyn cewa ai dama can akan hanyar nuna warayya da fifiko aka gina adalci agidan dan da danta kamil ne ya kawo mace kamar nur firdaus da yanxu an dauki mummunan mataki akansa batare da bata lokaci ba.
haka ta gama koke koke da zage zagenta tabar musu falon tare da masa barazanar cewa bazata taba xuba ido a danne gaskiyar nur firdaus agidan nan ba saidai duk abunda xai faru ya faru.
sanadiyar wann baqaqen maganganun datay yasaka bai samu wani fuska ko fahimta a wajen mahaifinsa ba.
hakanan suka rabu ya dawo sashensa da damuwa aransa dan baban nasa baice masa eh ko a'a akan batun da ya masa na bincike ba.
ata fannin nur kuwa har saida lkci yaja sosai snn ta farka da tsananin ciwon ciki sabida intense anxiety da depression daya lullumeta atake ya saukar mata da period inta dayazo ba akan lokcinsa ba.
dakyar da wahala naima ta hanata fita tareda mata bayani da kuma karya akan cewa javeed baya nan janet tace mata yaje Abuja so babu wani amfanin ta kara zuwa sashensa nemansa
iyaka da wann karyan naima ta samu hanklin nur harta zauna tana kula da ita duk dama nur taki cin komi sai kuka, intay ne ta sha kunu ko hadin madararar da suke hada mata na kayan mata dake shi baida wani yawa da kuma nauyi.
duk ta rasa meke mata dadi daga tay kuka saita dan kwanta tanamai ambaton Allah dan sosai ta fara karaya da lamarin yadda komi ke faruwa da ita, shin kuskure ne tay data tsaya yin tunani akan fears da trauma na rayuwarta? everybody has the ryt to feel scared to say a thing of his horible past traumas, to feel vulnerable with loved ones, za kaji kana tsoron rasa wani abu, and even get stucked on who to really trust, but just when she is abt to tell javeed komi sai kuma ya ruguje.
sabida karyan da naima ta mata na cewa javeed baiya nan ya saka ranar gabaki daya bata saka ran sake fitowa ba.
fannin su simran da su lady sid kuwa gabaki daya a gindin anty suad suke karewa da gulma
wann na zugata tanan wann na zugata tacan wani abun mamakin ma shine anty suad ta san kan gaskiyar maganan nur na cewa case din rape ne amma dake ta mugun tsanar nur firdaus yasaka ko kadan bata tantance maganan dake fita a bakinsu ba musmn ma na hjy zubaida dake kara cinna musu gobara a makirce tana dada bawa javeed laifin komi dayake faruwa
da yamma lis bayan sallahn magrib da isha javeed ya sake komawa ya same babansa a daki da maganan alfarman dayake nema akan nur firdaus
saidai masifa kawai alhaj attah ya masa yace masa gaskiyan suad ne he is just becoming emotionally weak akan nur firdaus
kuma yana sone kawai ya jawo masa abun magana da gori acikin danginsu shiyasama ya kasa nitsar da nur yaji maganan nan daga bakinta snn shi sam baiga amfanin yin bincike ba tunda dama waka abakin meshi ya fi dadi.
Duk masifa da bakaken maganan dayasha hakanan yay shiru baice komi ba dai ya cigaba da rokonsa akan yabashi dama amma kuma sam bai kulashi ranar ba.
washe gari sassafe ya sake dawowa still ya samu anty suad ma tazo da bori wnn karon barazana kawai take musu cewa inhar javeed bazai saki nur a koreta agidan ko akama iyayenta ba zata kai maganan nan can moroco, javeeed ya zaba ko nur ko ahalinsa. snn kuma inde soyayya zai iya rife masa ido yaqi zantar da gaskiya toh bai cancanta abarsa ya cigaba da rike duk wani dukiya da kuma affairs na mufasa organisations ba
babu wani boye boyen hassada tace saidai a bawa danta kamil ragamar rike komi tunda har mace yar karama kwaila tana iya juya kwakwalwar javeed akan ahalinsa..
nan ma tagama bayaninta har ta fita basu ce mata komi ba dan duk sunsani har da sharrin zugi da lady sid take mata kuma dama babban burinsu kenan komi na gidan ya dawo hannun danta kamil dan ya zamo itace jakadiya data ke juya ragamar komi.
duk sunsan da haka aransu amma koda javeed ya budi baki zai magana babansa ya kara rufesa da wani sabon fadar, wanda cewa kawai yake baison yaji komi game da nur firdaus, kawai yay fixing matsalar dan bazaiyu ya jawo musu abunda zai saka harya dauki dukiyar ahalinsu gabaki daya ya damka ahannun suad da danta kamil ba.
