Chapter 69 Reading NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt Arewa Novels

NUR FIRDAUS BOOK 2 HAUSA NOVELS COMPLETE BY SURAYYAHMS.txt

Author :  SURAYYAHMS Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   69 / 112

204K to 207K   out of 335.4K words

ya amsata mata yanamai kare fayyace mata physical and spritual dangers din dake cikin harka da nagaza which is the main reason da javeed yaki gaya mata directly yaki kuma ya sakata acikin case din gabaki daya

yace mata is totally razia s choice to be part of this, javeed has even offer her money taki karba but she deemed to use the opputunity leave her parent and chase her dreams and careers, ....yace mata wallh babu hannun javeed acikin tafyr razia, shidai kawai dama itace damuwarsa kuma ma is just to shade his bride's name behind the scene dats all kuma javeed yaso yagaya mata bayan auren sum but dats was the day she insulted his mother and chase him away while yana kan shirin mission din nan..

hakanan sultan ya dinga mata bayani with all the truth but not excat, dole ne dai yasaka all the loops nd holes all the gaslighng nd emotional manipulation har saida yasakata ta gane cewa javeed dinsa was just trying to protect her againt this very ppll da suka rike rayuwarsa yanxu suke azbtar dashi


Duk sai taji ta rude jikin ta yay sanyi gabobinta duk sun sassare dan komi dawowa mata brain inta yake kamar ruwa and is making perfect
sense musmmn wasu abubwn da razia ta dinga yi mata alkcn shirin auren yanxu suke zame mata soo clear ashe ma razzy tasan soyayyarta da javeed tuntuni kuma tasan duk abunda ke faruwa

sulalewa tay kan kujerar tanata kuka kawai tace ma sultan din ya kyaleta she want to be alone to be able to process all this information on her mind..


baice komi ba saida ya share hawayensa zai fita kafin ya kalleta yace mata dama javeed yace ya gayamata cewa koda bai rayu ba she shud knw dat he truly love her very much

kallonshi take idonta na fidda hawaye har ya fice batace mai komi ba yana fita ta fashe da kuka sosai



daga can dakin kuwa dr ruqayya tana cikin magana akan javeed wayar alhaj attah ne ya katsesu yana daukawa kuwa yaji muryan anty suad shiru yay yana dan saurararta yana sauke wayar da wani irin sauri ya juya sai ga sultan nan ya riko hannun sultan din agaggauce yace masa yaje ya kira nur suje kasa falonsa da sauri

snn yace ma dr ruqayya tacigaba da bada javeed jinin kawai suna da enuf of it a blood bank dinsu karta damu..


nur nakan kuka sultan yaxo yace mata tazo yanxun nan is sumting vry urgent abt javeed

tanajin sunan javeed batasan sanda tamike tsaye tafara binsa ba kusan atare suka isa falon alhaj attah taga daga su sai anty suad sai alhaj su hudu kacal an kunna wani katon shared screen share location tagani morocco..

ga mr haidar Ali sai wata tsohuwa fara sol da wani irin dark grey eye ball kamar na kuliya gata kyakkwan kamr ita tay kanta tasaka fararan kaya daga sama har kasa ganin duka manyan gidan sun rusuna sun gaisheta yasaka itama da rusuna har kasa ta gaisheta matar tasassaka musu albarka..

matar tadan kalle fuskar nur kadan tay murmushi snn tafara musu bayani dan acewarta basu da isashen lokcin jira

bayani tahau musu cewa matsalar javeed yana cikin kabarin mijin astah nagaza
cikin daren nan suje subude kabarin su kunce kurwan javeed su rabashi da wann bakaken aljanun sabida cakka mai wukar datayne ta hadashi jini da jini under demonic oath da bakaken aljanu snn zasu zuke jininsa ne har sai sun kashesa a matsayin revenge din familynta dayay wiping ya shafesu a doron kasa,.

itama kanta tace musu dakyar ta samu wann bayanin awajen ancestaral spirit dinsu saida tay kwanaki tana aiki ajeji snn suka gane komi.