javeed duk yay banza da wnn maganan yanata rokon shide abashi kwana ukun nan sabida bazai iya sakin matarsa nur firdaus ko yahau walakantata da iyayenta hakanan kawai batare da ya fahimce komi ba, duba da yadda ha kwace kurucyrta ya aurota ya ajeta awaje daya babu waya babu kawaye babu karatu duk yahanata motsi,
toh inhar maganan ya zamo ba gaskiya bane yacutar da ita kuma yasan bazai taba sanin yadda zai yi ya gyara tsakaninsu ba gara kawai yay bincike..
bai gama magananr bama cikin fushi alhj attah ya katsesa da tsawa yana cewa tabbas ya yadda da maganan suad ynxu, kawai dai babu wani bincike, he is just attaching his weak emotions dan ya rufa ma nur asiri shiyasa kwata kwata baison yaga gaskiyar da ake nuna masa, kuma bai damu da martaban gidansu akan yarinyar nan ba, yace masa idan har bai dau kakkwarn mataki akan case din nan ba he cannot be trusted to continue to rule the mufasa organisation tunda har bazai iya daukar hukunci akan nur firdaus ba cikin fushi ya kalli idanunsa yace javeed kabani kunya..
javeed yay kusan minti uku bai dauke idonsa cikin na babansa ba dan mamaki ma yake basa da ya bar maganan anty suad ya soma rufe masa ido shima.
tun jiya da safe yake rokonsu subashi dama akan nur firdaus ta dan zauna agidan dan yay bincikensa amma koyaushe yaxo bakar magana kawai suke gaya masa masu zafi, wani tunani ya raya aransa wanda ya taho masa tare da sauke ajiyan xuciya me nauyi.
gyara tsayuwrsa yay cikin sauke muryanshi kasa kasa ya kalle baban nasa da wani irin yanayi a muryansa yace shikenan naji, i failed you, i cannot rule mufasa dan kawai ina son na bincike lamarin mata ta. and maybe ure all ryt i have been doing dis work with so much weak emotions tunda dai nine ma rabaka da matarka but no one truly cares how i am alwys pretending to be strong and okay for all of our sakes, yanxu ne nazama weak dan na nemi alfarma nay bincike akan matata? ohh how can i even neva not be, how can i rule without weak emotions, i am over bearing the burden of killing ur beloveth wife and my own mother dan haka inkunce haka ma aigaskiya ne cikin lumshe ido da budewa yace "dad abar maganan nan kawai..i wll fix it, and i am sorry for asking. da hawayen bacin rai a idonshi ya juya ya bar wajen baiko rufe mai kofarsa ba..
kirar sunansa alhaj attah yake da karfi amma ina bai kara juyowa ba ya tafi bai kuma kara dawowa sashen ba har dare ya rufa duk hankalin alhaj attah sai ya kuma tashi sosai.
fannin anty suad kuwa koda ta koma yau wani sabuwar zugin lady sid ta sako mata akan cewa kawai ta kai karar javeed wajen mother dan alhj attah
bazai taba kin request din javeed ba,.
ce mata suke inhar aka cigaba da barin nur firdaus agidan gaskiya ba ayi wa sauran mutanen ahalinsu adalci ba.
washe gari javeed na zaune a dakinsa suna waya da mr aqeel da sassafe babansa yazo..
suna hade ido ya katse wayar ya hade ransa baiko kallesa ba kawai ya gaishesa a dan tsime snn ya mike tsaye tareda bashi wajen zama yanamai tambayarsa ko lafya yazo harnan bai aiko an kirasa ba?...
cikin sauke ajiyan zuciya alhaj yace jiya kabar min kofata a bude so i figure it was an invite.
babu yabo babu fallasa javeed yace hmm toh kay hakuri i will close it next time
kallonsa alhaj attah yay da wani irin emotions yace javeed taurin kan nan ya isa haka mana!! banajin dadi idan kana furta min ire iren wayannan maganganun mezai kawo maganar mutuwar mahaifiyarka kuma, cmn son..u knw i will do anything for u amma meyasa kai bazaka iya aje son ranka kodan ka cire ni a kunya ba javeed.
muryan javeed kasa kasa yace " nasani, i am soo selfish haka duk kuke gani..shikenan nayi kuskure.. kayi hakuri for making this situation hard on you.
mikewa alhaj attah ya kai bakin kofa snn ya tsaya batare da ya kallesa ba yadan cizza labba snn yace "u can have ur 3 days amma fa kasani daga zarar kwana ukun dana baka ya cika...