komi saida ta gaya musu yadda zasuyi shi dalla dalla in sunje kabarin tareda jadadda musu cewa dolene suje da nur firdaus tunda anbata labarin komi daya faru a wann satin dolene zasu bukaceta wajen kunce javeed sabida aikine wanda baida yawa amma yana da mugun hatsari wanda kwararren me haddar ayoyin qur'ani ne zai iya snn suje da makamai duk abunda ya fita a kabarin su kashesa.

kafin su gama wayar ta sakama nur albarka tace mata tay kokari sosai and she will soon welcome her in their mufasa home in morocco.

da sanyin murya nur tay godiya batare da tasan cewa wnm din itace mother hauwar da ake magana akai ba.

Duk dama anty suad bawai har ranta taso haduwar nur da mother in a good way ba amma dake zancen ceto ran javeed ake sai bata nuna komi a fili ba


they have only 1hr to do everything, sultan, nur da alhaj attah ne zasu tafi kabarin ynxun nan babu bata lkci..

15 minutes kawai ya basu suje su shirya su samesa agaban helicopter...snn yay warning din anty suad karta gaya ma kowa komi har sai sun dawo.


sai yau nur ta koma sashenta a wann lkcin tana shiga na'ima tamike tsaye da mamakin ganinta nur tace ta zabar mata kayan da zata iya shiga jeji dashi dan yadda akayi describing wajen is not dat freindly

nan da nan na'ima kuwa ta kawo mata all black cooperate dats comfortble and perfect for the action

Rigar ciki karami ne amma is thick yana da long chester coat me buttons daya zarce idon gwiwarta da wandonsa dogo ta saka bakin socks da flat booth ta killace kanta da karamin bakin hijab ..

tana fita ta samu sultan ya saka wani irin kananan kaya dark colours da leather jacket he is loaded with guns ya dauko wani katon dagger na tonon kabari ya bawa mr aqeel aka kai jirgi shiya bawa nur black face cap da face mask da gloves da gun yace tasa gun din a aljihunta..

kafin nan alhaj attah ya fito shima sanye da wasu irin comfortable kananan kaya ajikinshi suma bakake he is well loaded too..

17 minutes kwata kwata ya musu suka shiga jirgin, sultan ne yake jansu har suka kai jejin da kabarin yake.......
[02/06, 21:19] BLUE💙: EPISODE 77
AREWABOOKS@SURAYYAHMS.

Suna isowa jejin tun basu sauka izuwa kasa ba nur firdaus taga wajen gabaki daya ya kaure da matsanancin duhu da wani irin sanyin ruwan teku kai kamar ba acikin garin lagos suke ba dan jejin is far far away daga cikin gari almost kusa suke da atlantic ocean acikin wani karamin waje dats filled with terracotas headstones ga tsofin makabarta dasuka riga suka burme suka dawo kamr kogon tsafi wanda basai an gaya maka ba sun jima wajen shekara da shekaru. sacred cemetry ne na early settlers wanda ake rumour cewa spirits din kabarukan yana tashi kowani dare.

akan wani katon fili kusa da ruwan tekun suka aje jirgin nur ta kankame jikinta tana tafiyarta ahankli.

atsakiyarsu take amma duk da haka bakaramin tsoro takeji ba dan hatta sautin iskan dake kadawa awajen is wildly scary
ga karfi ka kara ga sanyi sai yanxu taga asalin amfanin face mask gloves da cap din da sultan ya bata dan har tsikar jikinta tashi yakeyi.


sultan dake gefenta yana rike da jakar daya saka dagger dinsa aciki shikam ko ajikinsa kamar baisan me ake kira tsoro ba, alhaj attah ne ya musu jagora har suka kai wani dullumin hanya acikin jejin snn yace musu su tsaya daga nan

suna tsaye ya ciro wata ligher daga aljihunsa ya kunna hasken asalin wuta yay addua snn ya kutso kanshi cikin hanyar dayake gaba wanda tun suna hango haskensa har ya bace musu battt aciki.

sun fi minti biyar atsaye daga ita sai sultan basuce ma junansu komi dan rawa jikinta yakeyi ahnkli, Duk tama kasa daga idonta sama bare takalle tarin gumakan dake jere ajejin cikin wann uban duhu.

karar wayar sultan ne ya fargan da ita arazane tadaga ido tadan kallesa taga yana amsawa yana saukewa da sanyin murya yace "Amaryanmu is time to go in are u ready?

cikin hadiyar yawun dayazo mata abazata ta gyada kai sn tace uhum..

dan kauda kai yay ahnkli yace okay"..amma..are u sure you wanna do this? ta sake kallonsa yace "kigaya min karki damu is natural to feel scared inkina jin tsoro u can back down..

dan shiruu tay kafin nan ta shanye bugun zuciyar datakeji ahnkli tace "i will do anything to save my husband, kaide inde kanajin tsoro sai ka gayamin i can replace you.

tana rufe bakinta baisan sanda yay dariya ba, girarsa nasama a dage cikin kyabe baki yana dariyar yace hmm okay i am begining to understand why javeed is crazy abt you now lets go and finish this mrs mufasa..

dan karamin murmushi tay batace mai komi ba tafara gaba yay sauri ya jera da ita har suka isa inda alhaj attah yake tsaye

suna isowa ya kallesu hanklinsa adan tashe yace "muyi sauri sauri mubar nan wajen nan babu kyau.. sultan yace yes sir..wani hanya suka bi Alhaj attah ke nunawa ma nur inda zata saka kafarta sabida karta fadi akasa ko ta taka wani burmammen kabarin bare ajata ciki

ahankl har suka kawo kan wani kabari da akayishi awani gindin bishiya snn aka masa katon slab na cement aka rufe da chains da padlock.

suna tsayawa ajikin kabarin ya kalle sultan batare da yace mai komi ba ya fahimce meyake nufi nan ya bude jakarsa ya fito da dagger alhaj attah ya karba ya ciro wani abu daga aljihunsa kamar ruwa ya zuba ajikin daggern ya masa wanka dashi shiya fara bugawa akan cementin bugu daya ta fashe, kafin nan sultan ya amsa tareda cire jacket dinsa ya daura a kwankwasonsa ya dinga buga chain din saida yay raga raga da dashi da mugun makullin da aka rufe slab din da shi snn suka cireshi da kyar suka matsar gefe.

wani irin duhune acikin kabarin lkcin dakyar nur take sauke numfashi tsabar tsoro

alhaj attah ya kunna hasken wutar lighter sa, ya leka kadan yaga sauran kwarangal ne kawai aciki da wani tumin abubuwan da aka danne da hannun gwarangal din...

hannu ya musu suka karaso suka leka sugani nur firdaus ce ta fara hango wani abu kamar babyn robber ayayinda ake haskawa da wani irin karfin zuciya nur ta lumshe idonta tay tsamm tayiyyi addua snn ta tsuguna agaban kabarin takai hannun ta dake rawa rawa ta zaro abun waje da sauri tasake ya fadi akasa ganin mutum mutumi ne da akay da laka anyiyyi rubutun tsafi ajikinsa an daure shi tammm da wani irin jan zare tundaga kai har hannu kafa inda koda yana raye bazai taba iya bude ido ko yay motsi ba..

cikin karkada kai Alhaj attah yasaka hannu ya dauka yafara karanta musu rubutun tsafin da aka rubuta da sunan javeed da irin manyan baqaqen aljanun da aka hada jininsa da su..

yana kkrin mikawa nur idol din danta fata kuncewa sukaji wani abu ya fado dum daga samar bishiyan suna juyawa sukaga wani irin murjejen maciji ya tunkarosu

nur harta firgita zata jaa baya alhaj attah ya tarota ya dan zare mata ido yace mata karta jo tsoron komi tayi focusing akan warware idol din karta damu da komi da zaina faruwa...