cikin katsesa javeed yace "zan saketa, and i will leave her alone not bcos i dont love her uptill now, but for ur sake. ina so ka sani babu wani abu mafi muhimmnci agareni a duniyan nan da ya wucemin kai.. baba ure the only one i can and i will secrifice my love for karka damu...
hawaye ya cika idon alhaj attah amma bai juyo ba kawai ya kada kansa cikin jin nauyin sa ya fita da sanyin jiki.
yana isa dakinsa yadau maganinsa ya sha snn ya bude wani drawer ya fito da katon frame na hoton matarsa ya rungume hoton sosai cikin sauke numfashi har ya sulale ya koma kan capert ya zauna dan babu wani abu me makurar masa wuya face yaga shida kansa ya jefa javeed acikin wani mayuwacin hali
nevertheless yaji tsananin farinciki da alfahari aransa da javeed ya furta masa cewa zai iya haqura da soyayyar dayake ma nur firdaus dan sabida shi..
altho it breaks him to know dat inhakan ya faru javeed will neva evar be the same person dan yasan javeed bai taba son kowa kamar nur ba
yana cikin wann yanayin maraicin sai ga sallamar hajya zubaida wanda bai amsa ba har saida ya maida hoton matarsa mazauninsa snn ya bata izini ta shigo
wani kalar makirci tazo dashi, tanamai sauke murya kasa tana marairacewa tana tabbatar masa da cewa komin yaya ne she is just being a mother to javeed, shiyasa ta tono da gaskiya ma su anty suad dan tagama lura simran bazata taba tonawa javeed asiri ba saboda tanason javeed din sosai.
hakanan ta zauna ta dinga masa wasu makirtaccun bayanai akan son da simran takey ma javeed wanda duk ba ji yake ba shi tunaninsa kawai yadda dansa zai dawo wani abu daban ne bayan ya rasa nur firdaus.
bayan komi ya lafa mishi da yamma ya sanar da anty suad cewa yabawa javeed daman yay bincike amma javeed ya yanke hukunci cewa daga zarar bai samu komi ba zai sake nur firdaus kuma zatabar gidan.
hakan sosai ya mata dadi, dan lady sid da simran sun bata assurance cewa javeed bazai taba samun wani gaskiya da yawuce wann ba
wanda ya jawo tun aranar anty suad ta fara suggesting cewa daga javeed ya raba kansa da nur firdaus din kawai babu wani bata lkci aranar za'a aura masa aure da simran danma kar aje ahada wani shaidar makirci abayan idonsu snn akawo musu zancen kara dawowa musu da ita...
tunda aka furta wann maganan simran ta haukace da murna da farinciki agidan harma ta kasa boyewa ta kuma kasa dannewa
she just can belive dat in 3 days time zata amsa sunan matar javeed mufasa and finally her longest awaited dream of 35 years is now coming to pass.
bakaramin murna a daki sukayi yau da ita da hajya zubaida ba
[11/06, 16:31] BLUE💙: Arewabooks@surayyahms
nur bata san duk wayannan abubuwan da ke faruwa ba
sai washe gari da sassafe da anty suad ta aika akirawota
gabanta na tsananin bugawa ta saka hijabinta taho..
wasu kalar tsauraran dokoki ta saka mata na cewa dolene ta karasa dutynta na inlaw a gidan bawai tana zama a daki ba dolene tazo tay musu gaisuwa da sauran su snn she made it clear to her cewa in 3 days time zata bar musu gidansu but after they make her life soo miserable untill she regret ever messing with the mufasas.
hakanan nur ta gama jin duk wani zagin da zasu mata batace musu uffan ba kuma batayi kuka agabansu ba suna gamawa ta juya ta koma cikin sashenta ta cigaba da mika kukan ta wa Allah da tunanin cewa javeed baya gidan ne shiyasa tajishi shiru
dan tsabar son su walakanta nur yasaka suke aikowa wai ta fito tay inspecting musu family dinner bata jin dadin jikinta amma hakanan taje main kitchen ta bada oder akay komi a tsanake
bayan isha tun lkci bai gama yi ba anty suad taje har dakin alhaj attah tace lallai saiya saka javeed ya fito cin abinci tunda ai sun bashi babban dama shima dolene kawai ya sauke kansa yana musu biyayya agidan.
baice mata komi ba ya kira javeed din 8pm kowa ya hallara akan main dinning for the dinner
nur ta saka abaya gabanta bakaramin faduwa yay dataga javeed ya fito ba amma dataga bai ko kalleta ba sai ta sauke kanta kasa har ta zauna akusa dashi
the table was so quiet nur taki ta daga idonta duk rawa rawan jiki da motsin ido da simran takeyi akansu bata daga ido ta kalleta ba.
ana gama serving dinsu kamar an kunna generator su anty suad da hajy zuby