dakyar ta iya aminta da hakan har ta daga ido akan macicin daya wani mike tsaye da kansa guda biyu ayayin da mazan suka tunkare macijin subiyu

da saurin cikin kkrin dawowa da hanklnta kan idol din hannunta na rawa tafara kirar sallah kamar yadda mother tace mata tay, dama saita kira sallah kamar sau uku snn ta kama bakin kullin zare ta kuncesa ta hannun dama irin anticlockwise din nan sabida su shaidanu da hannun hagu suke kulle sharri

kowani jan zaren kuma ta tabbata ayatul kursiyun bai kufce abakinta ba

with the spiritual snake and human fights dake gudana ata bayanta dakyar ta nitsu ta kira sallahn snn ta kama bakin zaren tafara sinceshi ta dama tanayi tana karanto ayatul kursiyu duk rawan da jikinta yake kasa rufe ido tay sabida ayayinda take karantawa duk wann rubutun jikin idol din suna bacewa ga wani irin dumi dake tasowa acikin kabarin wanda kafin kace wani abu har tay zufa hakanan ta gama warwarewa tass...

hannuta na rawa ta mike tsaye da zaren da idol din a hannunta tanata karanto dayan ayoyin dake cikin suratul baqara da mother tace mata ta karanta
tanakan karantawa ne taga su alhaj attah sun dawo wajenta da kawukan majizan, acikin kabarin suka zuba ko karasa kai karshen aya bata kai ba idol din yawani tarwaste a hannunta ya dawo garin gasa..

da zaren hannunta da kasar alhaj yace mata duk ta sakasu acikin kabarin tana sawa yace musu suja baya

daga cikin jakar sultan suka fidda kwalban fetur ya tuntuda acikin kabarin lkcin har ya kunna wata taba da lighersa ya zukka tabar dkyau tay wuta snn ya jefa acikin kabarin sai boom ta kama da wani irin wuta...

wani irin ihu sukaji na tashi akabarin duk suka ja baya alhaj attah kam ko gizau yana tsaye jin muryoyo sunfi dari da hamsin mata da maza da yara
dukkanin decendant din nagaza da sauran kurwowin da Astah take daukowa tana possesing dinsu sune suke konewa aciki kurmus.

nur na tsaye a kangare batasan ma sultan yabar gefenta ba saida tagansa ya dawo da sauran jikin macijin da suka kashen ya jefasa wutar shima...


har saida ihun ya kare tass snn suka dauki slab din suka rufe kirif within 7 minutes suka fito daga jejin suka kama hanyar gida wanda tunda suka shiga jirgin nur ta kasa gane kanta dan wani irin zazzabi ne ya rufeta jingina kanta akan chair tay shiru tanajin wayar da alhaj attah yakeyi da mother hauwa

ita take kara bashi tabbacin cewa the war is now over saura suyi abu na karshe nur batadaiji me suka fada ba har suka iso gida.

lokacin wajajen goma da rabi na dare ake nema suna kaiwa ciki nur firdaus bata kula da surutun da anty suad ta tarbesu da shi na cewa jinin javeed ya tsaya har yayi motsi ba nan tawuce dakinta straight ko amsa gaisuwar na'ima batay ba ta cire kayan jikinta tashiga bathrum tay wanka kafin nan hanklinta ya dawo jikinta tukuna

nn ta fito ta sha maganin zazzabi tasaka simple morocan casual sleep gown me laushi da na'ima tacire matashi yana da tsayi har kasa da kauri snn yana da hularsa dark green colour ta saka dogon hijabi akai snn ta dawo dakin da javeed yake dan tagane ma idonta me ake ciki.


nan ta samu babu kowa a dakin sai su ukun, Dr ruqayya da dayan home doctor din suna can sama dayan dakin suna dudduba abubuwa a file din javeed din dan tunda jinin ya tsaya javeed ya fara motsi suka shiga lab suka fara yan gudanar da wasu kananan bincike.

anty suad nur tagani tsugune wijiga wujiga tana daddaka wani ganye gashi nan green colour a ido amma koda take dakawa sai yabi ya dawo purple


tace bayan tafiyarsu jeji ne danta kamil ya kawo mata aikan ganyen agurguje ya juya, wai healing and blood cleansing portion ne daga mother hauwan shima wanda shine final jinyar da za'a ma javeed na wanke jini da warkaswa.

sauri sauri take danta gama dakar tun kafin nur firdaus ta dawo cikin dakin dan tanaso ace mother hauwa tasan itace tazuba ma javeed ruwan maganin warakar nan akan ciwonsan sabida tasamu abun burga tareda masa tuni ko gori msmn inya fara mata rashin mutunci ko rashin kunya akan kudi amma inaa saitaga ga nur din tadawo dakin garau kuma abazata.

shigowar nur yasaka annurin dake kan fuskarta ya wani dauke caakk aikuwa tana gama dakawa alhaj attah ya saka hannu yakwashe nikakken ganyen duka ya zuba a kwarya ya gauraya ruwan ya dawo purple sosai snn ya mika ma nur firdaus a amtsayin wacce tasha wahala da jinya sosai

yace tay adduar samun lafiya da sunan Allah snn ta zuba ma javeed akan ciwon dake bayansa izuwa kan kwarzinin..

da sanyin jiki nur ta karba tay adduointa masu rai da lafya tana rokon a'sshifa daga ubangiji mai tsarki.

tana gamawa da shi da sultan suka juya mata javeed din snn tasaka hannu ta debo ruwan ta shafa masa a duka raunin dake bayansa na kwarzanin ta jikasu sosai sann ta juye ruwan acikin wajen ckkin wukan carefully da addua abakinta..

anty suad ta nade hannu abaya da turmusasshen fuska sai wani irin dan uban hararar nur din takeyi da wani irin takaici dake cinta arai tana jin mugun tsanar nur sabo na dawo mata ranta ayayinda kowa hanklnsa yake wani waje basusan ma halinda take ciki ba ..


bayan nur tagama ta saukar da kwaryan direct tanufi bathrum dashi dan ta wanke wanda tana barin wajen kuwa javeed ya wani irin firgita kamar zai tashi tsaye yana dan juya bayansa kuwa wani katon gudan jini ya bulloko bulll daga bayansan kamar hanta ya zame kasa yana motsi wasuk wusuk shikadansa da alamar yana neman hanyar guduwa.

a mugun tsorace anty suad ta wani rungumi bango tana kan furta inalillahi wa inna ilaihi
rajiun alhaj attah ya rike javeed din dake numfashi me karfi duk dama idonsa a rufe yake tam

ahankli ya maidashi kan gadon
yana ajeshi wani katon tsuntsu ya fansalo daga cikin jinin yana fuka fuka da wings dinsa zai tashi sama kafinsu hankara sai tau tau tau sultan yaciro gun ya daukesa da harbi har sau uku tsuntsun yadanna ihu da muryan mace snn ya fado akasa tare da narkewa zuwa yankakken jini..

amugun tsorace nur ta fito daga bayin kusan a rude taga jikin anty suad na rawa rawa tanata salati ga jini a kasa

lighter sultan ya fitar a aljihunsa ya danna akan wani abu kmr kyalle snn ya jefa acikin jinin wuta ya kamaci bal bal bal yana ci kamar na hauka wani dan uban ihun mace sukaji natashi aciki zaka rantse da Allah inka shigo zaka ganta ido da ido ana konata..

gabaki daya su dr ruqayya da likita da suke shirin tafiya gida saida sukazo dakin a rikice dan suga meke faruwa dan harta lady sid ma dake can can kasa saida taji karar ihun abayan kujera taje taboye kanta tanata salati sabida kara matar takey bana wasa ba duk gidan saida ya dauka da ihun

...haka workers suka fito wujiga wujiga ana ta mamakin wnn ihun har saida wutar ya mutu kurmuss sann akaji sauki...

Janet ce aka saka ta kwashe burbushin tokar jinin tay waje dashi snn tagyara wajen yay fess alhaj

69 / 112